← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 64

Sashe 58

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka Ammar ya koma gida jiki a saɓule, yauma yana komawa Mufeeda ta karanto damuwa a kyakywar fuskar sa, ɗan ƙyaleshi tayi tai masa sannu da zuwa, se binta yake da kallo yana tuna lokacin da yake mata faɗa akan wasu laifukan amma ba zata taɓa kare kanta ba sedai ta bashi haƙuri.

Hakanan yaji kunyarta tana kama shi, ya tuna lokacin da take nuna ita a duniya babu wani namiji da take so seshi yaita Gwaleta, tayi abu danta burgeshi amma yai banza kamar be san me tayi ba, amma bazata karaya ba gobe ma se tayi wani abun da zesa yaji daÉ—i.

Gaba É—aya tausayinta ya sake kama shi.

"Wai na canza kamanni ne? Naga ana ta kallo na"

"gani nayi kin ƙara kyau"

Murmushi tayi tace "Kyau se Yaya Ammar amma ni ina naga wani kyau"

Ammar yace  "eh nagode, ko baki faɗa ba nasan ai ni mummuna ne"

"Idan ka kuma cewa mijina mummuna sena É—au mataki akan ka"

Kallon ta Ammar ya ci gaba da yi sannan yace  "Am sorry Mufeeda"

Kallon sa tayi cikin rashin fahimta tace  "Sorry for what?"

"Nasan kinyi haƙuri dani a zamanmu, nayi miki abubuwa da dama na rashin kyautawa, ina neman afuwar ki Mufeeda, ina jin kunyarki mussman idan na tuna abubuwan da suka faru a baya"

Juyowa tayi ta tattara dukkanin hankalin ta akan Ammar, ta riƙo hannayen sa a nata sannan tace
"Mijina Alkhairanka sunfi kura kuranka yawa da matsayi a idona, a zamana da kai nima haƙuri kake dani ai, idan harna manta alkhairin ka na kalli kuskurenka bazan taɓa yi maka Adalci ba, kasawa zuciyar ka ni babu abunda kayi min, Ni jina nake nafi kowace mace sa'ar miji, Allah ya barni da abun sona"

Tai maganar tare da sumbatar hannun sa.
Murmushi yayi yana kallon ta Mufeeda akwai hikima da iya kalaman kwantar da hankali
"Ina sonki Mufeeda"
"I love you more my heart, amma gayamin kace ranar daka fara ganina ka fara sona how comes?"
Murmushi yayi yace  "Ranar da na fara ganin ki, wannan iyayin naki da shagwaɓa har raina naji sun burgeni, a fili kuma abun ya ban haushi, ƙaramar yarinya kamar ke kina wannan abubuwan? Da na koma gida duk abunda zanyi sena tunoki, idan na kwanta bacci se in dinga mafarkin ki, lokacin da kike turomin saƙoni kullum nagani se naji daɗi, duk ranar da baki turo ba se inta fushi babu dalili "

Dariya suka dingayi tare, ta shafa gemun sa tace
" Gayamin meke damunka ne? "

Girgiza mata kai yayi yace
" Babu komai "

"ƙarya ba hakinka bace Mijina, duk yadda ka kai ga ƙoƙarin ɓoyemin damuwar ka ina ganewa, gayamin meke damunka? Ko har yanzu nayi ƙanƙanta in san damuwar Mijina"

Girgiza mata kai yayi ya É—an lumshe ido yana tuna irin abunda Faruka ya aikata shida Fa'iza, a hankali yace "Family issues ne Mufeeda, karki damu"

"Shikenan, amma kabi komai a sannu kaji mijina"

Ya jinjina mata kai, sannan yace  "ki shirya Anjima da daddare insha Allah zamu je ki duba Saima, yau aka yi mata aiki, munyi waya da Jabir yace babyn yazo ba rai"

"Allah sarki, Allah ya bata lafiya, ai da sauƙi tunda ba ita ta mutu ba"

Murmushi yayi yana ƙara riƙe hannun ta a nasa yace
"Allah ya raba ki da cikin nan lafiya, Jaririya ta"
"Ameen Babyn Jaririya"
Suka yi murmushi gaba É—aya.

******************************

Su Maman Nur kuwa aka karɓi Jaririn ta aka kai shi Asibiti, su kuma akaƙi sakin su, Hajara tace kotu take so akai su sunyi mata ƙazafi ga tada tarzoma a unguwa, da ƙyar aka shawo kanta ta yadda aka sake su, amma sunji a jikin su dan kamar 'yan gudun Hijira haka suka koma, wasu babu takalmi haka aka kamo su.
Abun kunya ace an kama matar Aure akan dambe da tada tarzoma ki bar gidan mijin ki ki tafi yawan gulma, abun takaicin ace harsa namiji baligi wanda ba muharraminsu ba suke zama a teburin sa suyi hira

(Mace kenan, wata ko me kifi ta tare zata siya ta dinga masa rangwaÉ—a kenan tana kashe murya tana yayana, dan yayi mata ragi wanda ba lallai tayi wa mijin ta ba, Mata aji tsoron Allah, a dinga kama kai)

Aure dayawa ya mutu a sanadin wannan tashin hankali da akayi a unguwar su Mufeeda, da ƙyar aka sake su yayin da aka miƙa Sa'idu ga 'yan sanda domin tattara bayanai a gurfanar da shi a kotu, sakamakon tara matan daba muharramansa ba yake hira da su, yana haɗa husuma.

******************

Se la' asar Saima ta farka daga nannauyan baccin da take yi, ƙanwar mamanta ce a gurin ta, ta temaka mata ta zaunar da ita, da yake an samu ci gaba a yanzu likita yace a bawa saima tea, saɓanin da da idan akayi theater se ace se mutum yayi tusa za'a bashi Abinci.

Ta gama shan tea ɗin tana kashingiɗe tana jin yadda wani irin zafi ke ratsa inda aka yanka ta, dan Allurar harta sake ta, cikin zuciyar ta kuma na ƙunar rashin Jaririnta, seda ta haihu take jin da ɗan yana da rai Jabir kome zeyi ba zata barmasa ɗanta ba kamar yadda ta faɗa a baya ba, se dai yaje wadda ze aura ta haifa masa.
A hankali ta lumshe ido hawaye na bin kuncin ta, zuciyar ta na mata raɗaɗi, muryar ta can ƙasa tace
"Jabir duk a sanadin ka har yankamin ciki aka yi, amma nice abar wulaƙantawar ka"
Sunkuyar da kai tayi tana ci gaba da share hawaye.

Ƙanwar maman ta tace "wai Saima bazaki dena wannan kukan ba, ki fawwalawa Allah mana, kima gode Allah da ya barki da ranki da lafiyar ki, Allah ya kaimu baɗi iyanzu ki kuma haifo mana wani"

"Ba Ameen ba Gwaggo, bazan koma gidan Jabir ba"

"Meyasa?"

"Gwaggo ni kaɗai nasan abunda nake fuskanta a gidan nan, bar masa gidan sa shine mafita baze ƙarasa hallaka ni ba"

Suna cikin maganar ne mariƙin Saima ya shigo da matansa duba ta, bayan sun gama yi mata ya jiki sun zauna ana ɗanyin hira, sega Jabir ya shigo hannun sa ɗauke da leda, kamar na Allah ya durƙusa ya gaida 'yan uwan Saima, ya ƙarasa gaban gadon ta yace
"Saima ya jikin naki?"
"Ban sani ba da sauƙi ko babu sauƙi be shafe ka ba malam ina fatan kazo min da takaddata ta saki?"

Mariƙin ta cikin fushi yace  "ke Saima meye haka? Mijinki nefa kike gaya masa wannan maganganun, ya sake ki akan me?"

"Kawu duk abunda ya sameni Daga Allah ne, Amma Jabir ne Sila, wallahi na koma gidan sa kasheni zeyi da baƙin ciki, dama ko bance ya sakeni ba yace ze sakeni dazarar na haihu, ya auro wadda zeyi Arziki ta sanadin ta"

Maimakon kawun Saima ya tsaya yaji ba'asi kawai ya balbale Saima da Faɗa ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, ya zage ta tsaf harda gori a gaban Jabir, yace seta koma gidan ta dan baze iya ci gaba da riƙe ta ba wanda yayi a baya ma Allah ya Amfana.

Seda wata metron tazo ta kori duk na cikin É—akin saboda hayaniyar da suke, aka bar gwaggon Saima kawai, bayan fitar su Saima ta samu ta zayyanewa Gwaggon ta halin da take ciki.

"Allah sarki marainiyar Allah ina gefe ai ban san halin da kike ciki ba, ban san irin zaman da kika yi a gidan kawun naki ba kenan"

"Dan Allah gwaggo kisa baki, wallahi ba zan iya zama da Jabir ba"

"Shikenan kwantar da hankalin ki, nima ban goyi bayan kikoma ba, bari inje in samu kawun naki muyi magana"

Kusan mintuna Ashirin da fitar Gwaggo bata dawo ba, turo ƙofar ɗakin aka yi Mufeeda ce da Ammar, sekuma Fiddausi da mijin ta Aminu.

Saima na ganin su tayi murmushi tace
"Sannunku da zuwa, maraba"

Fiddausi tace  "yana ganki ke kaɗai babu kowa?"

"sun reception suna magana, ga guri ku zauna, Mufeeda naso mu haÉ—u kafin in haihi Allah beyi ba"

Mufeeda ta ƙarasa gaban gadon Saima ta zauna tace  "Bakomai Anty Saima sannu ya jikin naki?"

Nan suka gaisa suna mata sannu, Mufeeda tace  "Amma jinin naki ya sauka ko?"

"Eh Alhamdilillah, Jijjiga nayi shine aka yimin aiki"

"Allah sarki Anty Saima sannu"

Tai maganar cikin tausayawa tana riƙe hannun Saima.
Ammar yace  "Nida ta tayarmin da hankali ranar da Aminu ya kirani yace wataƙil ma kin mutu, ta kasa zama ta kasa tsaiwa, to gashi dai Anty Saima tana raye.

Suka yi murmushi ana ta hira da Saima, taji daɗin zuwansu, sun ɗebe mata kewa, ta samu sassauta daga ɓacin ram da take ciki.

Mufeeda tace  "Anty Saima babyn ba rai ko? Allah ya kawo mafi Alkhairi"

"Babu rai yazo Mufeeda"
Tai maganar tana goge ƙwalla.

Mufeeda tace  "Anty Saima ya zakiyi kuka? Ki gode Allah da kina raye Allah ya baki wani"

"Mufeeda kenan dole inyi kuka, wata tara yaron ma ciki na na saka rai, Amma Allah yayi ikon sa"

Fiddausi tace  "kiyi haƙuri Saima, ki kwantar da hankalin ki, kin san baki da cikakkiyar.....

Ai ba ta ƙarasa maganar ba kawun Saima ya shigo yana banbami yace

"ba dai baki da mutunci ba kin dage sekin kashe Aurenki, to idan ya sake ki ki nemi gurin zama ba gida na ba, dan bazan ƙara riƙe ki ba wahalar da nayi dake a baya ta isa"

Gwaggon Saima tace  "ka dai ji kunya, dama can ba wata tsiyar kuke tsinana mata ba, tayi zama ne tamkar baiwa a gidan ka, a matsayin ta na 'yar ɗan uwan ka, nayi imani da Allah da' yar ka ce bazace ta koma ba, shima shegen yaron kwaɗayayye ashe 'yar gidan Alhaji Saminu Kwangila ce yake ƙuzun Aure, ai nasan yaran gidan maza yaje ya kwasa, nidai tunda ya sakarmin ' yata yaje ya ƙarasa, fuskarsa ta nuna dama haka yake so"

Mufeeda ta silalae ta bara ɗakin dan ba zata iya jure kallon wannan wulaƙancin ba, kowane tarkace sedai a ɗora shi akan mata.
Chapter 58 · 0% Book details