← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 64

Sashe 43

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bana buƙatar Addu'ar ki, inkina da gaskiya ai bekamata da nayi wannan zancen ki tashi kice zaki tafi ba, Yarinya se girman kan banza, ga sana'ar Mijin ta yafi na kowa lalacewa a tsukin nan"

Har Mufeeda zata fita daga ɗakin ta tsaya ta kalli maman Nur tace  "Allah sarki matar mangal, se gashi kina aike gidan direban a daidaita sahu atemaka miki da abunda attajirin mijin naki ba ya iya ajiye miki, ashe ma dai wani kuɗin ƙaryar banza ce, kuma karki ƙara sa kamin mijina a shirmen ki Jahila 'yar ƙauye kawai"

Maman Nur ce ta antayo wata zazzafar Ashar "Ke kin isa kizo gidanta ki zage ta"

"Na zage ta ɗin uwata ce? Tun da nazo layin nan nake baku girman ku Amma bakwa ganewa, wallahi babu matar da zata min in ƙyaleta, kuji da kanku ku ƙyaleni inyi rayuwa ta"

Anty hauwa ce ke ƙoƙarin sasanta abun amma ina suka haɗe kai suka dinga zagin Mufeeda.

Mufeeda tace "Anty kwantar da hankalin ki yanzu zan tafi, Amma duk wadda ta zageni ta zagi iyayen da suka kawo ta duniya, kuma wallahi kaf cikin mazan su babu me karamci da girman mijina, kar wadda ta sake zagar mana sana'a babu wadda nazo gidan ta yin barar abunda zamu ci "

Maman Amir tace
" Dalla rufe mana baki karki ƙara haɗa faƙirin mijin ki da mazajen mu"

"Aini banga alamar kuɗin mazajen naku a jikin ku ba, dan da mijin naki kuɗin nasa na Arziki ne da be barki da wannan koɗaɗɗen zanin da rigar ta ɓarke daga hammata ba"

Ai Mufeeda na faɗar haka kowa ya kalli Maman Amir, aikuwa sega riga a ɓarke ta hammata aikuwa aka ƙyalƙyale mata da dariya.
Mufeeda tai ficewarta a hasale tana jin zafin yadda ake cin zarafin sana'ar mijin ta.

Kanta ne yake wata irin sarawa kusan kwana uku kenan, ta miƙe layin su domin zuwa ta siyo ko paracetamol ne ta sha, amma kafin ta kai ƙarshen layin sega wannan mutumin da ya biyo ta rannan, basarwa tayi zata wuce yace
"'haba adon gari, ina murna yau kayana ya tsinke a gindin kaba na sake tozali da wannan zuƙeƙiyar halittar amma zaki basar dani ki wuce "

"Wai dan Allah malam kai baka tsoron Allah, baka tsoron kaima wani yayi maka abunda kakewa wani?"

"Na gane ke matar Aure ce, dan har gidan ki nasani, rannan ta ƙofar gida na kuka wuce keda mijin ki, Amma fa kinga a wannan zamanin kowa samawa kansa mafita yake, ki ƙyale wannan faƙirin mijin naki, kizo mu jone zan sakar miki kuɗi kiyi yadda kike so, dukda ina da mata huɗu zan saki ko dukan sune idan kina so dan in Aure ki "

" Auzubillah talakan mijina ya fiye min wawan dattijon banza irin ka, gara talauci sau dubu da Arziƙin daya fito daga hannun Asararre irin ka dukiyar taja da in akabi diddigi ta Haramce"

"Haka kika ce?"

"Na faÉ—a ko zaka yi wani abu akai?"

"shikenan bari mu gani, zan tabattar miki da talauci masifa ne"

Mufeeda fasa zuwa siyan maganin tayi ta koma gida tana tunanin meyasa wannan masifun suke bibiyar ta haka?.

Ammar na zaune yana kallo da daddare Mufeeda na zaune a ƙasa, itama idon ta akan talabijin yake amma tunanin ta sam baya tare da ita, tayi nisa a tunani, ƙwanƙwasa gate ɗin da aka yi ne yasa Ammar ya tafi ya buɗe.

Mijin maman Nur ne, suka gaisa da Ammar,
"dama zuwa nayi dan Allah ka jawa matarka kunne, daga sallamo mata ta dsga Asibiti ta shiga ta tayar min da hayaniya a gida dan Allah a jama ta kunne karta sake"

Wani banzan kallo Ammar yai masa yace "Gaskiya bana tunanin mata tace, idanma itace wani abun suka yi mata dan sam bata da neman rigima"

"A'a sufa matan nan na yanzu ba shedarsu ake ba, be kamata in kawo maka ƙara ka goyi bayan ta ba"

"Naji amma ni nafi kowa sanin halin ta, idan ba wani abun suka yi mata ba haka kurum ba zata je gidan ka tana hayaniya ba, Amma hakan ba zata sake faruwa ba, Allah ya bata lafiya"

(wato Ammar yace Allah ya bada haƙuri ne baze iya ba)

motsin shigowar sane yasa Mufeeda ta buÉ—e idon ta.

Ammar ya samu guri ya zauna ya zuba mata ido, seda gaban ta yai mummunar faÉ—uwa kallon da yake mata dan na tuhuma ne.

"Ina kika ce min zaki É—azu?"

"maƙota na shiga yin barka"

"Da kin cemin zaki barka kika ɓuge da neman rigima a gidan mutane ko? Yanzu wanne wanda yayi Sallama dani maƙocinmu ne yace daga sallamo matarsa daga Asibiti kin shiga kin tayar musu da rigima, wai matar dama ance jinin ta ya hau, ke wai dama haka kike ne?"

Shiru Mufeeda tayi ta sunkuyar da kanta, Ammar yai faÉ—ansa iya son ransa Ya gama sannan ta É—aga kai ta kalle shi tace
"Allah ya baka haƙuri bazan kuma ba"
Wasu lokutan wannan halin na Mufeeda ba ƙaramin haushi yake Bashi ba duk laifin da zece tayi bazata taɓa musa masa ba, sedai taita bashi haƙuri ko kuma taita kuka.

Ta miƙe a hankali jiri na ɗibar ta ta tafi ɗaki, ƙirjinta yai mata nauyi se kokawa take da numfashi, tana shiga ɗaki ta samu guri ta kwanta ta rintse idon ta tana maimaita Innalillahi wa inna ialaihi raji'un.

Se ƙarfe goma Ammar ya miƙe ze tafi ɗakin sa yaga wayar Mufeeda akan kujera tana vibrating.

Masoyan Mufeeda ayimin afuwa labarin ne yazo a haka, ban fara rubuta shiba seda na kammala tsarashi, ayi haƙuri a bini a sannu dan ganin yadda zata kaya.

Bana son wannan stickers É—in ko kuma thanks kawai Comments nake so dan Allah

Dan Allah in kin/ka karanta atemaka a dinga tayani sharing saboda masu bina pvt suna tambaya ta wasu pages É—in abubuwa sunmin yawa.

Masu bina private suna sanar dani ƙorafi su ko shawara ina godiya daku da masu Comment

Fansa É—ina na watpad don't forget to vote

Har yanzu ƙofa ta a buɗe take domin gyara, sharhi ko kuma shawara
Ayshercool
07063065680
[16/07, 10:00 PM] Ayshercool: ✨✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨

( *Sai Mata* )

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP

__Happy marriage life to my lovely friend_, __MARYAM MUSA ƁAIDU_I WISH YOU A VERY HAPPY MARRIAGE LIFE DEAR_

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                 
             
                          Page 22

Har Ammar ze share wayar ya tafi É—akin sa se kuma ya É—au wayar ya nufi É—akin Mufeeda.

Yana zuwa ya tarar har tayi bacci ta dunƙule a guri ɗaya ko kayan jikin ta bata canza ba da alama dai baccin ba shiri ya ɗauke ta, fuskarta duk hawaye se ajiyar zuciya take.
Ɗan girgiza kai Ammar yayi ya zauna gefen gadon ya ɗagota ya cire mata hijjabin jikin ta, a wasu lokutan Mufeeda na da  nauyin bacci sosai dan haka ya rage mata kayan jikin ta data kwanta da su, ya ƙura mata ido ta ɗan rame sosai, Amma tubarkallah tana da kyau dai dai gwargwado, musamman idan tana bacci se yaga ƙuruciyar ta ta ƙara fitowa,  iya goshin ta ya ɗau zafi sosai yayin da sauran jikin ta yayi sanyi saboda kuka.

Ammar ya daɗe yana kallon ta yana jin wani abu na masa yawo a jikin sa ba tare da ya tabattar dame hakan ke nufi ba, a hankali ya janyo pillow ya kwantar da ita a kai yana cigaba da kallon fuskarta, sosai yake jin tausayinta be kamata ya cigaba da yi mata faɗa any how ba, hakan yana sata a cikin damuwa sosai, gefe guda wayar Mufeeda na ci gaba da vibrating, har ya miƙe ze bar ɗakin yaga vibration ɗin wayar ze iya tashin ta dan haka ya dawo ya sunkuya ya ɗau wayar, baƙuwar lamba ce babu suna ya danna alamar amsawa ya kai kunnen sa zeyi magana, shiru yayi yana sauraren abunda me wayar yake faɗa, kunnuwan Ammar ba zasu iya jure jin abunda wannan la'anannen dabe san darajar Aure yake faɗa ba, Idan kunnuwan sa ba ƙarya suka jiye masa ba to tabbas kalaman soyayya ne wanda ya kiratan yake faɗa

"tun ɗazu nake kiran ki saboda inji daddaɗar muryar ki ko da zagina kiyi in samu inyi bacci cikin kwanciyar hankali, Amma kinƙi ɗaga waya ta, kice wani abu mana mufeeda, Shikenan tunda ba zaki magana ba ɗaga wayar da kika yi ma ya tabbatar min kina lafiya, Ina son ki fiye da yadda wannan mijin naki me girman kai da baki da tabbacin yana sonki"

A hankali Ammar ya ajiye wayar, zuciyar sa tana wani irin bugu da ƙarfin gaske tamkar zata tsaga ƙirjin sa ta fito, gashin jikin sa duk ya mimmiƙe saboda ɓacin rai, ya kalli inda Mufeeda take kwance tana bacci, se faman sauke ajiyar zuciya take she's looking so innocent.

Da ƙyar Ammar yaja ƙafar sa ya bar ɗakin yana ci gaba da jin Yadda zuciyar sa take bugawa.

Ɗakin sa ya koma ya samu gefen gado ya zauna ya dafe kansa da yake jin tamkar ba nasa ba, yanzu duk iƙrarin Soyayyar da Mufeeda take masa ƙarya take, zata iya cin Amanar sa tayi soyayya da wani a waje da Auren sa a kanta, lallai mata ba abun yarda bane.

Yana wannan tunanin message ya shigo wayar sa
"KA SA IDO AKAN MATARKA TANA AIKATA RASHIN GASKIYA A BAYAN IDON KA"

Wannan shi ne ire iren saƙon da'ake yawan turo masa
Chapter 43 · 0% Book details