← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 64

Sashe 9

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya tsuke fuska yace
"Meye kuma abun kukan? Kince inzo in duba ki nazo kuma seki dinga min kuka? Wannan se ace wani abun nayi miki ai" yai maganar in very serious tone

Maimakon ta shiga taitayin ta sema wasu hawayen dake kuma bin fuskarta wannan karon hadda sauti, cikin shagwaba ta fara magana

"Ni wallahi ban warke ba, ko sauƙi banji ba, yau ma a kwance na wuni, Yanzu Yaya Ammar ba dan na roƙe ka ba ba zaka zo ka duba ni ba ko? Cikin dare rashin lafiya ta kamani ba wanda ya sani kai na fara gayawa a sume aka kaini Asibiti, Amma kaƙi zuwa duba ni, ni ka tsane ni kuma ban san me nayi maka ba"

Ta ci gaba da kukan ta cike da shagwaɓa kaman wata 'yar yarinya ƙarama hawaye wani na bin wani.

Ammar yai ƙarfin halin cewa "look ko ki dena wannan kukan, ko kuma in tashi in tafi"

"to zan dena"

"ba cewa zakiyi zaki dena ba, kidena kawai, goge wannan hawayen"

Ta É—an lumshe ido sannan tace "Niba handkerchief a gurina sedai ka bani naka in goge"

Kallon ta yayi galala ya haÉ—e rai yace "goge da mayafin ki"
Noƙe kafaɗa tayi
"A'a ni da handkerchief ɗin ka nake so zan goge, nasan yana Ƙamshin turaren ka"

"naga Alamar kin warke, Allah ya ƙara afuwa" yai maganar yana ƙoƙarin miƙewa

Ta kwantar da kai tare da kwantar da murya tace "dan Allah da manzon sa karka tafi yanzu"

"Ni wannan abubuwan da kike ne bana so, shi yasa bana son zuwa inda kike, ina sauri ne ana jira na ai nazo na duba ki"

"Yanzu tafiya za ka yi?"

Shiru yayi mata ya durƙusa ya ɗau mukullin babur ɗin sa da wayar sa, ya tsaya yana gyara links ɗin hannun rigar sa itama ta miƙe tsaye, Amma abunka da mara lafiya jiki ba ƙwari tana tashi taga duhu a idon ta duniyar tana juya mata, dafe kanta tayi data ji ya sara mata.
Yuuuuu ta tafi zata faɗi, Cikin zafin nama Ammar ya riƙo ta.

Da ƙarfi zuciyar Ammar ta buga, gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi, be taɓa riƙe macen da ba maharramarsa ba yana sane se yanzu, jikin ta rau yake da Zazzabi me zafin gaske.

"Wash Allah kaina ze fashe"

Tsoro da fargaba ne suka kama Ammar, kar wani yazo ya ganta a jikin sa, ga kuma jikin ta zafin daya É—auka.
Jingina ta yayi a jikin bango yace "zaki iya tafiya ko inyi magana cikin gida a zo a shiga dake?"
Girgiza masa kai tayi tace
"na rage jin jirin zan iya shiga gida da kaina"
"Sannu ɗan ƙara hutawa seki shiga"
Ta jinjina masa kai

Baba ne ya dawo ya tarar da Ammar yana shirin tafiya, mufeeda kuma zata koma cikin gida, Ammar ya tsaya ya gaida Baba, yai masa ya me jiki.

Baba ya amsa masa cikin mutunci ya kalli Mufeeda yace "Auta na ya jikin naki"
"Da sauƙi Baba"
"Masha Allah" Baba ya dawo da kallon sa kan Ammar yace
"Ammar ko?"
Ammar ya jinjina kai yace "Eh hakane"
Baba yace "Yawwa dama ina son ganin ka, biyo ni"

Galala Ammar yayi yana fatan "Allah yasa ba riƙe Mufeeda da yayi ya gani ba yai zafon wani abun"

Murmushi Mufeeda tayi tare da yin gaba abunta ba tare da ta kuma waiwayo ba

More Comments More typing

Domin sharhi, gyara ko shawara
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

*ELEGANT ONLINE WTITERS*

                            Page 5

Cikin gida mufeeda ta koma tana me farinciki tare da roƙon Allah yasa Ammar ya amince.

Har falon Baba Ammar ya shiga suka ƙara gaisawa da baba, Baba ya dube shi yace
"Ammar a wace unguwa kake sannan menene sana'ar ka?"
Ammar yaji gaban sa ya fadi tare da mamakin wannan tambayar amma ya dake ya bawa Baba amsar tambayar sa, Baba ya cigaba da yi masa tambayoyi game da shi yana bashi amsa.

Baba ya nisa yaxe "to dama abunda yasa na kira ka kuna nayi maka wanna tambayoyi ba komai bane face auta tazo ta sameni da maganar ka,  kuma yanayi ya nunamin kanada hankali da nutsuwa, to nidai gaskiya mutum me son abunda yaran sa suke so matuƙar be saɓawa shari'a ba, da farko Auta karatu take sonyi amma katsam ta sauya tunani, kuma bana tauye abunda yarona yake so ince lallai se yabi nawa abunda nake so, tunda harta furta ta zabi Aure akan karatu nace bari inyi maka magana idan ka shirya ka turo magabatanka, ina so abun ya zamana anyi shi anan kusa, sedai ina son bayan auren ka barta ta ci gaba da karatun ta"

Ras! Ras!! Ras!!! Gaban Ammar ya faɗi, ya ɗago ya kalli mahaifin Mufeeda da nufin ya sanar da shi shi babu wata alaƙa ta soyayya a tsakanin sa da Mufeeda, Amma ya ga dattijon ya masa matuƙar kwarjinin da baze iya kallon sa ya gaya masa hakan ba, nan da nan gumi ya dinga tsatstsafo masa ta ko ina.

"baka ce komai ba"

"To Baba nagode insha Allah zanyi magana da magabata na"

Baba yace  "yayi kyau, Allah ya Sanya Alkhairi a tsakanin ku"

Da ƙyar Ammar ya baro gidan nan zuciyar sa na bugun uku uku, shi dai gaskiyar magana Mufeeda tayi masa ƙanƙanta a aure, ta ina zeyi zaman Aure da wannan jaririyar yarinyar? Shi sam babu wani abu makamancin son ta da yake ji a ransa, shi be taɓa jin yana son wata ba balle yace ga yadda akeji, ita kanta budurwar sa zainab bawai dan yana jin yana sonta yake niyyar auren ta ba, se dan tana da irin shekarun da yake son mace ta kai kafin ya aure ta, gashi tsoron sa da take ji da kwarjinin sa baya bata damar nuna masa soyayya, dan sam Ammar kallon shiririta yake wa wannan abubuwan na soyayya.

Allah ne ya kai Ammar gida lafiya, ba dan yasan a yadda yake tuƙin ba.
Yana zuwa gida ba wanda ya kula ya shige ɗakinsa ya rufe ƙofa ya samu guri ya zauna yayi shiru

"Waima yaushe nace wa yarinyar nan ina sonta da har za tayi min haka?"

Wayarsa ya lalubo a fusace ya nemo lambar ta ya danna kira.
Tana daga kwance ta janyo wayar tasa a kunnen ta, ai tana É—agawa Ammar ya fara masifa

"ubanwa yace miki ina sonki? Me yasa zaki je ki gayawa mahaifinki ni kike so? Ni sa'anki ne ko sa'an Auren ki ne ni? Kina jarirya da ke har kin san wani menene aure wata ƙwaila da ke, ni bani da ra'ayin auren ƙwailar mace mara aji kamar ki dan haka tun wuri ki koma ki gayawa mahaifinki kin fasa"

Sosai Mufeeda taji zafin maganganun Da Ammar ya gaya mata, jaririya! Ƙwaila! Mara aji! Dakewa tayi ta kwantar da murya tace

"Wash Allah kaina, har yanzu fa ban warke ba yaya Ammar a kwance nake, ka bari idan na warke seka gayamin abunda kake son gayamin, idan kuma na mutu shikenan ka huta"

Jikin sa ne kuma yayi sanyi, dan ya manta É—azu a yanayin da ya barta, tsaki yayi ya katse kiran ta ajiye wayar tace

"hmm Ammar kenan wannan izzar da ta kemin ɗawainiya da kai sena sauke maka ita, nice Jaririya kuma ƙwaila sena nuna maka WATA KISSAR.. Se Mata, zaka ga ƙwaila ganin idon ka"

Ta gyara kwanciyar ta, ta kwanta ta ja bargo ta rufe jikin ta.

******************

Kusan kwana uku Ammar ya kasa gayawa kowa abunda ke faruwa duk a takure yake ya rasa meke masa daÉ—i

Yau Da safe Ammar ya tashi sam babu walwala ya shiga ya gaida Umman sa fuskar sa a haÉ—e alamar bayan rashin fara'a akwai damuwa a tare da shi.

Halima ta kawo masa kayan karin kumallo ya zauna ya ɗan cakali kaɗan ya miƙe ze fita, umman sa tace
"Ammar zauna za muyi magana" ba musu ya nemi guri ya zauna

"Ammar me yake damunka ne? Kwana biyu naga sam baka walwala, ko Abincin kirki baka ci, gayamin meke faruwa ne?"

Kaman ya ƙi gaya mata, amma yaga idan yai shiru be gayawa mahaifiyar sa ba waze gayawa?
Dan haka ya zauna ya warware mata komai tunda ga hÉ—uwar sa da Mufeeda zuwa yau, murmushi tayi tace

"Masha Allah a ina ne gidan su yarinyar? "

Ammar yace "Umma ba fa sonta nake ba, yarinya ce me ƙarancin shekaru da rawar kai, tayi min yarinta da yawa ni bazan iya auren ta ba"

Umma tace
"kaga dakata, ai Addini be hana aure tsakanin ku ba, kuma ƙarancin shekaru ba'a nan zaman aure yake ba, dan haka zamu ci gaba da Addu'a, dan dama na gaji da yawan saɓani da kake samu da mahaifin ka akan rashin auren nan"

Ammar yace "haba Umma kinfi kowa sanin bana son in auri yarinya tazo ta dingamin hauka, ta rainani yarinyar nan da kaɗan tafi yayayyiya fa, nifa bana son auren yarinya ƙarama tazo ta dingamin shirme"

Kallon sa Umma tayi tare da yin murmushi tace  "yaro man kaza, kana raina ta kana ce mata jaririya se kaga jaririyar ta baka mamaki, ai duk mace mace ce komai ƙanƙantarta, da kasan baka sonta ai tun a lokacin seka gayawa mahaifin ta, ko kuwa se yanzu daka Gaya masa unguwar da kake da gidan ku sannan zaka ce baka son ta in kayi haka baka kyauta ba"

"Umma ni dai dan Allah ki sama mun mafita amma gaskiya bana son ta"
Chapter 9 · 0% Book details