← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 64

Sashe 23

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tura baki tayi tana É—an harararsa
"ni wallahi na girma tunda baka taɓa goyani ba, ko Abinci ma da kaina nake ci ba kai kake bani a baki ba"

"Ke yanzu na baki Abinci a baki seki ci?"

"Au meze hana? Kaima fa rannan na baka a bakin nan kaci"
Tayi ƙasa da muryar ta daidai kunnen sa tace
"Kuma da'akaci ba'ayi min Comment ba, Yayi daÉ—i ko akwai abunda zan gyara a Abincin ba'a gayamin ba"

Ammar ya É—anyi murmushi yace "Aini har yanzu ina tunanin anya ke kika dafa? Saboda ci kawai nake saboda ina jin Yunwa amma ba daÉ—i"

Yau ba ƙaramin mamaki Mufeeda take ba, Ammar yana mata hira kaman a mafarki, Mufeeda ta riga ta gama gano Ammar a ɗan zaman su ta gano abubuwan da yake matuƙar so, dukda magana seya ga dama yake yi amma actions ɗin sa in tayi wani abu yasa take gane abubuwan da suke birge shi.

Mufeeda tace "to ko zamu shiga kitchen É—in tare?"

"kin isheni da surutu fa, kuma ni bacci nake ji"

"yanzu la'asar fa tayi zakayi bacci"

"eh kwanciya zan in huta"

"Abincin fa?"

"Se an jima zanci, ɗakko min pillow guda biyu a ɗaki" ba musu ta miƙe taje ta kawo masa pillow, ya jere pillows ɗin ya kalle ta yace 

"oya ga naki nan kwanta"

"Aini bana jin bacci"

"eh kwanta, nasan muddin na kwanta bazaki bari inyi baccin ba damuna zakiyi"

Kallon sa take yi, sekace wata yarinya 'yar shekara biyar É—in nan.

"ni gaskiya Yaya Ammar wanki ne dani, zan wanke kaya na da bedsheets, na haɗasu  a ɗaki se kuma inyi bacci? Bayan ina da aiki"

Ya kalleta yace "kece zaki wanke kaya su fita? kiyi jiƙa jiƙa dai, ba fita za suyi ba"

Zata kuma magana, ya janyo ta ya kwantar da ita akan pillow yace

"kar in ƙara jin bakin ki" dan yasan Mufeeda bazata taɓa bari yana bacci ita kuma idon ta biyu ba, wannan bakin nata ma ya isa ya hana shi bacci.

Haka ta kwanta tayi shiru, shima ya kwanta a nasa pillow, babu daɗewa Mufeeda ta fara ajiyar zuciya bacci ya ɗauke ta, shi kuma ya kasa baccin ƙamshin man gashin ta da tuararen jikin ta suka kashe masa jiki amma ya kasa bacci, baƙin gashin ta ya zubawa ido da yake ta sheƙi.

Jin ta fara sauke numfashi ne alamun bacci ya sashi a hankali ya kai hannun sa kanta, ya taɓa gashin nata.

Sam bata san yana yi ba, haka ya dinga shafa gashin nata a hankali na wani lokaci, a hankali Ammar ya miƙe daga inda yake kwance ya shiga ɗakin ta, ko ina tsaf dashi a ɗakin nata.

Drower É—inta ya buÉ—e yaga kayan data naÉ—e na wanki, yasa hannu ya É—auka ya wuce ta a falo ya fita tsakar gida.

A zamansu da Mufeeda na ɗan lokacin nan, akwai halayen ta da suke matukar burgeshi, duk rikicin ta da shagwaɓarta tana matuƙar bashi girma, dama Ammar mutum ne me matukar son girma, komai ya bata komai ƙanƙantar sa ta dinga godiya kenan tana masa addu'a shida iyayen sa, dukda shi in tayi abu baya yabawa, amma yana jin daɗin addu'ar da take masa, da nuna tausaya masa da take yi.

Se magariba ta buɗe ido, ta juya taga babu Ammar a gurin, ta miƙe ta duba taga ya fita beci Abincin ba, tana fitowa tsakar gida taga ya haɗa kayan sa da nata ya wanke, ya wanke napep ɗinsa a tsakar gida, mamaki ne ya cika Mufeeda, taje tai alwala tayi sallar magariba sannan Ammar ya shigo gida.

Falo ta fito ta sameshi ya zuba Abincin sa ya fara ci.
"Mijina wanki fa naga kayi min" shiru yayi mata yana danna remort, tare da tauna Abincin sa.

"Yaya Ammar ka wankemin kayana, yanzu idan akazo aka tarar kamin wanki ace matarka bata da imani, ka fita ka nemo Abinci sannan ka dawo kamin wanki"

Ya ajiye spoon din yace "ni za'acewa bani da Imani na bar wannan 'yar Yarinyar tana wanke kayan ta, hadda abun shimfiÉ—a ta"

"Amma Yaya Ammar...
" Ke Yimin shiru, kin isheni da surutu, ga leda can ki É—auka naki ne" yai maganar ransa a haÉ—e dan karta kuma magana, ta É—akko ledar ta duba popcorn ne a ciki da tarkacen chocolate.

Murmushi tayi tace 'Nagode Baby"
Harararta yayi tai saurin cewa "yi haƙuri ashe fa nice babyn, mijin baby, babyn ka ta gode Allah ya ƙara maka buɗi na alkhairi"

"Ameen" ya amsa.

Seda ya gama cin Abincin tace "Yaya Ammar dan Allah ka dinga dawowa da rana kana cin Abinci, ka dena wuni a rana".

Kaman baze magana ba se kuma yace "Idan ban wuni a rana na nemo ba, me zan baki? Me zan kaiwa su Abba?"

"Allah sarki Minjna, gobe insha Allah za'a kawo mana gara se a É—ebarwa su Umma, muma mu samu seka É—an huta na kwana biyu"

"Gara kuma? Me yasa za'a kawo gara?"

"ai duk wanda aka aurar a gidan mu Baba yana masa gara"

"ya bani 'ya, ya rangwantamin kayan aure, Sannan kuma ya bani gara abun yayi yawa ai, zan iya baki Abinci dai dai ƙarfina amma baza' a ɗora masa ɗawainiya ba, hakan tamkar na gaza ne"

Taje jikin Ammar ta kwanta a hannun sa tace  "tabbas Yaya Ammar ko ƙasa kake ɗauka ka bani zan karɓa inci ba tare da nayi ƙorafi ba, saboda nasan abunda kake da shi zaka bani, ba gazawa ce tasa Baba yake bamu gara ba, sedan sanin cewa maza kuna kashe kuɗi lokacin Aure, dan Allah yaya Ammar karka ce A'a bazaka karɓa ba"

Shiru yayi bace mata komai ba, wayarsa ce ta fara ringing, Jidda ne ke yawo akan screen É—in wayar sa, É—agawa yayi tare da yin sallama.

Suka gaisa sama sama, shi izza da rashin son raini, ita kuma jidda a fusace take da shi.
Jidda tace
"idan baka komai ina son ganinka gobe in Allah ya kaimu"

Ammar yace "zan duba inda lokacin zanzo" daga nan ya kashe wayar sa.

"Yaya Ammar wacece wannan"?
"kin fiye tambaya fa"

"Yaya Ammar kenan yanzu laifi ne dan na tambaya?"

"Yaya tace" ya bata amsa a taƙaice.

"Amma baka bani mun gaisa ba?" tai maganar tana saka popcorn a bakin ta

"zaku gaisa wataran"

"Hmm wacece kuma Fa'iza?"

"ƙanwa ta ce, cousin ɗina ce"

Ta gyara kwanciyar ta a jikin sa tace "Wadda ta kira ka rannan fa da daddare?"

"Ke É—agani ban sani ba, kin fiye tambaya"
Murmushi tayi masa tace "Yaya Ammar kenan, daka san abunda mace take ji idan taga mijin ta da wata mace daban, da baka ce na fiye tambaya ba"

Kare mata kallo yayi cike da rainin
hankali yace
"wace ce macen?"

Wani irin kallo tayi masa, ta miƙe tsaye har zata wuce ɗakin ta ta dawo ta bayansa ta sunkuyo da kanta kunnen sa 
"kowace mace, mace ce komai girman ta komai ƙanƙantar ta, tunda ɗaurin kallabin wata yarinyar yana iya zaunar mata da mutum a gida, ai nima na kai acemin mace baby na, kishin ka ne yasani nake abunda nake"

tayi kissing É—in sa a goshin sa tace
"I love you baby"

Ta juya ta tafi É—akin ta, Yayin da Ammar yabi bayan Mufeeda da kallo.

Wannan yarinyar me take nufi ne? ÆŠaurin kallabin ta yake zaunar mata da mutum a gida, to wata ke nufi kenan.
Miƙewa yayi ya tafi ɗakin sa kaman wanda ƙwai ya fashewa a ciki, yai shirin bacci ya kwanta, amma ya kasa bacci, haka kurum yau yake jin Nishaɗi, wanda ya rasa na menene, gaba ɗaya duk inda ya juya ƙamshin turaren mufeeda ne ke tashi a jikin sa, lumshe ido yayi yana tuna yadda ya farka ya ganta a ɗakin sa, da yadda ya dinga shafa gashin ta kaman kar ya dena.

Sosai Ammar ya kasa bacci, ya dinga juyi akan gadon, Seda ya fito ya sha tea sannan ya koma ya iya bacci.

*******************

Yauma yana baccin safen sa tazo ta tashe shi,

"Mijin baby ka tashi zanyi wanka"

Ya buÉ—e ido yace "dan zakiyi wanka se kinzo kin tasheni?"

"kaifa kace in zanyi wanka in maka magana ka kaimin ruwan, kace kar in sake shigar maka toilet, toilet dina ba ruwa"

Tsaki yayi ya miƙe, ya fita tsakar gida ya ɗebo ruwa a bucket ya kaimata toilet, harze fita taje gaban sa ta juya masa bayan ta
"Yawwa mijina É—an aljanna, Allah ya barmin kai saura ka zugemin riga ta"

Ƙara tsuke fuska yayi, da kamar ya share ta, amma a ransa yace
"bari in zuge mata karta zaci wani abu a ranta"

Cikin fushi Ya kama zip ɗin da nufin ya zuge mata da sauri ya fita, tana sane ta ƙwala ihu wai ya haɗa da fatar ta, kuma ƙarya take, ɗan Riki cewa yayi yace

"Subhanallah, tsaya in gani ban sani ba na haÉ—a da jikin ki"

Ƙin tsayawa tayi ya duba, ta dinga tsalle tana kuka wai ita bayan ta zafi, Ammar yace
"yi haƙuri zo in ƙara sa zuge miki, ba ina sane na haɗa da jikin ki ba"

Fuskarta harta fara hawaye, gaba É—aya Ammar yaji ba daÉ—i, zata ga kaman yana sane yai mata

"A'a ni bana so, dama tunda naga ka haɗe rai baso kake ba ka zugemin da baya na, ni ƙyaleni in ƙarasa abuna".

Tafara kici kicin cire rigar ta, ai ba shiri ya juya ya bar mata É—akin, yana fita ta zauna ta sha dariyar ta sannan ta shiga tai wankan.

Da ta fito falo taƙi kulashi wai ita lallai haushin sa take ji, ko hirar ma yau ƙin yi masa tayi tai zamanta a kujera tana tura baki.

Haka ya gama karyawa yana yi yana kallon ta, da sassafen nan maimakon ta karya chocolate take sha, kaman yayi magana amma ya ƙyaleta.

Ya gama karyawa ya kalle ta yace
"zan tafi"

Ta kalleshi tace "adawo lafiya" ta ci gaba da cin popcorn É—in ta, sabon da Ammar yayi in ze fita seta raka shi tana masa rangwaÉ—a tare da addu'a, yau da bata yi ba seya ji babu daÉ—i, yana fita kafin ya kunna babur É—in sa ta tura masa
Chapter 23 · 0% Book details