Sashe 37
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har Ammar ya kammala shirin sa ya fice be kuma ganin ta ba, shima da ya fita be dawo gida ba se bayan magariba, bayan magariban ma daya dawo bega Mufeeda ba, ta ajiye masa duk abunda ya kamata wanda ze buƙata, amma bata falon.
*************
Washegari bayan fitar Ammar sannan Mufeeda ta fito falon, ta kammala ayyukan gidan ta zata ɗora girki amma taga bata da kayan miya, gashi bata kula Ammar ba balle ta gaya masa babu kayan miya, shiryawa tayi ta fita yin cefane, tunda ta fito kan babban layin taga Wata ƙatuwar Mota tana binta, bata kawo komai a ranta ba ta cigaba da tafiya.
Taje gurin Sa'idu me kayan miya domin Siyayyar kayan miyan, Sa'idu yace
"ko kece Amaryar kusa da gidan Maman Nur?"
"Eh Nice" ta bashi amsa a taƙaice.
"Allah sarki, da alama naga ke ba irin halinku É—aya ba, kina da nutsuwa da hankali, amma yakamata ki kula sosai kiyi taka tsantsan dasu dan basu da kirki sam basu san ciwon kansu ba"
"to ni jna ruwa na? Ko tambayar ka nayi?"
"A'a naga kina da nutsuwa ne, shiyasa nace bari in miki magana kiyi hankali da su"
"Malam dan Allah bana buƙatar jin wannan maganganun naka, ka sallameni in tafi dan Allah"
"to shikenan, amma ni gaskiya na gaya miki"
Tsaki Mufeeda tayi ta karɓi kayan miyan ta tace
"Riƙe gaskiyar ka bana so" tai gaba abunta.
Biyo bayan ta me motar nan ya ci gaba dayi yana mata horn, juyowa tayi domin ganin dalilin da yasa ake mata horn bayan ta bashi hanyar daze wuce.
Parking me motar yayi, me ya buɗe murfin Motar ya fito, Babban Mutum ne a ƙalla ze shekara Arba'in da biyar, ya ƙaraso inda Mufeeda take yana wani ƙarama ta kallo yana murmushi, Sanye take da dogon Hijjabi tun daga Sama har ƙasa, ya gyara tsayuwar sa yace
"Baby tun ɗazu nake binki, ina ƙoƙarin yi miki magana amma ban samu dama ba"
Banza tayi masa tana ƙoƙarin wucewa, Ya kuma shan gaban ta kaman zasu haɗe yace "Haba 'Yar kyakywa, ya ina miki magana kinƙi saurara ta, ki tsaya kiji dame nazo mana"
"Malam meye hakane? Nifa matar Aure ce ka dena bi na dan Allah"
Kallon ta yayi daga Sama har ƙasa yace"Ke ɗince matar Aure? Nima ai mijin Aure ne, dan Allah ki bani lokacin ki two minutes kawai Beb, Akwai saƙo me girma da nake ɗauke dashi daga zuciya ta zuwa gare ki dan Allah ki saurareni mana, Kyakywar Baby kamar ki nasan bazaki wuce your sixteen age ba, baki dace da tafiya a wannan ranar ba"
A fusace ta kalle shi tace "Tir da Wannan saƙon naka, mara mutunci Ka kiyaye ni na gaya maka ina da Aure dan me zaka dinga bina haka? Wallahi zan maka tijara in taraka mutane a gurin nan na gaya maka, dalla ban hanya wuce dattijon banza kawai, wanda be san darajar Aure ba"
Ganin Mufeeda ta haƙiƙance ne yasa ya bata hanya karta tara masa jama'a, aikuwa da gudu2 sauri2 ta ƙarasa gida se haki take.
Duk abun nan daya faru akan idon Sa'idu me kayan miya, riƙe baki yai yana jinjina kai, Yace
"Au dama duk ustazancin nata na ƙarya ne, ance me Napep ne mijin ta me kuma ya haɗa ta da wannan me motar? Taɓɗijan mata na abunda suke so a duniya, Fuska biyu da rana tsaka lallai yau akwai zazzafar Jarida a majalissa" Nan ya ci gaba da ƙanan surutan sa.
Koda ta koma gida, mita ta ci gaba dayi da mamakin maganganun wannan shashashan mutumin mara mutunci, Seda tayi salla ta huta sannan ta É—ora girki, loka2 idan ta tuna abunda mutumin nan yai mata ta kan yi tsaki.
Sosai take missing É—in Ammar, tayi kewar murmushin sa, da sauran NishaÉ—in da yakan sata, amma idan ta tuna abunda Zainab ta dingayi masa ranar, da kuma Yadda take kiran sa a waya se haushi ya kamata.
Yauma ya gaji sosai bayan isha'i ya dawo gida, gaba É—aya kwanakin nan da Mufeeda ta watsar da shi se yaga gidan yayi masa faÉ—i, gidan baya masa daÉ—i, kosan fitowa falon ba yayi ko Abincin ya fara ci se yaji baya masa daÉ—in ci, gashi yanzu duk wanda ze bashi Abinci inba na gidan sa ba ba yajin daÉ—in sa.
Abunda yake ƙara bashi mamaki be wuce Yadda take takatsan tsan gurin kiyaye ɓacin ransa ba, Amma ƙiri Ƙiri tayi masa laifi amma ta maze tana fushi, to zuwa ze ya rarrashe ta ko kuwa?
Wata zuciyar tace "kai aikuwa daka faɗo wannan 'yar Yarinyar zaka bawa haƙuri, ita fa tayi maka laifi"
Wata zuciyar kuma tace masa "But at least ya kamata kasan halin da take ciki" haka yaita saƙe2 a ransa.
Seda yayi Sallar isha, har ya zauna ze ci Abincin ya fasa ya miƙe ya nufi ɗakin ta, ya tarar da ita tana zaune a tsakiyar gado tana wasa da gashin kanta data tsefe, yai Sallama ta amsa ba tare da ta kalle shi ba, tunda ya shigo ɗakin yaji yana tashin wani sasanyan ƙashi me daɗin gaske.
Ya tako a hankali ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita, yayin da ta maze ta basar dashi kaman yadda yake mata a wasu lokutan idan yana fushi da ita.
"Wai Fushin me kike yi hakane?"
"Bakomai" ta bashi Amsa
"Kin min laifi kin koma kina fushi, Allah ya shiryeki, tashi muje kici Abinci"
"Ni na ƙoshi"
Haɗe rai yayi ya ƙura mata ido, juyawa tayi ta sakko daga kan gadon tana tura baki, ta fice falo.
É—an girgiza kai yayi yabi bayan ta.
Ammar ya takura ta ta dinga cin Abincin nan badan ranta yana so ba dan har ƙwalla tayi, yace idan tai masa kuka ze ɓata mata rai sosai.
Suna cikin haka Wayar sa ta fara ringing, Idonta ya sauka akan Sunan Fa'iza da ke screen ɗin ƙaramar wayar sa, miƙewa Yayi ya tafi ɗakin sa Amsa wayar.
A É—an hasale ya É—aga wayar yace
"Ke lafiya kike kirana yanzu? Meye hakan kikayi?"
"Bakomai Yaya Ammar bugowa nayi in kwashi gaisuwa kawai, Sannan kwana biyu baka zo gidan mu ba"
"Abunda zaki gayamin kenan ya hana ki kirani tun rana?"
"to ai nasan lokacin kana aiki"
"Yanzu kuma ina hutawa ne, karki ƙaramin haka na gaya miki" yayi tsaki tare da kashe wayar sa yace
"Wannan wace irin takura ce? Mutum yayi Auren ma be huta ba? Da suke damuna da kira ni ina naga halin kuma Auren wata macen? Yanzun ma inji da rigimar wadda nake tare da ita mana" yai ta mita ya fito falo
Koda ya dawo falon ya tarar bata nan, Kwanukan yadda ya tashi ya barsu haka itama ta barsu a gurin, shi ya tattare Kwanukan ya kai kitchen, ya tsaya yana wankewa dan ya lura bata barin ko cokali ya kwana bata wanke ba.
Yana kammala wanke wanken akan ɗauke wuta, harze wuce ɗakin sa ya ƙyaleta ya jiyo sheshsheƙar kukan ta ta Window.
Ƙofar ɗakin ta ya tura ya shiga, ya kunna fitilar ƙaramar wayar sa ya haske ta, duk tayi jifa da fulullukan dake kan gadon ta, ta baje gashin kanta se sheshsheƙar kuka take, haushi ne ya kama shi, daze balbaleta da Masifa se ya tuna tunda suke bata taɓa masa makamancin haka ba, idan har ya ƙyaleta a haka be kyauta ba gata Yarinya ƙarama.
(Gareku Maza, ya kamata a dinga yiwa Mata Uzuri a wasu lokutan, idan har ya kasance mace tana kaman ta kyautatawa, wani lokacin ta birki ce saboda ɓacin rai ayi haƙuri a kai zuciya nesa, kar kace zaka hau ka ƙara mata tension, ka danne taka damuwar hankalin ta ya kwanta tukuna)
Ammar yaje ya kwaso fulullukan da tayi watsi dasu a ƙasa ya mayar da su kan gadon sannan ya hau gadon.
zuba mata idanu Yayi yana haskata yama rasa ta ina ze fara.
Gajiya tai da kallon da yake mata, ta zame ta kwanta ta juya masa baya, kashe fitilar wayar Yayi shima ya kwanta ya matsa kusa da ita dai dai Kunnen ta Yace
"Waike wace irin rigimammiya ce haka? Kinmin laifi baki bani haƙuri ba, kika fasa min waya bayan baki san da wa nake waya ba"
Gaba É—aya jinta tayi wani iri Yadda suke kwance a guri É—aya yake mata magana.
Ta dake tace
"Nasani mana, da 'yan mata kake waya"
"Shine kike fushi dan nayi Waya da
'yan Mata? Ai bani na kira su ba, su suka kirani fa"
Banza tayi masa ta ƙara matsawa gaba.
Aikuwa Ammar ya ƙulu yasa hannu ya fizgota yace
"Ni kike wa wulaƙanci dan ina lallaɓa ki, ranar da nake Waya da Maryam nake magana, kije kiyi abunda kika ga dama"
Jiki a sanyaye ta riƙe Hannun sa
"Yaya Ammar ɗina, Nasan nayi maka laifi amma ban san a wannan karon me yasa na kasa haƙuri in karɓi laifina ba, Yaya Ammar ina shiga damuwa idan naga wata ta raɓeka, ina iya jure komai amma banda wannan, dan Allah kayi haƙuri bazan ƙara ba, Wayar ka ma dana Fasa kayi haƙuri please, ka karɓi tawa kasa layin ka seka bani ƙaramar in riƙe, kayi haƙuri kaji "
" bana son wayar ki, ai bani na sai miki ba"
"Eh nidai naji ka karɓi tawa please"
Shiru Yayi bece mata komai ba yama rufe idon sa, miƙewa Zaune tayi tace
"Dan Allah Yaya Ammar badan halina ba, kayi haƙuri Insha Allah ko dawa zakayi waya bazan ƙara maka haka ba, yanzun ma sharrin sheɗan ne"
tai maganar tana riƙe hannun sa, ɗisar Hawayen ta yaji a hannun sa ya ɗan kalleta, dukda a duhu ne tayi kalar tausayi, tayi regretting har zuciyar ta.
A hankali ya janyo ta jikin sa yana taɓa gashin kanta dake matuƙar birge shi, amma bece mata komai ba.