Sashe 13
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yaya Ammar meyasa kake wahal dani haka? Yaya Ammar ba laifi na bane da nace ina sonka, Ana ta tambaya ta me muke shiryawa game da shirin biki bani da amsa ko ganin ka kaƙi kazo inyi"
ta kasa ƙarasa maganar se fashewa da ta sake yi da kuka, shiru Ammar yayi yace
"Zaki gayamin sunan ne ko zaki cigaba da kukan?"
Cikin fushi tace "bazan faÉ—a ba É—in kuka zan cigaba, kuma Insha Allah sena dena sonka tunda baka da tausayi" ta kashe wayar ta.
Sam irin wannan matsalolin Ammar yake gudu shiyasa sam baya soyayya yake mata kallon shirita, musamman Soyayya da ƙanƙanuwar yarinya, banda wannan dalilin akwai abunda zesa yarinya ƙarama kamar Mufeeda tayi masa tsawa haka? Ƙwafa yayi ya ajiye wayar tare da jan ƙaramin tsaki
Daga baya mufeeda taga rashin kyautawar abunda tayi ta zauna ta tsarawa Ammar message ɗin ban haƙuri ta tura masa.
Yayi mamakin abunda tayi beyi zaton zata bashi haƙuri ba, maimakon yayi responding seya shareta daga nan bata ƙara neman sa ba shima kuma be ƙara neman ta ba.
Baba ya biyawa Mufeeda kuÉ—in WAEC da NECO tana ta zuwa extra lesson, duk yadda suke da Fatee da irin surutun Mufeeda bata gaya mata Ammar ya kawo kuÉ—in Aure ba.
Mazewa kawai take yi, bata jin daɗin yadda bata samun damar jin muryar Ammar, sam baya nuna damuwar sa game da ita, amma ta dake ta watsar da shi ta ci gaba da Addu'a, dukda ba ƙaramin azabtar da zuciyar ta take ba, Amma hakan baya hana ta ta tura masa saƙonin barka da safiya, barka da juma'a ko kuma saƙonin kwanciya bacci tare da yi masa addu'oin tsari.
Ammar yana gani amma baya tankawa, amma duk lokacin da ya ga saƙonin yana jin daɗi, duk lokacin daya ga tayi jinkirin turo masa saƙo ya dinga duba wayar sa kenan, Amma fa baze iya ce mata ya gode ba, ko kuma yaji daɗin ganin saƙon ba.
Mama tayi mitar tayi tambayar harta gaji akan dalilin da yasa Ammar baya zuwa, ta zuba mata ido tana taya 'yar tata da addua, dan sam ta kasa gane inda wannan al' amri ya dosa ga tana yin magana mahaifin Mufeeda zece tana sukar lamarin auren ne.
Sam walwalar Mufeeda tayi baya, duk ta rame.
Yauma tana kwance akan gadonta ta zubawa fankar dake saman É—akin ta Ido Mama ta shigo É—akin ta kalleta tace
"to seki tashi yau yaga damar zuwa, yace ai masa sallama dake"
Mufeeda najin haka ta miƙe zaune da sauri, Mama ta kalle ta ta girgiza kai, Mufeeda bata taɓa tunanin Ammar zezo ba, ba tayi zatonsa a wannan lokacin ba.
Mufeeda ta shiga ta wanke fuskarta, ta zira doguwar rigar material baƙi da ja tayi rolling da mayafi baƙi ta fesa turare ta fita.
Yau shida wani ta ganshi sunzo wanda bata san wanene ba, suna ƙofar gida a tsaye, a hankali ta ƙarasa inda suke ta kalli abokin nasa tace "ina wuni?"
Jabir ya kalleta yace "lafiya ƙalau Amaryar mu, ya haƙuri da abokin mu?"
Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.
Ammar ya lura tayi rama kome ke damunta oho? So yake su haɗa ido amma taƙi dan ƙwalla ce a idon ta, a hankali tace
"mu shiga ciki"
Jabir yace "ina nan a sha soyayya lafiya"
Hararar Jabir Ammar yayi sannan yabi bayan Mufeeda cikin takunsa na ƙasaita.
Cikin sitting room dake harabar gidan ta shiga yana biye da ita.
Gaba ɗaya ɗakin ya gauraye da ƙamshin turaren sa, Guri Ammar ya samu ya zauna, Mufeeda ta samu guri itama ta zauna.
Ba tare da ta kalle shi ba tace
 "ina wuni?"
"lafiya, ya Mutan gidan?"
Goge hawayen ta tayi tace "suna lafiya"
Ɗan ƙura mata ido yayi sannan yace "ke wai ke kuka baya baki wahala ne? Me kuma nayi miki yanzu?"
Tura baki tayi tace "ni meye ma ba kayi min ba, Yaya Ammar yaushe rabon da in ganka? In tura maka saƙo babu reply, baka kira na a waya, ji nake kaman in haƙura kowa cemin yake baka sona"
Ƙura mata ido yayi yadda take magana tana tura baki, tana shagwaɓe fuska tana wani lanƙwasa wuya kaman karta dena.
Ammar ya kalleta yace "Aini dama ban iya soyayya ba, ban san yadda ake yi ba, ke kikace kina sona, ni dama irin wannan shirmen ƙuruciyar ne bana so shiyasa nake son in auri babbar mace wadda ta gama hankali"
Murmushi tayi dukda fuskarta da guntun hawaye tace
 "Hmmm ni bani da hankali kenan?"
"ina me hankali ze zauna yaita kuka kaman ƙaramin yaro koda yake ai yarinyar ce, dan baki fi a sa zani goya ki ba"
A ranta tace aikuwa zaka ga yarinta yadda ya kamata, Sosai tayi dariya tace "daza'a goya ni da naji daɗima, dana dena kukan"
Ɗan murmushi yayi abunda bata taɓa gani yayi kenan ba, dama idan yayi murmushi yana matuƙar yin kyau haka?
Leda ya miƙa mata bata karɓa ba tace "menene wannan?"
"karɓi ki gani mana"
Hannu tasa ta karɓa, shi kuma ya miƙe ze tafi ita ma ta miƙe da sauri
"Haba Yaya Ammar mintunanka nawa zaka tafi? Ni dan Allah karka tafi yanzu"
Ɗan tsuke fuska yayi yace "Zaki fara ko?"
"Yaya Ammar yaushe zaka dawo?"
"Se wani lokacin"
"idan ka tafi seka daÉ—e baka zoba fa"
"Me zanzo inyi miki? Kallon wannan shiriritar taki da yarintar ta kokuwa?"
"Nice nake shiritar ko? Shikenan ka gaida Mama, Nagode sosai Allah ya ƙara Arziki"
Be amsa ba ya juya ze fice tace "Yaya Ammar"
Ya waigo, ta tako gaban sa, ta É—an É—auke idon ta daga kallon cikin idon sa tace
"I Love you so much My Ammar" ji yayi zuciyar sa ta shiga bugawa da sauri da sauri.
Ta raɓa ta gefen sa ta wuce
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
    *WATA KISSAR...... *
          ✨✨✨✨✨
           ( *Sai Mata* )
    Â
            Â
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞
( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.Aâœï¸
*_A SHORT LOVE STORY_*
*Story and written by*
'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''
Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba
Watpad @ Ayshercool7724
What's app 07063065680
Gmail [email protected]
  Â
ELEGANT ONLINE WRITER'S
      Â
           Page 7
Gida Mufeeda ta shige dauke da ledar da Ammar ya bata ta nufi É—akin Mama ta ajiye mata ledar
Mama tace "wannan fa?"
"shine ya bani"
Mama tasa hannu ta buɗe ledar, keyholder ne da sticker na engagement se kuma cingam da tarkacen chocolates, Mufeeda ba ƙaramin jin daɗi kyautukan nan tayi ba, ta koma ɗakin ta ta dinga murna.
Ammar kam Jabir ya sashi a gaba da tsokana
"gaskiya Ammar yarinyar nan tana da kyau tubarkallah kayi dacen mata, fatana Allah yasa ka riƙe ta amana"
Ammar yace "wannan ce matar? Anyi dacen haÉ—ani da raino dai dan banda yarinta da shiririta babu abunda ta iya"
"kai kake ganin haka, Amma ni banga ƙanƙantar nan ba da kake ta faɗa sedai tana da ƙarancin shekaru kam"
"Hmm bazaka gane ba, ni nasan halin ta, amma ina wannan 'yar yarinyar ta isa aure, yarinya ƙarama da ita sedai ayi rainon ta"
Jabir yayi dariya yace "idan aka gama rainon nata sekuma me?"
"Sekuma ƙaniyar ka" Ammar ya bashi amsa, sosai Jabir yake dariya yana son ganin yadda wannan dramar zata kaya
Mufeeda ta rubutawa Ammar saƙo
"Babyn baby naga saƙonka nagode sosai Allah ya ƙara buɗi kaman kasan ina son chocolates sosai nagode agaida Mama"
Washegari Mufeeda taje makaranta, ajinsu yayi tsit babu malami a ajin, ana rubuta sunan masu surutu kowa yaja bakin sa ya tsuke, banda Mufeeda da bakin ta yaƙi rufuwa saboda farincikin da take ciki, ta ɗakko leda ta ajiyewa Ƙawarta fatee akan cinyar ta.
Fatee ta buÉ—e leda taga sticker da key holder da yawa a ciki, ta É—akko keyholder ta karanta ganin sunan Ammar da Mufeeda a jiki yasa ta sakin wani ihu, gaba É—aya attention É—in 'yan aji ya dawo kansu, fatee tayi saurin toshe bakin ta, ta kalli Mufeeda cikin mamaki tace
"Mufeeda ni har kin fara bani tsoro, dan Allah dagaske wannan me napep É—in ne ya kawo miki kuÉ—in aure? Ke kuwa me kika yi masa haka, ya amince dake?"
Mufeeda tace "Allah ne ya haÉ—a ba wayona ko dabara ta ba"
Fatee tace "shekaru nawa aka sa?"
Mufeeda ta Harare ta tace "six months yanzu saura wata huÉ—u da rabi ma"
"Amma Mufeeda lokacin ai ko ss3 bamu shiga ba, kuma karatun naki fa? Wallahi kinyi ƙarama da Aure"
"ke kika ga nayi ƙarama, karatu kuma na cigaba a gidan Yaya Ammar, wannan ki rabawa 'yan aji"
Haka kuwa aka yi Fatee ta bi mutane ta raba musu, nan da nan aji ya É—au sowa, da hayaniya Mufeeda zata yi aure, kowa da abunda yake faÉ—a ita kuwa ta maze ta haÉ—e fuska.
***************
Gidan su Ammar suna ta shir sosai, dukda Ammar ba farinciki yake da auren ba amma yana ta ƙoƙari akan abunda ze haɗa na kayan lefe, dan baya son an kai kuɗin aure kaɗan kuma ace kayan lefe ma na kirki ya kasa samuwa, akwai wani gidan mahaifiyarsa na gado tace yaje ya gyara can ya zauna ko ya siyar a sai wani a wajen gari, haka kuwa aka yi aka saida gidan kuma yayi daraja sosai ya sai wani a wajen gari ɗan matsakaici me kyau, sauran kuɗin ya ci gaba da shirye2.