← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 64

Sashe 30

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fa'iza tace "kinji abunda nake gaya miki ko Yaya Jidda wallahi ki dinga zuwa, idan ba haka ba ana ganin ƙanƙantar ta da haka zata raba shi da kowa, tunda tun yanzu ya fara goyon bayan ta"
Jidda tace "kuma fa hakane, zanyi ƙoƙari inje gidan nasa, zan kuma yiwa umma maganar ta ja masa kunne, akan ya kula da 'yan uwan sa, dan nasan ita zata gaya masa yaji ko kuma Maryam, in be ga dama ba idan Maryam ta faɗi magana ze rusa maganar uban kowa ya ɗau tata, duk wannan masifar tasa ita baya yi mata"

Fa' iza tace "haba dai Yaya Maryam É—in?"
"ita fa, ai baya shiri da kowa a cikin mu kamar ita, indai Maryam na san abu ze hana kansa ya hana uban kowa ya bata"
Jinjina kai Fa'iza tayi, a ranta tace "dole inje in ziga Yaya Maryam itama, zata taimaka min"
Suka ci gaba da hirar su daga nan suka yi sallama.

A hanya Fa'iza tana tafe tana zancen zuci akan ya zata ɓullowa lamarin Ammar, taji ana mata horn tsayawa tayi ta juya, me motar yazo dai2 inda take sannan ya sauke baƙin gashin motar yace
"Manya maganin ƙanana, ke kuwa talaka na ganin ki"
Murmushi tayi tace "Ba gashi ka ganni ba, yaushe rabon da in ganka?"

"Shigo motar se muyi magana" ba musu ta zagaya ta buÉ—e gaban motar ta shige.
Ya kalleta yace "Ni ko a bikin Ammar ban ganki ba ina kika shiga haka?"
Tsaki ta É—anyi tace

"me zanje inyi masa a gurin bikin, dan abun kunya kuna gani kuka barshi ya auri wannan 'yar mitsitsiyar Yarinyar, bayan a duniya ya tsani Auren ƙaramar Yarinya"

"kinfi kowa sanin Halin sa ɗan uwan ku ne, ke zaki gayawa wani halinsa, shekaranjiya na haɗu da shi da matar tasa ya kaita Asibiti se zuba shagwaba take yi, Wallahi Yarinyar nan za tayi saurin tafiya da Imani namiji, duk jin kan Ammar lallaɓa ta yake ranar, ina ga ko ciki ne da ita "

Wani dogon tsaki ta ja tace
"dan Allah ka dena ɓata min rai, dan abun kunya 'yar wannan Yarinyar Ammar zewa ciki, mtseww"

Dariya sosai Faruk yayi yace "Kai
Fa' iza, to shi kna ruwan sa, Wallahi tun ranar ɗaurin Aure da naga yarinyar nan na kasa samun nutsuwa, wallahi dana ga Yarinyar nan kafin bikin su da bazan taɓa bari Ammar ya aure ta ba, Idan naga Yadda take wa Ammar shagwaba wani irin kishi ne yake kamani, Wallahi ina jin ƙaunar yarinyar nan har a cikin zuciya ta"

Wani irin Murmushi Fa'iza tayi tace "dagaske kana son ta"
"Wallahi Fa'iza ina mata so bana wasa ba, ni ko ban Aure ta ba kawai dai in same ta, kin gane ai balle ma ina son in Aure ta, wallahi tunda naganta mata ta dena birgeni"

Jinjina kai tayi tace
"Me ze hana mu haÉ—a kai mu taimaki juna?"

Ya gyara zama yace "kamar Yaya kenan?"
Murmushi tayi tace "zamuyi waya"

********************

Kasa nutsuwa Yaya Jidda tayi, dan haka ta tambayi mijin ta zata fita unguwa, shiryawa tayi ta tafi gidan su Ammar.

Koda Mufeeda ta buɗewa Jidda ƙofa taga kammanin ta da Ammar, sannu da zuwa tayi mata tai mata iso ciki, wani irin kallon banza take bin Mufeeda dashi.

Tun kafin Jidda ta shiga falon idon ta ya sauka akan jibgin kayan Abincin dake ɗakin tsakar gida, tayi ƙwafa suka shiga falon.

Ta kalli Mufeeda tace
"Ina Ammar É—in?"
"be daÉ—e da fita ba kuma, yana gida tun É—azu, amma se in kira shi a waya"

"Ammar É—in da yake fita tun farar Safiya shine yake zaune a gida har bayan azahar sannan ya fita"

Shiru Mufeeda tayi tace "bari in kawo miki ruwa"

"Ke dawo bana son gulma, ni bazan sha ruwan ki ba, sannan ki buɗe kunne da kyau ki jini, Wallahi daga yau idan wani daga dangin mu yazo kika kuma masa wulaƙanci sekin bar gidan nan dan baze yuwu ba, 'yar mitsitsiya dake kin san wulaƙanci, su Fa' iza sa'anin kine da zasu zo ki musu rashin mutunci, ko gidan uban kine? "

Mufeeda ta girgiza mata kai alamar A'a, Mufeeda a ranta tace" wannan ce Jidda kenan? "

" to ko yanzu yai niyya ze iya sakinki ya auri wata, 'yan uwa kuwa ba' a canza su, ance miyar ki hadda kaji alhalin be kaiwa namu iyayen ba, shafaffiya da mai, ni ina tunanin kin haɗawa Ammar da ƙulumboto dan Ammar ba sakaran namijj bane, daga zuwan ki ki kainainaye shi, kalli uban kayan Abincin daya tile miki a ɗaki, Amma iyayen mu ko oho, se anyi magana yace bashi da kuɗi ina ya samu kuɗin daya siya miki wannan kayan haka? Algunguma baki isa ki rabamu dashi ba"

Jidda taiwa Mufeeda cin mutunci tsaf, Sam Mufeeda bata tanka mata ba, se dai zuciyar Mufeeda kaman ta fashe, ga Jidda ta girme ta sosai balle tace zata rama.

Seda ta gama sannan ta tashi ta tafi, bayan tafiyar ta se da Mufeeda tayi kuka dan ba ƙaramin jin zafin abunda Jidda tayi mata tai ba.

Ammar ne ya dawo ya tarar da ita a falo, ba haka ya saba ganin ta haka ba in ya dawo, amma ya basar ya miƙo mata leda yace

"gwada wannan takalmin in gani É—azu na ganshi yayi kyau na siyo miki"

Ƙoƙarin maida hawayen idon ta take, Ammar ya ga idon ta da ƙwalla, ya ɗan haɗe rai yace
"kukan me kike yi?"

"bakomai bafa kuka nake ba"

"bana son ƙarya, meke damunki?"

"bana jin daÉ—i ne"

A fusace yace "ƙarya kike lafiyar ki ƙalau, meya same ki? Bana son ƙarya"

Domin sharhi, gyara ko shawara
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

                  

                        Page 16

Ƙura mata ido yayi, a hankali tace "bafa wani abun damuwa bane, radio nake ji aka faɗi wani labari daya bani tausayi, shikenan fa bari in gwada takalmin nan dan tun kan isa na hango ƙafa ta tayi cif a ciki"

Ammar yabi Mufeeda da kallo ba dan ya yadda da abunda tace ba, amma ƙiri ƙiri ta basar da zancen ta karɓi takalmin ta saka, na zaman tsakar gida ne amma kalar pink ne me tudu yayi kyau sosai, ta miƙe ta ɗanyi juyi tace
"yaka gani yayi min kyau kuwa?"
GyaÉ—a mata kai yayi,
tace "Nagode mijina Allah ya baka gidan Aljanna"
"Ameen ya Allah"

*****************

"Maman Sadiq maƙociyarki me kallon gidan ki ta shigo miki kuwa? "

Maman sadik tace "Hmm ta shigo min maman Amir ke kin ganta wata 'yar yarinya da ita, amma mijin ta baki ganshi ba ƙato da shi, ni ba dan na ganta kalar wayayyu ba da cewa zanyi a ƙauye ya auro ta"

ÆŠayar tace "dan Allah ta shigo muku? Ranar da ta shigo muku ina ga bana nan, kaddai' yar Yarinyar da naga ya sata a a daidaita sahun sa ce matar?"

Maman Amir tace "Wallahi itace maman Nur"

"Taɓɗijan niko zanso in ƙara ganin ta"

Maman Sadiq tace "ke kina ganin ta 'yar Yarinya se shegen ji da kai, watan ta guda a unguwar nan fa sannan ta shigo mana, tana wani jin kai a gurguje ta tafi, nace kin gamin yarinya da kinibibi,' yar da da auren wuri aka min na haifeta"

Maman Nur tace "Kedai bari da mijin nata wata tsiyar ne da shi da ta É—aga mana kai, amma duk layin nan shi ne matsiyaci É—an adaidaita sahu ne fa"

Maman Ameer tace "kema dai kya faÉ—a"

Maman Sadiq tace "Maman Nur ya kamata akaiwa maƙociyar tamu ƙyallen Ankon sunan ki na haihuwa"

Maman Amir tace "wallahi kuwa mu kai mata muga meza tace"

Maman Nur tace "haka za'ayi ɗakko ƙyallen muje"

Suka ɗakko ƙyallen Atamfa suka nufi gidan Mufeeda.

Tana tsakar gida tana aikace aikacenta aka buga ƙofa cikin ƙaramar Muryar ta tace
"waye?"
Suka amsa da "mune".

Ta buɗe musu ƙofa suka shigo, tun daga tsakar gidan suka fara ƙarewa gidan nata kallo basu yi zaton cikin gidan ta yana da kyau haka ba.

Tai musu iso cikin falon ta suka gaisa, ta kawo musu ruwa da É—an abun motsa baki na garar ta, nan suka dinga ci suna zuba surutu, ita dai Mufeeda sam bata da saurin sake wa da mutane dan haka sedai ta kallesu tayi murmushi kawai.

Can maman Amir tace "yawwa Mufeeda dama ƙyallen ankon sunan Maman Nur ne muka kawo miki ko mai gidan ze sai miki"

Mufeeda ta karɓi ƙyallen ta gani tai murmushi ta miƙa musu tace

"Aikuwa Atamfar tayi kyau sosai, se dai ni da ban daɗe da Aure ba kayan lefe na na nan ko taɓawa banyi ba, sedai ince Allah ya rabaki da cikin lafiya, idan kika haihu zan sako abunda Allah ya horemin in shigo inyi miki barka"

ÆŠan buÉ—e baki maman Nur tayi tace "kodai me gidan ne baze miki ba, amma Atamfar fa babu tsada dubu biyar ce fa"

Mufeeda tace "Anty kenan aike yanzu kinfi buƙatar Addu'a fiye da wannan Atamfar, kuma insha Allah zan saki a Addu'a Allah ya raba ki da cikin nan lafiya"
Chapter 30 · 0% Book details