← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 64

Sashe 44

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"to Amma waye wannan yake turo masa saƙon? Ya akayi me turo saƙon ya samu lambar sa har yasan Matarysa tana aikata rashin gaskiya a bayan idon sa?"
Yadda Ammar ya ga dare haka ya ga rana, bacci ya ƙauracewa idanunsa.

*********************

Ƙarfe biyu da rabi na dare Saima ce kwance tana bacci yayin da gefen ta Jabir ke kwance  yana chatting, A hankali ta buɗe ido tana kallon sa ba tare da yasan tana kallon sa ba, voice message ɗin da aka turo masa ya buɗe yana saurarar, amon muryar mace ne ya fara tashi

"My Jabir i can't wait to see you as my husband, na ƙagu lokaci yayi ni kaɗai nasan me make ji akan ka, Amma ni matsala ta ɗaya gaskiya bana son zama da kishiya, bazan iya sharing ɗin ka da wata 'yar talakawa ba, Daddy ze baka gida ya canza maka mota wataƙila ma har muƙami yayi maka a cikin kamfanonin sa, Amma gaskiya ni batun zama da wata ne akwai damuwa"

Jabir yayi ƙasa da muryar sa yace
"My love karki ji komai ni kaina na ƙagu in mallake ki, dan babu wani farinciki da nake tsinta a Auren nan, Mata ta babu abunda ta iya, Ni ban san wani irin tsautsayi ya kaini na Aure ta ba, bayan ga irin ki, yanzu dai so nake ta haihu tukuna kar ace na sake ta da ciki, Amma da zarar ta haihu zan san abun yi"

Ba shiri Saima taji abunda yake cikin ta yayi wata irin juyawa saboda maganganun da Jabir yake yi, A hankali ta miƙe zaune saboda nauyin cikin dake jikin ta, Jabir yana kallon ta haka ta dinga bin bango da ƙyar ta shiga banɗaki, tana shiga ta durƙushe ta dinga zubar da Hawaye tana tuna yadda ta ƙaunaci Jabir, lokacin da take hasashen tayi dacen miji, take tunanin duk cikin mane manta Jabir ne ze riƙe ta ya kula da maraicinta, se gashi Jabir ɗin nata ya sauya komai ya dagule mata, babu wanda zata kaiwa kukan ta se Allah, ba uwa ba Uba, a hannun ƙanin mahaifinta ta girma, cike da tsangwama da bautarwa basu da burim da ya wuce suga ta wulaƙanta dan haka batun ta kai kokenta gidan su be taso ba, ta daɗe a banɗaki tana kuka sannan ta fito, yanzu ma a durƙushe ta dawo ta sa hannu ta ɗau fulo ta kwanta a ƙasa Jabir yana kallon ta amma be ce mata uffan ba ya ci gaba da Chatting ɗin sa.

Bacci ya ƙauracewa idanun Saima, har ƙarfe uku na dare Sannan Jabir ya kwanta, a hankali ta kuma jan jikin ta zuwa banɗaki tayi alwala ta koma ɗaya ɗakin ta shimfiɗa sallaya, nafila tayi ta idar ta ɗaga hannun ta zata yi Addu'a amma ta kasa se kuka me taɓa zuciya da ta dinga yi.

*******************

Babban abunda ya bawa Mufeeda mamaki be wuce yadda tun Asuba da Ammar ya fita salla be ƙara dawowa ba kuma be fita da babur ɗinsa ba, har ƙarfe sha ɗaya na safe babu shi babu alamar sa, Wayarta ta ɗauka ta kira shi amma sam yaƙi ɗagawa daga ƙarshe ma ya kashe wayar sa ta dena shiga.

Addu'a Mufeeda ta dinga yi na Fatan Allah yasa na lafiya dan be taɓa yin hakan ba, Mufeeda ko karyawa ta kasa yi, dan damuwar da take fama da ita kwanan nan, da yawan kukan da take yi yasa take fama da ciwon kai dan sam ko Abinci ba ta iya ci.

Wasa wasa har Azahar babu Ammar babu ɗuriyar sa, da ƙyar ta dafa tea ta sha kaɗan ta ajiye gaba ɗaya hankalin ta a tashe yake.

***************

Maman Nur ta saka mijin ta a gaba "wai ni da kaje ka samu wannan me Napep É—in game da abunda matar sa tazo tayi min me yace maka, baka yi min bayanin komai ba fa"

Baban Nur yace  "to me zance miki labarin bame daɗi bane, dan naga alamar baya son laifin ta, cemin yayi wai ba yadda zata tayar da faɗa idan ba wani abun akayi mata ba, shi matar sa ba fitinanniya bace"

"kan bala'i haka ma yace, to kai me kace masa?"

"Me kuwa zance masa? Nace masa dai ya ja mata kunne"

"Amma wallahi ka fiye abun haushi, wato kaine baka kishi na ko? maimakon kayi masa rashin mutunci ka nuna masa ɓacin ranka akan abunda tayi, kawai se kace yaja mata kunne, be yadda tayi laifi ba ta ina ze ja mata kunne? Tunda kai ba zaka iya ba ni zanyi, wallahi se fitowa da rana ya gagari yarinyar nan dani take zancen zan sauke mata wannan girman kan nata"

"Akan me zaki hana ta fitowa da rana? Ke kika ajiye ta?"

"kaga ba ruwan ka dan Allah kasa ido kawai, zata gane bata da wayo zan koya mata hankali yadda gaba in ance  idan ta ganni tayi min rashin mutunci seta gudu da ƙafar ta"

******************
Mufeeda ta tsorata sosai da rashin dawowar Ammar gida, gashi har magariba tayi amma babu shi babu alamar sa, waya ta ɗauka tana ƙoƙarin kiran Umman Ammar ta sanar mata abunda yake faruwa amma wayar taƙi shiga, shiru tayi ta fara tunanin ko wani abunne ya same shi, Alamar buɗe gate taji, dama idan ya dawo yana da key, yake sawa ya buɗe kawai.
Da sauri ta tashi ta fito tsakar gida, Ammar ne ya shigo fuskar nan tasa tamkar kumurci babu alamar Afuwa, tana ganin yanayin sa gaban ta ya faÉ—i, Amma ta dake tace "lafiya kuwa Yaya Ammar daga tafiya sallar Asuba na neme ka na rasa? Hankalina fa ya tashi sosai"
Wani mugun kallo yayi mata dase da 'ya' yan cikin ta suka juya, ya wuce ta ya shige falo, da ya shiga É—inma be tsaya a falon ba É—akin sa ya wuce kai tsaye.
Bata karaya ba tabi bayan sa dukda irin mugun kallon da yayi mata.
"Mijina dan Allah ka gayamin ina ka tafi haka?"
"get out from here" yai mata wata irin tsawa da ta razana ta matuƙa.
"Yaya Ammar daga tambaya sekamin tsawa haka?"
"Ki fita tun ban tattaka ki a gurin nan ba, ki fitar min daga É—aki nace"
Gaba ɗaya jikin ta rawa yake, ga Yunwa ta wuni ba taci Abinci ba ga ɓacin rai ga wannan masifar da Ammar yake da bata san dalilin ta ba, wani irin jiri ne yake nema ya kada ita ƙasa dan haka ta dafe kanta ta fita.

Gaba ɗaya hawayen ma yaƙi zubowa se zafi da ƙirjinta yake yi, bata taɓa tsammanin halin Ammar ya kai haka ba, bata taɓa tunanin zafin zuciyar sa ya kai haka ba? Shikenan laifi wanda tasan tayi da wanda ba tayi ba se ya ɗora mata yaita faɗa, ko'a ɓata masa rai a waje yazo ita ya sauke mata, abun ya fara damun ta.

********************
Sosai Saima take dana sanin sanin Jabir a rayuwar ta, gaba ɗaya taji Aure ya fita daga ranta, ta ɗauki shawarar Mufeeda idan Jabir yana mata rashin mutunci ƙyale shi take bata tanka masa, tsanar da tayi wa Jabir a yanzu harta kai ga taji bata ƙaunar cikin dake jikin ta, dan haka ta ƙudurce a zuciyar ta ranar data haihu zata karɓi takardar sakin ta daga hannun Jabir tun kafin yaci zarafin ta ya kore ta akan 'yar masu kuɗin da yake hari, yake ganin zasu yabke masa talauci idan ya auri ' yarsu, sannan ta ajiye masa abunda ta haifa idan yasa kowa ze Auro tazo ta kula masa da ɗansa amma ba zata shayar da abunda ta haifa ba, Abunda Jabir yake mata yasa gaba ɗaya haushin maza take ji ta ƙudurce a ranta ba zata ƙara yin wani Auren a rayuwar ta ba, idan har Jabir da suka shafe shekaru suna soyayya ze mata haka bayan Aure to bazata sake Aure ba dan babu sauran wani namiji me imani da yayi saura duk haka halin su yake.

*******************
Mufeeda tana ta fama da damuwa ta kasa gayawa kowa dan gani take hakan tamkar tona Asirin Auren tane, kuma koda ta gayawa iyayen ta aka sasanta komai ze iya wucewa a gurin ta, Amma ba lallai ya wuce a gurin iyayen ta ba.
Tana kwance akan kujera bata jin daɗin komai aka ƙwanƙwasa ƙofa, jiki ba ƙwari ta tashi taje buɗe, tana buɗewa taga Anty Maryam ce, Yayar Ammar, murmushin dole Mufeeda ta ƙaƙalo tayi wa Anty Maryam tare da yi mata maraba.

Suka gaisa Maryam tace "kin ganni unguwa naje na dawo naga na biyo ta layin unguwar ku nace bari inzo mu gaisa"

"Aikuwa naji daÉ—i Anty Maryam, dama baya nan duk kaÉ—aici ya dameni, bari in dafa miki Abinci"

"A'a Mufeeda ba sekin wahalar da kanki ba, kin ganni seda na cika cikina na fito"

Nan suka shiga hira da Mufeeda, Amma Anty Maryam ta karanto damuwa ɓoye a bayan murmushin da Mufeeda take yi, ta ɗan dube ta tace
"Mufeeda baki da lafiya ne?"
"A'a Anty Maryam lafiya ta ƙalau"

"Amma naga kinyi wannan ramar haka? Kodai wani abun yana damunki ne?"

Wani murmushin dolen Mufeeda ta kuma yi tace "Ba abunda yake da muna fa ke kika ga na rame, amma komai lafiya" tana magana ne yayin da ƙasan zuciyar ta ji take kaman ta fashe da kuka.

"Mufeeda idan kinsan akwai matsala ki gayamin, idan wani abun yake miki ki faɗa tun wuri ayiwa tufkar hanci, nasan halin Ammar sarai ɗan uwana ne amma zama dashi se me haƙurin gaske ki gayamin idan akwai matsala"

Shiru Mufeeda tayi sannan ta É—ago ta kalli Anty Maryam tace
"Anty Maryam gaskiyar kenan na gaya miki ki yarda dani" tai maganar tana ƙoƙarin maida ƙwallar dake ƙoƙarin zubo mata, ganin Mufeeda bata da niyyar gaya mata abunda ke damun ta yasa ta ƙyaleta, aka jima tai mata sallama ta tafi.
Chapter 44 · 0% Book details