Sashe 21
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda Mufeeda ta kammala gyaran gidan ta, ba wani abu da zata yi bata da tabbacin Ammar ze dawo da rana ko baze dawo ba dan haka ta gyara masa ɗakin sa ko ina tsafa se ƙamshi yake, ta samu takadda ta rubuta masa
"My love to you is endless Baby, good night, have a very sound sleep tonight i will be with you in your dreams, I Love you, mijina" ta ajiye masa a kan gadon sa
Daga nan ta nemi guri ta zauna ta fara tsifar kanta dan a ganin ta ya tsufa.
Ta fara tayi nisa a tsifar dan harta tsefe rabi taji ta gaji, ta tufke rabin data tsefe, ta ajiye tsifar tayi kwanciyar ta a falo, bacci ne ya ɗauke ta bata farka ba se ƙarfe ɗaya, ta tashi taji tana jin Yunwa dan haka ta haɗa cornflakes ta sha sannan ta tafi yin Salla.
Tayi raka'a biyu taji ana buga gate É—in, bata yanke sallar ba ta ci gaba da sallar ta, seda ta idar sannan ta É—akko Hijjabi ta tafi buÉ—ewa.
Har sun fara zage2 "wai dan wulaƙanci tana ji suna buga ƙofa amma anyi banza da su an barsu a waje"
Halima tace "wataƙila tana wani abunne"
Ta ƙaraso cikin sassanyar muryar ta tace "Waye?"
Halima tace "Mune Anty Mufeeda" ai gaba É—aya suka kalli Halima "Anty kuma?"
Mufeeda ta buɗe ƙofar, Halima ta gane a cikin su dan tazo gurin bikin ta ranar kamu da kuma dinner, ta faɗaɗa murmushin fuskarta tace "Bismillah ku shigo"
Suka shiga tai musu jagora zuwa falon ta, suna tafe suna hararar bayan ta.
Tai musu jagora har cikin falon ta, ko ina na gida ƙal da shi, se ƙamshi ne ke ratsa kafofin hancin su.
Suka nemi guri suka zauna suna kuma ƙarewa falon nata kallo a wulaƙance, Kayan kujerun ta suka kalla hakan ya tabattar musu da Mufeeda ba 'yar matsiya ta ce ba, dan kayan ta masu tsada ne.
Mufeeda tace "Sannun ku da zuwa kun kwaso rana, Yaya Halima naita sa ido inga kinzo amma baki zoba se yau ko? Nikam nayi fushi"
Halima tai murmushi tace "haba Anth Mufeeda washegarin da' ak kawo ki Umma ta bada Abinci akawo muku, har mun shirya zamu zo, na kira Yaya Ammar amma yace kar muzo bacci kike"
Mufeeda tai murmushi tace "Hmm Yaya Ammar kenan, bari in kawo muku ruwa kun kwaso rana"
Ta tashi ta tafi kitchen, ita kam fa'iza mamaki da baƙin ciki ne suka haɗu suka hana ta magana, duk yadda ake faɗin yarintar matar Ammar bata zaci zata ganta a haka ba, ga Yarinyar da kyau ga wani iyayi da take yi abun haushi.
Mufeeda ta É—akko musu ruwa da lemo me sanyi a fridge, ta É—ebo musu snacks ta kawo musu tace
"ku fara da wannan bari in shiga kitchen in É—ora muku girki"
Ta koma kitchen tana ƙoƙarin ɗora musu girki, Nasreen tace
"Ya kika ga kamun Luda yin ta, kinga dai matar Ammar"
Fa'iza tace "Nagan ta kam, amma Ammar ya bani kunya duk wannan jiji da kan nasa kalli abar da ya auro"
"ba wannan ya kamata ki duba ba, mafita ya kamata ki nema"
Halima tace "wai Yaya fa'iza me kuke yi hakane? Ya zamuzo har gidan ta ku dinga munafuncin ta"
Nasreen tace "dalla rufewa mutane baki, ina ruwanki kema munafuka wai Anty Mufeeda meye wani Anty, wallahi kin girme ta"
"to dan na girme ta ai ƙanin mahaifiya ta take aure, kuma nima ai tana bani girma na dukda haka, ni banga aibun ta ba wallahi"
Fa'iza tace "dalla ƙyaleta mu ci gaba da zancen mu"
Ana haka Mufeeda ta fito daga kitchen ta dawo tace "bari in kunna muku yv kafin abincin ya dahu"
Halima tace "to Anty Mufeeda ko in taso in kama miki wani abun ne, mun saki aiki rana tsaka"
"laa kinji Yaya halima da wani batu wai kun sani aiki ba wani aiki"
Ta tafi tana kunna tv, sarai Mufeeda ta lura da wank irin mugun kallon banzar da Fa'iza da Nasreen suke mata, Amma ta maze ta kunna tv ta dawo ta zauna tace
"nikam Halima wannan Antyn nawa ban gane taba" ta faɗa tana nuna fa'iza sanna ta nuna Nasreen tace
"har gara wannan na ganku tare ranar kamu amma na manta sunan ta, Amma ita ban gane ta ba"
Halima tace "wannan Antu Fa'iza ce, wannan kuma Anty Nasreen duk cousin's É—in Uncle Ammar ne"
Mufeeda tace "Masha Allah, Sannun ku fa"
Nasreen ta ɗan taɓe baki sannan tace "yawwa"
Mufeeda a ranta tace
"ashe cousins É—in sane, wannan wani abun ne ya kawo su, akwai wani abu a ransu, amma bari inga iya gudun ruwan su, zan É—ago inda suka dosa kafin su tafi "
Fa'iza tace "Nikam a jinki nawa akayi miki aure haka?"
Mufeeda tai murmushi tace "Jss 2 nake"
Nasreen tace "da alama kam, ke gidan ku ba'a karatu ne? Aka miki aure da ƙananun shekaru? Sekace a ƙauye"
"anayi mana nima har zan ci gaba da karatuna amma Allah beyi ba, Allah ya haɗa ni da Yaya Ammar yace na ƙarasa in muna tare tunda muna son juna baze iya jira in gama ba, kuma duk wanda yaje Islamjyya yasan origin ɗin Auren wuri, ai ba wai ɗabi'a ce ta mutanen ƙauye ba, yana da asali a addinin musulunci, bari in dubo girki na karya ƙone"
Kallon juna Fa'iza da Nasreen suka yi tare da jinjina kai.
Ta kammala dafa farar taliya dama tana da Miya, dan haka É—umama miyar kawai tayi ta zubo musu.
Ta kawo musu manyan kuloli da cokula ta ajiye, Fa'iza tace
"Ke duk wannan Abincin kika dafa? Abincin naki kuwa ze ciyu?"
Mufeeda tace "indai har Yaya Ammar zeci Abincin dana dafa to komai matsayin mutum zeci wannan Abincin, sedai kuma in mutum be niyyar ci ba, Yaya Halima sakko muci Abinci naga su Anty Nasreen ba Yunwa suke ji ba"
Halima sam bata ji DaÉ—in abunda su Nasreen É—in sukayi ba, da ta san haka za suyi da bata rako su ba, ta sakko suka kwashi girki it da Mufeeda, Nasreen taga kaji a miya kuma ranta ya biya dan haka ita ma ta sakko, ita kuwa Fa'iza se haÉ—e rai take.
Se la'asar suka shirya zasu tafi, Nasreen tace "kin san da'aka kawo ki bamu zo ganin gida ba, zo ki nuna mana, ta shiga dasu ko ina amma tai mirsisi ta hana su shiga É—akin Ammar.
Fa'iza hadda baƙaƙen maganganu Amma Mufeeda tace baza su shiga ɗakin mijin ta ba, da dai sunzo kafin akawo tane shikenan, Amma tunda Ammar ya fara kwanciya a ɗakin babu wanda ze shigar masa ɗaki ko waye kuwa.
Haka suka tafi, Halima taji daɗin abunda Mufeeda tayi sosai, ɗari Biyar ɗin da Ammar ya bata kafin ya fita ita ta takurawa Halima ta karɓa.
******************
Yauma Ammar se bayan isha'i ya shigo gidan, yauma da kaya niƙi niƙi a hannun sa ya shigo, Mufeeda tayi masa sannu da zuwa ta taya shi shiga da kayan, ya zauna a falo akan carfet ya mimmiƙe ƙafafuwan sa, dan ya gaji sosai.
Ta kawo masa ruwa me ɗan sanyi ta bashi ya karɓa ya sha, yana lumshe ido saboda gajiya.
Mufeeda ta zauna wajen ƙafafuwan sa tana ja masa yatsun ƙafan
Tace "Sannu mijin bebi" jinjina mata kai yayi yana jin daɗin yadda take jan yatsun ƙafafuwan nasa.
"Nasan kayi salla a waje, a kawo Abinci ne?"
Ammar yace "yanzun ma wani girkin kika kuma yi?"
Ta miƙe tsaye tace ina zuwa, taje kitchen ta kawo masa Abinci, ya kalli taliyar tana ta tururi a cikin flask, bece komai ba, ta zuba masa ta miƙa masa ya karɓa ya jujjuya taliyar yana kallo sannan ya fara ci, aikuwa turawa kawai yake, yaji daɗin taliyar nan sosai, gashi tunda ya fita ruwa kawai ya iya siya ya sha.
Mufeeda kallon sa take yi, tausayinsa ne ya kamata da ganin yadda yake cin Abincin kasan yana jin yunwa sosai, tun safe yake yawo a gari neman halak ba tare da ya dawo gida ya huta ba, dole duk inda ya samu yayi bacci.
Ta ture ɗankwalin kanta gefe dan zafi ya ishe ta, ya kalli kan yaga ta tsefe rabi, kitson da yake matuƙar so, ajiye fork ɗin yayi yana kallon ta, seda tace
"ya dai naga kana kallo na? Ko nayi laifi ne?"
da sauri ya basar yace
"kwashe kayan Abincin nan na ƙoshi"
Murmushi tayi masa tace "to Mijin so"
Ta kwashe kayan ta shiga ɗakin ta, ta fito da kibiya da mataji zata ci gaba da tsifa dan tuni Mufeeda ta gano Ammar yana matuƙar begen kitson kanta, wanda shi sam besan ta gane ba.
Ta fito falo ta zauna ta fara tsifa, Ammar yace "me kike yi hakane? Me yasa kike tsefewa?"
"ya tsufa ne, dama kuma na gaji da tsifar dan Allah ka tayani tsefewa" tai maganar tana miƙa masa comb.
"ke na miki kama dame saloon ne? Ta yaya zan iya wani tsefe miki kai? Ni bazan taɓa wannan ƙazamin kan naki ba, ban iya wani tsifa ba"
Tura masa baki tayi tace "Aini kaine me Saloon ɗina, kuma zaka dinga tayani tsifa wallahi ko in bar kan yaita zama a haka bazan ƙara tsefe ko guda ɗaya ba ko ze shekara"
"Saboda kin iya ƙazanta ko. Idan kuma gashin ya zube fa?"
"Shikenan na huta dama damuna yake da zafi, ji nake kaman in ɗan rage shi da almakashi aini yarinya ce Allah ze yafe min, au ni namanta ma na kulaka bayan ɗazu da safe nace zan taɓa gemunka ka hanani"
Ɗan taɓe baki Ammar yayi ya miƙe tsaye, wannan Yarinyar bata rabo da Rikici.
Ta jingina da kujera tace "Yau bazaka sha shayin naka bane? Ko so kake kayi Tumbi? Kaci Abinci fa yanzu kuma za kaje ka kwanta"
"bazan sha ba" ya bata amsa.
Har ze shiga ɗakin sa yaji tace "Mijina Dan Allah Wacece Fa'iza a family ɗinku?"
Ji yayi gaban sa ya faÉ—i ya waigo da sauri yace "kamar Yaya wace Fa'iza?"
"ÆŠazu suka zo suda Yaya Halima, mun daÉ—e dasu anan tare"