← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 64

Sashe 56

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D. P. O yace "to Hajiya kinji, kina ta zaƙewa a Bima ta haƙƙin ta da kin haƙura anyi sulhu da haka bata faru ba, kinga yanzu dole mu haɗa da ita saboda abunda suka yi babban laifi ne kuma dole a hukunta su tare"

Maman Fa'iza tace  "Fa'iza abunda kikayi kin kyautatawa kanki kenan, duk yadda na rarrashe ki akan ki haƙura da batun Ammar baki haƙura ba shine zaki kashe masa Aure, Yarinyar da babu ruwan ta baiwar Allah tsakanin ta mutane girmamawa, shikenan kije dan kanki, duk hukuncin daya dace ai mata ayi mata officer "

Abubakar yace " A'a Mama be kamata a barta a nan ba tunda mace ce, abamu belin ta amma dole Ammar yazo gurin nan ku gaya masa abunda kukayi, wallahi kaji kunya Faruk kaci Amanar Ammar "

****************

Ammar daya fita, gidan Alhaji Idris ya wuce yasa aka yi masa sallama dashi,
Koda Alhaji Idris ya fito yaga Ammar ya wani yatsine fuska, Ammar be kula da yadda Alhaji Idris ke masa kallon ƙyama ba yace
" Dama nazo ne muyi magana ta fahimta da kai, na samu labarin kana bibiyar mata ta wai kana sonta, kuma ta gaya maka matar Aure ce ita, da farko naso in kaika hukuma kai tsaye amma naga gara inzo muyi magana nida kai, a matsayin ka na dattijo be kamata inyi maka haka ba, shiyasa nazo da kaina gurin ka dan Allah ka fita harkar mata ta, nine mijin ta tana da Aure dan Allah ka fita harkar ta"

Wata irin dariyar ƙet irin na riƙaƙƙun 'yan duniya Alhaji Idris yayi, sannan yace
"hmm yaro man kaza, ai ita duniya faÉ—i ne da ita meye a ciki dan naga matar da bata dace da kai ba nace ina so? Ai ba wani abu dan tafi da cewa dani dan.....

" Rufemin baki tsohon banza dana wofi, nazo maka da niyyar muyi magana ta kirki amma kaƙi i will show you what am capable of doing, Wallahi badan da hukuma ba da da kaina zan illa taka, an gaya maka mata ta irin sakarkarun matan banzan da karnuka irin ka suke bine? Wallahi inba Allah daya bani ita ba babu me iya rabani da ita, kuma bari kaga hukuma ce zata rabani da kai"

Alhaji Idris yace  " Nikuma zan nuna maka tasiri, da kuma ƙarfin da dukiya take dashi, zanyi Amfani da hukumar da dukiya ta in wulaƙanta ka, kana kallo matar da kake taƙama da ita talauci seya sa ta tsere ta barka, ba dai ni kazo ƙofar gidana kana ɗagawa murya ba, zaka gani sena jefa ka cikin talaucin da babu me ciro ka"

"ƙarya kake munafuki, Allah baya barin zalunci kuma idan taƙamar ka dukiya wanda yayi ka ya baka dukiyar shize maganin ka" Ammar ya juya ya bar gurin cikin zafin nama da tafasar zuciya.

Wasa2 har ƙarfe takwas na dare, babu labarin Inda aka kai su Maman Nur, mazajen su na ta yawo gidajen radio suna sanar da sojoji sun kwashe musu mata basu san inda aka kaisu ba, wadda tasa aka kwashe su an nemeta an rasa shikenan anyi kidnapping ɗin matan su.

Se wajen sha ɗaya na dare aka bada sanarwar cewa, ba wanda ya sace su Sojoji da suka zo suka tafi dasu State CID, sashen kula da manyan laifuka, ana zarginsu da tada tarzoma a unguwa da yunƙurin yin kisan kai ta hanyar dambe da illata junan su da suka yi harda karya ƙafar Jariri da dasa masa kai.
Haka mazajen su da 'yan uwan su suka É—unguma suka tafi State CID amma aka hana su shiga akace su koma dare yayi.

Inda aka kaisu Maman Sadiq kamar kabari, ga matsi ga sauro na Jaraba a gurin nan ko juyi ba zaka iya yi a ciki ba, ga gurin se tsami yake yana wari, ko Abinci babu wadda taci haka suka dinga kuka a gurin nan, Sa'idu kuwa Hajara tace a kai shi barrack a koya masa discipline idan ya kwana bakwai a miƙawa 'yan sanda shi suyi binkice a kai shi kotu a tuhume shi akan haɗa fitina da bibiyar matan mutane.
Aikuwa Sa' idu yaga masifa, dan ba ƙaramin tumurmusa yasha a hannun sojoji ba, gashi gaba ɗaya cinikin sa an kwashe a gurin dambe, an watsar masa da kayan miya, ɗan babur ɗinsa na can, ga duka daya sha gashi an sashi tsallen kwaɗo ko iya tashi ba yayi.

Ammar Yana zuwa gida É—akin sa ya wuce ba tare da ya kula Mufeeda ba, tana ganin haka tasan a zuciye yake, seda ta bari kamar awa É—aya da dawowarsa sannan ta tafi É—akin nasa bakin ta É—auke da Addu'oi.

Ya ƙule akan gado zuciyar sa tana ta tafasa, wai shi wannan tsohon banzan ze kalli tsabar idonsa yace wai yana son matar sa, matarsa ta Aure

(ba dai kace ƙwaila bace? Ai wani ƙwailar yake so 🤭🤭🤭)

Kan gadon sa ta hau cikin murya me sanyi tace 
"Mijina koba ka faÉ—amin ba nasan a cikin damuwa kake, shiyasa tun a baya na kasa gaya maka abunda ke faruwa, idan ina ganin damuwa a fuskar ka ji nake tamkar zuciya ta tayi bindiga"
Ta matsa kusa da shi ta rungume shi ta fara shafa sumar kansa, kaman me raɗa tace  "dan Allah ka kwantar da hankalin ka, karka sani cikin damuwa dan ina kana fushi gani nake kamar a duniya nika ɗai aka tsana, kayi haƙuri Mijina Allah yana tare damu, kayi haƙuri, Allah yana son bawan sa me haƙuri kuma baya barin zalunci nasan baze wuce gurin wannan mutumin kaje ya ɓata maka rai ba, sam mutumin nan babu Allah a ransa"

Ƙara rungume Mufeeda yayi a jikin sa kamar wani ze ƙwace masa ita, ya dinga shaƙar ƙamshin turaren ta kamar me koyar magana yace
"Mufeeda kina sona?"
"Surely, with all my heart, karka manta Soyayya ce tasa na Aure ka a lokacin da bana zaton kai kana sona"
"Mufeeda" ya kuma kiran sunan ta
"Na'am abun sona" ta amsa masaz
"zaki iya rabuwa dani?"
"Babu wani dalili bayan mutuwa da ze rabani da kai, in ba da ƙwaƙwarar dokar Addini ba"
Ya ƙara rungume ta yace  "Mufeeda ban taɓa Soyayya ba se akanki, ban taɓa sanin haka Soyayya take ba, Mufeeda"
"Na'am My Ammar"
"Ban san meye kishi ba seda na zauna dake, ke kika koyamin Soyayya, seda na fuskanci meye Soyayya sannan na gane na fara sonki ne ranar da na fara ganin ki, na ɗakko ku a babur ɗina, Salon ki na daban ne, na riga na saba da komai naki, bana tunanin akwai wanda ze iya jurewa zama dani kamar ki, na saba da ƙuruciyar ki, Nishaɗinki, haƙurin ki, ladabin ki, da kuma kawaici bana tunanin akwai macen data haɗa dukkanin abunda kika haɗa, ko akwai ta nike kawai nasani, Mufeeda komai naki yana burgeni, komai kikayi looks beautiful to me"

Shiru Yayi yana sauke ajiyar zuciya, yayin da hannayen Mufeeda ke
cigaba da shafa sumar kansa tare da mamakin jin wannan kalamai da suke fitowa daga bakin Ammar, ko wane lokaci tayi abu dan ta birge shi baya kulawa, Ashe yana jin daÉ—in abubuwan da take masa tankawa ne baze ba se yau data ciyo shi.
Tana cikin tunanin ne ya sake kiran sunan ta, bata gaji ba ta sake amsa masa
Ammar ya É—ora da cewa "Rayuwar Ammar ba zata cika ba idan babu ke, Mufeeda ban san haka kishi yake ba, wanda na nuna a baya ashe shirme ne, seda wani ya tsaya a gaba na yana gayamin wai yana son abunda yake mallaki na, sannan na gane menene kishi, wallahi zuciya ta kamar tayi bindiga, badan ina tsoron abunda ze biyo baya ba da sena illa tashi sedai kome ze faru ya faru"
Tana jin yadda jijiyoyin kansa suka miƙe, jikin sa ya ɗau zafi ga bugun zuciyar sa dake fita da sauri saboda ɓacin rai.

"Mufeeda takace kai kaÉ—ai mijina, bana ganin kowa idan ba kai ba, Yaya Ammar Allah daya haÉ—ani da kai shine kaÉ—ai na yadda ze rabamu, ina maka so irin wanda baki be isa ya bayyana ba, ka kwantar da hankalin ka dan Allah, ni kai nake so ba wani mahaluki daze iya raba mu"

Ta ƙara kwantar da murya cikin sigar shagwaɓa da rarrashi tace  "dan Allah ka kwantar da hankalin ka, karka illa ta min kanka, kaji fa Babyn ka ma yana cewa  sorry Daddy we loves you "

Duk da a cikin ɓacin rai Ammar yake seda yayi murmushin abunda ta faɗa yana shafa cikin nata.

Mufeeda tayi iya yinta gurin samarwa da Ammar farinciki tare da gusar masa da dukkanin damuwar da yake ciki, suka nunawa juna tsantsar soyayya da ƙaunar juna.

*****************

Da safe Ammar ya tashi da farinciki yadda Mufeeda keta ƙara bashi kulawa duk dan ya saki ransa, gefe ɗaya idan ya tuna Alhaji Idris se yaji kamar yaje ya ɗau doka a hannun sa, Amma dole in ya fita yanzu yaje Hisba ko gurin 'yan sanda ayi masa tsakani da shi da iyalinsa.

Mufeeda kam idan ta tuna irin kalaman da Ammar yak mata jiya seta jita tamkar a wata sabuwar duniyar masoya, bata taɓa tunanin jinsu daga bakin Ammar ba, bata taɓa zaton yana jin daɗin abubuwan da take masa ba se jiya.
Yanzu ma da kanta take bashi Abinci tana masa hira, ya saki jiki yaci sedai ita Mufeeda ba wani ci tayi ba.

Ya janyo ta jikin sa yana shafata yace  "ƙwailata dan Allah kj dinga cin Abinci karki haifo min  yaro a rame"

Ta tura baki tace 
"Nifa ban gane ba ana cemin ƙwaila kuma a dinga mazewa a zomin ɗaki in dare yayi ba"

Dariya Ammar yayi yace  "tunda kika ce ke Aure kike so ai so kike ki zama babba, gayamin me kike so in siyo miki"

Da sauri tace  "ɗanyen mangwaro"

Ɗan tsuke Fuska yayi yace  "meye wani ɗanyen mangwaro ina maganar arziki kina wani ɗanyen mangwaro"

"Aini maganar Arziki a gurina yanzu ka baani É—anyen mangwaro"
Chapter 56 · 0% Book details