← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 64

Sashe 32

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya Mufeeda tayi, Umma ce ta fito daga É—aki hannun ta É—auke da carbi, alamar sallar walha ta yi, tace

"Yau Allah yayi an kawo min Mufeeda kenan? Tun ina magiyar har na gaji"

Nan ma cikin girmamawa Mufeeda ta gaida Umma, ana haka Halima ta shigo daga aiken da aka yi mata, tana ganin Mufeeda ta fara murna tace

"Anty Mufeeda ashe zaku zo É—in tun É—azu nake kallon hanya"

"Yaya Halima ni na makarar damu ai, Amma ai gashi munzo"

Duk rashin saurin Sabon Mufeeda yadda iyayen mijin ta suka karɓeta ba ƙaramin yi mata daɗi yayi ba, sun nuna mata karamci da dattako, jinsu take kaman iyayen ta, sosai ta sake suna hira, anan Har hira ta kawo Abba yake gaya mata yana kiwon dabbobi a kangon jikin gidan sa, nan suka shiga hira sosai har Mufeeda take nuna sha'awar ta akan kiwo.

Yadda take hira da iyayen sa cikin mutuntawa kaman iyayen ta ba ƙaramin burge Ammar yayi ba, Ammar ya miƙe yaje Napep ɗinsa ya kwaso kayan Abincin da suka zo dasu da Yadda aka kasafta kayan.

Abban Ammar yace
"A ina ka samo wannan kayan haka Ammar?"

"Dama kayan garar Mufeeda ne"

Abba yace "gara kuma Ammar? Ina fatan ba zuwa kayi kace se an maka gara ba, dan nasan halin ku matasan yanzu akan gararar nan se kuyi wa mace gori dan abin kunya" Abba ya É—anyi maganar a hasale.

Wato Abba halinsu ɗaya da Ammar, sam basa son aga gazawar su, musamman akan abunda yake haƙƙin su ne suyi shi.

Mufeeda tace "A'a Abba, da cewa yayi ma baze karɓa ba, Baba ne ya kawo haka yake yi duk wadda ya aurar ya bata gara, Amma dan Allah kayi haƙuri ba shi yace a kawo ba"

Abba ya kalleta ganin kaman ba taji daÉ—in yadda yayi wa Ammar É—in ba, yace "Hmm zaki kare mijinki ko? To ni a yanzu yamin laifi zan iya zane shi ma"
Sunkuyar da kai Mufeeda tayi tana murmushi, daga nan yayi musu Nasiha da Addu'oi.

Seda Mufeeda tabi Abban Ammar ya nuna mata yadda dabbobin sa da yake kiwo suke, a cikin maganar sa zaka gane tsohon É—an boko ne, Ga Mufeeda da shegiyar tambaya, duk abunda ta tambaye shi se yayi mata bayani dalla-dalla. .

Bayan tafiyar Mufeeda Abba yace "Ammar kana surutan cewa Kai tayi maka Yarin ta, to a manyan da kake hange da wuya ka samu Yarinya me hankalin ta, dukda nagani tana nuna ƙuruciyar wasu lokutan amma ka bita a hankali Yarinya ce me biyayya, ina jin nauyin ta ne amma ba dan haka ba seka koma da kayan Abincin nan, ka kula da matar ka, ka sauke dukkanin haƙƙoƙin ta da yake kanka"

Ammar yace Insha Allah suka yi Sallama da Abba ya bar Mufeeda a gidan su.

Bayan tafiyar Ammar ya kira Halima a waya, tana É—agawa yace
"kiyi wa Mufeeda kitso kafin in dawo É—aukar ta"
Ta amsa masa da "to"

Mufeeda da Halima ne suka zage suka tsiri alkubus, Yadda Mufeeda take aiki ba ƙyuya babu ganda ba ƙaramin bawa Mahifiyar Ammar mamaki tayi ba.

Da azahar suka kammala girki, suka gyara ko ina, aikuwa sunyi santin girkin nan sosai, Halima tayi wa Mufeeda kitso ƙanana masu kyau ba tare da ta gaya mata Ammar ne yace ayi mata ba, Bayan sun gama kitson Kuma tai mata jan lalle, kaman wata amarya tayi kyau sosai.

Ta samu food flask ta É—ibarwa Ammar Abincin, ta ajiye masa se bayan sallar isha'i sannan Ammar yazo É—aukan ta, taji daÉ—in wuni a gidan su Ammar dan sun mata kara suka nuna tamkar su suka haifeta, sosai suka karrama Mufeeda.

Da zasu tafi Abba ya kira Ammar ya nuna masa Akuya Aure ɗaya da kaji masu ƙwai yace ya bawa sirikarsa, za'a cigaba da kula mata dasu anan.
Ammar yace "ba shakka an gode, to ni wanne ka bani?"
Abba yace "kai sau nawa ina baka dabba, idan kaza ce ka yanka ka cinye abarka, ai bazan kuma baka ba"

Mufeeda tai murmushi har ƙasa ta durƙusa tana yiwa mahaifin Ammar godiya.
Abba yace "bakomai 'yar Auta, Allah ya baku zaman lafiya ya ƙara muku ƙaunar juna, muma mungode sosai"

Umma ma seda ta haÉ—awa Mufeeda su tsintsiya da manyan jakar omo, sannan suka yi sallama.

Seda Ammar ya biya da ita gidan Yaya Maryam ta gaishe ta, taita mita akan meyasa be kawo ta da wuri ba se a daren nan, suka bata nata kayan da suka kawo mata sannan suka tafi gida.

Suna komawa Mufeeda ta gabatar masa da Abincin da tazo dashi, seda Ammar ya kwashi girki ya ƙoshi sannan yace
"waye yayi girkin nan?"
"Nice" ta bashi amsa

Ya basar yace "shiyasa beyi daÉ—i ba"

Ta kalle shi tace "Abba dai yace yayi daÉ—i"

"Ai dan karki ji babu daÉ—i ne yasa shi cewa yayi daÉ—i, amma babu daÉ—i"

Seda yaga ya ƙoshi ya wani fara beyi daɗi ba, tattare Kwanukan ta fara yi tana tura baki, se yanzu ya lura da hannun ta da yayi Jawurrr da lalle, ƙurawa hannayen ta ido yayi, ta kwashe Kwanukan ta, ta kai kitchen ta wanke tai tafiyar ta ɗaki.

Ƙin zama tayi a falo, shi kam Ammar dariya ma ta bashi, ita a dole fushi take.

Har ƙarfe goma Ammar yana falo yana kallon wani Film a Bollywood, ba zato babu tsammani yaga Mufeeda ta ɗare cinyar sa, shi a zaton sa tuni tayi bacci, se ƙamshin turare take, rigar ta ta bacci iya gwiwar ta, kanta babu ɗankwali se bakin ta da take shan sweet.

Ammar yace "Ya haka?"

"Na kasa bacci, kuma naji kana kallo shi yasa na fito"

Ammar kaman ze kuka yace
"kinga É—agani banyi shafa'i da wuturi ba"

"in muka gama kallon base kayi ba"

"waike baki san yanzu lokacin sanyi bane? Ba'a son yawan taɓa ruwa ba?"

"to ba se in dafa maka ruwan alwala ba"

A ransa yace "wannan 'yar yarinyar in banyi dagaske ba yauma seta hanani bacci"

Dan haka ya haÉ—e rai yace
"Malama ki É—aga ni"

Maimakon ta ɗaga shi, sema ta gyara zaman ta ta miƙe ƙafafuwan ta akan nasa, kaman yadda yayi ta jingina bayan ta a ƙirjinsa ta ci gaba shan alawarta da zuwa yanzu bakin ta ya zama ja jawurrr saboda kalar alewar.

Daskarewa yayi a gurin ya kasa magana balle ya motsa, lallai yau ya ƙara tabbatar da tsagwaron yarinta akan Mufeeda, Ammar yayi ƙam dashi kaman gunki, sun kusa mimtuna goma a haka, ko a jikin ta kallon ta kawai tame.

Ta fara taune alawar nan a bakinta, sekuma ta janye ƙafafuwan ta ta juyo ta kalle shi tace
"Au naman ta ban maka bismillar alewa ta ba gashi na taune ta, bari in tafi dan na fara jin bacci"
Ta miƙe da nufin ta tafi amma ba zato ba tsammani Ammar ya janyo ta.

Abunda yayi ne yai matuƙar bata mamaki, dan ko a mafarki batayi zaton hakan ba.

Seda Ammar yasa baki ya shanye alawar da ta tauna a cikin bakin ta tsaf, sannan ya cika ta ya miƙe kamar beyi komai ba ya wani maze ya haɗe rai yai tafiyar sa ɗakin sa

(🙄🙄 to su Yaya Ammar manya)

Ashe dai kuna son littafin nan haka? Ai ban sani ba seda nayi tsallaken update na rana É—aya nasha tambaya.
To yaseen in ba Comments posting se Allah ya kaimu Monday.
Ina godiya masoya da addu'oinku da kuma shawarwari.

Domin gyara, sharhi ko shawara ƙofata a buɗe take
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

                  

                        Page 17

Binsa tayi da kallo har ya shige ɗakin sa, tashi tai ta koma ɗakin ta, tana ƙara mamakin abunda Ammar yayi mata.

Da safe harta tashi ta gama breakfast be fito ba, tana ƙarasa gyara gida ne ya fito yana wani basarwa, Mufeeda ta kalle shi tace
"barka da Safiya Babban Mutum"

Be amsa ba se jinjina mata kai da yayi, ya nemi guri ya zauna, ya fara breakfast É—in sa yana wani mazewa, murmushi take yi tasan abunda ya faru jiya ne yasa yake ta wannan basarwar.

Seda ya gama ta koma kusa dashi tace "Hubby kalli lalle na yayi kyau kuwa?"
Kallon hannun yayi da zuwa yanzu ya fara zama maroon, ya gyaÉ—a mata kai, amma bece komai ba.

Ta kawo masa breakfast É—insa ya fara yi, yanayi yana wani mazewa gaban sa taje ta zauna ta zuba masa ido ya É—ago idon sa ya sauke a nata yace

" Se kinsa na ƙware kike min wannan kallon haka?"
"A'a bazaka ƙware ba, kallon Soyayya ne sedai ka ƙara jin daɗin Abincin, A bani a baki mana duk randa ka ciyar da ni da hannayen ka masu tarin Alkhairan nan nafi ƙoshi fa"

Hararar ta yayi yaci gaba da antaya loma, tayi ƙasa da murya tace
"haba Autan Abba mijin Autar Baba, ba dan halina bafa kaga ni Yarinya ce zanyi maka kuka fa"

"ga guri nan maza zauna kiyi kukan, tunda ke a rayuwar ki Kuka kamar jin daÉ—in sa kike yi"

Tura baki tayi ta riƙe hannun sa

"dan Allah baby ka bani a baki, nice fa Jaririyarka ce seka barni da yunwa?"

Kallon ta yake yadda take ta zuba taɓara.
Chapter 32 · 0% Book details