Sashe 33
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammar ya haÉ—e rai yace
"kinga idan baki bari ba zan tashi yanzun nan in bar miki gidan"
"Allah in baka bani ba zanƙi cin Abincin yau"
"to karki ci mana cikina ko naki?"
"cikina ne, Amma ni bazan iya zama ina kallon abun ƙauna ta beci Abinci ba, dama nasan baka sona"
"Dama na taɓa cewa ina sonki ne?"
"Baka taɓa cewa kana sona ba, Amma nasan ana sona ko ba a gayamin ba na riga na sani"
Kallon ta yayi ta É—ago itama ta kalle shi tare da kashe masa ido.
"Ni dai bance ina so ba, saboda a yanzu dai raino kawai nake yi, ni banga abun so a gurin ƙwaila ba, banda rawar kai da Yarinta babu abunda kika iya"
Ta gyaÉ—a kai tace "Shikenan nagode, Nikam har zuciya ta idan nace ina sonka, to ina nufin abunda na faÉ—a"
Ta miƙe ta koma kan Kujera tai shiru, ƙarshe ma ta kwanta ta rufe idon ta, Yanayin yadda yaga ta yine ta ɗan bashi tausayi, Amma dai bece mata komai ba ya kammala breakfast dinsa, kaman ya miƙe yaje yai haramar Fita, se yaga be kamata ya tafi ya barta tana fushi ba duba da Yadda take shiga damuwa idan taga baya walwala.
Hannunsa ya Miƙa ya ɗan ja yatsan ƙafar ta, a hankali ta buɗe ido ta kalle shi,
"Sakko in baki Abincin, kar inje kice bana baki Abinci"
Ba tace komai ba ta Sakko tazo gaban sa ta zauna, Yanayin Fuskarta ya nuna ƙirirs take jira tayi kuka, dan ba ƙaramin haushin abunda Ammar ya faɗa taji ba.
Ya haÉ—a mata abun karyawa ya kalleta yace "dawo nan" ya nuna mata inda zata zauna daf dashi, ta matsa ta zauna ya fara bata Abincin a baki tana ci.
Ya É—an girgiza kai yace "Rigumammiya kawai se kace 'yar Yaye"
Tura baki tayi tana sosa gefen fuskarta, tamkar irin shagwaɓaɓɓun Yaran nan.
"Na ƙoshi fa"
"kin ƙoshi wa kike nufi ya cinye ragowar ki?"
"To ai na ƙoshi cikina ya cika"
"ɗan wannan Abincin ne kika ƙoshi, oya buɗe bakinki ki cinye sauran"
"Allah in kace se naci zan iya yin Amai"
Haɗe rai Yayi yace "kenan ɗan wannan Abincin kikeci shiyasa ba kya ƙiba, sekin cinye"
Hannu tasa ta É—aga rigarta tace "kalli fa cikina ya cika sosai"
"Nagani rufe" ta sauke rigar ya ɗan ƙura mata ido sannan yace
"Allah ya shirye ki"
"Mekuma nayi?"
"A'a bakomai Addu'a kawai nayi miki"
Ƙarshe Ammar ne ya tattare Kwanukan, dan yau rikici take ji sosai.
Yana shirin fita ne yaro yayi Sallama da yake yau gidan a buÉ—e yake, Mufeeda ta amsa ta fito tsakar gida, ta kalli yaron tace
"Ya akayi ne?"
Ya miƙo mata kofi yace "wai gashi inji Umman mu wai dan Allah ki ɗan zuba mata madara da milo zata sha tea, idan kina da Butter ki ɗan san mata taci bredi"
Mufeeda tace "ayya ka koma kace mata dan Allah tayi haƙuri, bani nake siyan kayan ba, me gidan ne yake siya kuma bana bayar da abu seda izinin sa"
Yaron yace "to" ya juya ya tafi.
Ta koma falo tana tsaki,Ammar da yaji yadda suka yi da Yaron yace
"Meyasa baki basu ba? Kefa kikace abunda ka bayar shine rabon ka"
"hmm Yaya Ammar kenan, ina sane na hanasu, kai baka san wannan rainin hankalin na wasu matan ba, ranar suka shigo nan suka nemi su rainamin hankali dan sun ganni ƙarama, Yanzu dana basu shikenan sun Sami gurin zuwa, duk abunda ka siyo tare zamu yi amfani da shi, duk nasan irin wannan abubuwan tun a unguwar mu"
Ammar yace "Kinga kowa rainaki yake saboda ke Baby ce, kowa yana miki kallon Yarinya, waini gayamin ma me yasa kika ce kina son Aure ne a shekarun nan naki?"
"Saboda nima Mutum ce, kuma ina son kasancewa da abunda nake so, zuciya ta ta makance bata ganin kowa a wannan lokacin in ba kai ba, ni dai nasan ina sonka sosai, kuma bazan iya cewa ga dalilin da yasa nake son naka ba, koda yake na maka ƙanƙanta kuma baka sona amma shi so babu ruwan sa, karka makara rana ta fara yi fa, Adawo lafiya "
Ta juya ta koma ɗakin ta, Shiru Ammar yayi na wani ɗan lokaci daga baya ya miƙe ya fita sam beji daɗin yadda sallamar su ta kasance yau ba duk se yaji babu daɗi.
Koda yaro ya koma ya gayawa Maman sa Saƙon Mufeeda take bala'i
"Jimin 'Yar matsiyata babu a house anzo gidan miji an samu shine zata yiwa Mutane Iskanci, bata san mune masu unguwar ba, in ba tayi wasa ba sena sauke mata wannan wulaƙancin da take ji dashi se zaman unguwar nan ya gagare ta" haka ta zauna ta dinga mita tana Masifa.
Daga ƙarshe dai haka ta saka Mayafin ta ta fita yin cefane, gurin me kayan miya taje ta tarar da mutane sosai a gurin ta samu guri ta zauna. Seda ya ɗan sallami Mutane sannan ya kalleta yace
"uwar biyu me za'a zubo miki ne?"
Ta gaya masa abunda ze haÉ—a mata, sunayi suna hira da Sa'idu me kayan miya.
Sa'idu Yace "Amma Maman Nur wannan ne watan haihuwar ki naga da ƙyar kike tafiya"
"Wallahi kuwa sa'idu a wannan watan nake sa ran haihuwa duk na gaji da cikin nan wallahi"
"Ai se haƙuri tunda kin kusa saukewa, mudai fatan mu ki haihu Asha suna muci shinkafa"
"Hmm Anya shinkafar nan kuwa, ai abun se Addu'a kasan Baban Nur da wulaƙanci wani lokacin, yaci basussuka sun masa Yawa, muna ta rigima da shi akan abunda ze bani na taro waishi bashi da kuɗi, ni ko ba abunda ya dameni so nake in fita kunya, kaga su Maman Amir ɗin nan ba ƙananan munafukai bane, Alla Alla suke in haihu suga abunda zanyi kallon su kawai nake, ina zan bari suga walle na"
Sa'idu yace "gaskiya kam be kamata ba"
Yana cikin haÉ—a mata kayan miyan ne sega Maman Amir itama tazo yin cefanen.
Suka gaisa ta kalli Maman Nur tace "Maman Nur ina su Nur É—in kika fito cefane da kanki?"
"wallahi suna makaranta, ga gidan ba kowa kin ganni ko karyawa banyi ba na fito kafin kayan miyan su ƙare"
Maman Amir tace "maman Nur kidena zama da yunwa fa, kina É—auke da ciki kina wasa da Abinci"
Me kayan miya yace "gaya mata dai"
"Hmm kin san me maƙwaciya ta tayi min? Wai na aika ta sanmin Milo in sha tea, amma ta hanani"
"Haba dai ke dama seda na gaya miki Yarinyar nan ba Mutunci za tayi ba"
Me kayan miya yace "Wai wace Yarinyar ce ne?"
Maman Nur tace "wata 'yar mitsilar Yarinya ta jikin gida na, matar wannan me a daidaita sahun, banza bata saba sha a gida ba, anzo birni ana iskanci"
Suka haÉ—u suka dingayi da Mufeeda suka zage ta tsaf a teburin me kayan miya
(Mata kenan Allah ya shirya)
*********************
Yau Ammar be dawo da azahar ba, se bayan sallar isha'i ya dawo, ya É—auka ze dawo ya tarar da ita yadda ya barta amma yana dawowa ta É—an tsuke fuska cikin shagwaba tace
"shine se yanzu ko? Ina ka tsaya yau baka dawo da wuri ba?"
"inda kika aikeni" ya bata amsa
Tayi murmushi tare da duƙar da kanta tace
"Allah ya bada haƙuri, Allah ya huci zuciyar Manya"
ÆŠan Murmushi yayi yace
"ban Abinci, tunda na fita banci komai ba"
"Bana hana zama da yunwa ba?". Tai ƙasa da muryar ta tace "idan aka ƙara se nayiwa mutum abunda baya so"
Ya kalleta yace "Mene bana son?"
"Idan ka kuma zanyi ka gani, ko in maka tausa ne? Naga ka gaji da yawa"
Da sauri yace "A'a bana so"
"Tausar tawa ce baka so? Zaka rage jin gajiyar"
"A'a nagode kawomin Abinci inci, ina so mu É—an fitane zaki rakani unguwa"
Ta kawo masa Abinci shima ta nayi tana damun sa.
"Yaya Ammar naga kaman gemun ka ya ragu fa"
"Eh na rage sumar kaina ne, akamin gyaran fuska"
"to kuma se a rage maka gemu?"
Ɗan tittiraza ƙafa tayi tace "Ni gaskiya dan Allah kar a ƙara rage wa, haba dan Allah ni ina son gemun fa"
" zanje kuwa a aske shi gaba É—aya"
"da bazan ƙara kallon ka ba se ya fito" tai maganar tana miƙewa.
Seda ya kammala cin Abincin sa sannan suka shirya zasu fita ya kalleta yace
"Idan anyiwa mutum haihuwa me ake bashi?"
"Waye ya haihu?" ta tambayeshi
"Matar Aminu ce ta haihu har anyi suna ma, ni namanta ya gayamin"
Mufeeda ta jinjina kai tace "zaka iya sai musu rigar Baby, Amma riga tana tsada sosai indai me kyau kake son basu, amma kaman ka basu kuÉ—in kawai ina da turaren wuta, se in bata nima"
Ammar ya jinjina kai sannan suka gama shiri sannan suka fita.
Kaman haÉ—in baki suna zuwa suka tarar da Saima da Jabir a gidan.
Saima na ganin Ammar tare da Mufeeda tace
"Gaskiya munji kunya, kamar in gudu yau gani ga Amaryar Ammar ban taɓa zuwa ba"
Fiddausi tace "Ai nidai zatamin uzuri saboda nayi nauyi ne lokacin"
Mufeeda dai ba tace komai ba se Murmushi da take yi ta zauna suka gaisa da su Aminu da Matansu.
Aminu yace "Ammar se yau zaka zo kaga Jaririyar ko? Yau kwana tara da haihuwa"
Ammar yace "to komu koma ne? Ai badan Fiddausi ba ba zanzo ba, kai kaje gida nane?"
Aminu yai murmushi yace "Allah ya bada haƙuri"
Tunda suka zo Jaririyar take kuka, aka miƙawa Ammar Jaririyar, Amma sam be iya ɗaukar Yara ba, yanayin yadda ya riƙe yarinyar kasan be iya ba.
Mufeeda taje kusa da shi tace "Yaya Ammar ai ba zata yi shiru a haka ba, kalli yadda ka ɗauke ta fa, kawo ta ka gani" tasa hannu ta karɓeta, tana jijjiga yarinyar amma ba ta dena kuka ba, wuyan Yarinyar yayi ƙananan ƙuraje saboda zafi kuma yarinyar nada jiki, Mufeeda tace
"Maman Baby dole taita kuka fa, zafi take ji"