← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 64

Sashe 22

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Be amsa mata ba ya shige ɗaki abunsa, ƙyale shi tayi dan taga alamar gajiya a tare da shi, amma ta barwa ranta dole Ammar ya gaya mata matsayin fa'iza da Nasreen a gurin sa.

Yana zuwa ze kwanta yaga takaddar data ajiye, ya É—auka ya karanta, É—an murmushi yayi ya ajiye takaddar a akan side bed ya kwanta.

****************

Motsin da Ammar ya dinga ji a banÉ—akin sane ya sa shi farkawa daga baccin da yake yi.

Shiru yayi ya lumshe ido yana tunanin meye yake motsi a toilet É—insa, be gama tunanin ba Mufeeda ta fito jikin ta É—aure da towel kan ta babu É—ankwali ta gama tsefe kanta ta wanke shi.

Ammar ya buÉ—e ido da sauri yace "Ke meye haka? Me ya kawo ki banÉ—aki na?"

Murmushinta me ƙayatarwa tayi masa tace "tap ɗina ne yaƙi zuwa, ni kuma bazan iya kai ruwa toilet ɗina ba kaga ni ƙarama ce bazan iya ɗaga babban bucket ba shiyasa nazo nan nayi wankan"

Tsaki yayi yace "to jeki maza fitar min daga É—aki"

maimakon ta fita seta girgiza gashin kanta da yake jiƙe da ruwan wanka, ai kuwa ruwan har fuskar Ammar

"Wai Mufeeda meke damunki ne, ya haka?"

Cikin kalar Halayar Yara tace "Yi haƙuri  kanne ya jiƙe, shine nake jijijjigawa dan ruwan ya fita, ka dubamin idan kan ya fita dama jiya kace kaina ƙazamine"

Girgiza kai Ammar yayi ya ja bargo ya rufe kansa ya juya mata baya.
Murmushi Mufeeda tayi a ranta tace "Yaya Ammar kenan ai ka gamu da yarinta kenan"

Ta zaga gurin ƙafar sa da ya bari a waje, taja yatsansa na tsakiya tace

"ai ka bar ƙafar ka a waje"

Banza yai mata yaƙi kula ta, yana ji tana jan yatsun ƙafarsa, kawai Mufeeda ta kalli gashin ƙafarsa ta ja ɗaya be kula ta ba, ta ƙara jan wani ai ba shiri Ammar ya miƙe zaune yace

"Meke damunki ne?"

Ta ɗan kwaɓe fuskarta tace "bakomai fa, so nake ka tashi ka karya"

"Naji amma yanzu fita kije kisa kaya, sannan karki ƙara zuwarmin ɗaki kiyi wanka in zaki yi wankan ki gayamin in kai miki ruwan"

"to shikenan naji zan tafi, Amma in ka fito sena taɓa gemunka dan ban manta ba"

Ta kashe masa ido, ta juya ta fice tana girgiza gashin kanta yana fidda ruwan dake jikin sa.

Yayin da Ammar yabi bayan ta da kallo zuwa kan santala santalan ƙafafuwan ta, tunda ga kan gashinta har ƙafafunta ɗigar da ruwan wanka suke.

Ammar ya dafe kai yace "kai wannan 'yar mitsitsiyar Yarinyar se rigimar tsiya, wai gemu na zata taɓa, wani lokacin kamar me hankali amma shirmen ta yayi yawa, dama nasan nikam na auri ƙuruciya da rawar kaine kawai, ni da ko ɗaukar ƙana nan yara ba nayi, amma wai gemuna zata taɓa"

Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

     

    Page 12

Ammar ya sakko daga kan gado ya shiga a gurguje yai wanka ya fito falo, kamar ko yaushe falon ta tasaf tayi turaren wuta, ta ajiye kayan breakfast a falon, se dai ita bata falon zama yayi ya haɗa ya fara karyawa, har ya kammala bata fito ba abun ya bashi mamaki, yana daf da fitane sannan ta fito cikin doguwar rigar ta, ta atamfa ta tsikara ɗaurin ɗan kwali a gaban goshin ta, masha Allah, Ba ƙaramin kyau tayi ba dukda bata saka jambaki ba yau fuskarta ba kwalliya amma tayi kyau, kaman Ammar yayi magana amma ya fasa.

"Hubby har kayi breakfast kai kaÉ—ai, shiryawa fa nake yi amma har kayi shirin fita?"

"Eh na makara yau, zan tafi"

"Amma nifa yau kai zaka bani Abinci, amma zaka tafi gashi ko ganinka ban gama yi ba"
tai maganar cikin sigar shagwaba da rararshi, ta ƙaraso gaban sa ta riƙo hannayen sa tace

"please My Ammar ka tsaya inyi breakfast seka tafi, Allah ban ganka ba sosai"

"Ke wai duk wani salon damun mutum kin sani, ni tafiya zanyi ba kiga na makara ba"

Tura baki tayi ta É—an haÉ—e rai "dan Allah Yaya Ammar ka zauna inyi breakfast seka tafi, in ka tafi Allah bazan ci ba"

Ammar yace "karki ci É—in cikin kine ai ba nawa ba"

Ya ƙwace hannun sa ze tafi, ta riƙe shi gam, idon ta har ya fara kawo ruwa za tayi kuka, Ammar ya girgiza kai yace
"Shikenan ni karki min kuka, muje ki zuba in kuma ba kiyi sauri ba zanyi tafiya ta ne"

Murmushi tayi tace "zanma yi saurin"

Haka Ammar ya dawo ya zauna, ta haÉ—a breakfast ta nayi, rigar ta cif a jikin ta kaman a jikin ta tela ya É—inka.

Haka Ammar ya zauna jaririyarsa ta gama cin Abincin ta, seda ya miƙe ze fita ta cire ɗankwalin kanta taje gaban sa tace

"Yaya Ammar ka dubamin idan gashi na ya fita"

dama gashin nan ya daÉ—e yana tsolewa Ammar ido. Ajiyar zuciya yayi yace

"Ke na gaji, ki bari idan na dawo zan duba miki"
yayi waje da sauri, Yayin da Mufeeda ta bishi tai masa addu'ar da ta saba yi masa.

A ƙasan zuciyar sa yana jin dama ya taɓa gashin nan, dan har ya bushe ta shafe shi da mai.

************
Su fa'iza kam bayan sun tafi jiya suna tafe suna zagin Mufeeda suna tsine mata.
Daddare suna chatting ita da Nasreen, Nasreen tace
"ke yanzu na samo mana wata mafita"

Cikin zaƙuwa Fa'iza tace "wace mafita ce haka?"

"Kin san Anty jidda ma ba son Auren nan take ba"

"haba dai?"

"Wallahi dagaske nake, yanzu abunda za muyi shine, muje gidan ta mu zigata, muce Yarinyar tayi mana wulaƙanci mu dai ɓata ta sosai a gurin ta, tunda kinga ba zamu tunkari umman sa mu gaya mata ba mussman inda wannan banzar haliman"

"haka za'ayi Nasreen, Allah ya kaimu gobe gidan Jidda zamu je".

Haka kuwa akayi Washegari haka suka wanke ƙafa zuwa gidan Jidda, tayi murnar ganin su suka baje ana ta hira Fa'iza tace
"Anty jiya fa mukaje gidan Yaya Ammar, wallahi Anty Ammar ya bada maza ke kinga matar tasa kuwa?

Jidda tace
"na ganta mana ya zan masa tunda shi ya zaɓo ta"

Nasreen tace "haba Anty jidda me wannan 'yar yarinyar zata morawa Ammar banda abun namiji dai?"

Jidda tace "ba shi yace yana so ba, itace ta ganshi ta nace masa sekace mayya seda ya aure ta, da akwai wata bazawara nan kusa dani ita yake so, amma ya koma ya auri wannan yarinyar"

Kallon juna Nasreen da Fa'iza suka yi, suka maze Nasreen tace

"'hmm ai baki ga abu ba Anty, kinga wulaƙanci da tayi mana? Munfi minti goma sha biyar a ƙofar gida muna bugu taƙi buɗewa, ke kinga kallon banza da take mana wai taga dangin miji"

Fa' iza tace "ba wannan ba anty jidda, data bamu Abinci baki ga kaji a ciki ba manya manyan yanka, nace Allah sarki su Abba su basu ci ba amma daga aure ya saiwa matarsa kaji fal, banda na kitchen wanda ba'a soya ba"

Anty Jidda ta jinjina kai tace
"hmmm Allah sarki, se anyi magana yace shi bashi dashi sana'rsa ba wata babbar sana'a bace, Amma har ya iya saiwa matarsa kaji iyayen sa ko oho, wallahi ze gamu dani ai zanje gidan"

Nasreen tace "ai gara dai kije wallahi Anty Jidda dan in ba'a ɗau mataki akai ba ana mata kallon ƙaramar yarinya gaida su Abban ma seya dena zuwa balle ya basu wani abu"

(Abunka da mata, wanda mune maƙiyan junan mu) haka suka dinga ziga jidda suna gaya mata abunda akayi da wanda ba'ayi ba, seda suka tabbatar sun kunna ta ta hau sosai sannan suka bar gidan.

*****************

Yau Ammar da Yamma ya dawo be kai dare ba kaman yadda ya saba, yana komawa yaga Mufeeda da wasu shigar dukda be gaya mata ze dawo ba, kayane Pakistan a jikin ta kanta ba É—ankwali, Mufeeda tayi murnar dawowarsa, sedai kaman kullum yauma a gajiye yake, ta jera masa sannu ba a dadi, kafin taje ta kawo masa Abinci ya zare rigar jikin sa ya bar vest da dogon wando. kafin Mufeeda ta dawo iskar fanka dake busa shi har ya jingina da kujera ya fara gyangyaÉ—i.

Mufeeda na fitowa daga kitchen taga Ammar yana bacci, bata taɓa ganin sa da vest ba, kodai yasa shirt ko kuma Jallabiya.

Ganin sa haka yasa ta ga yaƙara mata wani uban kwarjini, da ka ganshi kaga ƙaƙƙarfan namiji, ga gashi kwance a ƙirjinsa bacci kawai yake abunsa
Mufeeda na matuƙar Tausayin Ammar, neman halak akwai wahala, hartazo ta ajiye Abincin be buɗe ido ba.

A hankali cikin fargaba da tsoro taje kusa da shi, a hankali ta riƙo hannun sa cikin nata tace
"Yaya Ammar ka tashi kar wuyan ka yayi ciwo fa, ga Abincin na kawo maka"
Ɗan buɗe idon sa yayi ya mayar ya lumshe, ƙurawa fuskarsa ido tayi, sannan ta kai hannun ta zata taɓa masa gemu caraf ya riƙe hannun ta yace

"ai ina kallon ki" dariya tayi me cike da É—aukar hankali tace
"kana jina amma kaƙi kulani seda zan taɓa gemun ka ko? Ka bari in taɓa sau ɗaya mana"

Ya É—an kalle ta yace "A'a ba yanzu ba"

A shagwaɓe tace "se yaushe?"

"Sekin girma" ya bata amsa
Chapter 22 · 0% Book details