← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 64

Sashe 26

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"kiyi shiru bana son kukan nan, in baki ci Abincin nan ba, nima bazan ci ba"

A hankali cikin raÉ—a yace mata
"ina da chocolate a aljihuna in kika ci zan baki, kinji Jaririya ta"

ganin Ammar duk jin kan nasa ya zage yana rarrashi ne yasa ta saki fuskarta tayi murmushi, Ammar ne ya bata Abincin cikin salo na rarrashi, gaba ɗaya ta manta da ɓacin ran da take ciki, dan ita wannan rarrashin nata da yake da bata Abinci yasa ta manta da komai.

Seda ya tabbatar taci da yawa ta ƙoshi, Sannan ya ƙyaleta shima yaci nasa, karshe a jikin Ammar tayi bacci, ya ɗauke ta ya kaita ɗakin ta ya kwantar da ita.

Seda ya tsaya ya ɗan zuba mata ido, haka nan yake jin tausayinta, she's simple minded ita dai burin ta kar yayi fushi da ita, ya daɗe yana kallon ta sannan ya tashi ya tafi ɗakin sa, da yaje ɗakin nasa ma tsaf da shi ta canza masa bedsheets, ta rubuta masa takadda ta ajiye masa, takaddar ɗauke take da kalaman soyayya dana ban haƙuri.

Ɗan murmushi yayi yace "She's so kind" ya ajiye takaddar a ƙasan filon sa ya kwanta.

Da safe Ammar yana ta shirin fita ya buÉ—e wardrobe É—insa ze É—auki kaya, Mufeeda ta shirya masa wardrobe É—in tsaf, amma bega inner wears É—insa ba, wayarsa ya É—auka ya kira Mufeeda tana kitchen taga kiran Ammar, ta É—aga wayar tace
"Hello Baby na ka tashi lafiya?"

"lafiya ƙalau, Amma Niba baby bane, ina kika ajiyemin inner wears ɗina?"

"Ina kitchen ne, zanzo in É—akko maka"

"Ok" suna gama Waya Ammar ya shiga wanka.

Seda ta kammala ta tafi É—akin Ammar zata É—akko masa kayan da yake nema, tana zuwa ta duba wardrobe É—insa ta É—akko masa

"Hmm Yaya Ammar kenan ga kayan anan kusa amma wai be gansu ba, ko ina ya duba oho"

Tana É—agowa taga ya fito daga wanka, boxers ne kawai a jikin sa yana goge ruwan wanka.

Tsorata Mufeeda tayi ta zare ido, bata taɓa ganin namiji a haka ba, wasu zara zaran gashi ne a jikin sa, tun daga kansa ƙirjinsa zuwa ƙafafuwan sa, taga yayi wani irin girma da kwarjini, nan ta shiga zazzare ido.

Ammar sarai ya ga tsoro a fuskar Mufeeda
Ammar yace "Yawwa kin É—akko min?"

Jinjina masa kai kawai tayi tana kallon sa, yace "miƙomin su nan, ni ba'a nan nake ajiyewa ba"

Jiki a sanyaye tana kallon sa tana ɗauke ido, ta ƙaraso ta miƙo masa kayan, maimakon ya karɓi kayan seya riƙe ta, ƙara zare ido tayi tana jan numfashi.

"Me kike Kallo" girgiza masa kai tayi tace "bakomai fa" tai maganar kaman za tayi kuka

"A'a sekin gayamin me kike kallo?"

"wallahi bakomai, ba kallon ka nake ba"

"ki gayamin ba abunda zan miki"

"Wallahi bango nake kallo ba kai ba"

Murmushi ya É—anyi a ransa yana tuna yadda take masa rangwaÉ—a da shagwaba ashe ma matsoraciya ce haka.

Ya ɗan kashe mata ido yace "ko zaki taɓa gemun ne?"

"A'a aikace ba yanzu ba"

"A'a na canza ra'ayi ki taɓa mana"

Noƙe kafaɗa tayi tace
"A'a Abinci na ze ƙone"

Sakin ta yayi ta fita da sauri hada haÉ—awa da gudu, sosai ta bawa Ammar Dariya.

Har ya shirya ya fito bata son kallon sa sosai, ko surutun yau babu, da taga zasu haÉ—a ido seta sunkuyar da kai, idan kuwa suka haÉ—a ido se Ammar yace "ko in zone? .

Da sauri take cewa A'a

Haka ya karya ya fice yana dariyar yadda tayi da ido daya riƙe ta.

Domin sharhi, Gyara ko Shawara
Ayshercool
07063065680

✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

                  

                        Page 14

Ammar be kai dare ba yau tun azahar ya dawo gida, amma yana zuwa ya tarar da Mufeeda a falo kwance akan kujera, da ƙyar ta iya amsa masa sallamar sa ya kalleta yace
"ya dai?" tace
"bakomai ya naga ka dawo da wuri yau?"
"kince in dena kaiwa dare, na dawo da wuri kuma kina tambaya ta"

ÆŠan murmushi tayi tace "ai ban san zaka dawo yanzu ba, ban girki ba"

"haka kike zama da yunwa in ba na nan, salon Ace bana baki Abinci?"

"Ai bana jin yunwa ne, kuma ga cornflakes can, idan naci ya isheni, Abincin yafi daÉ—i idan ina ci ina kallon ka"

Murmushi yayi yace "yanzu me zaki ban, ina jin Yunwa"

"ina da miya, bari inje kitchen É—in in gani"

Ammar ya lura da ita kaman jikin ta babu ƙwari, a hankali take komai, ta dafo masa Abinci ta kawo masa, ta koma kan kujera ta kwanta.

Ammar yace "wai meke damunki ne?"

"Ciki nane yake min ciwo fa"

"Shine kike ta faman haÉ—e rai haka, wannan ciye ciyen naki ma ya isa su saki ciwon cikin ai"

Shiru tayi masa ta lumshe idon ta, ya kalle ta yace
"ki sakko kici Abinci seki sha magani"

Girgiza masa kai tayi alamar A'a,.
Ammar yaci Abincin sa ya ƙoshi, ya ture Kwanukan gefe, ya ɗakko wayarsa yana game, a tunanin sa Mufeeda ba dagaske take ba.

Can ta ɗan fara juyi tana riƙe cikin ta, tana numfarfashi.

Ya kalleta yace "idan banÉ—aki zaki shiga ki tashi ki tafi mana"

Haushi ne ya kamata, tana fama da kanta amma yana mata wata maganar daban, a hasale tace
"Idan banɗakin zani ai na sani, ko na taɓa fitsari a falo ne? In haka kake gudu seka dinga samun pampers kar in ɓata maka guri tunda dama ni Jaririya ce"

Mamaki ne ya kama Ammar, ko da wasa be taɓa tunanin Mufeeda zata gaya masa baƙar magana ba.

Ƙara riƙe cikin ta tayi tana rintse ido, Ammar binta yake da ido kawai, miƙewa tayi tana durƙusawa ta tafi ɗakin ta.

Ɗan taɓe baki yayi ya ci gaba da danna wayarsa, idon sane ya sauka a inda Mufeeda ta tashi, tayi staining na jini a gurin, ɗan zare ido yayi, dama Mufeeda ta isa fara period ne? 🙄

Miƙewa yayi ya samo ruwa da Omo ya goge gurin, da yake bada yawane inda ta ɓata ɗin ba, shi da farko ya ɗauka kawai rigima take ji, se yanzu ya tabattar bata jin daɗi ne.

Ya bita ɗakin dan ganin halin da take ciki, yana shiga ɗakin nata ya tarar ta cire kayan jikin ta, daga ita se underwear hatta ribbon ɗin kanta ta cire shi, gashin ta a wargatse tana durƙushe a gaban gado, ta tattaro bedsheet ɗin kan gadon ta tada kai dashi tana kuka, ga fanka se gudu take amma ita ta haɗa gumi sosai se kace me naƙuda.

Daidaita nutsuwar sa yayi, ya ƙarasa da sauri ya ɗago ta, ya ƙare mata kallo, Mufeeda ba farace tas ba amma chocolate ce me haske, fatar ta tana da matukar ɗaukar ido se sheƙi take, ga wannan sassanyan ƙamshin da take me kashe masa jiki

A hankali yace " sannu ban zaci abun ya kai haka ba, daure kisa kayan ki se muje Asibiti"

Ɗan ƙura masa ido tayi sannan ta ƙara kwanciya a jikin sa tace
"bazan iya tafiya yanzu ba, ka bari ya lafamin, kuma ma daka ƙyaleni ze dena fa"
"No gara muje Asibitin dai"
ÆŠan lumshe ido tareda yamutsa fuska alamar tana jin jiki, a hankali kaman me raÉ—a tace
"bari ya É—an lafamin, yanzu ina jin ciwon sosai"

"shikenan sannu"
Bata iya amsawa ba se lumshe ido da tayi, a hankali Ammar ya kai hannun sa kan gashin ta yana shafawa, zuciyar Ammar ta shiga bugawa da ƙarfi tana raya masa abubuwa da dama akan Mufeeda, Amma wani ɓangaren na zuciyar sa na ƙoƙarin kawar masa da tunanin da yake.

Ɗan yamutsa fuska ta kuma yi tana miƙe ƙafafuwan ta tace
"Yaya Ammar Ciwo"
Ya riƙe hannayen ta yace "Sannu ze dena Insha Allah"

Gaba ɗaya tausayi take bashi, yana tuna wani littafi daya taɓa karantawa me suna (MATA A LOKACIN HAILA)

Mata na shiga mawuyacin hali a wannan lokacin, wani yanayi ne wanda inba wanda yake jinin ba baze gane ba, sukan shiga halin takura, yawan ƙunci, kasala tashin zuciya, yawan faɗa da saurin fusata, kwaɗayi kaman masu ƙaramin ciki, yawan kuka ko san kaɗaici da dai sauran su, ga uwa uba Wannan ciwon da wasu matan kan yi, ciwo ne me wahala matuƙa wata duk lokacin da za tayi seta kwanta rashin lafiya sosai, ciwon mara me haɗe da ciwon ciki da gudawa, ko kuma ciwon baya da ƙafafuwa, wasu kuma hada amai da zazzabi ƙuraje su fito su ɓata musu fuska, wannan ma ya ishesu shiga damuwa, wata idan tana wannan ciwon kaman zararriya haka take, wata harta gama Al'ada bata san saka kaya, se dai marasa nauyi, wata kuma komai sanyi zata dinga kwanciya a guri me sanyi ko cin abu me matukar sanyi, da dai sauran su.
  Dan haka yake da mahimmanci miji kokuma wanda yake tare da Mace ya gane idan mace tana irin wannan yanayin ayi mata uzuri, ba kowane lokaci mata suke wani abun suna sane ba, sedai dan kusan gaba ɗaya rayuwar su cikin yanayi ne na hormones da suke sauyasu lokacin al'ada, lokacin da suke da ƙaramin ciki ko kuma idan cikin ya tsufa.

Kallon ta ya ci gaba daya, bacci ne yayi gaba da ita, dan haka Ammar yasa mata filo ya kwantar da ita ya fita.
Chapter 26 · 0% Book details