← Book details Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 92

Sashe 9

Auren Wata Tara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

maciji jikinta cikin Sauri ya taimaka mata Inda anan take ta sume kai tsaye Asibiti ya nufa da ita bayan an duba Saran da macijin yayi mata nan akayi mata allura aka bata magani. Gidanshi ya koma da ita nan ya cigaba da kula da ita ganin har lokacin Bata farka ba gudun zargin mutane ya sanyashi daukarta ya tafi da ita garinsu Batsari Inda ya ajeta gidan baffanshi dan mahaifanshi sunjima da rasuwa a hannun kanin mahaifinshi ya taso nan aka cigaba da kula da ita harta farka Saidai me koda ta farka. bata iya magana Saidai ta kalli mutane Cikin ikon Allah da addua da komai aka samu harta fara magana Saidai me duk tambayar da akayi mata game da Iyayenta ko y'an uwanta bata iya tuna komai duk yanda taso tunawa sai ta kasa. hakan yana damun Malam sosai kuma yana tausaya mata gata dai ba wata babba ba Dan a lokacin bazata wuce 18 years ba Saidai abunda ya basu mamaki ta rik'e sunanta Zarah. Saida Zarah ta shekara guda gidansu Malam batare da ta tuna kowa nata ba ga kuma karfaffar soyayyar da ta shiga tsakanin ta da Malam sosai suke San junansu Wanda lura da hakan ya sanya Baffa jin dad'i kanin mahaifinshi kenan Wanda shi ya tsaye musu har aka daura musu Aure. ranar wannan masoyan sun shiga farincikin marar musaltuwa A funtua suka tare sabon gidan Malam da ke jabiri zamansu yaci gaba da wakana cikin soyayya da k'aunar juna saboda Zarah macece mai biyayya hakuri uwa uba Kirki Dan a zamanta da mutanen unguwar sai dai Sam barka Dan kowa Santa yake da kaunarta aminiyarta d'aya a unguwar Saratu watau maman su Asmy a lokacin yarinyarsu d'aya Hauwa'u a lokacin suna cikin halin talauci Wanda hakan sosai ke damun Zarah hakan yasa bata iyacin Abu bata bata ba sunyi zama cikin mutunci da amintaka dukda Saratu ta girmi Zarah amma haka take girmamata kuma suke girmama juna. "ana haka ne Zarah ta samu ciki Wanda tunda ta samu cikin takeshan wahala ta ke jin a jikinta cikin kamar shine ajalinta A tattare suka samu ciki da Saratu Inda lokacin mijinta ya samu warwara saboda daman yayi karatu Inda ya samu aiki a Bangaren agric saboda daman karatun malamin gona yayi . kwana a tashi ba wuya wajen Allah a yanzu cikin Zarah ya shiga wata Tara Inda ranar wata Juma a ta tashi da nakuda kai tsaye Asibiti aka wuce da ita sosai take shan wahala tasan rayuwarta tazo karshe a lokacin ne kuma ta tuno da rayuwarta Ta baya Tana cikin halin nakuda ta ce " . a kira mata Malam "haka ko akayi shigowarshi d'akin tayi daidai da haifo santaleliyar y'arta sak mai kama da Ita kamar an tsaga Kara an karya. Ajiyar zuciya Ta sauke Kallon nurse tayi dake shirin Tafiya don a shirya d'iyar tayi cikin k'arfin ta ce " mik'omun naga kyautar da Allah yayi mun" mik'a mata y'ar akayi Inda ta tsaya tana kallonta hawayen tausayin y'ar na zubo mata shafa kanta Tayi Tare da kissing din goshinta ta ce "Allah yayi maki Albarka Zarah ya sa mai taimakon Addini ce Ina sonki Sosai y'ata saidai Allah bai nufa Ba zamu rayu tare Allah ya shirya munke yayi miki albarka Albarkata taci gaba da bibiyarki har k'arshen rayuwarki " tari ne yaci karfinta Mik'awa Malam y'ar tayi tuni harta fara fita daga hayyacinta Tare da cewa " ga Amanar y'ata na a hannunka Malam ka kula mun da ita ka bata tarbiya ka zame mata uwa da uba ka bata duk kulawar da zan bata ka bata tarbiya harka Aurar da ita Malam ga Amanar yata nan " a lokacin ne maman asmy ta shigo ita ma cikin kid'imewa ta nufi gadon tana hawaye ta ce "me kike cewa haka Zarah ai cuta ba mutuwa bace haka haihuwar take kowa haka yakeji" Murmushin yake tayi tare da girgiza kai ta ce "bakisan irin abunda nakejiba shiyasa wannan ba zafin nakuda bane sannan ta kamo hannunta tana hawaye ta ce "Ga Amanar y'ata nan A hannunku ku rik'emun ita amana sannan ku bata tarbiya nasan zaku iya ". " Malam ne da har zuciyarshi ta karye Ya fara hawaye ya ce "Bazaki mutu ba Zarah ta Insha Allah muna nan tare Harsaikinga auran Zarah da kanki zaki Riki y'arki" . Kallon y'ar kawai take tana tari cikin k'arfin hali ta Ciro wata zoben gold dake hannunta Tare da awarwaron zinaren da dukansu tare aka tsinceta da su ta mik'awa Malam ta ce . "idan y'ata ta girma har lokacin Aurenta ku bata wannan shine Babban abunda zai taimaka mata wajen gano Dangina lokacin da zan maku Bayani ya K'ure sannan ku sanya mata suna na Fatima Zarah sosai tarinta ya k'ara tsananta kafin kuma daga karshe suji ta fara Salati ta na Salati har ta cika. Allahsrk mutuwa kenan mutuwar zarah ba Malam kadaiba hatta mutanen dake unguwar ta Girgiza su Malam ko Kullum kamar ba namiji ba haka zai zauna yayi ta kukan mutuwar zarah danma idan ya kalli y'arta sai yaji wani sanyi a ranshi tunda bata mutu ba har saida ta bar masa Jininta kuma photocopy d'inta Dan sak Zarah mahaifiyarta ce har dimple dinta sai kyau ma da tafi mahaifiyarta. Kasancewar maman asmy itama ranar ta haihu saboda tashin hankalin mutuwar aminiyarta itama nakudar tazo mata Tasha kukan wannan Babban Rashin da sukayi ita ta Shayar da Zarah tare da y'arta da taci suna Asma'u ita kuma Zarah daman tun ranar da aka haifeta kamar yanda mahaifiyarta ta fad'a haka Baba ya sanya mata sunan mahaifiyarta Zarah ". kulawa ta musamman maman asmy ta dinga bawa Zarah tare da Asma'u ta had'u ta dinga renonsu Malam ko yanzu baida wata jinjinar sana a saboda tundaga mutuwar zarah komai ya tsaya masa baya iya Zuwa ko ina koda akayi shekara biyu da mutuwan da zai koma harkar nomansa Ya samu Mai gonar har ya bawa wani haya nan ya dawo gida yaci gaba da tawakkali da Allah harya samu Aikin bakanikanci a wani garrage gyaran mashina da motoci Inda ya fara aikin A lokacin ne kuma danginshi suka fara korafin akan baiyi Aure ba yaci yayi Aure yanzu. Inda ya hadu da Wata zawara rabi'atu da yaranta biyu a lokacin kamar mutuniyar kirki haka ya aureta tare da yaranta duk yanda zaiyi saiya ciyar dasu Inda Ya maido da Zarah gidan Wanda a lokacin ta nuna Duk d'aya ne a gaban idonshi zata nuna tafi kowa son Zarah Inda Bayan idonshi irin azabar da take gana mata kare baici Malam bai tab'a ganewa ba saboda Zarah ta tashi da wani irin hakuri kome za a mata bata tab'a fada masa ba. ta haifi yaranta Biyu da Malam Safiya sai kuma khairat Azaba sosai take ganawa Zarah kasancewar ta sameta yarinya mai hakuri Wanda Malam baisan da hakan ba saidaga baya ya fahimta A unguwar ba Wanda baisan irin wahalar da rabi keba Zarah ba. Malam ya tsayewa Zarah Karatun boko da na arabi Zarah yarinya ce mai baiwar kokari Dan kokarinta saidai a kirashi na baiwa saboda yanzu za a ayi yanzu za a kwashe duk karatun da tayi tare sukayi da Asmy Dan sun zama kamar y'an biyu kuma maman asmy ta rik'e Amanar da aminiyarta ta bata danma Mama Rabi dake azabtar da ita Yaran Mama Rabi duk sun lalace saboda Rashin tarbiya da bata basu ba khairat ce cikinsu kawai ta fita zakka zarah tunda ta taso ta fara perioud take shan wahala dan duk wata saidai akaita ayi mata allura irin fita daga hayyacinta da take har suma take sannan tana da larurar tsananin sha'awa mai karfi wanda wani lokacin abun ya taso mata saidai a bata maganin bacci wanda shawarar dr din da aka taba kaita wajenshi ne dan ya bata magani ya basu hakan . wannan kenan. *FCT ABUJA* Manyan motoci ne na gani na fad'a Sunkai Sha biyar jere suke suna tafiya cikin gudu saboda bikin da za a gudanar na bud'e shahararren sabon shopping mall d'in da ya amsa sunansa. Wajen shake yake da manyan mutane tun daga kan y'an kasuwa "shahararrun masu kudi da sauransu *MD SHOPPING MALL*naga an rubuta a saman ginin yanayin yanda akayi rubutunma kad'ai ya isa ya sanyaka Yin k'auyanci. Waje ne da ya tsaru da kyau saika rantse ba k'asa Nigeria kake ba saboda yanda zakayi mamakin irin dukiyar da aka zuba a ginin ma b'ata lokaci ne. Nan aka fara gudanar da bikin bud'e Wajen Bayan jawabai daga bakin manya da shahararrun y'an kasuwa Inda akazo ga jawabi wajen mai gayya mai aiki wato mamallakin wannan shahararren wajen watau Mustapha Dikko *MD* . "hamshak'e ya ke a wajen banyi Tunanin yana jin hausa ba saboda kwata_kwata baiyi kama da hausawa ba Fari ne sosai kamar bature ko kuma ba indiye Sanye yake cikin bak'ar coated wacce ta amshesa ta kara fito masa da kyau da kuma hasken fatar sa kallo d'aya zakayi masa kaga asalin ba india sanye ya ke cikin siririn farin glass sumar kan nan nasa lufluf gwanin sha'awa da burgewa ga kuma sajenshi Dake zagaye da kyakyawar fuskarsa daya kara kayatar da tsananin kyaun da Allah yayi mishi. a gaskiya ni kaina saida na rude da ganin zubi da kyau irin na wannnan bawan Allah zan iya cewa tsawon rayuwa ta ko a film bantaba ga namiji da kyau irin haka ba duk inda karshe da baiwar kyau take tofa Yakai a kirasa da komai Dan guy din ya had'u karshen had'uwa (lol). Daga zaunen da yake batare da ya mik'e ba ya amshi abun maganar tare da Fara jawabi cikin zazzak'ar muryarsa Yanayin yanda yake.maganar saika d'auka wani sautin wak'a ne mai ratsa zuciya ke tashi. baiyi wata magana mai tsayi ba saboda shi daman Chan ba mutum bane mai fiya son magana da yawa ba Hasalima yanzu a k'agare yake A gama taron nan ya tafi dukda dalilinshi kowa yazo wajen amma ya k'agu saboda hayaniyar da ake a wajen dan shi ba mutum bane mai son hayaniya . camera ce A kansa ta gidajen television da dama kowa so yake ya d'auka jawabin harya gama ana haskasa da camerori. "Tsaki yaja yana
Chapter 9 · 0% Book details