Sashe 63
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon rashin yadda Ammar yake wa Alhajin, Alhajin ya miƙa masa mukullin motar, jiki a saluɓe Ammar ya karɓa yakasa cewa komai, Ya rubuta masa Account details ɗin ya bashi. Hakanan Ammar ya tsinci kansa da kasa musawa Alhajin saboda dattijantakar sa.
Ammar ya kai kuɗin ya karɓo receipt ya dawo kasuwa Amma Alhajin baya nan ya fita amma ze dawo.
Ammar ya zauna ya jira ko gurin tasa sana'ar beje ba, se bayan la'asar sannan Alhajin ya dawo, yana zuwa ya tarar da Ammar, yace
"Yi haƙuri Ammar, na zaunar da kai, da kasani ka tafi, ka kawomin receipt ɗin daga baya"
Ammar yace "A'a gara dai dana jira, gashi, kuɗin million bakwai ne ba biyar ba"
Ya miƙa masa receipt, yasa hannu ya karɓa ya dinga juya receipt ɗin yana kallon Ammar, yana nazarinsa, yace
"Nagode sosai Ammar, na É—auka " ya zura hannu a Aljihu ya É—akko bandir É—in kuÉ—i naira dubu É—ari ya bawa Ammar.
"A'a bazan karɓa ba, ba seka biyani ba"
"Ammar ba biyan ka nayi ba, kyauta ce fa"
Girgiza kai Ammar yayi yace "Nagode, Amma ka barsu" daga nan ya juya ya tafi.
Jabir ya fara gane kuskurensa, dan satin Fatiyya biyu bata girki sedai suci takeaway, ga yawo kamar masifa, bashi da ikon ya tambaye ta ina taje? Ko ina zata? Data raya mata seta fice abun ta, sekuma ya ganta, be isa tayi abu yayi magana ba seta balbale shi da masifa, ga rashin kunya da ƙazanta, zata gyara jikin ta Amma banda mahallinta, ga gayyar ƙawaye kowa ƙawar ta ce, Abun duniya ya fara damun Jabir, da yana ganin Saima bata iya komai ba, se gashi Fatiyya kamar rainon gaɓaye jaka take, ko magana bata iya ba, ga rashin kintsi.
A hankali Alhaji Haruna yake karantar Ammar, Ammar ba ruwan sa da kowa, da yaje kasuwa abunda ya kaishi kawai yake yi, dan ko Abokai bashi da su.
Alhaji Haruna duk lokacin da ya tashi Aiken kuɗi seya aiki Ammar, kuɗi bana wasa ba maƙudan kuɗi masu nauyin gaske.
************* *********
Ammar kafin ya fita se yayiwa Mufeeda aikin gida, da daddare ma idan ya dawo haka, wataran kuma ya kira Halima a waya yace tazo ta taya
Mufeeda aiki, Ammar yace idan cikin ya cika wata tara ze maida ita gida koda Naƙuda zata tashi baya nan.
Ranar data shiga wata na tara, Cikin dare kusan ƙarfe biyun dare labor ya kama Mufeeda, tashin Ammar tayi a gigice tana jin ciwon har cikin kanta.
Gaba ɗaya Ammar ya ruɗe, tausayinta ya kama shi, kamar ze kuka yace "Sannu Mufeeda, bari in fita inga inda zan samo abun hawa"
Riƙe shi tayi gam ta hana shi fita ko ina, se salati take, vest ɗin Ammar kuwa da ta riƙe ta seda ta tale har cikin sa.
Ta dinga sintiri a ɗakin, Ammar ya kasa fita, gani yake daya fita wani abun ze sa meta, se Addu'a yake Allah ya raba ta da cikin lafiya, tun tana iya tafiya harta durƙushe tana ambaton Allah.
Waya Ammar ya ɗakko a gigice yana ƙoƙarin kiran waya, kawai yaji kukan Jariri yana ɗaga kai yaga Mufeeda ta haihu yaro Jariri yana ta tsala kuka.
Jifa yayi da wayar ya taho kanta da sauri, ya riƙo hannun ta yace
"Sannu Mufeeda" murmushi tayi masa tare da gyaÉ—a kanta, ta nuna masa Akwatin da ta shirya kayan haihuwar ta, kamar yadda Mama ta gaya mata, ta nunawa Ammar yadda ze yanke cibi da komai.
A ƙarshe dai Ammar ne ya gyara komai, hatta kayan jinin data ɓata da ɗakin shi ya zage ya gyara su tsaf.
Dama Mama ta koyawa Mufeeda komai, in case haihuwa zata ka mata babu wani a kusa.
Kamar ba Mufeeda ce tayi labor ba, ya dafa mata ruwa tayi wanka ta kintsa jikin ta, Jaririn ƙato dashi se kuka yake yi.
Haka Ammar ya rungume Mufeeda da Jaririn yana godiya ga Allah, wai Yau ƙwailarsa ce ta haifa masa Jariri, waze maka wannan kyauta inba Allah ba, Ga mace ta gari ga ɗa.
Da safe duk wanda suka kira suka ce Mufeeda ta haihu se yaita mamaki, Mussman idan akace ita kaÉ—ai ta haihu, kafin kowa yazo gidan Ammar ya share ko ina ya dafa Abinci taci.
Da Mama taje gidan tayi mamaki taga ko ina tsaf, Mama tace
"Auta dan Allah ke kaÉ—ai kika haihu?"
"Hajiya Mama kenan, wallahi da gani se Yaya Ammar, Allah ya bani da sauƙi ko ciwon mara da kikace banji ba lokaci ɗaya ciwon ya taso min cikin dare"
"Sannu Autar Mama, ga farfesu nan na taho miki dashi ki samu kici"
"A ajiye se an jima, Yaya Ammar ya dafa Abinci naci"
"Ikon Allah, lallai Allah yasaka wa yaron nan da Alkhairi"
Kwana uku da haihuwa Ammar ya shigo da wata ƙatuwar Akwati, wanda suke ɗakin Mufeeda suka fito suka basu guri.
Ammar ya kalle ta yace "Ƙwaila ta Ammar"
Ta tura baki tace
"Ai wallahi na zama mace, tunda na haifi wannan me kukan"
Murmushi yayi yana jan hancin ta, ya turo mata Akwatin gaban ta, ya karɓi yaron ya kwantar da shi, Sega Ammar yana ɗaukar Jariri, da baya ɗauka dan gani yake yayi ɗan mitsitsi dayawa.
Cikin Mamaki ta buɗe Akwatin, kayan Jariri ne, duk abunda ake buƙata kayan wanka diapers ba abunda babu, itama ga sabon kaya kala uku da turaruka da sabon takalmi da Jaka.
"Kayan robobin kuma suna É—akin tsakar gida, na siyo fulawa da shinkafa, abun hakika kuma Abba ya bayar, sannan kuÉ—in da muke tarawa na bar miki nawa da nakin, seki haÉ—a ayi hidimar suna"
"Yaya Ammar, ina ka samu kuÉ—i haka muna fama da kanmu? Yaya Ammar meyasa ka takura kanka"
"ba takura bace, haƙƙina ne inyi, kuma na daɗe ina tara kayan, Anty Maryam nake bawa kuɗin ta siyo, fatana Allah ya barmin ke, sannan ya raya mana Ibrahim Khalil a tafarki madaidaici ina Alfahari dake Mufeeda"
Rungume Ammar tayi tana kuka tace
"Allah ya ƙara Arziki Mijina, Allah ya baka abunda kake nema duniya da lahira, mungode, mungode, we loves you Abu Khalil"
"Mentioned it not sweetheart, ni yakamata inyi godiya"
Ta tattare kayan ta kira Mama tace "Mama ku tayani godiya, kinga siyayyar da Yaya Ammar yayi mana"
Nan ma Mama taita Addu'a da saka Albarka.
Yaya Fadeela tace "Mufeeda gaskiya ki bani sirrin wannan soyayya haka, Allah sarki nan muka dinga surutan kinyi ƙanƙanta da Aure yayi miki girma, kawai se mu gaki da ɗa, ohh Auta manya"
Mufeeda tace "kyaji dashi dai"
********************
Abun duniya ya ishi Jabir, Fatiyya tasa shi gaba da rashin mutunci ga gori na masifa, gashi ba damar ya kai ƙararta gidan su, ba akaiwa iyayen ta ƙara ɗan su, gantali ga
Almubazzaranci, daga iyayen sa har 'yan uwan sa basu isheta kallo ba.
ÆŠaure take da towel ta fito daga cikin banÉ—akin dake cikin É—akin hotel É—in, ta kalli mutumin dake kwance akan gado yayi É—aiÉ—ai, ta É—an yamutsa fuska tace
"Alhaji ka tashi kayi wanka ka maida ni inda ka É—akko ni, bana jin daÉ—i"
Washe baki yayi yana shafa cikin sa yace
"Fatiyya manyan mata, nifa banƙi mu kwana anan tare ba"
HaÉ—e rai tayi tace "Kafiye wasa, dan Allah ka tashi jini nake zubarwa fa"
Zaro ido yayi yace
"jini kuma? meya haÉ—a ki da zubar da jini?"
"Inaga ciki ne dani fa, kamar ɓari zanyi"
Alhaji Idris yace "ke se kace ba wayayyiya ba, tun abaya da muke tare da ke baki yi ciki ba se yanzu? Daga yin Auren seki bari kiyi ciki"
"Kaga nifa ban san da cikin nan, dan Allah kayi ka maidani, dan banzo da mota bane da bazan tsaya jiran ka ba"
"Kai Amma ban gama shagali na ba kin katsemin jin daÉ—i"
"Koma meye ai kaine ka janyo shi, dan Allah Alhaji Idris kayi sauri"
Haka ya tashi ya shiga yayi wanka, sedai me yana fitowa ya tarar da ita a kwance kamar ba rai a jikin ta jini ya malale a gurin.
A gigice ya zaro ido, ya dinga jijjigata yana kiran sunan ta Amma shiru, bata Amsa ba, da gudu yasa rigar sa ya fice, fitar tasa tayi dai2 da kawo Abincin da suka yi order, yaga Alhaji Idris ya fice da sauri, da sauri ma'aikacin yabi bayan Alhaji Idris yaga ya shige mota ya, aikuwa ya haddace lambar motar sa.
Ya koma É—akin ya tarar da Saima a kwance cikin jini male male.
Ranar suna Jariri yaci suna Ibrahim Khalil, Dai2 gwargwado anci ansha, Ammar yayi bajinta daidai ƙarfin sa.
Mufeeda ta samu Alheri sosai.
Anty Murja ce ta zaunawa Mufeeda saboda jego, Sam Ammar da Mufeeda basa jin kunyar Anty Murja, su barta da rainon É—a su shige É—aki suyi ta cin dariyar soyayyar su, Anty Murja tayi mamakin yadda Ammar yake barkwanci da dariya haka, yadda yake haÉ—e rai da miskilanci idan za'ace yana magana ma seka Musa, Amma wataran a falo suke soyayyar su shida Mufeeda, ba ruwan su da idon Anty Murja.
Ranar da Ammar ya koma kasuwa Alhaji Haruna yasa aka kira masa shi, Ammar yaje suka gaisa.
Alhaji Haruna yace "Ammar kwana biyu baka shigowa kasuwa lafiya kuwa?"
"lafiya ƙalau, me ɗakina ce ta haihu shiyasa"
"Masha Allah, Amma babu Labari, Allah ya raya abunda aka samu, Amma gaskiya zanzo har gida in ga Jariri"
Ammar yace "to Nagode sosai, Allah ya kawo ka"
Bayan Alhaji Idris ya bar hotel ɗin nan ya gudu ya bar gari, yana ta shirye2 barin ƙasar aka kira shi a waya aka sanar masa hukumar custom sun kama kayan da yayi order, Nigeria bata buƙatar irin wannan kayan, gaba ɗaya ya gigice ya rasa abunyi, gaba ɗaya dukiyarsa ya narka akan kayan nan Amma wai custom sun kama kayan.
yana ƙoƙarin kiran abokin
kasuwancinsa 'yan sand suka zo suka kama shi a gurin.
Jabir ya shiga tashin hankali jin A hotel aka ga matarsa tayi ɓari, kuma abokin iskancin nata ya gudu, Jabir yayi kuka, dan yasan Alhakin Saima ne ya kama shi.
Ya shirya ya tafi gidan Gwaggon Saima, yasa aka yi masa Sallama da ita, ba tasan ko waye ba ta fito, tana ganin Jabir ta haÉ—e rai tace
"malam me kake mana a ƙofar gida?"