← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 64

Sashe 3

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mufeeda bata tsaya jiran meza'ace ba, ta zari hijjabi tai waje, kaman yadda ta zata Ammar ne a tsaye a gefen Napep É—in sa.

Da sauri ta ƙarasa inda yake
"Yaya Ammar kaine? Ina wuni?"
"Lafiya ƙalau, dama nazo in tambaye ki ne, ko kune kuka manta kaya a Napep ɗina, tun shekaranjiya nake yawo da su"

Ajiyar zuciya tayi  "Kayan ɗinki nane Yaya, na shiga damuwa sosai, zuciya ta ta bani zaka kawomin dama, dan na yarda kai me amana ne"

"Seki kiyaye gaba, idan kin shiga abun hawa ki dena surutu, in ba haka ba wataran dake za'a tafi"

Ya Ɗakko kayan ya miƙo mata
Bata karɓa ba ta tsaya tana kuma ƙare masa kallo, murmushi ta sakar masa tace

"bana surutu a abun hawa ai, ranar ma dan kai ne, nagode sosai Yayana, Allah ya ƙara Arziki, ya kiyaye ka daga sharrin maƙiya, Allah ya azurta ka da halal ya nesan taka da haram, Allah ya sakawa iyayen ka da Alkhairi Addu'ar su da tarbiyar suce ta sa ka zama mutumin kirki "

Ammar yana mamakin yadda yarinyar ke sarrafa harshen ta. Ba ta karɓi kayan ba tace
" Dan Allah ina zuwa"

Ta koma cikin gida, ba tafi mintuna biyar ba ta fito hannun ta ɗauke da leda, ta miƙawa Ammar.
Ya kalleta yace "menene wannan?"

"Yaya Ammar yaba kyauta tukuici, bani da abunda zan biya ka, kawai dai na baka ne"

Girgiza kai yayi  "bazan karɓa ba, ungo kayan ki, ina sauri zani wani guri ne"

Kallon sa tayi "zaka zance ne? Idan baka karɓa ba zan barka da kayan sedai ka koma da su ko ka barsu anan dan wallahi bazan karɓa ba"
Tai maganar tana kallon cikin idon sa, dagaske take abunda take faÉ—a.

Hannu yasa ya karɓa, sannan ta karɓi kayan ta, cikin iyayi tace
"yauwa ko kaifa Yayan Mufeeda"

A ransa ya maimaita "Mufeeda"
Tace "ungo wannan invitation ne, bikin yaya ta za'ayi a wannan satin dan Allah kazo kaji Yaya na"

"ban miki Alƙawari ba gaskiya, Amma Allah ya sanya Alkhairi ya basu zaman lafiya"

Wani irin kallo take masa wanda ya kasa gane kallon menene haka?

"Idan ba kazo ba bazanji daɗi ba, kuma zanga kaman kamin wulaƙanci ne, ko kuma maybe... Shikenan dai nagode ka gaida Mama, Allah ya kaika gida lafiya, ya tsareka daga sharrin maƙiya"

Ta juya ta nufi gate É—in gidan su, yai shiru na É—an lokaci ya shige baburin sa ya tafi.

ÆŠakin Baban su ta nufa, tana zuwa ta tarar da yayyen ta na gidan Aure sun cika falon baban su da mahaifiyarsu suna ta hira ana shirye2.
Tana zuwa taje gaban Maman ta ta ajiye mata kayan É—inkin tace

"Mama ga kayan nan, me Adaidaita sahu ya kawo min, seki dena haÉ—emin rai"

Wani daga cikin yayyen ta ya kalle ta

"Ahh kaga professor, kuma Autar Baba da Maman ta"

Mufeeda Ta ɗan tura baki  "Autar Baban dai, Mama tafi son Yaya akaina, kuma na fasa zama professor ana aurar da Yaya nima Aure zanyi"

Dariya suka dinga mata, Babbar yayar su tace  "kiji min yarinya da rashin kunya, kin fasa zama professor kafin kiyi auren?"

"Na fasa dan Yaya na barin gidan nan Mama zata kasheni da sa aiki, dama kaman bata sona nima Aure zanyi"

Mama tai murmushi tace "naji bana sonki É—in, nafi son Amina ke kam baki da nutsuwa ga wauta, tunda babanki yana sonki ai shikenan, waye ma ze aure ki a haka, baki iya komai ba, se son jiki da rashin kunya, ko Saurayi baki da shi"

"Wallahi na samo Saurayi, me Adaidaita sahun da yakawo min kayana nake so"

Yanayin yadda tayi maganar ne kanta tsaye da confidence É—in ta yasa ta bawa kowa dariya, suka É—au maganar tata shirme.

Domin gyara, sharhi, ko shawara
07063065680

Kuma yaseen ba comments se Allah ya kaimu September zan cigaba da typing.
✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                         Page 2

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

"ke bama son shirme, ubanwa ze miki wani aure, tafi kije kici Abincin dare ki kwanta" cewar Yayan Mufeeda

Baba yace "kaga Abubakar ku ƙyalemin professor auta, yadda take so haka za'ayi, tunda gidan su ne, ku yanzu duk ba 'yan gidan nan bane ba' yan karo ne"

Mufeeda tace "Yawwa Baba gaya musu, dan Mama tafi sonsu, yanzu idan muka ga dama duk korarsu zamuyi kowa ya tafi gidan sa"

"sosai makuwa Auta na"

Haka Baban mufeeda ya ci gaba da zigata tana ta zuba taɓarar ta.

*************
Mufeeda se rawar kai take tana iyayi, anata shirye shiryen biki, sati guda ta dauka ta dena zuwa makaranta se yawon rabon Katin gayya ta, komai da ita ake yi, yayin da gefe guda kullum cikin tunani take yi, zuciyar ta na son sake saka Ammar a idon ta.

Mufeeda duk kayan gyaran fatar da Amarya take yi itama se tayi, tare suka je ƙunshi da gyaran kai, komai angone ya biyawa Mufeeda yadda ya ya biyawa Amarya, gidan su mufeeda su takwas ne, huɗu maza huɗu mata, daga Yaya Amina se Mufeeda, shekaru biyar ne tsakanin Amina da Mufeeda.

Angon Yayar Mufeeda yasan Mufeeda sosai, saboda ba ƙaramar gudunmuwa ta bashi ba lokacin da yake neman Auren yayarta, ita ta taya shi campaign gurin Yayar ta, duk saurayin da Amina za tayi indai beyi wa Mufeeda ba in ta dinga kushe shi se Amina taji bata son mutumin nan sun rabu.
daga tace wancan be iya sa hula ba yana da ƙaton kai, ko kunnuwan sa sun fiye tsayi, se tace wancan ƙatuwar ƙafa ce da shi idan ta aure shi zata haifi ɗan se an je kamfani za'a masa takalmi, se tace wancan kwaɗayayye ne kullum yazo aka bashi abu se ya karɓa, harta kai ta kawo idan Amina tayi Saurayi se tace
"Mufeeda zo kiga wannan saurayin yayi kuwa?"
Mama taita faɗa tana "Amina baki da wayo, kina zaune ƙanwar bayan ki, shekara kusan biyar kika bata, Amma ita ke zaɓa miki Saurayi ki biye mata haka zakiyi ta zama a gida ba aure"

Mufeeda bata da jiki sosai, tana da hasken fata, ba doguwa ce can ba, Amma tana da kyau dai dai gwargwado, kana ganin ta kaga yarinya, Amma akwai baki, ga iyayi da rawar kai, dan kusan duk tafi yayyen ta baki, yayyen ta ba ruwan su da hayaniya a nutse suke, basu da yawan magana, Amma mufeeda ta fita zakka, ita akwai baki da neman rigima ga rashin haƙuri, shiyasa sam basa shiri da maman ta.

****************

Ammar yana zaune a tsakar gida dashi da 'yar Yayar sa Halima, Halima itace Babbar jikar gidan su Ammar, daga Yaye Umman sa ta riƙe ta.
Halima ta gyarawa Ammar É—akin sa ta fito da invitation a hannun ta tace

"Uncle Ammar, waye ya gayyace ka biki ne?"

Seda yaga katin ya tuna, ya É—anyi tsaki yace
"wallahi wata fitinanniyar yarinya ce ta bani wai bikin yayarta, yadda shi kawai"
"haba Uncle baza ka bikin ba? Ba kyau fa a gayyace ka walima kaƙi zuwa, Amma gayamin ko Anty na ce?"

Haɗe rai Ammar yayi yace "ke bana son shashanci, yarinya ce fa ƙarama kin girme ta"

"Amma ya akayi harta baka invitation? Wallahi uncle seka ga 'yan yaran fa munfi iya soyayya"

"kunfi iya hauka dai, koke baki isa Aure ba, ina zanje ina kula' yar da da aure nayi da yanzu na haife ta"

Dariya Halima tayi
"Allah ya ja da ran uncle É—ina, to ai da haka da haka"
HaÉ—e rai Ammar yayi kaman bashi ke hira ba yanzu
"Ke rufemin baki, yaushe na fara wasa dake?"
"Allah ya baka haƙuri"

Gyaran murya suka ji a soro, alamar za'a shigo, mahaifin Ammar ne ya shigo ya kalli Ammar yace

"kai dai kam kaji kunya wallahi, Allah Ammar da kai mace ne masallaci zanje in samu duk wanda yayi min in Aura masa kai sadaka, ace mutum ba zuciya duk sa'aninka da ƙannen bayan ka sunyi Aure amma kai kana zaune, se anyi magana ka kama wani kai se 'yar shekara talatin kai bazaka auri yarinya ba, dama wace yarin ya ce zata aureka, duk ka tsofe a titi ka zama tuzuru, tun wuri kayiwa kanka faɗa kafin ayi da kai kai kake yi da kanka, in ba sokake daga ga shiga guri mutane su fara kaffa kaffa da yaran su mata ba, saboda ka tsofe ka zama tuzuru ba Aure, wanda da kayi Aure tuntuni da yanzu kaima nan da 'yan shekaru zaka aurar da' ya"

Ture Abincin da yake ci yayi, dan ji yayi yana tsaye masa a wuya Ire2 wannan faɗan na mahaifinsa ba ƙaramin ɓata masa rai yake ba, ba dama ya shiga cikin gida ya zauna mahaifinsa ya dinga masa mita kenan akan maganar Aure.

Mahaifiyar Ammar ta fito daga ɗaki tana faɗin "dan Allah malam ka dinga haƙuri, Shifa Auren nan lokaci ne, kuma Alhamdilillah tunda rashin auren besa yana ɗakko maka magana a waje ba, ba ruwan sa da 'yar kowa, kuma yin Aure ai se mutum nada ƙwaƙwƙwarar sana' a ko?"

Mahaifin Ammar yace "ai dama ke kike goya masa baya yake ƙara sangarcewa, kalli kowa gidan nan yau faten wake ya sha amma shi kinyi masa girkin sa daban, shi bazeci faten wake ba, yace se ya gama karatu degree biyu yayi, yace seya samu sana'a wannan babur ɗin da yake ja be isheshi ba indai ba ƙarya ya ɗorawa ransa ba, ni anya ma ba Aljana ce ta aure shi ba?"
Chapter 3 · 0% Book details