Sashe 53
Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
isa bata samesa a gidan Ba dak'yal ta samu tayi sallah ta kwanta Dan wata gaji ya a tattare da ita A sallayar da tayi salla a palour ta kwanta bacci ya d'auketa sai wajen 5pm MD ya shigo gidan dawowarsa daga kd kenan karewa d'akin kallo yayi tare da kallonta yanda ta dukunkune a kan prayer mat tana bacci harya k'arasa shigowa palourn yana mamakin baccin nan da ta tarka da sauyawar da tayi cikin satittikan nan ga wani fresh da take dukda MD baisan alamomin masu ciki ba Amma kawai zuciyarsa saita tsarga masa ko ciki gareta saurin barin tunanin nan yayi sanin irin magungunan da ta dinga d'irka tsawon watanni zaiyi wahala ta samu ciki a y'an shekarun nan ma Inma basu mata illa ba a nashi tunanin " a hankali ya shiga Kiran sunanta saida ya daddabata tukwana ta tashi tana murza ido harta gama wartsakewa kallonta MD yayi ya ce "Me yasa kike baccin yamma kinsan bakyau" Muryarta mai kama da ta mai bacci ta ce "Nima bansan ya d'auke ni ba ko har anyi la'ar ne" Tun dazu yanzu har 5 "Firgit Zarah ta mik'e ta ce " subhanalla tun fa 2 na kwanta har 5 banyi salla ba "Cikin Sauri ta wuce toilet din palourn Dan ta dauro alwala harta gama salla MD yana tunanin wani abu a ranshi Bayan ta salamce fuskantarta yayi ya ce " Na tambayeki mana?Inajinka"ta fad'a a hankali"Yaushe rabonki da perioud"Shiru tayi kamar mai nazari kafin ta ce "two weeks " Kin tabbatar kuwa?Gyada masa kai tayi ta ce "Eh" okay "kawai ya fad'a tare da maida kansa ya jingina da Bayan cushion yana lumshe ido a ransa ya ce " To me yake damunta'"ya rage sati guda yarjejeniyarsu Ta k'are cikinsu babu Wanda baiyi sanyi ba Musamman Zarah da takejin wani iri a ranta Hakan yasa yanzu suka rage Rashin jituwa ita da shi Amma kuma idan ta tuna Ta kusa rabuwa da Kalular Auren nan da aka lak'a mata saitaji sanyi a ranta bangaren Hafiz Sosai ya shiga shirye shiryen biki ba kama hannun yaro bangaren Zarah ko ba wani shirin da take Dan tayi wani irin sanyi sanyin ta na da ya dawo harma ya fi na da Asmy sai mita take akan halin ko in kula da take nunawa a bikin yauma suna zaune a jikin wani block cikin b'acin rai Ta ce "Wai me kike nufi Zarah duk sanda na d'auko miki maganar hidimar biki saiki banzatar dani " Kauda kai Zarah tayi tare da kwantar da kanta bisa cinya ta ce "Asmy Kuyi komai da kikaga ya dace please kidainayimun zancen bikin nan" kama hab'a Asmy tayi ta ce"Lallai Zarah yanda nake tunani kin wuce nan kamarya nadaina yi miki zancen bikinki me kike nufi wai ki fito fili ki fadamun"Zarah batasan dalili ba kawai saiji tayi hawaye sun fara zubo mata Wanda in za a kasheta bazatace ga dalilin kukan ta ba "Saurin kama hannunta Asmy Tai ta ce " subhanalla meye haka wai zarah"Fad'awa jikinta Zarah tayi tare da fashewa da kukan da taso rikewa "sosai Asmy ta rude ta fara cewa " meye haka Zarah karki tayarmun da hankali daga magana sai kuka me aka miki karkija hankalin mutane su dawo Kanmu please "Kasa mata magana Zarah tayi sai kuka da take Chuchu ce data hangosu ta Iso gurin ganin yanda Zarah ta lafe jikin Asmy tana shashekar Kuka ya sanyata cewa " subhanalla me akayi mata Asmy "cike da damuwa Asmy ta ce " wlh ba komai daga fara zancen biki kawai tahau mun kuka"Ikon Allah to ko batason bikin ne?kamarya su shekara hud'u suna soyayya da mutum biki yazo tace bataso ai bata isa ba abunda bazaiyu bane bama tana so kilan wani abun ne"Dak'yal suka samu Suka lallab'ata suka wuce hostel Wanda suna shiga ta fad'a Gado tare da Kara fashewa da sabon kuka Kallon juna Asmy da Chuchu sukayi sannan suka Kalleta zaune sukayi suna Kallon ikon Allah ba irin Lallashin da basuyi mata ba Amma batayi shiru Ba Saida ta gama kukanta mai isarta kafin ta Bari daka Kalleta kasan Tasha kuka Wayartaace dake hannun Asmy tayi ringing dubawa tayi taga Yusuf ne "D'auka tayi nan yake shaida mata driver ne yake jiran Zarah tun d'azu" okay gata nan "Asmy ta bashi amsa " dafa Zarah tayi da tayi shiru zuwa lokacin Chuchu na gefenta tana Lallashinta dukda basusan meya sanyata kuka ba Ta ce "Ki tashi driver na jiranki" banza tayi mata"saida ta maimaita ta ce "magana fa nake maki Zarah" tukwana ta tashi tare da Goge hawayenta cikin muryarta data fara dishashewa ta ce "Bani wayar to" Mik'a mata wayar Asmy tayi harta amsa saikuma ta riko hannunta ta ce "Ki fad'amun me yake damunki please Zarah baki da sirrin da zaki iya b'oyemun bai kamata ki boyemun wani abu meya ke damunki wai kwanannan"ba komai " ta fad'a tana goge sabon hawayen da ya zubo mata"Hmmm to wannan kukan da kike na meye"ba komai Kawai na tuno da Mamana ne da bansantaba shiyasa"ta fada tana Goge sabon hawayen daya zubo mata tayi saurin Mikewa tare da d'aukar wayarta ta ce "saida safe" saida tayi control d'in hawayen dake zarya a idanunta kafin ta fita amma kallo d'aya zakayi mata kasan tayi kuka shiru Chuchu tayi Jin Abunda Zarah ta ce saida tabar d'akin kafin ta kalli asmy da itama jikinta yayi sanyi ta ce "Me take nufi Asmy mamanta bata raye daman" eh tun wajen Haihuwarta ta rasu bata Santa ba ko a hoto saidai kawai anbamu labarin kamar yanda zarah take itama haka mahaifiyarta take banbancin ba kowa ne zai iya ganesaba hannun Matar uba ta tashi"hawaye harsun zubo a idon Chuchu ta ce "wayyo Allahsrk momcy gsky dole tayi kuka Rashin uwa ba k'aramun Abu bane kamarni Tun ina ciki bansan mahaifina ba Sai a hoto amma gwarani gaskiya akanta tunda ina da mahaifiya mancewa ma nake da rashin mahaifin da nayi saboda kallo biyu nakeyiwa yayana na uba da kuma na yaya shiya mayemun gurbin abba na amma Kuma wai ya kuke da ita ne dafa na d'auka gidanku d'aya saidaga banbanci sunan uban yasa nake tunanin ko cousin ne?Dan murmushi Asmy tayi ta ce " mubar maganar nan chuchu"Jin haka ya sanya Chuchu Jan bakinta tayi shiru karsuce tana musu shishigi Zarah ko kallo d'aya MD yayi mata yasan tayi kuka Saboda yanda idanunta sukayi ja ga kuma Rashin walwalarta data shigo da ita a hankali ya kirata da sunan da yake kiranta watau Mamy "Cikin sanyi ta d'ago ta Kallesa saita maida idanunta kasa " Baki da lafiya ne?Girgiza masa kai tayi"wani Abu akayi miki?nan ma girgiza kai tayi ,"To me ya sameki "kukan da ta dinga Rikewa ne tun a hanya ya Kufce mata batasan sanda ta fashe da sabon kuka ba " subhanalla ya fad'a tare da komawa Inda take ya kama hannunta ya ce "Me akayi miki" Shiru nan ma saici gaba da kukan da tayi "Janyota jikinshi MD yayi saboda a rayuwa ba abunda ya tsana sama da sauraran kuka kukanma na mace wannan yana d'aya daga cikin abunda Yasa ake ganin kamar Amera ke juya sa nan ko haka rayuwarsa take bayason ganin wani cikin damuwa musamman Wanda yake tare da su bare kuma Amera matarsa da suka zauna tsawon shekaru goma " shafa bayanta ya fara cikin sigar lallashi kamar wata baby Yana cikin Lallashinta Har yaji saukar numfashinta alamar tayi bacci Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya dinga kallonta yana nazarin meke damunta ya lura dai kamar akwai abunda ke damunta d'an karta tashi ya barta a jikinshi dukda yana buk'atar tashin Saida tayi baccinta ta gaji dukda a takure yake koda ta bud'e idanuwanta Kallon gefenta ta fara ya tabbatar mata da Cikin namiji take sai sannan tunaninta ya dawo mata cikin Sauri ta Zame jikinta a hankali daga nasa kallo d'aya tayi masa tayi kasa da kanta Tare da saurin Mikewa ta shige bedroom sallah kawai tayi danko yunwa bataji tarasa cikin kwanakin nan biyu abunda ke damunta ga tunanin mahaifiyarta da ya sanyata gaba sosai ta fara shiga kogin Dana sanin abunda ta aikata dukda tasan Asmy itace makasudin faruwar komai kwance tayi kan bed tare da lumshe ido kamar mai bacci Tana jin shigowarshi ta k'ara lumshe ido Zaunawa yayi gefen bed din tare da juye take away din d'aya sanya akayo musu a plate ya ce "taso kici abinci" Shiru tayi kamar mai bacci"Nasan kina jina kikamun banza ko Mamy"Kamar bazata tashi ba saikuma ta bud'e ido a hankali tare da mik'ewa ta tashi zaune tana jin kanta na ciwo kauda kai tayi bata bari sun had'a ido ba Plate din ya Aje gabanta tare da cewa"Ki juyo kici karya huce nasan ba abunda kikaci"a sanyaye ta ce "Na koshi?Baki isa ba sai kinci maza karki sake mun musu kinsan abunda bana so kenan"Sosai ta kwabe fuska kamar taga kashi haka ta fara cin abincin da ba dadinsa takeji ba Dak'yal tayi chokali shida ta Aje ta ce " na koshi"Kallonta ya dingayi yana Nazarinta a hankali "Ganin irin kallon da yake mata ya sanyata tsarguwa da kanta taki bari su hada ido" Kince kinyi perioud wannan watan? cike da kosawa ta gyad'a masa kai"shiru yayi kafin ya ce "Kishirya na kaiki Asibiti idanma Maleria ke damunki a baki magani" Kamar zatayi kuka ta ce "Ni wlh banason zuwa Asibitin lafiya ta qalau kaina ne kawai yake ciwo" Dage kafada MD yayi ya ce "Jikinki" yana gama fad'ar haka ya fita da harara ta bishi kafin taja tsaki kasa kasa tana tunanin tambayar da yayi mata sau biyu na perioud a ranta ta ce "Ko ina ruwansa da perioud dina "ba adau lokaci ba taga shigowarsa d'auke da ruwa a cup zaunawa yayi gefenta tare da b'allo parasitimol guda biyu ya ce " Anshi tana yamutsa fuska ta amsa Bayan ta amshi ruwan da ya mik'o mata saida ta rumtse ido kafin ta Had'iye saboda warin maganin da ya ke neman tayar mata da zuciya kakarin kamar zatayi amai yaga ta fara cikin Sauri ya d'aga pridge din d'akin ya fiddo fresh milk saurin budewa yayi tare da kafa mata a baki tana farasha