← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 64

Sashe 50

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ƙarya ne ba dai Mufeeda ce ta gaya miki haka ba, ba zata taɓa faɗin haka ba"

PLEASE IF YOU READ IT HELP ME TO SHARE IT,
DON'T FORGET TO VOTE AND COMMENT

JIYA NA KUSA CIN DUKA A WAJEN MASOYA MUFEEDA 🤣

Domin Sharhi gyara ko shawara you are free to contact me via my what's App Number
Ayshercool
.. ✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨

( *Sai Mata* )

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

ELEGANT ONLINE WRITER'S

         

                        Page 25

Mufeeda tana fama da laulayi Sosai, har gwara 'yan kwanakin nan ta ɗanji sauƙi, Ammar kam kullum cikin sintiri yake gidan Anty Maryam, Amma bata saurarar sa duk lokacin da yaje haka ze dawo gwiwa ba ƙwari.

Yanzu ma Sallama yayi sedai yau Anty Maryam bata nan, Mufeeda ce kawai se 'yar Anty Maryam wadda ba tafi shekaru uku ba suna kallo da Mufeeda a falo, A hankali Mufeeda ta amsa Sallamar Ammar É—in, ya shigo falon da suke ya tarar da Mufeeda a falon, kallo É—aya tayi masa ta É—auke kai.
Ɗan Murmushi Ammar yayi yace  "Lallai Auta Sauƙi ya fara samuwa, yau kina falo wannan kwalliya haka"

Bata ce masa komai ba sema maida hankali da ta sake yi akan Tv, 'yar Anty Maryam Ammar ya bawa biscuit yace  "Amrah ina Umminki?"

Cikin maganar yara tace 
"ta tafi unguwa ta bammu nida Anty Mufeeda"
"Shikenan maza jeki É—aki kici biscuit É—inki keda teddynki"
Cikin murna yarinyar ta tashi ta tafi ɗakin su na Yara tana murna, Yaran Anty Maryam duk suna makarantar kwana ne (boarding) , daga ita se Yarinyar ta ƙarama.

Ammar ya zauna a kusa da Mufeeda yana ƙare mata kallo, ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tayi taƙi kallon sa.

"Mufeeda nine bakya son gani ko?"
Tura baki tayi taƙi kallon sa.

"you look so beautiful Masha Allah"

Da sauri ta kalle shi tace "Ka manta ne ƙwaila fa kake wa magana kar in rainaka fa naji kana cewa nayi kyau"

Ƙasa yayi da murya yace  "Eh nasan ƙwailar ce, Nace kiyi hakuri please mu koma gida, nima fa bani da lafiya koda yake naga kin dena sona Amma ayi haƙuri dan Allah"

Cikin tsiwa tace "Dan Allah nika matsa daga kusa dani, na gaya maka daga gidan nan se gidanmu zan wuce, bazan sake zama da kai kanamin faÉ—a kullum ba"

"Mufeeda nine fa"

Shiru tayi tana zumɓura baki, Janyo ta yayi yana ƙoƙarin kissing ɗin ta, ta dinga ture shi tana girgiza masa kai.

Sallamar Anty Maryam ce tasa shi sakin ta yana maida numfashi, miƙewa Yayi Da Sauri, Anty Maryam ta kawo kai ɗakin ta tsaya tana yiwa Ammar kallon tuhuma.

Basarwa Yayi yabi gefen Anty Maryam ya fice ba tare da ya kula ta ba, ta kalli Mufeeda da tayi kicin kicin da fuska tace
"Lafiya kuwa Mufeeda?"
"lafiya ƙalau"
"Kodai Akwai matsala ne?"
Girgiza mata kai Mufeeda tayi, bata son ci gaba da takura mata dan haka ta ƙyaleta.

*********************

Bayan barin Mufeeda gida wata mata ta sake tarewa a jikin gidan Mufeeda, tunda ta shiga gidan Su Maman Amir taga take taken basu da mutunci, basu da Aiki se gulma da zagin mutane, kuma da wata ta tashi a cikin su zasu hau yi da ita.

Ammar yana kwance a falo yaji ana knocking, kamar kar ya tashi amma ya miƙe yaje ya buɗe, yana buɗewa yaga Fa'iza a tsaye, Murtuke Fuska yayi yace  "Malama lafiya?"
Murmushi tayi tace 
"laa Yaya dama kana gida? Ziyara na kawo maka"
"Nagode, Amma bata nan dan haka zaki iya tafiya"
"Amma Yaya Ammar ai ko ruwa ka bari Insha, na kwaso rana da gajiya wallahi"
"Baki da hankali ne? Bakije me nace ba? bata nan, ya zaki shigo gida Alhalin matar gidan bata nan, daga ni seke? Ki tsaya anan in miƙo miki ruwa amma ba zaki shigo ba"
Haka tabi Ammar da kallo ya rufe ƙofar sa ya shiga gida ya miƙo mata ruwa ya koma.
Jinjina kai Fa'iza ta shiga yi kafin daga bisani ta bar gurin tana wani tunani a ranta.

Bayan Su Anty Maryam sun kammala cin Abincin dare, ta lura kamar akwai magana a bakin Mufeeda, ta kalle ta tace  "Mufeeda ya akayi ne?"
Ɗan shiru Mufeeda tayi sannan tace  "Dama Anty.. Inn.. Ina so in koma ne"

"Kin gaji da zaman nan kina kewar mijin ki ko?"
Saurin girgiza mata kai Mufeeda tayi tace  "A'a Anty Maryam, naga bashi da lafiya ne ko Abinci ba yaci, kuma ya bani haƙuri yayi nadamar abunda yayi"

"ki gayamin gaskiya, ko dai shi ne ya takura miki yace sekin koma?"

"A'a Anty be takuramin ba sam, kawai dai.."
Anty Maryam ta katse ta ta hanyar cewa "Shikenan naji, amma karki gaya masa zaki koma, zanga yadda za'ayi ki koma É—in, koba komai ai mun hora shi"

*****************
Wasa2 Saima rashin lafiya take sosai, Amma Jabir kawai cewa yake rakine irin nata, ta kumbura sosai ga damuwa tayi mata Yawa komai da ƙyar take yi, Jabir kam yana ta rawar ƙafa akan Fatiyya dukda kasancewar ta 'yar masu kuɗi hakan be hanashi yin bajinta yana kashe mata kuɗi ba, yayin da tsakanin sa da Saima se ido, kullum yana kan waya ko chatting, gani yake gaba ɗaya Saima ta koma masa wani iri, ta dena kwalliya kullum cikin larura take, gashi ta raina shi shiyasa sam baya saurararta.
Yanzu ma yana zaune yana chatting É—in sa se dariyar sa yake, Saima ta kalle shi tace
"Jabir yanzu haka zamu ci gaba da zama? Tsakanina da kai se ido ina fama da rashin lafiya ko a jikin ka sedai ka kalleni, ko kuma ka zauna kayi chatting da mata, babu ruwan ka da halin da nake ciki? Jabir kaji tsoron Allah"

"kinga Malama ya isheki, me kike so in miki? Zan cire miki ciwone? Ko kuma ni na ɗora miki? Kuma kina batun ina chatting da Mata danme ba zanyi ba? Kalli yadda kika koma kin Zama wata ƙatuwa kwalliyar ma kin dena, Kullum ke kenan cikin ciwo, nan ciwo can ciwo kaman akan ki aka fara ciki, nace kije gidan ku idan kika haihu seki dawo amma kin nace kinƙi tafiya, ya kike so in miki? Ba dai Abinci kikeyi wa ba, gashi nan na siya na ajiye kiyi taci"

Share Hawaye Saima tayi tace  "Jabir da ina da gata da tuni na barma gidan ka, kasan bani da kowa se Allah se kai, da na sa ran na samu mijin marainiya ashe ba haka bane, kake zancen kullum cikin ciwo nake bana kwalliya, da a haka ka ganni kace kana so? Kaifa ka maidani haka, kuma da kayi haƙuri na ɗan lokaci ne dana haihu Insha Allah zan koma yadda nake, Amma ina rabaka da Auren kwaɗayi Jabir, wallahi kaji tsoron Allah "

" Ubanwa yace miki Auren kwaÉ—ayi zanyi? "
" karka sake ka zagi Ubana, kuma ba uban wani ne ya gayamin ba da kunne na naji, za'a baka gida da Mota saboda rashin zuciya, duk Ni'imar da Allah yayi maka kana da gidan kanka, kana da Mota Amma kana hange, wallahi Jabir haƙƙi na baze barka ba"
"Oho ke kika sani, 'yar baƙin ciki dan kinga faƙiran' yan gidan ku basu kawo ki da wani abun Arziki ba shine kikewa wasu Hassada, ko gishiri da Sunan gara ba'a kawo ki da ita ba"

"Yanzu Jabir hadda Gori zakayi min? Amma ai haƙƙin ciyar dani a wuyan ka yake"

"Dalla rufemin baki, Aure ne se nayi kuma chatting yanzu na fara"

"Shikenan Jabir kayi abunda kake so, Amma wallahi se Allah ya sakamin, dan bazan taɓa yafe maka ba, Azzalumi mayaudari ka lallaɓani ka Aure ni da daɗin baki da Komai, Shine yanzu ka samu abunda kake so, zaka Auro wata har tana ba zata zauna dani ba, kaje ka yi indai kaine gaka gata nan, dana haihu ka sawwaƙemin yadda za kuji daɗin zama"

Tsaki yayi ya wuce ya barta a falon tana kuka.
Chapter 50 · 0% Book details