← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 64

Sashe 8

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarfe takwas na safe ya farka daga bacci ya ɗakko wayar sa yana duba saƙonni.
Message ɗin Mufeeda yaci karo da shi a what's App ɗin sa kafin ya buɗe message din ya buɗe hoton kan dp ɗin ta, itace akan dp ɗin da kayan dinner ɗin yayar ta, tana sanye material maroon, tayi kyau matuƙa.

Ɗan taɓe baki yayi ya buɗe voice message ɗin

"Yaya Ammar É—ina bani da lafiya, kaman zan mutu nake ji, narasa me ke mun daÉ—i kamin Addu'a dan Allah"

Shiru yayi yana kuma kunna message ɗin yana ƙoƙarin gane da gaske take yi ko kuwa dai wani abun take shiryawa, tsaki yayi ya ajiye wayarsa ya fita yai brush ya yi breakfast ya ɗau babur ɗin sa ya fice.

Seda Mufeeda ta kwana huɗu a Asibiti, likita ya tabbatar musu typhoid da malaria ke damun ta, da yake Asibitin kuɗi ne, kusan duk seda likitoci da Nurses ɗin Asibitin suka santa, kullum cikin kuka take, ko ya taji ciwo se kuka, idan Mama ta takura ta taci Abinci se ta hau kuka, idan akazo Allura kuwa ba ƙaramin dambe ake sha da ita ba, ga rashin son magani taɓara daban2 kafin a sallame su, Baba ne ke lallaɓa abarsa Mama kam kusan dukan ta take yi.

Aka sallame su da sauran magungunan su suka tafi gida, Alluran da akai mata suna da ƙarfi saboda ta sha wahala, dan haka tun kan suje gida take cewa bacci take ji, suna zuwa gida ɗakin ta fes mama ta gyara.

Bata fara neman komai ba se wayar ta, ta kunna tana sa ran ganin saƙon Ammar kona ya jiki ne amma bata ga komai ba.
Haushi ne ya kamata kaman ta sa kuka, ji tayi kan ta kaman ze cigaba da ciwo ba shiri ta ajiye wayar ta kwanta domin ta samu bacci.

Hausawa suka ce sabo turken wawa. A kwana huÉ—un nan Ammar ya fara tunanin anya yarinyar nan ba dagaske take bata da lafiya ba? Last seen É—in ta tun lokacin da ta tura masa message É—in nan, Zuciyar sa na ta gaya masa abubuwa daban2.

Yaya Fadila tazo gida domin sake duba Mufeeda, taje ta tarar tana bacci amma duk ta rame sosai, Fadeela tace  "lallai Autar Baba an sha jiki, duk ta rame"
Mama tace

"Aikam ta sha jiki, kuma ta ƙarawa kanta wahala dan bata shan magani, ai zaman jinyar nan tata ba ƙaramin ɓata min rai yayi ba, ta fiye rakin tsiya kaman ba mace ba shiyasa bana so tayi rashin lafiya"

Suna cikin hirar wayar Mufeeda ta fara ringing a gefen pillow É—in Mufeeda, A hankali Fadeela tasa hannu ta É—akko wayar.

My Yaya Ammar

shine akan screen É—in, dariya Fadeela tayi tace
"Mama sirikinki ne fa ya kira"
Tsaki Mama tayi tace
"sirikin Dr. Dai"

Fadeela tai murmushi ta É—aga wayar tayi sallama
Ammar ya amsa ba tare da wata doguwar magana ba yace

"Ina me wayar?" ba ƙaramin mamaki Fadeela tayi ba saboda abune mawuyaci ka banbance muryoyin su in ba ka zauna da dukan su ba, Amma sallama kawai tayi yasan ba Mufeeda bace, gashi cikin gadar yake magana, Fadeela tace

"bata da lafiya bacci take"

be kuma cewa komai ba ya kashe wayar sa.

Fadeela tace "Ikon Allah yau ni naga isa da izza, kinji yadda yake magana kuwa Mama?"

Mama tai tsaki tace
"Ai se taje taita yi yaron da ko damuwa beyi da ita ba tun ranar É—aurin Auren Amina wata na biyu kenan ban ganshi a gidan nan ba, ko dubiya bezo ba ni na kasa gane kan wannan shirirtar, ga baban ku ya goya mata baya yace zece ya fito, ko lokacin da yazo gidan nan ko É—an murmushi babu a fuskar sa da ganin sa zeyi masifa "

Fadeela tace
"Mama yadda auta take da rawar kai da shagwaba ta auri gayen nan zata sha wahala, a muryar sa zaki gane yana da izza da isa, kuma Mama ya mata girma kalle shi fa ki kalli ƙirar jikin sa, ita kuma kalli ɗan nata jikin wallahi mama kiyi wani abu akan lamarin nan, kar ku biye wa haukan ta"

Cikin damuwa Mama tace  "Fadeela ya zanyi nayi2 babanku ya gane amma yaƙi, ya goyi bayan ta yace yadda take sonsa ɗin nan idan bamu goya mata baya ba zata iya shiga wani halin, nayi rarrashin nayi nasihar amma ina kin santa da kafiya musamman idan baban ku ya goyi bayan ta akan abu"

Haka suka ci gaba da tattaunawa akan lamarin.

Se kusan la'asar Mufeeda ta tashi daga baccin, tayi wanka ta É—anci Abinci shima seda suka haura da Mama.

Fadeela tace "professor Auta wannan gardin ya kira ki fa"

A ya tsine Mufeeda ta kalli Fadeela "Waye kuma gardi?"

"Wannan Saurayin naki me fuskar shanu, wanda yazo bikin Amina"

Da farko Mufeeda bata yadda ba, ta harari Fadeela tace
"Mama ki gayawa Yaya Fadeela babu ruwan ta dani karta ƙara cewa Ammar ɗina gardi, sedai mijinki ne gardi"

Fadeela tace "Ashe har da zuwa ki ga yawa Baba ke Aure kike so ko? Hmm yarinya  ba dai Aure ba? ba zaki gane ba yanzu"

Share fadila tayi ta koma É—akin ta, ta É—akko wayar ta, da mamakin ta tana duba call log sega kiran Ammar, tsalle Mufeeda ta dinga yi a É—aki tana murna.
Ta nemi guri ta zauna tana tunanin ko ta kira shi? Se kuma ta fasa tace se dare tasan maybe yanzu yana aiki.

Se bayan sallar isha'i kusan tara da rabi na dare sannan ta É—akko wayar ta ta kira Ammar, Amma abun haushi be É—aga ba, missed call biyu tayi masa amma ne É—aga ba.
Haushi ne ya kamata ta ajiye wayar a gefen ta ta kwanta tana zumɓura baki kaman tana gaban sa.

Bacci ne ya fara É—aukar ta, cikin baccin ta ji wayar ta na vibrating, Ammar ne seda ta saki murmushi sannan ta É—aga wayar tasa a kunnenta sallama yayi mata
Seda ta ƙara ƙasa da muryar ta sosai kaman tana jin jiki sannan ta amsa masa Sallamar

  (tafa warke har faɗa suka kusa yi da Yaya Fadeela ɗazu saboda an ce masa gardi amma ya kira ta noƙe murya kaman yanzu take jin rashin lafiyar 🙄🙄🙄)

"Na kira É—azu kina bacci ya jiki?"

Seda ta ƙara ƙasa da murya cikin shagwaba da wata irin sassanyar murya tace
"Ni banji sauƙi ba bani da lafiya har yanzu, banji sauƙi ba ji nake kaman zan mutu, Yaya Ammar ba zaka zo ka duba ni ba?"

Kaman an masa dole yace "meya same ki?"

"komai ma ya dameni zazzabi nake sosai, kwana na huÉ—u a Asibiti, dan Allah Yaya Ammar kazo in ganka kar in mutu bamu haÉ—u ba please"

Ji yayi gaba É—aya wata kasala ta saukar masa yanayin yadda auta ke magana, seda ya numfasa sannan yace

"zuwana baze hana rashin lafiyar ki ba, sedai zan miki Addu'a Allah ya baki lafiya"

Kawai ta saka kuka babban abunda Ammar ya tsana a rayuwar sa kenan kuka
"nidai dan Allah kazo, idan na ganka zanji sauƙi, in kazo dubani zaka samu ladan gaida mara lafiya, kai na fara gayawa bani da lafiya amma bazaka zo ka dubani ba ko? Shikenan nagode dama ni na damu da kai in na mutu Baba ne kawai ze kewa ta"

Ta ajiye wayar ta ci gaba da kukan ta, da yake bata katse kiran ba Ammar yana jin sheshsheƙar kukan ta.

Katse kiran yayi tare da dafe kai yace "Ohh My God"

Mufeeda kam ta sha kuka, da surutai
"nikam wace irin ƙaddara ce na kama son wanda be damu da niba, Ni dama haka son yake? Wayyo Allah na"
Ji tai kanta ya fara nauyi dan haka ta lumshe idon ta tana jiran bacci ya É—auke ta.

Ammar ya rasa yadda zeyi, haka nan idan ya tuna kukan da Mufeeda take a waya se yaji idan be je ya duba ta ba kaman be kyauta ba, Amma a matsayin wa zeje dubiyar? Baya son tambayar su Jabir shawara yanzu zasu raina masa hankali, dan haka kawai ya share.

Mama ta lura kaman jikin mufeeda ya dawo, dan wuni tayi a kwance ko Abinci ta kasa ci se complaint take da kanta.
Da ƙyar ta samu tayi sallar magariba shima a zaune tayi saboda ciwon kan da take ji sosai.

Yaro ne ya shigo yai Sallama ya tarar da Mama a tsakar gida ya gaishe ta da yake ɗan maƙotan su ne, yaron yace
"Wai Mufeeda taje inji Ammar"

Mama ta taɓe baki kaman tace baza ta zo ba, Amma ta fasa tace "kace tana zuwa"

Mufeeda kuwa dukda tana fama da kanta tana jin jiri amma haka ta miƙe ta ɗauki ɗankwalin Abayar ta ta yafa ta fito waje
Mama ta kalleta tace "yau naga tsiya kekina fama da kanki amma shine har kin fito, kai Allah yayi miki magani"

Mufeeda ba tace komai ba ta shiga É—akin Mama ta É—akko Babbar Dadduma tai waje abun ta, zuciyar ta cike da farinciki da É—okin ganin Ammar.

A jikin gate ɗin su ta tsaya ta na kallo shi daga inda yake tsaye opposite ɗin gate ɗin yana danna wayarsa, ita dai a duk lokacin da ta ganshi ƙara yi mata kyau yake da kwarjini.

Ta tura masa message

"Ka shigo gareji, Yanzu Baba ze dawo, ya ganni a waje ze min faÉ—a"

Ɗaga kansa yayi ya hango ta, ya taka a hankali ya shiga gate ɗin gidan su, har ta shimfiɗa daddumar ta zauna, da yake da wuta ko ina da haske. kana kallon ta zaka gane bata da lafiya, dan ta rame sosai ta ƙara haske.

Ƙamshin turaren sa ya kashe mata jiki tare da ƙara masa kwarjini a idon ta gaba ɗaya ta kasa ɗaga kai ta kalle shi ta sunkuyar da kanta ƙasa.

Sema da ya zauna akan daddumar ya zama na yana daf da ita, suna jin Ƙamshin turaren juna, taji gaba ɗaya kamar yau ta fara ganin sa.
kaman kullum yauma fuskar sa babu wata fara'a

A hankali tace "ina wuni?"
Ya kalle ta yace "lafiya Ashe ma kin warke?"

Ai kaman ya taɓa mata inda yake mata ƙaiƙayi ta tura baki kawai ta fara share hawaye.
Chapter 8 · 0% Book details