← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 64

Sashe 12

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaya Amine karki gayawa kowa, nasani Nina ke son Ammar bashi yake sona ba, Amma kullum idan na roƙi Allah abunda yafi Alkhairi se inji ina ƙara ƙaunar sa, idan na roƙi Allah ya zaɓa min abunda yake alkhairi ba son zuciya ta ba se inga al'amura na gudana yadda yakamata, ban taɓa tunanin Ammar ze amince ya kawomin kuɗin auren sa ba a haɗuwa uku rak da muka yi ba, ina da damuwowi da yakamata in tattauna da Mama ko Anty Murja amma sunfi karkata ga kushe abunda da nake so, yaya Fadeela harda wai zan auri matsiyaci ɗan napep, naso in mayar mata amma kinga ta girmeni sosai kuma Mama zata min faɗa, Amma ita soyayyar gaskiya ai ba ruwan ta da wannan, dukda Aurena da Ammar be saɓawa addini ba, Yaya Amina dan Allah ki sani a cikin Addu'arki"

Rungume Mufeeda Amina tayi tace  "Autar Baba insha Allah zan ta yaki da addua, Sannan ni har ga Allah ina sonki da Ammar dan ni banga aibunshi ba, musamman yana da nutsuwa ba irin mashiritan matasan nan bane, me ake da namiji mara aji, Ai Ammar ɗin ki yana da class ne shiyasa yawan dariya ai bashi da amfani, karki damu da ana cewa baya fara'a yana da izza wallahi indai zaki masa biyayya kiyi Amfani da wata kissar kin gama da shi, ki dena kuka kinji"

Murmushi Mufeeda tayi tace "shiyasa nake ƙaunar ki Yaya Amina"

Bayan tafiyar su Yaya Fadeela Yaya Amina bata tafi ba saboda mijin ta bezo É—aukar ta ba, Mufeeda kuma ta tafi Islamiyya.

Amina tace "Mama be kamata ki dinga biye su Yaya murja ba akan auren Mufeeda, Mama wasu suna nan saboda se sunyi boko sun bawa shekara talatin baya babu aure, Kuma abunda auta tayi na faÉ—ar aure take so ba tayi laifi ba, da kuma zuwa tayi ta É—akko muku magana fa? Mama dukkanin mu 'ya' yankine da aurar da Mufeeda cutar da itane Baba baze yadda ba, É—azu fa kuka ta tafi É—aki tana yi, bata jin daÉ—in yadda kuke kushe Ammar dan Allah mama kidena biye wa su Fadeela "

Ajiyar zuciya Mama tayi tace
"ba ƙin abun nake ba Amina Ni gani nake kaman yaron nan zata sha wuyar zama dashi ya mata girma nesa ba kusa ba, zuwan sa fa uku kacal gidan nan sam bata gaban sa ko waya banga suna yi ba"

"Mama kina tunanin akwai hijabi tsakanin mu da addu'ar kine? Tun muna yara kike mana addu'ar miji nagari, ki sawa ranki wannan shi ne mafi alkhairi a gurin auta, Mama ba kuyi tarbiyar mu akan kwaɗayi ba da son abun duniya, kuma a haka muka tashi, shiyasa kika ga Auta ma abun duniya be dame ta ba, duk abunda ta ɗaga tace tana so, to tana son sa dagaske, dan Allah mama kija Auta a jiki tun yanzu itama ki fara nuna mata zamantakewa kaman yadda muma kikayi mana, in ba haka ba ta fara iƙrarin zata fasa tunda bakya so, kuma idan ta fasa mekike tunanin za tayi gaba? "

Ajiyar zuciya Mama tayi dan jikin ta yayi sanyi tace
" hakane Amina, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, Amma ni auta da wanne ma zan fara mata ne? Ni ƙanƙantar ta nake gani, ta ina zan fara nuna mata dabarun zaman auren?"

Dariya Amina tayi tace " ta inda kika fara mana"

**************

Abokan Ammar suka tambayeshi cikakken sunan Mufeeda saboda sticker daza'ayi musu amma yace be sani ba

Aminu ya sha mamakin abunda Ammar ya faÉ—a, Jabir yace "Ammar wannan abubuwan fa da kake yawa ne, haba dan Allah ya za'ayi ace baka san cikakken sunan ta ba?"

Ammar yace "to nasani ne? Nafa gaya muku da haÉ—uwar mu a titi da saka auren nan haÉ—uwa uku ce zuwa huÉ—u rak ta yaya zan san sunan ta, nidai naji ana ce mata kome? Muneefa ko Mufeeda i thinks Mufeeda ne"

Aminu ya riƙe haɓa yace "tirƙashi yau nake ganin ikon Allah, Sunan nata ma baka sani ba, Allah kaɗai yasan dalilin daya haɗaku, Allah yasa itace maganin wannan haɗe ran naka"

Jabir yace "Ammar ka kira ta ka tambaye ta dan Allah"

Ammar ya kallesu "Allah ya kiyaye"

"to bamu mu semu kira ta"

Ammar ya miƙa musu wayar sa, Jabir ya ɗakko wayar sa ze ɗau lambar Mufeeda, Ammar yace
"ka kira ta a waya ta"

Haɗa ido Jabir suka yi da Aminu suka ƙyalƙyale da dariya
Ammar ya ƙara haɗe rai dan baya son raini.

Mufeeda kam tana kitchen tana wa Mama girkin dare wayarta ta fara ringing, tana ganin lambar Ammar jikin ta na rawa ta É—aga wayar

"Hello Yaya Ammar É—ina"

Jabir yace "Ahh yi haƙuri Amaryar mu bashi bane, fatan kina lafiya?"

Yamutsa fuska Mufeeda tayi, tace "ina Yaya Ammar É—in?"

"yi haƙuri shi yace a kiraki, cikakken sunan ki yace ki gaya mana akwai abunda za'ayi da shi"

Tura baki tayi cikin shagwaba tace "shi meyasa baze tambayeni da kansa ba? Dan Allah yana ina?"

Jabir yace "taɓ lallai abun naku nayi ne, kai ungo wayar ka"

Ammar ya haɗe rai yace "idan bazata faɗa ba shikenan ba zan karɓa ba, bana son shashanci da yarinta"

Mufeeda na iya jiyo abunda Ammar yace, ji tayi hawaye na ƙoƙarin zubo mata jiki a sanyaye tace

"Shikenan nagode sosai, jin muryarsa da nayi ya tabattar min yana lafiya nagode Allah, my regards to him"
ta kashe wayar ta.

Tausayin ta ya kama su, Aminu yace "A gaskiya Ammar ka canza salon ka, masoyi ko mahaukaci ne be cancanci wulaƙanci ba, ji yadda yarinyar nan ke murna tana ɗoki a baka waya, Amma kalli abunda kayi mata haba Ammar"

Jabir yace  "Ammar irinka idan Soyayya ta tashi kama ka ko, se mutum ya tausaya muku, irin wannan halin 'yan matan mu na Hausawa suke tsoro shiyasa basa iya nuna soyayyar su ga maza, Ammar so baya duba girma da shekaru, da yana dubawa da yayi wa Mufeeda Adalci daba ta faɗa soyayya da mutum irin ka  ba"

Sosai suka dinga caccakewa Ammar shi kuwa yayi shiru ya ƙyalesu ko uffan be ce musu ba.

*************

Daƙyar Mufeeda ta ƙarasa girkin nan ji take kaman an ɗora mata dutse a kirjin ta, bata taɓa zaton zata so wani ɗa namiji ya dinga yi mata wulaƙanci haka ba, yayin da wani sashi na zuciyar ta ke ƙara azalzalarta da ƙaunar Ammar.

Mama ce ta kira Mufeeda É—akin ta suka zauna, Mama tace
"Mufeeda ya Saurayin naki?"
Murmushi tayi ta sunkuyar da kai, Mama tace
"yaushe kuma kika fara jin kunya ta, É—ago kanki magana za muyi, naga tunda aka kawo kuÉ—in nan bezo ba meyasa? Anya kuwa yana sonki"?

Da sauri Mufeeda ta É—ago tace "yana sona mana"

"to Amma ai ya kamata ai ya dinga zuwa tunda aure zakuyi, da haka zaku fuskanci juna tunda zama zakuje kuyi na dindindin"

"Mama kin san yanayin sana'ar sa baya samun zama"

Mama tace  "dukda haka idan har kana son abu yana da kyau ka dinga zaga shi kana ganin sa, yana da kyau ya dinga zuwa yana ganin ki"

Nan Mama ta dinga yiwa mufeeda nasiha game da rayuwar aure da kuma mahimmancin haƙuri, mufeeda a ranta tace
  "Mama na kenan duk wannan abubuwan na sansu tun abaya da kike gayawa su Yaya Fadeela na haddace su, amma ta yaya zan gaya miki halin da nake ciki nasan tabbas idan na gaya miki abunda ke faruwa zaki iya soke maganar auren nan ni kuma ina ƙaunar Ammar" A zahiri kuwa shiru tayi tana sauraron Mama, seda ta gama sannan ta sallami Mufeeda.

Ammar daya koma gida yana ta tunanin maganganun su Jabir, idan ya tuna yadda tayi magana a sanyaye daga ƙarshe se yaji babu daɗi Tausayin ta ya kama shi, gefe kuma zuciyar sa tace "ai ba kai kace kana son ta ba, koma menene ita taga zata iya"
Ya zauna yana hira da Umman sa a tsakar gida, Umman sa bata da zance se tsare2 da shirin yadda bikin tilon É—anta namiji ze kasance.

Umma tace  "Ammar yaushe zaka gurin sirikata ne? Ɗazu naje kasuwa naga wata sarƙa me kyau na siyo da sauran kaya a saka mata a lefe"

Ɗan taɓe baki yayi yace
"kaman kin san tana yawan cewa a gaishe ki"

"Allah sarki yarinyar kirki, Amma baka taɓa gayamin ba, nikam Ammar ka nunamin hoton ta mana"

Be ce komai ba ya nunawa Umma hoton mufeeda akan dp ɗin ta, Umma ta karɓa tai shiru tana kallon ta a ranta tace  "tabbas yarinya ce ƙarama, Amma ina fatan ta zama mace tagari sannan sanyin idaniya ga ɗana"
A fili tace  

"tubarkallah Ammar sirikata ba dai kyau ba masha Allah, Ammar dan Allah ka riƙe yarinyar nan da Amana, jikina yana bani ita alkhairi ce a tare da kai, banda hantara da tsangwama dan Allah Ammar na san halin ka"

Halima ce ta fito daga É—aki tana faÉ—in "Umma in ganta"
Ammar ya karɓe wayar sa ya shige ɗaki ba tare da Halima ta ganta ba.

Koda Mufeeda ta koma É—akin ta, kuka ta zauna tana yi, tana goge hawaye gaba É—aya ranta babu daÉ—i, wayar ta ta janyo zata kira Yaya Ameena taga miss Calls É—in Ammar, take wani farinciki ya mamaye ta amma se wata zuciyar tace mata
"ƙila ma abokan sane suke kira bashi ba" tayi tsaki zata ajiye wayar saƙon Ammar ya shigo wayar ta

      

       "Meyasa bakya ɗaga waya?"

Kallon message É—in take yi ya kuma kiran ta, É—agawa tayi tasa a kunnen ta tayi shiru, ya saba idan ya kirata da karsashin ta take É—aga wayar sa, hakan yasa shi yin Sallama dan tabattar da ko ta É—aga, a hankali ta amsa sallamar tasa

"har yanzu baki da lafiyar ne?"

"lafiya ta ƙalau"

Ammar yace  "Meyasa na kira baki ɗaga ba"

Kawai ta fashe da kuka, tsaki Ammar yayi yace "meya haka? Meye na kuka kuma? Kinsan abunda ba naso kenan"

"Yaya Ammar ji nake kaman inje in cewa Baba na fasa Auren nan"

Maimakon yayi farinciki da abunda tace se yaji ƙirjinsa yayi mummunar bugawa da ƙarfin gaske

Cikin kuka ta cigaba da magana
Chapter 12 · 0% Book details