← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 64

Sashe 35

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammar baya falo ta nufi kitchen da sauri ta tarar, ya dafa tea ya zuba a flask ya shirya komai kaman yadda take yi, fitowa tayi tsakar gida ta tarar ya haÉ—a kan kayan sa da nata ya wanke, duk ya shanya yana wanke adaidaita sahunsa.

Da sauri ta nufi inda yake tace "Yaya Ammar dan Allah kayi haƙuri, ban san ya'akayi ban tashi da wuri ba yau"

"to ni nace kinyi laifi ne?"

"A'a amma bekamata ace kai kayi aikin gida ba yau"

ÆŠan kallon ta yayi ya É—auke kansa ya ci gaba da aikin da yake yi, rigar bacci ce a jikin ta iya gwiwar ta.

"Allah dai yasaka maka da Aljanna mijin so, har wanki kayi mana ni har kunya nake ji idan naga ka wanke min kaya na, ni yakamata in wanke naka"

Ya É—ago ya kalle ta yace "Nakin ma in kin wanke ba fita za suyi ba, balle ki wanke nawa"
Murmushi tayi tace "bari inzo in tayaka wankewa"

"No nagode kije kiyi breakfast É—inki rana tayi"

Ƙarasawa tayi ta riƙe duster da yake goge ruwan jikin Napep ɗin tace

"My love wai baka son in dinga samun ladane? Komai seka hanani yi"

"Aike ba afara baki lada ba, in kinyi abun kirki sedai a rubutawa su Mama"

Wani irin kallo tayi masa, wanda seda ya sashi yin murmushi be shirya ba yace
"Au Sorry namanta ashe fa ta isa afara rubuta mata lada da zunubi, ni shedane ma"

Zumɓura baki tayi tana kallon sa, aikin sa ya cigaba da yi, ya ɗago yaga still tana tsaye
"waiba cewa nayi kije ki karya bane?"

Juyawa tayi ta koma, taje ta zauna ta karya, seda ta gama sannan ya shigo falon ya kalleta yace

"Prof a haÉ—a min ruwa zanyi wanka"

Ba tace komai ba ta miƙe, taje kitchen ta ɗakko ruwan zafi ta shiga ɗakin sa, ya tuɓe gajeren wando ne a jikin sa, ya tsuguna a hanyar da zata wuce yana duba wani abu, ɗagowa yayi ya kalleta yace
"Wuce mana"
Se wani Sunkuyar da kai take kamar mara gaskiya.

Ta wuce shi ta shiga toilet, ta haÉ—a masa har zata fito yace
"tsaya inzo in duba, nafi son shi da zafi sosai"

Sauri take ta fito daga banɗakin ta bashi guri, amma ya riga ya shiga, ya kalli ruwan yaga yana tururi ya taɓa yaji da zafi, ya ɗago ze mata magana yaga tana ta sunkuyar da kai bata son kallon sa.

"duba kan Mirror ki bani sabulu"

Da gudu gudu ta fice daga banɗakin dan a matuƙar tsorace take, Ammar yana kallon yanayin ta, da ta ɗakko sabulun ƙofar toilet ɗin taje ta tsaya, kaman za tayi kuka ta ɗan zira sabulun tace
"gashi"

"Idan ba zaki miƙomin ba ki mayar bana so"

"to ai gashi ina miƙo maka"

Shammatarta yayi ya janyo ta cikin banÉ—akin.

A firgice tace "Wayyo Allah na Mama"

Ya riƙo ta gam yana kallon ta, gaba ɗaya a firgice take, jikin Ammar lulluɓe yake da gashi, ƙato ne na gaske, jikin sa a murɗe yake, kallo ɗaya zaka masa kasan ƙaƙƙarfan Namiji ne.

A hankali yace "wai meye hakane?, se wani sunkuyar da kai kike kaman kinga abun tsoro?"

Zazzare ido take tana ta sauke numfashi,

"Dan Allah Yaya Ammar ka cikani kayi wankan ka, ni bana son ganinka a haka"

"Meye ba kyason ganin?"

"dan Allah ka cikani"

Hannu yasa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, Kaman yayi dariya yadda take rarraba ido, amma ya maze yace
"Ki jirani a É—akin nan, idan kuma kika sake kika tafi nida kene"

Haka ta fito ta zauna a gefen gadonsa tana maida numfashi.

Ammar ya daÉ—e sannan ya fito, yana fitowa kaman É—azu ta É—auke idon ta daga kansa, basarwa yayi yaje ya ci gaba da shirin sa, juya masa baya tayi ta rintse idon ta ita a dole karta kalle shi.

"taso kizo"
Ta juyo a hankali taga ya saka dogon wando da shirt, tasowa tayi ta nufi inda yake tana raɓe raɓe, ya dube ta yace
"Mara kunya kawai, lokacin da kike yawo da underwear da nace kidena cewa kika yi sedai a raba falo, shine yau kike wani sinne kai, to ai nan É—akina ne dole insa abunda nake so"

Zumɓura baki tayi, yace
"ni kike zumɓurawa baki?"

Da sauri ta girgiza kai tace "Nifa ba zumɓura baki nake ba"

"ƙarya nayi kenan?"

Da sauri ta girgiza kai tace
"A'a yi haƙuri"

Mufeeda akwai bada haƙuri, da ance tayi laifi za tace Allah ya bada haƙuri.

"zo nan ki zauna" ya nuna mata bakin gado.
Ta ƙarasa taje ta zauna, ya durƙusa ya buɗe drower ɗin jikin Mudubinsa ya fito da wata leda.

Wata jaka ce silver me matuƙar kyau ya ciro ya miƙo mata, yace

"Wannan ce Jakar da kika saka a status É—inki?"

Zare ido tayi tace "Amma Yaya Ammar ai ba cewa nayi ka saimin ba"

"tambayar ki nayi itace?"

Jinjina masa kai tayi alamar Eh, idon ta cike da hawaye.

Ammar Yace
"to gata nan a kashe lafiya, lokacin da kika saka bani da kuÉ—in ta ne, Amma a kwanan nan Alhamdilillah idan na fita ina samun ciniki sosai"

Kasa magana tayi, kawai ta faÉ—a jikin sa ta rungume shi
"Allah ya biya ka da Aljanna mijina, Allah ya ƙara sutura da Arziki, Allah ya ƙara wa su Umma lafiya da nisan kwana, nagode, nagode"
Ji yayi kaman ya rungume ta sosai, se ya tuna za'a iya samun matsala dan haka yace
"to sarkin kuka, ke komai ma sekin masa kuka, godiyar ta isa haka"
Girgiza kai tayi tace

"ai babu kalaman da zanyi Amfani dasu da zasu nuna godiya ta a gare ka Hubby na"

"Wai kin gama jin tsoron nawane  da kika rungume ni? Mara kunya"

Cikashi tayi tana rufe ido, haka suka yi sallama ya fita.

Abunda ta lura shi ne duk lokacin da tayi wa Ammar wani abu da ya ji dadi baze nuna mata ya ji dadi ba, sedai zeta ƙoƙarin yi mata kyauta, ko wani abu da zeta farinciki.

Kamar yadda ya mata Alƙawari sati ya zagayo, ta shirya ya kaita taga gida,
Kaman Yadda Mufeeda ta tsara a ranar suka shirya zasu haÉ—u da yayyen ta a gida.

Ammar ya shiga da niyyar su gaisa dasu Baba, ya shiga ya gaida Baba, sun daɗe suna hira da Baba sannan ya fito ya shiga falon Mama, Su Yaya Fadeela, Anty Murja da Yaya Amina duk suna falon, Ammar ya shigo har ƙasa ya durƙusa ya gaida Mama
Mama tace

"Sannu Ammar ya gida, ya haƙuri da Auta?"
Murmushi yayi yace "Alhamdilillah"

Suka gaisa da su Anty Murja ma, an ɗan taɓa hira da shi kaɗan, yace ze tafi, Mufeeda ta tashi ta bi bayan sa

Seda sukace gareji tace
"Hubby yaushe zaka dawo mu tafi?"

"Se magariba insha Allah, yau ki huta sosai a gida"

Tai murmushi tace
"to ya za'ayi da Abincin rana fa?"

"Don't mind me, sena dawo É—aukar ki"

"Shikenan I will miss you for the whole day Honey, take a good care of yourself"

Juyawa yayi yana murmushi ya fice.

Ta koma cikin gidan, tana zuwa Yaya Fadeela tace
"Shegiya Auta se da kika samu jakar nan, waye ya saimiki?"

"Mijina mana"

Yaya Amina tace
"kai Auta Jakar nan fa da tsada amma kika takura masa ya saimiki"

"Yaya Amina kema kin san bazan takura masa ba, gani yai na É—ora a status, kawai shekaranjiya ya bani"

Anty murja tace "Lallai 'yar gatan miji, gwangwajewa, kuma dan Allah yana sakin jiki ya miki hira? Baya son Magana"

"Nida sauran Mutane É—aya ne da ba zamuyi hira ba?"

Yaya Fadeela tace "Oh ni Fadeela Allah rahimi, wai yau Autace a cikin mu ake hirar miji dake, Allah me iko"

Nan suka dinga hirar yaushe rabo, daga Auren ta zuwa yanzu ta ƙara ƙiba sosai kamar ba ita ba.

Cikin hikima Mama take bugun cikin Mufeeda don taji yanayin zaman ta da Ammar, amma yadda Mufeeda ke mata bayani ya tabattar mata Mufeeda na cikin kwanciyar hankali.
Mama tace
"Mufeeda mijin ki akwai tsatstsauran ra'ayi, ranar da yazo gidan nan ya gaishe mu, na bashi bushashshen kifi da Nono da aka kawo daga munjibir ya kawo miki, amma yaƙi karɓa wai basu kawo ba baze karɓe mana ba"

Mufeeda tace "to aini be gayamin yazo gidan nan ba"

"Yazo ya gaishe mu, ya kawo mana kayan miya fal"

"hmm be gayamin ba, Haka halin sa yake baya son aga gazawarsa ta ko ina, inaga ranar ne ya zomin da ƙaton kwalin madara, ko a zaton sa nina tambayeki"

"aini yaron ya birgeni, haka ake son magidanci ya zama me wadatar zuci, sannan kema tunda kinsan halinsa ki kiyaye duk wani abu da zakiyi daze nuna ya gaza miki a wani abun"

"Insha Allah Mama zan kula, kuma kinsan ni bame kwaÉ—ayi bace"

"hakane amma duk da haka ya kamata ace na ƙara gayamiki"

Mufeeda ta tafi gurin Baba, nan ma ta shan take sukaita hira da mahaifinta wadda ke nuna yadda suka yi kewar juna, seda Baba ze fita da azahar sannan ta baro É—akin sa.

Gurin su Anty murja ta koma suka ci gaba da hirarsu, taji daɗin haɗuwa da 'yan uwan ta yau, Ga masu ƙaramin ciki ga ƙananan yara haka aka dinga ɗora tukunya ana saukewa, Mama tasha hidima da' ya'yanta da kuma jikokin ta.

Ammar be dawo ba se bayan isha'i yazo É—aukar Mufeeda, Mama tace aje ace masa "ya shigo yaci Abinci sannan su tafi"

Bahaka yaso ba dan yana matuƙar jin kunya, haka ya shiga sitting room ya zauna, Mufeeda ta kai masa Abinci.

Ammar yace "Nifa gaskiya inajin nauyi inci Abincin nan anan, kizo mu tafi gida se inci a can"

HaÉ—e rai tayi tace "nice mara kunya da naje gidan Umma har na zage na dafa na ci ko, Bansan me yasa kake haka ba Yaya Ammar, Iyayena É—a suka É—auke ka ba sirirki ba, kaman Yanda su Umma suka É—aukeni 'ya, basa jin daÉ—in yadda kake yi É—in nan fa"

Ɗan Ajiyar zuciya yayi yace "bahaka bane, ni tun asali irin wannan yana bani wahala, kuma ina matuƙar jin nauyin su ne, ba wani dalili yasa nake hakan ba"
Chapter 35 · 0% Book details