Sashe 25
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ammar ka bar kuɗin ka, nauyin iyaline yanzu akan ka, bakomai ni ina da kuɗi a jikina" Yadda Ammar yake da kafiya haka Abban sa yake se haƙura yayi ya ƙyale shi ya shiga cikin gida.
Guri ya samu ya zauna suka sha hira da Umma, Yace a bashi Abincin safe yaci
Umma tace "ka baro gidan ka sannan mu kazo ka cinye mana Abinci, maimakon ka taho mana dana Amarya"
Ɗan murmushin yaƙe yayi yace "Umma kenan yau naku nake son ci"
"A'a kodai akwai matsala ne?"
"A'a babu wata matsala Umma"
Umma tace "Halima É—akko masa fulasan Mufeeda ya tafi dasu"
Ammar ya kalli Umma sororo yace "flasan Mufeeda kuma?"
Halima tace "Eh mana Yaya Ammar, sau biyu tana kirana a waya na karɓo mana Abinci, wallahi ta iya girki sosai, ran da mukaje gidan ka baka nan, Su Yaya fa'iza suna ta mata wulaƙanci wai matar ka 'yar Yarinya amma tana zubo mana Abinci tsit kake ji"
Shiru Ammar yayi bece komai ba, ya karya a gida, daze tafi ya bawa Umma kuÉ—in da yayi niyyar bata dana gurin Abba yai musu Sallama ze tafi yace "Halima biyo ni da Kwanukan nan"
Umma tace "to Ammar kace ina gaida 'yata, ya kamata kuma ka kawo mana ita, ko seta haihu munje barka"
Da sauri ya kalli umma, a ransa yace "ji umma da wani zance, wai seta haihu aka ga wannan' yar yarinyar da ciki ai naji kunya"
A fili yace "zan kawo tane, na tafi"
"to shikenan ka gaishe ta dan Allah, kace mata nagode sosai, Allah yayi albarka, Su Maryam ma da sukaje shekaranjiya suna ta ƙara yaba Sirikartawa, ka gaishe ta dan Allah, Allah yayi muku Albarka"
"Ameen" ya amsa
Tunani daban daban ne suka ziyarci zuciyar sa, ya akayi aka samu banbanci da abunda Anty Jidda ta gaya masa?
Halima tabi bayan sa da flasai, seda suka fita suka je gurin a daidaita sahunsa Ammar ya kalleta yace "yaushe kukaje gidana keda su Fa'iza?"
"wancan satin ran Asabar" ta bashi amsa
"Da kukaje akwai abunda ya faru da ku kaje ne?"
"A'a ba abunda ya faru, sedai su Yaya Nasreen ne suka dinga gaya mata baƙar magana, da zamu tafi suka ce zasu ga gida, ta shiga dasu ko ina tace ba zasu shiga ɗakin da kake kwana ba, shine suka dinga zagin ta, kuma bata kulasu ba, tace dai kome za suyi suyi ba zasu shiga ba"
Jinjina kai Yayi yace "Shikenan jeki, se an jima" daga nan ya hau Napep É—in sa ya tafi.
A hanya ya haɗu da Aminu, ya tsaya suna gaisawa, Aminu yace "lallai mutumin nan wato tunda Allah yasa aka kaimaka ƙwailar ka, ko neman mu baka sake yi ba, kaga yadda kayi wani shar da kai dan Allah me take baka ne?"
Ammar yace "ban sani ba, na shigo rannan naje gidan ka baka nan, Jabir ma kunyar sa nake ji, ina so muje gidan sa nida Mufeeda sannan kaima in kaita gidan ka, tunda Jabir yai Aure sau É—aya naje gidan sa se dai mu haÉ—u a unguwa"
Aminu yace "Kai Ammar ƙyale wannan Auren na Jabir, ƙaniyar sa kawai yake ci, Allah ya kiyaye kar auren nan ya mutu"
Da sauri Ammar yace "haba dai, saboda me auren da befi watanni huÉ—u ba zuwa biyar ba, shine ze mutu?"
"Ammar abun ne ba'a cewa komai, su matan se a hankali muma mazan hakan take, kasan halin Jabir shi kawai kyau da body structure na yarinyar yabi ya aure ta, amma she's not wife material at all, Sam bata ganin girman sa, rannan yake gayamin faÉ—a cikin dare shi da ita zagi in zaga"
"Subhanallah garin yaya haka ta faru da Jabir, sam bemun zancen ba"
"Ai zancen ne babu daɗi dan haka ba lallai yai maka ba, sedai mun haɗu zancen nada tsayi, Amma Jabir na buƙatar mafita"
Hama sukayi sallama da Aminu, Ammar ya tafi yana tunani a ransa, yayi zagi in zaga da mace kuma ya ci gaba da zama da ita baze yuwu ba, yana daga cikin illar Auren yaran nan da basu gama hankali ba. Wunin ranar haka yai ta saƙe saƙe, gefe yana tunanin yaze warware matsalar sa da Mufeeda.
Bayan sallar isha'i ya koma gida, Tana jin dawowarsa amma bata fito ba, yana ta tunani me yakamata yayi ne, yana son ya ganta amma sam bata fito falon bama balle ya ganta.
Yayi tunanin ze iya zama makircin su Nasreen ne abunda suka faɗawa Jidda, Amma baze iya tunkarar Mufeeda ya bata haƙuri ba, idan yayi hakan zata raina shi, ko kuma ta samu damar wulaƙanta su anan gaba, Amma yadda take kukan nan ya kamata ace ya ganta.
Tashi yayi ya nufi ɗakin ta, ya tura ƙofar ɗakin a hankali, akan dadduma ya hango ta ta duƙunƙune a cikin hijjabi, da alama kukan take, tausayinta ya mamaye zuciyar sa, ya ɗanyi gyaran murya yace
"ba'asan na dawo bane?"
Juyowa tayi ta kalle shi a sanyaye tace "bana so in fito kaƙi kulani ne" tai maganar wasu Hawayen na fitowa daga idon ta.
"Azo a bani Abinci, ina jin Yunwa"
Ai da sauri ta miƙe tsaye ta cire hijjabin jikin ta tare da ƙaƙalo murmushi tana goge hawayen ta tace
"dagaske ka haƙura zaka ci Abincin?"
Jinjina mata kai yayi alamar "Eh"
Cikin sauri tace "bari inje kitchen in É—ora yanzu zan gama"
"Shikenan ina falo ina jiranki" ya juya ya yafice daga É—akin, farinciki yasa ta kasa dena kukan da take, ta fito falo ta É—akko masa ruwa da cup ta kai masa kaman yadda take masa in ya dawo.
Yasa hannu ya karɓa sannan ya zaunar da ita a kusa dashi, yasa hannu yana goge mata Hawayen fuskar ta, yace
"kin san bana son kuka ko?"
Jinjina masa kai tayi, yace
"to me yasa kikeyi dan ki ƙara ɓatamin rai?"
"Ai kaine kake fushi dani kuma na baka haƙuri kaƙi haƙura"
"to ai yanzu na haƙura, sedai abunda nake so dake, ko a nan gaba karki kuskura kiyiwa wani wulaƙanci a cikin 'yan uwana, sannan duk wanda ya wulaƙanta ki ko ya miki wani abu ki gayamin zan ɗau mataki akai"
Girgiza masa kai tayi tace "A' a Yaya Ammar idan sunmin wani abun ma ni bazan gaya maka ba, bana son in dinga ɓata maka rai ko wani abu na ɓacin rai ya shiga tsakanin ka dasu na ɓacin rai saboda ni, kuma ni ba wani abu da suka yi min da zesa in kawo ƙararsu gurin ka, ni ɗinma da suka ce na musu ba daidai ba, ba ina sane bane kuma nace ka basu haƙuri "
Gaba ɗaya mamakin maganganun ta yake, ga wani tausayinta da ya kama shi, ita dai kar ransa ya ɓaci shine babban burin ta.
Ya kalle ta yace "kina cin Abinci kuwa? Naga kin rame"
Shiru tayi ba tace komai ba se kallon sa da take yi.
"je ki É—ora mana Abinci ina jin Yunwa kwana biyu nayi missing jagwalgwalonki, Umma tace a gaisheki wai jagolgwalon Abincin ki da daÉ—i"
Murmushi tayi tace "Yawwa gara da umma ta faÉ—a ai, nasan Abinci na da daÉ—i ai"
ÆŠan Murmushi yayi yace "dama kin kai musu Abinci ban sani ba? Ai shikenan tunda an wareni suna ta godiya, nima nagode sosai naga kaman ma sunfi sonki yanzu akai na"
"Idan na kuma yiwa su Umma abu kayi min godiya, zamu ɓata da kai zan dena kula ka, ni su Umma iyaye na" tai maganar tana ɗan zumɓura baki.
Ammar ba ƙaramin jin daɗin abunda ta faɗa yayi ba.
Yau taƙi zuwa ta zauna kusa dashi sosai balle ya shaƙi wannan dadaɗan ƙamshin turaren na jikin ta.
Ta miƙe da sauri tace "bari inje in ɗora Abincin nasan kana jin yunwa sosai"
Ta tafi kitchen ta ɗora sanwa, cike da farincikin yau mijin ta ya sakko daga fushin da yake da ita, yana nan zaune ya kallo wayarsa ta fara ringing baƙuwar lamba ce dan haka ya ɗaga tare da yin sallama, Muryar Zainab ce ta amsa sallamar, haɗe rai Yayi yace "ya akayi?"
"Shikenan Ammar bazan kira ka mu gaisa ba? Har yanzu ina nan ina dakon soyayyarka a raina na kasa mantawa da kai"
"baki san nayi Aure bane zaki dinga kirana duk lokacin da kika ga dama?"
Mufeeda dake kitchen ce ta fito zata je tsakar gida ta É—akko tsintsiya, karaf taji yana waya da mace, turus tayi ta tsaya tana kallon sa, shima É—aga kai yayi suka haÉ—a ido, wani banzan kallo tayi masa ta fice ta ci gaba da aikin ta, dukda jikin Ammar Yayi sanyi da irin kallon da tayi masa, amma be kawo komai a ransa ba ya ci gaba da wayar sa.
"Look zainab bana son shirirta, idan Allah ya baki miji kiyi haƙuri kiyi Aure kawai, ni bani da halin riƙe mata biyu" zata kuma magana ya katse kiran.
Mufeeda da ta koma kitchen kawai ta tsinci kanta da zubda Hawaye, dukda kasancewar ta yarinya ƙarama kuma me kawaici tana da matukar rauni a ɓangaren kishi.
Ta kammala ta zubo masa Abincin ta kawo gaban sa ta ajiye masa komai ta juya zata tafi, yace
"ke ba zaki ci Abincin ba?"
"Na ƙoshi" ta bashi amsa tana ƙoƙarin tafiya ɗakin ta.
"idan ba zaki ci ba, zoki É—auke Abincin ki nima bana ci"
Dawowa tayi ta zauna, ta zuba masa Abincin ta miƙa masa.
Nasihar Mahaifinsa ya tuna akan yayi haƙuri ya kula da Matarsa ƙaramar Yarinya ce, kar ya dinga nuna mata wannan yawan fushin nasa.
Ammar neman shiri yake da Mufeeda dan haka ya Karɓa ya matso kusa da ita, ya ɗebo Abincin a cokali ya kai bakin ta
"maza ungo karɓi kici, nasan kema kina jin Yunwa"
Girgiza masa kai tayi hawaye na bin idon ta tace
"Ni na ƙoshi"
"Haba Ƙwailar kar muyi haka dake mana, kince bana baki Abinci a baki, nace zan baki kuma kince ba kya so" ya kuma kai cokalin bakin ta, Amma ta ɗauke kanta tana kuka.
Sosai ta komawa Ammar ƙaramar Yarinya, har mamaki take bashi ace Yarinya kaman Mufeeda take kuka haka saboda kishi, ajiye spoon ɗin yayi ya ɗan zuba mata ido, sannan ya janyo ta jikin sa yace