Sashe 4
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammar kam ya kai ƙarshe a ƙuluwa da irin wannan faɗan na baban sa, dan haka ya miƙe ya bar Abincin, Mama tace "Ammar Abincin fa?"
na ƙoshi ya faɗa a taƙaice yai waje
Mahaifin sa yace
"Eh haka dai, daga nan kuma ze wuce gurin bautar yahudu, gurin ƙwallon ƙafa aikin sa kenan, shi wace mace ce ma zata iya jure wannan baƙar zuciyar tasa, komai abun fushi ne a gurin sa"
Haka mahaifin Ammar ya ci gaba da faÉ—an sa har ya gaji yai shiru.
Ammar be koma gida ba se gurin ƙarfe tara na dare, ya zauna suna hira da mahaifiyar sa, tana ta ƙara yi masa Nasiha kan ya dinga haƙuri da halin mahaifinsa
Ammar yace "Umma wallahi na rasa me yasa Abba kaman baya son ganina? Sa ya ganni seya fara faÉ—a"
"Ammar ba sonka ne ba yayi ba, gaskiya yake gaya maka, a duniyar nan kafin ayi da kai kake yi da kanka, kai namiji ne kuma dukkan lafiyayyen namiji a shekarun ka ya kama ta ace ya ajiye iyali"
"Umma baƙin Aure nake ba, yanzu fa zamanin mu da naku ba ɗaya bane ba, da yawa 'yan matan yanzu me kuɗi suke so, ni kuma bani da su, ga kwalin karatu amma babu ƙwaƙwƙwarar sana' a, haƙurin da kuke dashi ku iyayen mu, matan yanzu ba haka bane a gurin su, ba kowace yarinya ce tasan menene zaman aure ba, zama ne na haƙuri wadda zata fuskanci yau in akwai gobe babu, wace yarinyar zata yadda ta aureni ina tuƙa babur ɗin sahu?"
"Ammar duk lalacewar zamani akwai na Allah Ammar akwai matan ƙwarai"
"Hakane amma duk da haka nafi son in samu macen da ta gama hankali ko bazawara ce, danni bazan auri yarinya ƙarama da bata gama hankali inzo ina fama da shashanci ba"
Girgiza kai Maman Ammar tayi tace "yaro dai yaro ne"
****************
Gidan su Mufeeda ya fara ɗaukar harami, baƙi daga sassa daban daban sun hallara ana ta shirin fara Shagalin biki, duk inda Amarya da ƙawayen ta suka saka ƙafa nan Mufeeda take maida tata, ko aike Mufeeda ƙin zuwa take balle asa ran zata taya aiki.
Aka fara Shagalin biki, kowane ranar event Mufeeda ta sha kwalliya kaman itace amarya, taji a ranta inama ace Yaya Ammar zega kwalliyar nan tata data ji daÉ—i, nan ta fara tunanin yadda zata samu lambar sa tare da addu'ar Allah yasa kafin agama bikin nan ko taro É—aya ya zo mata.
Ranar É—arin Aure aka É—aurawa Yayar Mufeeda Aure, gida ya cika da jama'a anata shiga ana fita.
Maman mufeeda ta bata kaji da snacks akan faranti tace maza taje ta bawa wasu 'yan uwan baban su yanzu zasu juya su tafi.
Mufeeda ta fito da tray a hannun ta, anata tsokanar ta, suna ce mata professor Mufeeda sarkin rigima, da yake ƙofar gate ɗinsu an buɗe ta gaba ɗaya, hakan yasa kana hango masu wucewa, gidan su Mufeeda yana da kyau, ba babba ne can ba amma yana da tsari, yanayin Abincin da'ake shiga ana fita da shi ze nuna Akwai rufin Asiri a gidan.
Idon ta ta sauke akan Ammar, ya saka yadi Ash da baƙar hula, yana ƙoƙarin kunna babur ɗinsa.
"Kenan yazo amma be nemeni ba?"
Ai dire tray É—in tayi bata san ma wa ta bawa ba, ta fyalla da gudu tai waje tana faÉ—in
"Yaya Ammar É—ina"
Juyowa yayi yana kallon inda take tahowa, purple ɗin shadda ta saka, ta sha surfani tun daga sama har ƙasa, hannun ta ya sha lalle, ga zobuna da abun hannu, tayi ɗaurin ture kaga tsiya, tayi parking ɗin gashin ta da keta sheƙi, tayi kyau matuƙa kaman itace Amarya.
Ta ƙaraso inda yake se nishi take, ya kalleta yace
"ke bakya jin kunya kike gudu a gaban mutane?"
Ajiyar zuciya tayi tace "haba Yaya Ammar yanzu da tuni ka tafi bamu haɗu ba, harna fidda ran zakazo" tai maganar a ɗan shagwaɓe
"hmm to ai gashi nazo, ya taro?"
"Alhamdilillah"
"Allah ya basu zaman lafiya"
"Ameen Yaya Ammar, Amma ba har tafiya zakayi ba, kaci Abinci kuwa?
" No bashi nazo ci ba, nazo an ɗaura aure nayi Addu'a" yai maganar tare da shiga babur ɗin sa ze kunna, hannu ta sa ta riƙe makullin tana kallon sa.
HaÉ—e rai yayi yace "Ya haka? Cika min ina sauri ne"
Dukda wani uban kwarjini da yayi mata musamman daya haÉ—e rai, bata nuna masa ta tsorata ba ta dake tace "kai kullum cikin sauri kake ne? Ni gaskiya idan baka shigo ba bazanji daÉ—i ba, ya za'ayi in gayyace ka kuma ka tafi baka ci komai ba?"
Ammar yace "ke wai haka kike? Cikamin key É—ina zan tafi"
Ƙwalla ya gani a idon ta, tana zumɓura baki, tana karya wuya kaman za tayi kuka, ta ƙara riƙe key ɗin gam, ji yayi kaman ya balbaleta da masifa amma yaga ta wani nutsu ta koma kalan tausayi. Ɗan gajeren tsaki yayi yace "muje"
Murmushi tayi tareda cewa "ko kaifa"
Amma still ta cire mukullin ta riƙe a hannun ta dan karma yace ze tafi.
Cikin gida ta shiga dashi har falon baban ta, yana zaune yana gaisawa da baƙin sa tace "Babana ga Yaya Ammar wanda ya kawo min kaya na dana bari a mota na kawo maka shi ku gaisa"
Ammar ya durƙusa suka gaisa da mahaifin Mufeeda, yai masa Allah ya Sanya Alkhairi.
Baba yace
"Masha Allah, Yaya Ammar mungode fa, dan saura ƙiris Auta ta sha duka a hannun Mama, Allah ya saka da alkhairi, mungode sosai"
Ammar yace "bakomai"
Ya miƙe suka fito yace "ke bani key ɗina zan tafi"
Ta marairaice tace "dan Allah kayi haƙuri saura Mama ku gaisa ba dan hali na ba dan Allah"
Haka ta kuma Jan Ammar inda mahaifiyarta take, ya gaishe ta ya musu Allah ya Sanya Alkhairi, Nan ma Mama tayi masa godiya.
Mama tace "Mufeeda kawo masa kayan É—aurin Auren shima"
Ammar yace "A'a a barshi yana sauri ne"
Mama tace "Ai ba'ayi haka ba, kazo mana taro kace ba zaka karɓi komai ba"
Mufeeda Ta shiga ta haÉ—o masa kayan É—aurin Aure fal viva, kaji da lemuka, kayan snacks, Alewa da goro seda ta cika viva da shi, da ta fito da ledar Seda Mama ta bita da kallo ganin haukan da Mufeeda tayi, ba damar tayi magana tunda a cikin taro ne.
Yana tafe tana biye da shi har bakin Napep É—in sa, yace
"bani key ɗina kuma bazan ƙara zuwa gidan ku ba"
"Saboda me?"
"Saboda kin fiye rawar kai, ni kuma bana son rawar kai"
"to yi haƙuri na dena"
Wani kallo yai mata sannan yace "bani mukulli na in tafi"
Miƙa masa key ɗin sa tayi, Amma ta tsaya a jikin Napep ɗin ta zubawa Ammar ilahirin idanuwan ta tana ƙare masa kallo.
A ran ta tace "Masha Allah gaskiya Ammar yana da kyau"
Ammar ya fara fusata da lamarin Mufeeda, dan dana sanin zuwa gurin É—aurin auren ma yake, a zuciye yace
"ke Matsa zan tafi, kin sani a gaba kina ta ƙare min kallo"
Memakon taji haushin tsawar da yayi mata, sajen sa ne ya ƙara birgeta, ga ƙamshin turaren sa duk ya gauraye gurin a hankali cikin wani salo me cike da jan hankali ta furta
"Yaya Ammar"
Wani Yarrr yaji a jikin sa, tsigar jikin sa ta tashi sakamakon yadda ta furta sunan nasa, É—agowa yayi yana kallon ta
"Yaya Ammar se yaushe?"
Kallon ta yayi galala
"kamar ya se yaushe? Me zanzo inyi miki? Kin bar kayan ki na kawo miki, kin gayyace ni biki nazo miki, me kuma ya rage?"
"Alfarma É—aya nake so kamin Yaya na"
"Ina jinki"
Seda ta ƙara kwantar da murya cikin shagwaba tace
"Zaka min kuwa?"
Gaba ɗaya yadda ƙwailar yarinyar ke magana na nema ya jefa shi cikin wani yanayi dabe zata ba.
A ƙagauce yace "ina jinki"
Miƙa masa wayar ta tayi ta ƙara ƙasa da muryar ta tace
"dan Allah ka samun lambar ka Yaya na"
Hararar ta yayi yace
"ke bana son damu bana son shirme matsa ki ban guri, ko in bige ki da babur É—in nan"
Noƙe kafaɗa tayi "Allah bazan tafi ba se dai muyi ta tsayuwa, ko ka bigeni da babur ɗin, kuma fa ba damun ka zanyi ba, gaisawa kawai zamu dinga yi fa"
Dafe kai Ammar yayi, wasa2 sun kai mintuna Ashirin a tsaye a gurin nan.
"ke wai bakya ganewa ne ko ba kya ji? Ki matsa nace!"
Seda hantar cikin ta ta kaɗa, Amma memakon yaga tsoro ko karaya a fuskar ta, ɗan rintse ido kawai tayi alamar bata son shouting, ta buɗe idon ta ta kalleshi, ta langaɓar da kai tace
"please Yayana nifa ƙanwarka ce why are you shouting at me? Allah bazan takura maka ba"
Ta miƙo masa tanfatsetsiyar wayar ta, ganin Mufeeda na neman ɓata masa lokaci, kuma ci gaba da tsayuwar su haka zata jefa shi yanayin da ze sha wuya, ya karɓi wayar a gaggauce yasa mata lambar sa ya miƙa mata wayar ta.
Karɓar wayar tayi tare da yin murmushi tace "Nagode Yaya na, Allah ya baka ladan zumunci ka gaida su Mama"
Ta matsa daga jikin Napep É—in ya kunna yayi gaba yana mamakin hali irin na Mufeeda.
Ta juya zata shiga gida, ɗan Autan su Umman ta ya kira ta, ƙarasawa inda yake tayi, ya kalleta yace
"Mufeeda waye wancan?"
"Yaya nane"
"kamar ya Yayan ki?" É—an tura baki tayi tace "dan Allah Uncle karka tsanan ta bincike mene ne?"
Girgiza kai yayi yace "tun ɗazu Yaya ke nemanki, tace ta baki Abinci ki kaiwa ƙannen baban ku, Amma babu ke babu saƙon"
Se yanzu ta tuna dire tray ɗin tayi ta tafi gurin Ammar, taɓdijan ashe zata kaɗe a gurin Mama
"Uncle zomu koma gefe tambayar ka zanyi"
Ba musu ya bita suka samu guri suka zauna tace
"uncle dan Allah me yake sa kaji kana tunanin mutum? Ko ka dinga son ganin sa ko yawan mafarkin sa"
Murmushi yayi yace "Autar Baba kenan, Soyayya ke kawo haka"
Murmushi tayi ta miƙe tace "nagode uncle" tayi gaba abun ta.