← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 92

Sashe 15

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta ce "Wow ngd momcy a shirye nake yanzu ma mu fara" Daga yasin suka fara Dan karatun ya tafi yanda suke so. Washegari a tare sukaje suka bud'e account Inda ita Chuchu rakiya ce kawai tayi musu. Tun daga ranar Zarah ta zama Malamar Chuchu kullum rabin shafi take Kara mata kuma sosai take fahimta idan ta bata hadda sai ta d'ora mata wani shakuwa Ce da abokantaka ta k'ara shiga tsakaninsu ta musamman hatta lecture din da bata ganeba wajen Zarah take zaunawa tayi mata bayani" Sannan yanzu Chuchu ta nutsu ta koyi wasu daga dabi'un Zarah yanzu itama hijab take sanyawa dukda ba Koda yaushe ba da wasu kide kide duk ta rage ji <Kd> Zaune yake a garden d'in gidansa ya na shakar daddad'an iskan dake kadawa cike da ni'ima. lilo din da yake kai ya na jujjuyasa har wani lumshe ido yake zazzak'ar muryarta Take dawo masa a kwalwa hatta karatun da yaji tanayi yaji ya na masa gizau ya rasa ya akayi ba tunda yaji muryar mai karatun nan take dawo masa ba a kwalwa Tsaki ya ja a ransa tare da saurin barin tunanin da yake. Ya na nan zaune Jabir yazo yayi mamakin yau yanda fuskar abokin nasa a warware "Zaunawa yayi Inda suka shiga d'an hirar Kasuwancinsu" "MD ne ya ce " Ina son a shiryamun tafiya America gobe "okay Kai d'aya za ashirya maka ko tare da Amera " Sai sannan MD ya tuna da Amira tsaki yaja saboda haushinta da yakeji tunda ta tafi gidansu bata leko ba ya ce " "Ni d'aya zaka shiryamun ta na gidansu" da mamaki jaber ya ce. "Wai kana nufin tun sanda ta tafi bata dawo ba kusan two weeks lallai Abokina ka na hakuri wlh wai meyasa ba zaka bi shawarar Ammy ba akan ka k'ara Aure Kaga dai na farko Auren nan naka da Amera shekara Tara kenan bata tab'a d'ora girki ba da niyyar wai ta girkawa mijinta abinci ba Sannan ita ba haihuwa ta tab'ayi ba bare ka ce zaka zauna da ita Dan d'iyanta sanin kanka ne kunje Asibiti yafi sau nawa ance matsalar daga gareta ne dukda kana boye mata why zaka zauna mace d'aya ta dinga baka wahala tunda ka Aure ta Banbancinka da gwouro Kad'an ne kana da kudi da komai da zaka mori rayuwarka da su MD kayi tunani" "Nauyayyar Ajiyar zuciya MD ya sauke ya ce. " bazaka gane bane Jabir bazan tab'a yiwa Amera kishiya ba Dan bata haihuwa da misalin ace nine bana haihuwar itama haka zata zauna dani sannan har yanzu banga wace macen da zance wai ina da ra ayin aura ba" Numfasawa yayi saboda doguwar magana da bai saba ba sannan ya ce . "Amera na da kishi sosai bazata iya zama da kishiya ba sannan ina son matata bazanso abunda zai b'ata mata rai ba hasalima ni a tsarin rayuwata ban tsara auran macen da ta wuce d'aya ba mace d'aya nake da ra'ayin zama da ita kuma Babu saki a tsari na karma ka k'ara zomun da irin wannan maganar" "Shidai Jabir mamaki yaki barin fuskarsa zai d'aga baki yayi magana MD ya d'aga masa hannu dage kafada yayi tare da tashi Dan takaicin abokin nashi ya zauna mace d'aya na wahalsheshi. Washe gari MD ya bar k'asar Bayan Yaje yayiwa Ammynsa bankwana ya wuce america. Amera ko jin shiru mijin nata bai kirataba saida ta gama shiriritarta da yawonta iyayenta ko y'an komai kayi daidai ne cikinsu ba Wanda zaice shirya ki koma gidan mijinki. kiranshi tayi a waya taji layinshi na k'asar baya shiga Ta na kiran na America taga ya shiga amma baya d'auka sai sannan ta gane ya tafi america kenan . Aiko cikin rana tsaka ta d'auko akwatin kayanta cikin K'ananan kayan da ke jikinta ta d'ora mayafi tare da fitowa cikin Sauri iyayen da ke palour duk kallonta sukayi dadynta ya ce " " ina zuwa da tsakar ranar nan my merah"Tana Sauri ta bar palourn ya ce "Dad America na tafi gidan mijina bye saimun dawo " . ta na gama fad'ar haka tabar palour ta na fita ta kwalawa driver kira cikin Masifa da bala i ta rufeshi da fada akan zai bata mata lokaci shidai hakuri ya dinga bata Dan tun tana gidan ba mutunci garetaba ka tab'ata yanzu kayi ta aikinka Kai tsaye Airport ya wuce da ita. Koda ta isa America sosai Tasha fama kafin ta shawo kan mijin nata Dan ya nuna mata b'acin ranshi a fili kuma yayi zuciya da jikinta sosai hakan ya dinga damun Amera saida kyal ta samu ta na kuka ya hakura Dan tasan logar mijin nata ba abunda ya tsana sama da kukan mace . ranar dai amera ta d'an daure ba raki ba komai har Dan kanshi ya rabu da ita ya rasa wani irin mutum ne shi shekara Tara da Aure amma har yanzu baitab'a sanin gamsuwar da maza kecewa sunayi ba a tattare da matan su. <Zaria> Karatun su Zarah sosai yake gudu Dan yanzu haka harsun fara exam sosai suka maida hankalinsu ga karatunsu Masha Allah sun gama Exams lafiya sai kuma jiran result Inda kowa ya tafi gidansu dominyi Hutu dazasu rabu su Ukku saida sukaji ba dadi Chuchu hada hawaye A haka dai suka rabu akan zasu dinga waya Bayan sunyi musayar number" Chuchu tunda ta koma sosai Ammy taji dad'in irin shigar data ganta da ita ta hijab sosai taji dad'in sauyawar dabi'un na y'artata Wanda tun farko tasan sakacinta ne . Tunda Chuchu tazo bata da labari sai na Zarah nan Tabawa Ammy labarin karatun da Zarah ke koya mata yanzu har sunyi hizif Talatin sosai Ammy tayi murnar Haduwar y'artata da mutanen kwarai Itama har cikin ranta taji wannan zarar ta kwanta mata a rai sanyawa tayi ta kira mata ita Aiko cikin Sauri Chuchu ta kira mata ita Zarah na d'auka cikin d'oki Chuchu ta ce. "Momcy ga Ammy na zakuyi magana" ta fad'a ta na bawa Ammy wayar ". cikin nutsuwa Zarah ta gaishe da Ammy'inda Ammy ta amsa mata cikin Fara'a tare da yi mata Godiya akan Karatun da take koyawa Chuchu" cewa tayi" ba komai Ammy Ai anzama d'aya "sosai Ammy taji Zarah ta kwanta a ranta Dukda bata ganta a fili ba Amma a d'abi'unta da yanayin yanda taji muryarta sai taji ta na sha'awar Had'a zuri'a da ita a ranta ta ce " "inama ina da wani d'an da zai sota Bayan MD da na had'asu da ita Dan tasan MD kam yayi nisa ta ma hakura da masa maganar Karin Aure Dan tasan ba yi ba zaiyi. A haka har lokacin hutunsu ya k'are suka koma makaranta sai farincikin ganin juna suke nan aka d'ora daga Inda aka tsaya har suka cinye second semister Bayan sun koma wani hutun suna dawowa suka shiga aji biyu a lokacin ne kuma Hafiz zai tafi karo karatu England ranar da yazo mata bankwana school duk yayi sanyi Kallonshi tayi ta ce . "ya Hafiz naga duk kayi sanyi" Dagowa yayi tare da kallonta ya ce"kawai tafiyar nan da zanyi sainakejin gabana na fad'uwa kamar bazan dawo na taddaki ba sai nakejin kamar wani Abu zai shiga tsakaninmu ko wani zai raba mu Wanda bazan tab'a iya jurewa hakan ba" "Cikin tausasa murya Zarah ta ce " ka daina wannan tunanin ya Hafiz babu Wanda ya isa ya shiga tsakaninmu kaid'in ka zamemun wani bangare na jikina kayimun abunda ba kowa yayimun a rayuwa ba ka tsayemun a karatu na ni d'in y'ar halak ce ba butulu ba ya Hafiz bazan tab'a butulce maka ba insha Allahu zaka dawo muyi auranmu ta fad'a ta na rufe fuska" Sai sannan Hafiz ya sauke ajiyar zuciya Tare da sakin rai sunjima suna Hira kafin yayi mata bankwana cike da kewar juna suka rabu " Koda ta koma hostel duk tayi sanyi Samun Chuchu tayi ta na cika ta na batsewa tare da Harararta. "d'an murmushi Zarah tayi ta ce " yau kuma wa ya tab'o mana chuchun yaya" tana cigaba da turo baki ta ce "Ke ce mana momcy" wara idanu tayi ta ce. "Ni kuma to me nayi" Wancen mutumin mana da kika tsaya dashi kwata_kwata ba class d'inki bane yanzu asmy ke Cemun wai dashi aka sanya miki Aure kinji yanda Naji wlh kwata_kwata bakuyi match ba momcy ke Matar manya ce Wlh Harna fara kishi Dan da yaya na kika dace ba wancen bak'in ba.... _07026166536_ *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo*_ *AUREN WATA TARA* ```MALLAKAR``` *Hajara L Sadeq* ............*19 & 20* "Bata fuska Zarah tayi Jin shirmen da Chuchu take Dan a shirme ta dauki maganar wata maganar ta kawo musu Dan son barin zancen. Tunda Hafiz ya tafi kullum cikin waya suke da Zarah tare da video call Yau Zarah ta tashi da ciwon ciki hakan ya nuna mata zuwan perioud dintane sosai take murkashi akan Gado Dan su Asmy suna lecture Duk ta had'a zufa a haka har suka dawo suka sameta sosai suka shiga tashin hankali musamman Chuchu da batasan da larurar Zarah ba Dan kwanakin baya ciwon ya d'an lafa. Da damuwa ta ce " subhanallahi me yake damunki momcy"Asmy ce dake mikar da Zarah ta ce perioud dintane yazo mu maza mu kaita Asibiti bari na taro napep " Da mamaki Chuchu ta ce " Daman haka yake yi mata? "Eh haka take Asmy ta fad'a tare da saurin fita Dan ta taro napep inda Chuchu ta shiga Jerawa Zarah Sannu. Asibiti mafi kusa suka nufa Inda Asmy tayiwa Dr d'in bayanin
Chapter 15 · 0% Book details