← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 64

Sashe 11

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shidai Ammar be kuma cewa komai ba ya miƙe ya fice ya bar gidan.

Kai tsaye É—akin Jabir ya wuce, yana zuwa ya tarar Aminu ma yana can, yana zuwa be kula su ba ya samu guri ya zauna.
Gaba É—aya suka bishi da kallo Aminu yace
"Mutumin ya akayi ne? Ya muka ganka a haka?"
Shiru ya musu yana jan ƙaramin tsaki, se wani huci yake bayan 'yan mintuna ya kuma jan tsaki sannan yace
"KuÉ—in Aure Abba ya kaimin"

Jabir yace "what are you serious Man? Kai wallahi dani mace ne se nayi guÉ—a, Alhamdilillah"

Aminu yace "to kuma menene abun ɓata ran abun farinciki ya same ka sannan kazo kana cunkushe mana fuska"

Jabir yace "wait wai meyasa baka gaya mana za'a kai kuÉ—in aurenka ba? Wace me rabon ce ta rabauta da samun a very hardworking man as you?"

Seda Ammar ya kuma tsaki yai musu bayanin komai sannan ya É—ora da cewa "ni faruwar abun har tsoro yake bani ji yadda komai ke faruwa cikin gaggawa"

Aminu yace
"Ammar da yawa suna neman damar daka samu basu samu ba, a wannan marrar ka bawa yarinya budurwa dubu hamsin kuɗin aure iyayen ta su karɓa da murna har suce komai Allah ya hore ma ka kawo zasu baka gaskiya kayi dace"

Ammar yace "wacece budurwar? Ana gaya muku ƙwaila ce kuna wani surutu"

Jabir yace "kai Ammar kai duk wannan ne ya dame ka? Ba'a nan take ba ɗan nuna mana hoton ta mu gani mana muga wai me yasa ka damu da cewar ƙwaila ce"

"Ni bani da hotonta sedai akan dp É—in ta" ya faÉ—a yana cunkusa fuska

Yana É—akko wayar sa yaga message É—in ta tana godiyar ya kai kuÉ—in auren ta dubu hamsin.

Shiru yayi yana wani tunani, buÉ—e what's App É—insa yayi ya nuna musu hoton ta na kan DP É—in ta, ta canza hoto, iya fuskarta ne kawai akai tayi murmushi.

Aminu yace "wow Masha Allah, wallahi Ammar karkayiwa kanka sagededuwa, see fine Baby"

Jabir yace "dan Allah in baka so, ni zan ƙara dubu hamsin abani"

Harar Jabir yayi yasa hannu ya fizge wayar sa sega kira ya shigo, Ammar ya É—aga kiran kafin yayi magana ta fara

"Yaya Ammar É—ina, bani da lafiya Amma baka kuma cemin ya jiki ba, na turo maka message bakayi responding ba, Anyway nagode sosai ban zaci zaka bada wannan kuÉ—in a matsayin kuÉ—in aure na ba, Nagode sosai Baby na"

"What!! Baby kuma?"

Ai take su Jabir suka ƙyalƙyale da dariya dan Ammar ya tsani yaga ana wannan abubuwan.

Mufeeda tace "ba cemin kai ni jariri ya ce ba, gara in maida kai Jariri kaman ni se komai ya tafi daidai, Yaya Ammar dan Allah kazo in ganka please"

"Ke ki rabu dani ki dena wannan rawar kan, Auren nan ba yuwuwa zeyi ba, ni bazan auri ƙaramar yarinyar mara Aji ba kamar ki ba bana son shirirta"

Mufeeda ta kwantar da muryarta cikin kissa da murya me É—aukar hankali tace

" Ammar ɗina ni kaɗai, kuma Angon ƙwaila to be insha Allah, you know what? Am very lucky daga haɗuwar mu zuwa yanzu komai yana tafiya dai dai, Amma Idan har dan nace ina sonka shine bani da Aji me zakace game da Auran Sayyada khadija da manzon Allah salallahu alaihi wassalam? Idan har kace na maka ƙanƙanta da aure me zaka ce game da Auren Sayyada Aisha da manzon Allah salallahu alaihi wassalam? Haba Yaya Ammar ɗina babu rashin aji a abunda nayi fa"

Shiru Ammar yayi, yayin da Aminu yai ƙasa da murya yace Jabir "Wallahi yarinyar nan ta fi Ammar iya siyasa, kan uba a yanayin hotonta yarinya ƙarama amma tana tsara zance"

"Baby na zan kwanta bacci ka gaidamin dasu Mama, Sannan ka cewa Abokan ka kowa ya tafi gidan su abarmin kai ka huta dan Allah"

Domin gyara sharhi ko ƙorafi
Ayshercool
07063065680

✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             
                      Page 6

Shewa su Jabir sukayi, Jabir yace

"karki ji komai matar mu zamu tafi yanzu mu barshi ya huta"

Tana jin hayaniyar su ta kashe wayar ta tana murna, gaba ɗaya Ammar ransa ƙara ɓaci yayi yace  "Jabir meye haka wai kuke yi, sekunsa ta fara rainani meye hakan kukayi?"

Aminu yace "kai Ammar saurara tun wuri kasan abunda yake maka ciwo, wannan yarinyar kana ganin ta a haka nan gaba in bakayi wasa ba seta dinga juya ka, dan ta fika baki kai fushin kawai ka iya da zare ido"

"Allah ya kiyaye wannan abar ta juyani"

Jabir yace "ƙyale shi Aminu ze ga wannan abar ganin idon sa, abun da zamuyi yanzu shi ne, ka bamu sunan ta zamu je ayi muku sticker da keyholder za'a haɗa da chewngum wanda zata rabawa ƙawayen ta"

"Amma bada kuÉ—i na za'ayi wannan shirmen ba ko?"

Aminu yace "kwantar da hankalin ka da kuÉ—in mu zamu yi ba, da namu zamu yi dan haka akeyi, Amma lokacin da zakayi na kuÉ—in naka muna gefe"

Jabir yace "Ammar dan Allah kayiwa yarinyar nan hallaci, karka watsa mata ƙasa a ido ji musamman ta kira take maka godiya akan kuɗin nan dan Allah kadena wannan fushin kaman wanda za'ayiwa auren dole"

Ammar yace "to meye wannan in ba auren dolen ba?"

Aminu yace "ka gama muzuran ka a yanzu in ka shiga hannun ƙwaila se yadda tayi da kai"

ÆŠaukar wayar sa Ammar yayi ya fice ya bar É—akin

************
Haka nan badan mama taso ba ta fara shirye2 da siyayyar kayan auren Mufeeda aka sanar da 'yan uwa da abokan arziƙi an saka ranar auren Autar baba, wasu na san barka wasu na ya akayi ita za' a mata aure yanzu bayan 'yan uwan ta seda suka fara karatu (mutane kenan komai se sunyi magana)

Ɓangaren Ammar ma shiri suka fara yi sosai,' yan uwa da abokan sa na ta taya shi ƙoƙarin haɗa kayan aure, dukda baya son auren saboda Yadda iyayen sa suka ɗaukaki auren nan ya sashi dole shima yake nasa ƙoƙarin.

Yau yayyen mufeeda duk sunzo gida da yake sukanyi haka lokaci lokaci mussman lokacin farinciki, sukai ta caccakar Mufeeda akan tana murna Ammar ya bada dubu ɗari kuɗin auren ta ita dai tai musu banza taƙi kula su.

Yaya Fadeela tace "yarinya man kaza ba dai aure ba? Namiji ko gaki gashi nan, yau shiyace yana son ka yaka ƙarke balle kuma kafi damuwa dashi, inaji Mama tana mitar zuwan sa gidan nan befi uku ba amma kin manne masa ko damuwa beyi dake ba, kuɗin aure ya rasa nawa ze kawo se dubu hamsin"

Anty Murja tace  "ni ba wannan bama da ganin wannan koba a faɗa ba yafi ƙarfinki yayi miki girma maimakon ki samo dai dai ke, kin ɗakko wannan murɗaɗen kaman ɗan dambe"

Sarai Mufeeda ta gane inda zancen su ya dosa amma ta basar ta zumɓura baki tace
  "ni wallahi bemin girma ba ai ba a bayana zan dinga goya shi ba, ina ruwana da girman sa"

Fadeela tace  "Ji shashasha bama tasan me'ake nufi ba se ƙoƙarin rashin kunya, zaki cu uban ki kije ki aure shi, zakiyi bayani yadda ya kamata ba dai aure ba? Idan baki goya shi a bayanki ba zaki gane in kin shiga"

Haka suka dinga tsorata ta, Yaya Amina tace  "haba Anty Murja dan Allah, wallahi abunda kuke be dace ba ya zaku dinga razana ta, so kuke tace ta fasa? Dan Allah ku dena"

Mufeeda tace "ƙyale su Yaya Amina bazan fasa ba suyi tayi nidai ina son Yaya Ammar sosai"

Ita Amina Tausayin Mufeeda takeji sosai, rayuwar da suka yi tare su Fadeela ba suyi ta tareda Mufeeda ba.

Mama ta shigo ta same su, suka dinga caccake mufeeda wai tayi rashin kunya ga rashin aji yadda take rawar kai akan Ammar, gashi shiba Wani shahararren mutum ba amma se girman kai da isa a cikin sa.

Ƙarshe mufeeda se bar musu ɗakin tayi, dan taji dana sanin zuwan yayyen ta gidan nan.

Yaya Amina ta fita tsakar gida zata je kitchen ta zubo Abinci, ta jiyo sheshsheƙar Mufeeda a ɗaki. fasa zuwa zuba Abincin tayi ta shiga ɗakin ta samu Mufeeda ta haɗa kai da gwiwa tana kuka cikin tausaya wa Amina tace  "Mufeeda meyasa kike kuka?"

"Yaya Amina daga ke se Baba ne kawai kuke goyon bayana, Wallahi yaya Amina dana san dagaske Mama zata ƙi Ammar dana haƙura, wallahi ban san yadda akayi nake sonshi haka ba, baki ji yadda nake ji a zuciya ta ba ko sunan sa aka ambata, Amma Mama da su Anty Murja se hantara ta suke yi, idan har Mama bata son auren nan nasan idan nayi bazan zauna lafiya ba"
Mufeeda ta riƙo hannun yayarta tace "kin san wani abu Yaya Amina"

Amina ta girgiza kai cike da Tausayin Mufeeda
Chapter 11 · 0% Book details