← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 64

Sashe 16

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zainab ta taɓa aure shekarar ta biyu suka rabu da mijin, maƙwabciyar yayarsa ce Jidda, acan suka fara haɗuwa ta nuna tana sonsa, Jidda ta ƙara haɗasu ta ƙarfafa abun, shi dai Ammar kawai yayi niyyar auren Zainab ne saboda tana da shekaru a ganin sa itace tasan meye zaman aure, yanzu ma da aka kai kayan lefen nan Yayar sa Jidda se kushe abun take yi saboda yaƙi auren Zainab, dan ita zainab take so ya aura, koda taga kayan da Ammar ya haɗa ma se kushewa take tana "akace ƙwaila ce kuma a haɗa duk wannan kayan akai mata, naji cewa kayi kai ba son ta kake ba"
Ammar kam da baya son raini ya haÉ—e rai yace
"dan bana sonta bazan wulaƙanta musu yarinya ba, 'yar manyan mutane ce meye riba ta idan ankai musu kaya a tsiyace mutunci na ne ze zube, ba ruwanki da abunda zan kai"
Ummansa ce tai tayiwa Jidda faÉ—a akan sam abunda tayi be dace ba a matsayin ta na babba.

Mufeeda tayi murna mara misaltuwa ganin duk kayan nan nata ne, sam ba tayi tunanin wai yayyen ta an kawo musu da yawa ba, ita nan duniya gani take tamkar Ammar yafi kowane namiji bajinta.

Yayin da unguwar su ta ƙara ɗaukar gulma wai dan tsiya akwati uku aka kawo mata, dama ya za'ayi zaton wani kayan arziki a gurin ɗan keke Napep.

Mufeeda tuni ta manta da batun suyi faÉ—a da Ammar ta kira shi a waya, yana gaban umman sa a zaune da yaya Jidda da sauran 'yan uwa, yana É—agawa ko gaishe shi ba tayi ba cikin murna ta fara magana

"Yaya Ammar ɗina naga kayan da aka kawomin nagode Sosai Allah yasaka da alkhairi, Allah ya ƙara maka buɗi ni ban san ma wane irin godiya zan yi maka ba nagode sosai"

Kana jin muryarta kasan yarinya ce sosai, Ammar yace "Ameen ki gaida mutan gidan" ya katse kiran, umma tace
"Haba Ammar be kamata kayi haka ba, kayan da aka kai ba wani na kirki bane amma se murna take tana godiya gaskiya yarinyar nan tana da hankali"

Halima tace "nikam Yaya Ammar ta burgeni wallahi se murna take yi"

Jidda kam taɓe baki tayi tace "wai Umma me kike so yace mata ma, dole tayi murna tunda ba sonta ake ba ta cusa kai"

Sam Ammar baya son irin wannan shirmen na mata dan haka ya tashi ya fice.

Mufeeda ta kammala jarrabawar ta lokacin saura sati uku biki, shirye2 sunyi nisa sosai kai ya fara ɗaukar caji, ƙannen Mama ne suka je suka gano gidan domin su san yanayin kayan da za a sai mata, gida ne ƙarami amma harda gate da matsakaicin tsakar gida, akwai wadataccen falo da ɗakuna guda biyu a ciki kowanne da banɗaki, se kitchen a falo, da ɗaki ɗaya a tsakar gida da toilet, ta gefe jikin bango kuma an shuka flowers, daidai gwargwado gidan yayi kyau ana ta jinjinawa ƙoƙarin Ammar.

Baba ya saiwa Mufeeda duk abunda ya kamata, yana matukar jin damuwar aurar da ita daze yi da ƙarancin shekaru amma yana mata addu'a Allah yasa haka shine mafi alkhairi.

Mufeeda kam se shan gyara take tayi fes da ita kaman ba ita ba, tana zaune a gida tana cikin É—akin ta tana chatting ta jiyo ana gayawa Mama tsegumin ana tayi dasu a anguwa, ana kushe mijin Mufeeda ana zata auri talaka kuma har wadda take surutun abun a unguwa aka gayawa Mama, kuma abun takaicin makwabciyar su ce take yaya ta abun tana kushewa bayan ita 'yan mata huÉ—u ne a gaban ta babu wadda ta aurar.

Mama taji haushin abunda aka gaya mata ana faɗa akan auren autar tata, ai kafin mama tayi magana tuni mufeeda ta fito daga ɗaki fuskarta murtuk cikin ɓacin rai tace

"ita wadda take kushe min miji' ya'ya nawa ne a gaban ta? Nayi imani da Allah da yaran ta suka sami wanda be kai nawa ba so zata yi, yara daga me bleaching seme soya awara saboda rashin miji, kuma wallahi se naje har gidan ta na mata rashin mutunci tun......

"Ke rufemin baki" mama ta daka mata tsawa

"ki ƙyalesu suyita surutun mana ze fito a jikin kine? Kowa yayi nagari kansa meye na tada jiniyoyin wuya? Ke ko gajiya ba kyayi da faɗa"

"Amma Mama ina ruwan ta dani? Ni zan auri me a daidaita sahu nata mijin fa faskare yake yi da 'yan kame2, ni wallahi idan banje na zazzage mata ba zuciya ta ba zata yi sanyi ba"

Mama tace "to sekin dawo ina magana ki nayi, matar data haifeki ki ƙyalesu suyi tayi karki ɓata farincikin da kike ciki mana, wuce ki koma ɗaki"

Mufeeda ji tayi kaman zuciyar ta ta fashe, taso mama ta ƙyaleta taje taiwa matar nan rashin mutunci daga ita har 'ya' yan ta, dukda rashin kunyar mufeeda akan sa'anin ta ya ƙare amma yau kam taso mama ta ƙyaleta tayi wa matar  nan saukale.

Ta koma ɗaki tana ta ɓacin rai, tana ƙoƙarin gano meye aibun sana'ar Ammar da ake kushe mata shi, kuma ai ba dole ne dan yayyen ta na auren masu kuɗi ace itama seta auri me kuɗi ba.

Tana ta wannan tunanin Kiran Ammar ya shigo wayar ta, É—aga wayar tayi tareda yin shiru, Ammar yace "ina waje" da yake indai yazo haka yake ce mata

Dukda ranta a ɓace yake taji daɗin zuwan nasa dan akwai abubuwan da take so su tattauna.

Ɗakin mama taje ta sanar mata zata fita Ammar yazo sannan ta wuce, tai masa iso ya shigo inda suka saba zama, duk lokacin daya zo fuskarta ɗauke da fara'a da shauƙin ganin sa yake ganin ta amma yau sam fuskarta a haɗe, tunanin sa ko tun akan saɓanin da suka samu ne ranar daya ganta a mota, da yake tun lokacin be ƙara zuwa ba se yau.

A hankali cikin turo baki ta furta
"ina wuni"
Seda ya ɗan tsura mata ido a ransa yace "ikon Allah a da ko a mafarki akace zan auri 'yar mitsitsiyar yarinya kaman wannan cewa zanyi ƙaryane, amma abun mamaki waini ammar ni zan auri wannan' yar ficikar" yai ajiyar zuciya sannan yace

"baki da lafiya ne?"
Girgiza masa kai tayi alamar A'a,
"to me akayi miki?"

Kaman ya taɓo abunda yake damunta tace

"ɓatamin rai akayi, 'yan unguwar nan ne suke cewa wai zan auri me a daidaita sahu, na cewa mama ta bari inje in rama ta hanani" ta ƙarasa maganar hawaye na zubo mata.

Tabbas akwai ƙuruciya a cikin maganar ta, haka nan seyaji ta bashi tausayi yace

"kinga matsalar ki ko? Daga tambaya se kuka meye hakane? Kinga da tun farko baki ce ni zaki aura ba babu memiki gorin zaki auri me a daidaita sahu, amma gayamin me yasa kike sona?"

ÆŠan É—agowa tayi ta kalle shi tace "nima ban sani ba"

"Akwai dalili ki gayamin"

"nifa ban sani ba"

"shikenan tunda haka kika ce, kin fi son a cigaba da yi miki gori kin auri talaka, kalli gidanku fa kalli motar Baba kalli suturar da kike sakawa, amma kince ke se talaka kaman Ammar kike so dole aita ɓata miki rai, baki dace da Auren talaka kaman Ammar ba, karatu ne ya dace dake idan kin gama ki samu wani haɗaɗɗen mutum me kuɗi ki aura, amma kinga Ammar talaka ne sosai kalli suturar da yake sawa, bashi da komai kinyi garajen zaɓarsa a matsayin miji"

Zuba masa ido tayi  kawai ta fashe da kuka cikin kuka tace 
"Niba kwaÉ—ayayyiya bace, ni ba kuÉ—i nake so ba Yaya Ammar nake so, ban san Ya akayi na fara soyayya ba, ban san ya akayi nake sonka ba bayan ko damuwa bakayi dani ba, ni kuÉ—i basa gaba na"
Sosai take kuka hada sheshsheƙa, Ammar yayi ƙasa da murya yace

"at your age is too early ace kin fara soyayya zuciya ce kawai take ruÉ—arki, ni anya ba jumping aka yi miki a baya ba, dan kamata yayi ace kina Jss2 ko 3 yanzu"

A ranta tace " ka manta kamata yayi ace ina ciki ba a haifeni ba ƙarewar Jss3 "

A fili kuma tace " ni ba'aimin jumping ba shekara ta É—aya aka sani a makaranta saboda mama tace ina surutu sosai "

Ammar seda ya É—anyi murmushi dan komai na yara take yi yace

"No wonder you are still baby, bakifi a saka zani a goyaki ba amma kince ke aure zakiyi meyasa kika zaɓi yin aure yanzu akan karatu? Aure akwai challenges masu yawan gaske da ba lallai ki iya ɗauka ba a shekarun ki "

Ta zumɓura baki fuska duk hawaye tace
"tunda ni Baby ce seka dinga goyani ai"
"Waye ze goya kin?"
"Yaya Ammar ɗina"  girgiza kai kawai yayi yace
"baki gayamin meyasa kika zaɓi Aure akan karatu ba?"
"Nifa da nafi son in fara karatu, kawai na haÉ—u da kai naji tsoron kar wata ta rigani auren ka shikenan fa" tai maganar tana son ganin reaction É—in sa

Ikon Allah ita abunda ke ranta kenan

Ammar yace "Amma bani da kuÉ—i fa kuma gani mummuna nayi miki girma"

"Nifa ko gurgu ne kai a haka nake sonka, ni duk mazan duniya da nagani babu me kyan Baba na da kuma Yaya Ammar É—ina, kuma ai Arziki na Allah ne, dama dai ni nasan ba sona kake ba"

Murmushi yayi tare da girgiza kai yace
"kinga goge ragowar hawayen nan kar wani yazo wucewa yace wani abun nayi miki"

Tasa hannu ta goge hawayen fuskarta, Ammar yace
"me kike shiryawa na bikin naki?"

"Bikinmu dai" ta mayar masa

"Waike ba kya jin kunya ne?"
Kallon sa tayi ta ɗan lumshe ido tace  "wai kunyar wa zanji? Aiba ƙarya nayi ba bikinmu ne nida Yaya Ammar"

Tunda take Ammar be taɓa zuwa gurin ta ya daɗe haka ba sunyi hira me tsawo, amma yau Ammar hada murmushi dan haka ta saki jiki take ta masa yarin ta, dan ta ƙudurce wa zuciyar ta da ƙuruciyar tata zata yi amfani ta mallake shi.
Chapter 16 · 0% Book details