← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 64

Sashe 29

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh na gamu dake mana"

Anty Murja tace "Lallai Autar Baba, wallahi kin ƙara nutsuwa"
Suka dinga tsokanar ta.

Taji daÉ—in ganin 'yan gidan su, nan suka dinga hira, tana raha.

Sedai ba' azo da Yaya Amina ba cikin ta ya tsufa.

Mufeeda tace "Mama bari in kira shi, yazo ku gaisa"
Mama tace "A' a, ƙyale shi kar a takura masa"

Iyayen Mufeeda sunji daɗin yadda suka ga Mufeeda ƙalau da ita, alamu sun nuna gidan Ammar ba yunwa yana iya ƙoƙarin sa.

Se la'asar sannan suka yi mata Sallama, da zasu tafi Baba ya bawa Mufeeda Naira dubu goma taita godiya, suka ce ta gaida Ammar, sannan suka tafi.

Mufeeda taga uban kayan garar da Baba yayi mata, ta dinga murna tace "Allah ya biya ka da Aljanna Baba na, kwana biyu Yaya Ammar ya huta"

Bayan la'asar Ammar ya dawo, seda ta bari yaci Abinci ya huta take gaya masa su Mama sunzo.

"meyasa baki kirani kin gayamin ba?"

"Baba ne yace in ƙyale ka, maybe kana aiki kar a takura maka"

"Gaskiya banji daÉ—i ba, naso a ce nazo na tarar dashi"

"Dukan su suka zo harda su Anty Murja gaba É—ayan su"

"Naso mun haÉ—u dasu, but insha Allah very soon zamuje"

"duk suna gaishe ka"
"Ina amsawa"

Yana zaune yana kallo, yaga Mufeeda tana cin wani abu, ya kalleta yace
"me kike ci? Se an jima ki lanƙwashe kice ciki na ciwo ko?"

"gullisuwa ce fa"

Ammar yace "Madarar  kike gullisuwa da ita, za'a raba madara kowa ya ɗau tasa, in kika ƙarar da taki seki koma shan tea baƙi ko kuma cin cornflakes ba madara"

Ɗan tura baki tayi tace  "idan na shanye semu koma shan taka"

"Seki sha É—in in gani"

"Ai da kanka zaka bani, saboda bazaka iya shan shayi da madara ni kuma ka bani ba madara ba"
Hararta yayi ya É—auke kansa

Wani cup ta ɗakko me kyau da murfin sa a jiki ta miƙa masa kofin tace  "ungo naka"

Ya kalleta yace
"meye wannan?"
"taka gullisuwar ce"

"Ni bana shan wannan kayan shiriritar da yarinta, kedai kije kiyi tayi"

"da daÉ—i fa ka É—anÉ—ana kaji"

Girgiza mata kai yayi yace
"Ke nace bana so"

Ta ƙyale shi bata kuma takura masa ba, se bayan ya dawo daga sallar magariba Mufeeda tace

"Yaya Ammar zo kaga"

Tana ɗakin tsakar gida, dan haka ya leƙa ɗakin, kayan Abincin daya gani a ɗakin ne ya sashi yin turus, yace "Wannan fa?"
"Kayan gara ne dasu su Baba suka kawo mana"
Shiru yayi yana kallon kayan yace

"Amma wannan kayan ai sunyi yawa ya zamuyi dasu, ni badan ina tsoron kar Baba yaji babu daɗi ba gaskiya da bazan karɓi kayan nan ba"

"Haba Yaya Ammar meye sa? Ai bamu kaÉ—ai zamuyi Amfani da kayan ba, za'a É—ibarwa su Abba, Su Yaya Maryam ma duk a basu, Baba zeji ba daÉ—i idan kai magana akai"

ÆŠan girgiza kai Ammar yayi yace "Kayan nan sunyi Yawa fa"

"Yaya Ammar babu wani yawa da suka yi, da Baba baze iya ba baze takura kansa yace se yayi ba, dan Allah kawai ka bar zancen nan, muci Abincin mu kawai ko?"

Tai maganar tana leƙa fuskarsa, wani ɗan murmushi yayi wanda iya kacinsa leɓensa, ya koma falo, ya kalleta yace

" Ni zan kwanta seda safe"

"Amma ina fatan ba ranka ne ya ɓaci ba akan kayan nan?"

Girgiza mata kai yayi yace
"A'a inajin Bacci ne kawai"

"shikenan Allah ya tashemu lafiya"
Yace "Ameen" ya wuce É—akin sa itama ta wuce nata.

Harta kwanta taji kawai bata ji daɗin yanayin yadda ya tafi kwanta ba, dan haka ta miƙe ta fito ta tafi ɗakin sa.

Har ya kashe fitila ya kwanta, ta shiga da sallama sannan ta kira sunan sa
Amsa mata yayi sannan yace
"Ya a kayi?"

Gadon ta hau ba tsammani yaji Mufeeda a jikin sa, a hankali yace "lafiya kuwa?"

"Yaya Ammar zuciya ta ta kasa samun nutsuwa, gaba ɗaya yanayin ka tun jiya zuwa yau baya mun daɗi, dan Allah idan laifi nayi maka kayi haƙuri"

Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Ni nace kin min laifi ne?"

"Yanayin ka ke nuna kaman na maka laifi, bana jin daÉ—in ganin ka a haka, idan kuma akan kayan nan ne se in kira Yaya Usman yazo a mayar da su"

Tai maganar jikin ta a sanyaye, gyara kwanciyar sa yayi yace
"ni babu abunda kika yi min, kawai dai É—an Adam dole wataran ya tashi babu daÉ—i shikenan kawai"

Kwanciya tayi sosai a jikin sa tace "Duk da haka yana da kyau in san damuwar mijina, dukda Mijin nawa yana ganin Yarin ta ta, Amma bazan so in ganshi cikin damuwa ba"

Nannuyar Ajiyar zuciya Ammar ya sauke, yace
"Naji zan dena damuwa, tashi kije ki kwanta seda safe"

"Zan tafi Amma buÉ—e bakin ka"

"Me yasa zan buÉ—e bakina"

Yana maganar ne ta saka masa Gullisuwa a bakin sa, shiru yayi yana tunawa, tayi masa daÉ—i Sosai dukda shi irin wannan abubuwan basa gaban sa yana ganin kaman shirita ne.

Wata ta kuma saka masa a bakin sa, ƙamshin turaren jikin ta, da yadda ta kwanta a jikin sa ya sashi cikin wani farinciki dabe san dalilin sa ba.
A hankali cikin raÉ—a tace masa
"da DaÉ—i kuwa?"
"Babu daÉ—i kaman inyi amai"
Murmushi tayi tace
"koma babu daÉ—i tunda ka riga ka sha shikenan za'a raba madara dai dai, kuma tawa seta fi Yawa"

"Naji tashi ki bani guri, mara kunya ji yadda kika biyoni har É—aki kika wani kwanta min a jiki"

"Ba jikin mijina bane, kuma dai naga ni Yarinya ce"

Kasa cewa komai yayu, Ƙasan zuciyar Ammar kuwa bugawa yake da ƙarfi yana saƙawa yana kwance abubuwa daban daban game da matar tasa da yake mata kallon tayi ƙanƙanta da Aure.

Miƙewa Tayi daga jikin sa, ta sumbaci goshin sa tace
"Honey seda safe, I love you Baby"

Riƙe hannayen ta yayi, kaman ya hana ta tafiya, se wata zuciyar tace masa "She's still young, Yarinya ce raini ze shiga tsakani na da ita, tayi ƙanƙanta"

Sakin hannayen ta yayi kaman an masa dole yace "Seda Safe" ya juya mata baya.

Dukda a cikin duhu ne bin bayan sa Mufeeda tayi da kallo tareda É—an girgiza kai, Ammar akwai taurin kai da izza.

Ta koma É—akin ta, Ammar kam baccin sa rabi da rabi ne, juyi kawai yake akan gadon har Asuba.

Da safe yana fitowa yai tozali da ita akan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana ta kaɗa ƙafa ta sha kwalliya ta kashe ɗauri, bakin ta se shining yake da jambaki, ga ƙamshin girki dana turare ya gauraye falon, gani yake kaman tana sane take wannan abubuwan.

A hankali ya tako falon kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki, ya samu guri ya zauna, ta ɗago ta kalle shi tare da yi masa murmushi, ta taso daga inda take tazo gaban sa ta durƙusa ƙasa tace "Barka da Safiya Yallaɓai" kallon ta yayi tayi kyau sosai, yana jin daɗin yadda lokuta da yawa take bashi girma, wani lokacin kuma ta maida shi kaman ƙaramin yaro, yace

"lafiya ƙalau prof. Kin tashi lafiya?"
Miƙewa tayi ta zauna a kusa dashi ta ɗan tura baki tace
"Bayan jiya dan naje É—akin ka ka koreni"
Murmushi ya É—anyi bece komai ba, ji yake kaman yace mata tayi kyau, amma ya fasa.
Ta jingina a jikin sa tace
"A kawo breakfast ne?"
"Bari se anjima kaÉ—an"
"yau bazaka fita da wuri bane?"
"Eh se lokacin salla yayi zan fita"
Mufeeda a ranta tace

"Yaya Ammar manya maganin ƙanana, na gane Lagon ka sarai, Jambakin nan da gashin nan ba ƙaramin tafiya suke da kai ba"

Ta kamo hannun sa tace
"Yau Friday ya kamata a yanke maka farce" bece komai ba ita kuma ta ci gaba da wasa da yatsun hannun sa, can ta É—aga kai ta kalli fuskar sa takai hannun ta fuskar sa tace
"in taɓa?"
"in kika taɓa sekin biya"
"dan Allah sau É—aya fa"
"kika isheni sena aske gemun nan"
"aikuwa idan ka aske na dena kulaka, dan ina son gemun nan sosai"
Ammar yace
"tashi ki kawomin Abinci"
Ta tashi ta kawo masa Abinci, ta haɗa musu Tea, zata sa masa Madara yace "bar madarar nan ki shanye abarki, naga ta kusa ƙarewa"
"Se insha tea da Madara kai kuma ka sha ba Madara?"
"Eh kece 'yar gayu ai, ni ban damu da shan me Madara ba, kiyi Addu'a Allah ya hore kafin ta ƙare in siyo wata"

Shiru tayi tana kallon sa, duk faɗan Ammar yana da sauƙin kai Sosai, kuma yana matukar ƙoƙarin ganin ya wadata da Abinci, baya bata Abinci mara daɗi, ko alawar da tayi jiya da madarar be mata faɗa ba.

"Allah ya ƙara maka Arziki na halal My love"
"Ameen" ya amsa mata.

Suka kammala karyawa, ta É—akko nail cuter ta yanke masa farce tsaf.

Ammar yace "in Allah ya kaimu ranar Saturday zamu É—an fita, Umma nata mita har yanzu ban kaiki ba"

"Wayyo Allah daɗi, Allah ya kaimu lafiya nima na ƙagu ka kaini in gansu"

Wasa2 Ammar seda ya kusa makara zuwa masallaci saboda yadda Mufeeda ta narke masa a jiki take ta zuba taɓarar ta iri2.

Se azahar sannan yai wankan juma'a ya fita salla.

******************

Fa'iza taga abubuwa sunƙi tafiya yadda take so, ta kuma wanke ƙafa ta tafi gidan Yaya Jidda, suna ta hira Fa'iza fa sako maganar gidan Ammar
"Nikam Yaya Jidda kinje gidan Yaya Ammar kuwa?"

"hmm ina fa naje, idan naje gurin wa zani gurin wannan ƙwailar Yarinyar kokuwa? Bani da lokacin su daga shi har ita"

"Amma ai gidan É—an uwan ki ne Yaya Jidda ya kamata ku dinga zuwa kiga a wani hali hake ciki? Idan kuma ya tattara ya koma gurin ta gaba É—aya fa, ku kuma ko oho kenan?"

"Aini bana son zuwa inga abunda ze ɓata min rai, ranar da nayi masa magana akan wulaƙancin da tayi muku, seda mukayi faɗa dashi ya kare ta"
Chapter 29 · 0% Book details