← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 92

Sashe 52

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ai dole tace maki Mama kam yanda kike bada command irin y'ar nan taki"wlh ba haka bane abun ne ya fara bani Haushi bacci bacci saikace kasa"Wlh ko nima abun har mamaki yakeban kamar wacce tse_tse fly ya cixa kokuma wata me ciki ta zauna tayi ta bacci ba control" Gaban Asmy ne ya bada daram jin Abunda Chuchu tace Dan bata tab'a sanin bacci Alamun ciki bane Zarah ma dake fitowa daga toilet saida gabanta ya fad'i saikuma taja tsaki a ranta ga ce "Ni mema zai had'ani da wani ciki Allah na tuba wata takwas bansamu ba sai yanxu" Ta k'arasa shigowa "Daidai lokacin da Asmy ke cewa Chuchu " Ke waya fad'a maki mai ciki tana yawan bacci nidai ban tab'a jiba"Nima a novels karanta wlh "ta fad'a tana y'ar Dariya " Tsaki Asmy taja tace keda kike karanta novels dinma har kika sani"Murmushi Chuchu tayi ta ce "Hmm ai wlh ina mamakinku da kikace wai baku karatun novels ai novels duniya ne musamman kika hadu da mai dadi duk wata damuwarki jinta zakiyi ta yaye novels yana yaye damuwa yanda baki tunani wlh Ga dadi jinki kike kamar kiyi tsuntsuwa ki koma duniyarsu" Dariya Asmy tayi ta ce "Haka dai kike cewa nikam gani nake bazan iya zaunawa na karanta ba gani nake bata lokaci ne kema Rashin aikinyi ne kawai" hmmmm bazaki gane bane Matar nan"To Ganar dani "Dariya chuchu tayi ta ce '" Ai tunda kince bazaki iya ba shikenan"a a yanzu dai Naji bani wani na karanta Page d'aya Naji yanda abun yake"okay bari na dubo maki *Ni da yaya Arman* da na karanta kwanaki tun lokacin da ake typing dinsa na saya littafin yayi dadi over yanda baki tunani anzuba zallar Soyayya a cikin book dinnan an zuba basira kede bari ki karanta saikin bani labari "okay ban page d'aya Na gani" Wayarta Chuchu ta bud'e ta shiga tare da mik'a mata "karanta Page d'aya ma kadai ki bani labari "Ansar wayar Asmy tayi ta fara karantawa Zarah dai na jinsu har ta gama salla girgiza kai tayi ta ce "Ana shirin exams kina shirin koya mata karatun Littafi" Dariya Chuchu tayi ta ce "Page d'aya ne fa zata karanta momcy kema ko zaki karanta" Girgiza.kai tayi ta ce "Bani da time d'in wannan Exams na gabatomu ina ni ina fara karatun Littafi " Asmy ita da zata karanta Page d'aya ai batasan ta zarce har page biyar ba saida Chuchu ta warce wayarta ta ce " Yadai naga kinjima bani wayata chat zanyi"Cikin doki asmy tace "wayyo ya zaki lasamun Zuma a baki kuma ki barni Dan Allah ki bani naci gaba please banso ko da second d'aya a wuceni" Dariya Chuchu ta kwashe da ita ta ce "Keda kikace bani da aikinyi ai bazaki cigaba page daya nace ki karanta" ai bansan haka abun yake ba shiyasa nace haka wlh book din tundaga fara karanta Page d'aya ya tafi da imani na tundaga farkon salon soyayyarsu ya burgeni ba k'aramar love za a zuba a book d'innan ba da na lura Dan Allah ki bani na ida please "Dariya Chuchu tayi tace bari dai na tura maki ba Dan halinki ba Ai baki fara komai chakwakiyar love sai nan gaba Ayra da Arman Ai duniya ne Bari dai karna baki labari ki karanta da kanki" Zarah ce ta ce "Ikon Allah to ga wayata nima turamun Idan mungama exams na samu na karanta"Duka ba haka za ayi ba ku bari zansaya muku complete document a wajen marubuciyar saina tura muku ta what's app wannan doc din free page ne kuma.lokacin da na karanta a paid grp dintane Kunga ba Tarawa zanyi ba " Cikin doki asmy ta ce "Nidai fara turamun wannan din Kafin taturo cmplt din wlh marubuciyar ta iya salon labari mai d'aukar hankali" Dariya Chuchu tayi ta ce "Kaji uwar azarzabi ki bari na saya muku mana " A a aban yarda ba please ni bani number marubuciyar ya sunanta na maza na saya kar a barni a baya"Dariya Chuchu ta dake ta ce "aifa inaga haka din zanyi chan ku karata rubuta mata number tayi ta ce " Kiyi save da Hajara L Sadeq ko miss hajo"girgiza kai Zarah tayi ta ce "Kinji uwar ujila nima bani numberta sanda Nasamu time naso karantawa saina tuntubeta" Itama Rubuta mata number tayi ta ce "Na tura miki free page din ta what's app" Okay Thnks daughter "Zarah ta fad'a sai yamma driver yazo daukarta suka wuce Gidan MD tana lissafin sauran lokacin da ya rage mata ya saketa kowa ya kama gabansa sosai ta maida hankalinta ga karatun ta dukda yawan baccin da take bai hanata raba dare tana karatu dukda MD baya barinta sakewa a dare saboda koda yaushe yana nanike ita itako ta rabu dashi ne kawai Dan tasan na bankwana ne yake nan da one months kowa ya kama gabansa da idonsa ma bazai ganta ba tsaye take tana soya awarar kwai a kitchen tunda taji karnin kwan taji zuciyarta na tashi Tun tana daurewa harta kasa da gudu ta fito tare da rugawa palour ta fad'a toilet a guje nan ta fara kwarara amai MD yana palour yana mamakin me ya sameta bai tashi ba ya bita haryaga Fitowarta tana maida numfashi " Sannu"ya furta a hankali ta gyad'a masa kai tare da bajewa kan kujera tana ci gaba da maida numfashi "Baki da lafiya ne" ya k'ara maimaitawa "Girgiza kai tayi tare da yatsine fuska ta ce......... *07026166536 domin magana da marubuciyar kai tsaye* *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 1, *MU GANI A ASA...* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN WAI..* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..* _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA* _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA* _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda hu u N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda aya N300 *DOMIN TURA KU IN KAI TSAYE* 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya 0810 433 5144 Masu tura katin MTN 0814 179 9224 asar Niger zasu tura nasu anan. 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda hu u 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda aya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* _*Miss Hajo ce*_ ..........*63 & 64* "Lafiya ta qalau kawai ina suyar kwan ne karninsa ya dinga tasomun ya tayar mun da zuciya shine ya sanyani amai" okay Sorrry yanzu kin kashe gas din"girgiza masa kai tayi ta ce "a a a bazan iya komawa kitchen din ba" Mikewa yayi ya ce "okay bari ni na kaso " Bayan ya kaso gas din ya dawo "Kallonta ya dingayi yanda ta baje a kujera tana maida numfashi idonta Rufe kamar mai bacci jin shiru ya sanyashi lekata yaga Kamar bacci take " Mamy"ya kira sunanta A hankali"jin shiru ya tabbatar masa da tayi bacci"shiru yayi yana tunanin sauyin da ya gani tattare da ita cikin satittikan nan "Karewa beauty face d'inta kallo ya dingayi samun kanshi yayi da shafa Fuskarta tare da lotsa hannunsa a dimple dinta d'aya daya lotsa dukda kasancewar bacci ta ke " Black beauty "ya fad'a a hankali" After one week Hafiz ya zo ganinta A sch suka had'u kasancewar lokacin sun fito daga lectures farinciki d'auke da fuskarsa ya ce "Kinga ko yanda kika k'ara kyau da fresh kuwa my Zarah ko har amfara dilkan Amarcin ne" Rufe fuska tayi ta ce "Kai ya Hafiz ana sch ina aka samu daman dilka kawai idonka ne ke gane maka haka fa" Serious fa nake maki magana wlh kin k'ara kyau da fresh da komai ma"Uhm"Kawai Zarah tace cike da jin kunya sai wajen Yamma ya tafi Tukwana ta koma hostel Dan yau bata da niyyar komawa gidan MD Dan yanzu Abunda yake mata ba dadinsa take jiba ita kanta har mamaki take da yanda takeson abun Amma yanzu kwata_kwata ko feeling ta dainaji"Tana shiga Chuchu kadai ta tarar kwantawa tayi kan gadon ba bacci take ba duniyar tunani ta Lula Wanda a kasheta bazatace ga tunanin da take ba a haka har Asmy ta shigo"saida ta daddabata tukwana ta dawo "harya tafi Hafiz din" Eh "ta bata amsa a takaice" okay kunyi maganar shirye shiryen bikin dashi"Girgiza kai Zarah tayi ta ce "a a a " to saboda me Abu na tahowa yanzu ai ya kamata a fara tsara abubuwan tunda Kinga damun koma wata gudane za a k'ara ba wani isashen time"ku shirya kawai ni bani da wani shiri da zanyi ta fad'a tana hade fuska"Ikon Allah Asmy ta fad'a kafin ta ce "hmm kede kika sani" Bata kula ta ba Zarah da dare tana jin Suna dahuwar indomie Bayan sun gama Chuchu ta ce "Ki sauko muci momcy wai ko baki da lafiya" Girgiza mata kai Zarah tayi ta ce "Na koshi ina Lafiya kawai ina danjin kasala ne shiyasa" Gaban Asmy ne ya bada daram Kallon Zarah tayi ta ce "Kasala kuma?gyada mata kai tayi tare da juya mata baya " Chuchu ta ce "Ki sauko muci Bafa kici komai ba" na k'oshi banajin yunwa "Zarah ta fad'a tare da kauda kai Dan k'amshin abincin baiyi mata ba yana neman tasar mata da zuciya Asmy saida taga Chuchu ta fita tana waya tukwana takamo hannun Zarah tare da cewa " Sis kina shan wannan maganin nan kuwa?wani magani ?Zarah ta tambayeta ?Wanda Dr Halima ta rubuta maki mana"Sai sannan Zarah ta tuno ma da maganar cewa tayi "ohhh eh ina shansa ya akayi" Ajiyar zuciya Asmy ta sauke ta ce "Daman ina son fita kokontone tsoro nake Kar Aje ciki gareki naga duk kin sauya kwanannan" tsaki Zarah taja ta ce "Ke baki da hankalina wlh mai ciki kama da wa yake mema zai had'ani da ciki Bayan watan nan ma.Saida nayi perioud gashi ina shan magani kuma ma shida ba haihuwa yake ba karma ki damu kanki ba wani ciki da garan kawai ina tunanin Maleria ce Ke damuna" Ajiyar zuciya Asmy ta sauke ta ce "To gobe muje asibiti mana a gwada ki ko na cire zargin kokwantan da nake a raina" Ba Inda zani ni lafiya ta qalau please karki sake mun maganar nan marar ma'ana Asmy "washegari Bayan fitowarsu daga lecture driver yazo ya d'auketa koda ta
Chapter 52 · 0% Book details