← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 92

Sashe 62

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta ce " Kinki a kaiki Asibiti momcy taya zaki zauna jikinki da zafi haka "Girgiza mata kai tayi ta ce " zanji sauki"Asmy data shigo da Ruwan tea a hannunta data had'o mata ta ce "Ki tashi kisha zakiji k'arfin jikinki Kinga ba abunda kika ci tun safe" Nanma girgiza mata kai tayi ta ce "Na koshi bana son Cin komai Asmy " Matsowa Inda take Asmy tayi tare da Aje cup din ta tallabota ta ce "Bazaiyu ba saikinsha wlh kinji na rantse " badan Zarah ta so ba saidan yanda Asmy ta rantse dole saita sha ya sanyata yunkurawa ta karba a hankali Tana rumtse idon kanta dake mata ciwo "Kurba d'aya Tayi taji Madarar ta taso mata Batasan sanda ta saki cup d'inba sakamakon aman da taji ya taho mata da gudu ta Ruga tayi waje kafin ma ta k'arasa makwararar gidansu ta fara sheka amai Kamar zata amayar da y'an cikinta dangin Baban ta da na Mama Rabi da suka zo Duk Kallonta suka tsayayi Yanda Take kwarara amai Chuchu ce ta biyo ta ganin ba Wanda yayi yunkurin taimaka mata ya sanyata d'aukar butar data gani a tsakar gidan ta cika ruwa tare da nufar Inda take ta fara jera mata Sannu a lokacin ko magana bata iyayi Asmy ma wajen tayo su Suka taimaka mata ta gyara jikinta Daya daga cikin K'annan babanta ta ce " Keko Zahra'u Me yake damunki Irin wannan aman"shiru tayi ta kasa magana.Mama Habi ta ce "Dake fa ake" Dagowa tayi ta Kalleta ta ce "Bakomai Mama" A a daga ganinki kaga marar lafiya ni sai yanzu ma na lura maza shirya na kaiki Asibiti anyi ciwo ba magani ciwon ma kuma na amarya"Hakanan Zarah taji gabanta ya fad'i "Chuchu ce ta ce " Mama Anjima basai a kaita ba yanzu tad'an huta "Mama Habi tace " to shikenan Sai Anjima idan ta tashi kizo ki fad'amun "To Chuchu ta fad'a daki suka koma Inda Asmy ta dirmiya duniyar tunani tsoro da fargaba cike da ranta tsoranta Allah tsoranta ace Zarah ciki ne da ita tasan shikenan tasu ta gama " Chuchu ko lallaba Zarah tayi harta samu tayi bacci sai sannan ta sauke ajiyar zuciya ta Kalli Asmy ta ce "waiko tana da typord ne " Girgiza mata kai tayi ta ce " a a a "Ikon Allah kuma take Amai haka to Allah ya bata lafiya Gaskiya ya kamata Aje asibitin Kar wuri ya K'ure amarya ba lafiya " Shiru Asmy ta dirmiya duniyar tunani ganin haka ya sanya Chuchu janyo wayarta ta fara chat sai wajen la'asr Zarah ta farka ta tashi jikin da sauki Saidai kasala da ciwon kan Kad'an nan suka shiga yi mata Sannu har khairat data shigo Inda taje ta fad'awa Mama Habi Ta tashi "Da Abinci a plate Mama Habi ta shigo d'akin Bayan ta zauna Kallon Zarah tayi ta ce " Anshi kici Nasan ba abunda kikaci"Dagowa tayi kamar zatayi kuka ta ce "Na koshi Mama" wani kallo tayi mata ta ce "Baki isa ba Anshi maza kici kar ranki ya baci" Zarah tana amsar abincin kafin ma takai Baki taji zuciyarta ta tashi amai na shirin zo mata "Cikin Sauri ta mik'e tare da rugawa tayi waje duk da kallon mamaki Mama Habi dake zaune ta tab'a hannu ta ce " me nake gani haka ni Habiba"batayi amai sosai ba saboda ba komai cikinta nan fa Mutane aka fara ido ido musamman dangin Mama Rabi ita ko "Fitowa tayi ta ce " Subhanalla Zarah me nake gani haka kiyi amai da safe yanzu ma haka lafiya kike saikace mai ciki"Kallon da Mama Habi tayi mata ne ya sanyata yin shiru tsaki taja tace Tashi Muje ki sanya hijab d'inki muje Asibiti "tab'e baki Mama Rabi tayi ta koma ciki ita da y'an uwanta suna cewa " shidai abun duniya baya rufuwa kome akayi sai anjishi ba wani boye boye "girgiza kai Kawai Mama Habi tayi Da taimakonta ta shiga toilet Dan tayi wanka Bayan ta fito D'akin da su Zarah take ta shigo shigarsu kenan Khairat ta shigo Tare da Kallon Mama Habi ta ce " Mama Baba yace wai kije keda su Mama Zainabu Yana dakinshi"To kice masa ina zuwa ta fad'a tare da mik'ewa kallon su Chuchu tayi ta ce "ta shirya kafin na dawo" yanayin yanda suka samu Baba ne hankalinsu saida ya tashi dafe da kanshi kallo d'aya zakayi mashi kasan yana cikin tsananin damuwa "dak'yal K'anwar tashi da Yayar tashi suka karasa " Mama Zainabu ta ce "Lafiya dai Malam" Sai sannan ya d'ago ya ce "da sauki Zainabu Yanzun nan shigowar da kikaga nayi dangin yaron Chan ne sukazo akan wai Yaron ya ce ya fasa sun kasa gane kanshi tun jiya gidansu ba irin Fafatun da ba ayi ba karya maidasu kananan mutane amma ya murje ido ya ce " ya fasa Auren kuma ma aka kuskura aka daura zai iya sakinta a ranar Dan haka shine sukazo suka bamu hakuri akan muyi hakuri a d'auki abun matsayin kaddara wlh hankali na matuk'ar tashe yake ina farincikin zan Aurar da Amanar Allah Murnata ta koma ciki wlh nayi mamakin yaron nan yanda lokaci guda zaice ya fasa saida ya bari ana gobe d'aurin Aure kafin a sanya Ranar Auren karkiga irin rawar k'afar da yake gaba d'aya hankali na ya tashi kaina ya kulle na rasa ta Inda ma zan fara"Cikin tsananin tashin hankali Suka rafka Salati Mama Habi ta mik'e ta ce "Allah ya kiyaye yaron nan ba yaudarar yarinyar nan yayi ba Yayi mata ciki yace ya fasa" ciki"Baba Da ?Mama Zainabu suka fad'a lokaci guda hankali tashe "Yo eh mana ciki inba ciki ba me zaisa yarinya tayi ta kwarara amai Tun safe sannan kuma yazo lokaci guda yace ya fasa ai wannan ba maganar d'auka bace da walaki Goro a miya" Girgixa kai Baba yayi yana dafe saitin zuciyarsa da Yakejin wani irin zafi a dabarbarcewa ya ce "Ba haka bane Habiba na yarda da Zarah d'ari bisa d'ari bazatayi abunda bai dace ba na d'auki hakan a matsayin kaddara Da rubutun Allah ya rubuta ba mijin ta bane Dan haka ku hada lefensu ku mayar musu Har gida" Kallon Mama Zainabu Mama Habi tayi ta ce "Kije ke da su Kande ku mayar musu da kayansu ni kuma bari muje Asibiti wlh abunda nake zargi ya tabbata basu isa ba Saidai duniya ta zagemu amma bai isa yayi wannan yaudarar ba yaci bulus tana komawa d'akin ta samu Zara harta sanya hijab cikin muryar b'acin rai Dan ita daman zafi gareta ta ce " Wuce mu tafi "Asmy ce ta ce " Bari na rakaku Mama"Kallon Chuchu tayi ta ce "Ita kuma bakuwar ki barta ita kadai ki bari mu dawo A tare suka fita da Zarah hankalinta duk a tashe koda suka isa Asibiti Mama Habi cewa likitan yayi " Yi mata awon ciki"Gaban Zarah Ya bada daram Kallon Mama habi tayi tana so tayi magana taga yanda ta had'e fuska ya sanyata shiru Fitsarinta Dr ya d'auka Bayan yasa tayo a wata k'aramar kwalba ya tafi awo tagumi Zarah tayi Gabanta na tsananta fad'uwa ba ayi 20 minutes ba dr ya dawo Y'an rubuce rubuce yayi kafin ya d'ago ya kalli Mama Rabi ya mik'a mata takardar"Amsa tayi tace "Ba gane rubututtukan nan naku nake ba Dr fad'amun abunda ke damunta" Murmushi yayi ya ce "To shikenan Mama " Tana D'auke Da ciki ne Na wata Ukku da sati Ukku"Cikin tsananin tashin hankali Zarah ta d'ago ta kalli Dr Ta ce "Ciki kuma Dr" eh idan baki Yarda da result d'inmu ba zaki iya zuwa wani asibitin a aunaki amma Tabbas ciki ne dake na Wata hud'u ba Sati d'aya "Tashin hankali ne ya ziyarci zuciyar Zarah Wanda Bata tabajin irinshi ba a iya Rayuwarta ba " Batasan sanda Ta d'ora hannu aka ba Tana shirin kurma ihu cikin b'acin rai Mama Habi ta kwabe mata baki ta ce "Yiwa mutane shiru tashi muje" ta fad'a tana wartar hannunta "Sukayi waje kuka Zarah takeson tayi Amma tashin hankali yasa ta nemu kukan ta rasa Suna fita harabar asibitin Mama Habi ta ce " Tonon asiri ne zakiyi mana a Asibiti kowa ya fahimci halin da ake ciki ai ba yanzu ya kamata kiyi kuka ba yana nan gaba "Kuka Zarah ta fashe dashi Sosai ta ce " Wlh Mama karya yake bani da wani ciki sharri ne kawai zaiyi mini"d'auketa da Mari Mama Habi tayi cikin b'acin rai Ta ce "Yi mana tonon Asiri a titi Zakiyi bayani idan mukaje gida gaban mahaifinki bani ba " Tsaida mai napep sukayi suka shiga hade kai da gwuiwa Zarah tayi ta shiga rera kukan tausayin kanta Tabbas indai da gaske ciki ne da ita Musty ya cuceta ya gama da ita ya cuci rayuwarta "batasan sun isa gida ba Saiji tayi Mama Habi ta Ja hannunta bata dire ta ko ina ba sai d'akin Baba Kujerar Dake d'akin ta wullar da Ita tana huci ta ce " Kin cuce mu Zarah kin b'ata mana sunan zuri'a ana tunanin wuta a makera ashe a masak'a za'a sameta Kinban mamaki ko a mafarki ban tab'a tunanin zakiyi mana haka ba kin cuce mu kin cuci mahaifinki kin cuci mahaifiyarki dake k'asa sannan kin cuci kanki......... *domin magana da marubuciyar kai tsaye 07026166536* *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo ce*_ ...........*73 & 74* Kin cucemu Zarah kin b'ata yardar da mukayi miki"ta k'arasa fad'a hawayen bak'inciki na sauka daga idonta Dan Duk cikin Yayan y'an uwanta ba Wanda tafiso kamar Zahra"Kuka Zahra
Chapter 62 · 0% Book details