Sashe 53
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da Safe Ammar ya shirya yace zeje Asibiti yaga halin da Saima take ciki, Mufeeda tace seta bishi, yayi yayi ta zauna a gida tace ba zata iya zama ba binsa zata yi,
"Kinga kiyi haƙuri bekamata in tafi dake ba yanzu, ki bari inje inga halin da take ciki se inzo muje ki duba ta kinji Jaririya ta"
"Shikenan Allah yasa tana raye ya bata lafiya, muje in raka ka"
Ammar ya wuce gaba tana binsa a baya, suna fitowa tsakar gida ta shaƙi ƙamshin ɗumamen miyar kuka, ta kalli Ammar tace "Yaya Ammar ba kaji ƙamshin miya ba?"
"Naji mana, meyafaru?"
"Kaman daga gidan Anty Hajara nake jin ƙamshin"
Ammar yace "Maybe"
Marairaice Fuska tayi tace "dan Allah Yaya Ammar in baka kwano kace ta sanmin ko loma biyu ne?"
Wani irin kallo Ammar yayi mata yace "Idan tuwon kike so ki dafa mana, kawai se inje da kwano ince a baki tuwo se kace bana baki Abinci, naga ma dai ba shiri kike da maƙotan nan ba, kawai se inje in fara roƙon Abinci"
"Dan Allah Yaya Ammar, ita wannan da zaka karɓo min a gurin ta ba irin su bace, niko loma ɗaya ta bani"
Ammar ya fara ƙuluwa, haushi ya cika shi yaja babur ɗinsa yai waje ya barta a gurin, ɗaki Mufeeda ta koma tana kuka ji take kamar taci babu, ji take inba tuwon nan ba ba zata iya cin komai ba.
*****************
Ammar yana tashi gidan Aminu ya fara zuwa suka tafi Asibitin tare, bayan sun gaisa Ammar yace "Aminu wai dan Allah meyafaru ne? Jiya hankali na ya tashi sosai da abunda ka faɗa, kuma Mufeeda taji gaba ɗaya ta birki cemin da koke koke"
Aminu yace "Hmm Ammar ni nama rasa ta inda zan fara, wallahi duk Faɗan da muka yi wa Jabir sam baya ji, Jinin ta ne ya hau taita Jijjiga. jiya dai har na baro Asibitin likitocin basu ce komai ba, yanzu da Safen nan kuma na kira shi bata shiga"
Ammar yace "Allah ya kyauta, bari muje muji"
Koda suka je Asibiti suka tarar da Jabir a zaune a reception duk yayi wani iri, suka gaisa suka yi masa yame jiki?.
Ammar yace "Jabir wai ya akayi haka ta faru meyasa meta ne?"
Jabir yace "Wallahi da zan fita ne ta cemin kanta na ciwo, na ɗauka kawai rakine irin nata shiyasa ban kula ba na fita, kawai ina komawa gida na tara da duk jikin ta jini"
Wata Nurse dake reception ɗin tana cike files ta ɗago ta kalle su tace "Eh ai da yake ba 'yarka bace dole kace haka mana, kudinga girmama larurar mace me ciki koda kuwa tana da raki, da yake cikin ba' a jikinka ba yake ba dole kace tana da raki ai, ai gashi nan ta kusa rasa ranta, ko Awo bata zuwa ga jinin ta yayi mummunan hawa, bata shan magunguna da'ake rubutawa masu ciki, dan Allah ku dinga girmama larurar mata masu juna biyu komai ƙanƙantar ta ko kuma buƙatun su"
Aminu yace "Ayi haƙuri ranki ya daɗe yanzu wani hali take ciki?"
Nurse ɗin tace "ku jira likitan safe yazo tukuna, Amma tana ICU kuma a rubutun da likitoci suka yi a file ɗin ta, Jinin ta ya hau batasan ma waye a akanta ba sakamakon jijjigar da tayi, an rubuta muku hoton ƙwaƙwalwa zakuje ku biya, masu kula da ɓangaren zasu zo suyi mata, sannan likitoci zasu ranar daza'ayi mata aiki, dan ba zata iya haihuwa da kanta ba"
Aminu yace "Jabir kayi wauta wallahi, bekamata ace haka ta faru da Saima saboda kai ba"
Ajiyar zuciya Jabir yayi ya kasa cewa komai, haka suka dinga sintiri zuwa wajen biyan kuɗaɗe da'aka nema, 'yan dubiya suka dinga zuwa amma babu damar ganin Saima saboda tana ƙarƙashin kulawa ta musamman.
*******************
Rashin samun tuwon nan ba ƙaramin ɓatawa Mufeeda rai yayi ba dan seda tayi kuka tukuna, kuma taƙi cin komai ita kanta wannan abubuwan suna damun ta sosai, ga tunanin ko wane hali Saima take ciki daya dame ta, waya ta ɗakko ta kira layin Ammar, kafin ta tsinke ya ɗaga yasa a kunnen sa
"Yaya Ammar ya jikin Anty Saiman"
Ammar yace "Jikin ta da sauƙi Alhamdilillah, dan yanzu haka ma bacci take"
Ajiyar zuciya Mufeeda tayi tace "Masha Allah, Allah ya bata lafiya"
"Ameen, nima yanzu nake sa ran in taho, me zan taho miki dashi"
Zumɓura baki tayi kamar yana kallon ta tace "Ni bana san komai, dama dana samu tuwon nan ne da se inci, tunda ban samu ba na sha ruwa kawai"
"Ke wato tunda na fito baki ci Abinci bako? Keba kya tausayin kanki"
"Nima ban san me yasa nake haka ba, Amma ni wallahi tuwon nan nake so"
"to ni karkiyi min kuka, ko tea ki haÉ—a Kisha, zan san yadda za'ayi kafin in dawo"
Ammar ya dage yana rarrashi a waya, gaba É—aya ya manta da Aminu a gurin, Aminu yace
"Kaga mijin ƙwaila an dage ana rarrashi da alama an gamu kenan?"
"Aka gamu dame?"
"Ban sani ba, gaskiya wannan ƙwailar she deserves to be saluted, Kai Ammar ka wani kwantar da murya kana rarrashi, kai da kace raino zakayi ya akai ka haɗa ta da raino kuma?"
ÆŠan Murmushi Ammar yayi yaceÂ
"ba zaka gane ba that girl is so funny and romantic, ban san yadda akai komai ya canza ba"
Dariya Sosai Aminu yake yana tsonakanarsa.
Suka ƙara yiwa Jabir jaje suka bar Asibitin.
******************
Maman Nur suna zaune suna tafe ita da Maman Amir suna hira suka je gurin Sa'idu me kayan miya, nan suka tsaya suna munafuncin nasu da suka saba, Munafuncin Maman Sadiq suke yi, wai mijin maman Sadiq ke son ƙanwar Maman Nur, ita maman Sadiw ɗin bata sani ba, ya saiwa ƙanwar Maman Nur wayar dubu tamanin ya bar maman Sadiq da wayar dubu uku me fasashshen screen, Nan Maman Nur ta dinga zuba tana faɗar irin hidimar da yake musu, Sa'idu se zigata yake, suna cikin hirar Hajara tazo yin cefane, ko kallon su ba tayi ba ta gama cefanen tayi gaba. Tana tafiya Sa'idu yace
"Wai ita wannan 'yar waye girman kai kamar matar me A daidaita sahu, kuma kamar ita kaÉ—ai take zaune a gidan"
Maman Nur tace "Nifa banga alamar tana da miji ba, kamar zaman kanta take"
Sa' idu yace "zaman kanta take to se ku killace yaran ku, dan kar ƙarti su fara muku sintiri a layi"
Nan suka yi ta gulmace gulmacen su sannan suka tafi.
*****************
Fa'iza ta shirya ta tafi gidan su Ammar, tayi sa'a kuwa Umman tana nan, Umma na ganin tace
"Fa'iza yau kece a gari haka?"
"wallahi kuwa Umma, ina Halima ne?"
Umma tace "Halima ta tafi Makaranta"
Fa'iza tace
"Umma naje gidan Yaya Ammar fa"
"Allah sarki ya kika baro su? Mufeeda har ta gaji da mitar banje ba, ina jin kunyar zuwa gidan Ammar, bana son ka dinga zarya a gidan yara, karka takura musu"
Kwaɓe baki Fa'iza tayi tace "Nifa Umma ƙara na kawo miki"
"to ƙarar wa kuma?"
"Ranar da naje gidan Yaya Ammar wallahi a waje ya barni wai Mufeeda tana bacci bazan shiga a tashe ta ba, wallahi a waje yaimin korar kare"
Shiru Umma tayi tace "Ammar ɗin ne yayi miki haka?"
"Wallahi haka yayi min, ranar ma munje da daddare amma baki ga korar karen da yayi min ba, tunda Mufeeda ta nuna bata sona yake min wulaƙanci"
Shiru Umma tayi sannan tace "Amma basu kyauta ba, kiyi haƙuri Insha Allah zan musu magana, Amma Mufeeda mutuniyar kirki ce"
"Hmm kudai take wa kirki ni ban san me nayi mata ba, kuma goyon bayan ta yake, yafi sonta akan mu 'yan uwansa"
Umma tace "Haka naji Jidda tana ƙorafi akai, Amma ni dai ba tayi min nagani ba, Amma Insha Allah zan masa magana, kiyi haƙuri"
"bakomai Umma na dai gaya miki ne dan kisan me' ake ciki"
Haka Fa'iza ta ci gaba da ɓata Mufeeda a gurin Umman Ammar, Sannan tai mata sallama ta tafi.
Ammar yana ta sauri ya koma gida, se kuma yayi tunanin bari yaje gida ko ze samu Umma tayi tuwo ta bashi ya kaiwa Mufeeda.
Sedai yana zuwa ya tarar kamar ran Umma a É“ace, Umma taceÂ
"Yawwa Ammar naji daÉ—in zuwan ka, dama ina son ganin ka"
Ammar yace "to Umma Allah yasa lafiya"
"Ammar ɗazun nan Fa'iza ta bar gidan nan, ta kawomin ƙararka akan abunda kayi mata, tazo gidan ka amma kaƙi bari ta shiga gidan ka, wannan wane irin haline? Bekamata ka dinga fifita Matar ka akan 'yan uwanka ba, bance karkaso Matar ka ba amma dai ka kula da' yan uwan ka"
Ammar yaso yayi ƙoƙarin kare kansa, Amma wani abu daya koya a gurin Mufeeda shine, muddin lokacin da babba yake maka magana kayi ƙoƙarin yin magana da niyyar kare kanka, to hakan na iya tunzira mutum, dan haka Ammar yayi shiru Umma ta gama faɗan ta, sannan ya ɗago kai yace
"to Umma Allah ya baki haƙuri, Insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba"
Umma tace "Yawwa ina Mufeedan tana lafiya?"
Ammar yace "lafiya ƙalau tana gaishe ki, bari in koma in Abba yazo kice ina gaishe shi"
"to tsaya ina da gyaÉ—a me gishiri da aka kawomin bari in baka ka kai mata, sannan ka gaya mata akuyar ta ta haifi yara uku"
Bece komai ba se shiru da yayi zuciyar sa na tafasa, yana tunanin wane hukunci zeyiwa Fa'iza ya huce
Æacin ran da Ammar ya tarar ya hana shi gayawa Umma batun tuwo da rashin lafiyar Saima ba, ya karÉ“i gyaÉ—a harda tsintsiyar laushi ya tafi.
Ransa a ɓace sosai ya fito daga gidan ze tafi, Halima ce ta dawo daga Islamiyya taga Ammar yana ƙoƙarin tafiya
"Yaya Ammar Ashe kazo? Ina Anty Mufeeda?"
"tana lafiya" Ammar ya bata amsa ya shige A daidaita sahunsa ya tafi. Halima tayi mamakin ganin Ammar ya fito daga gida ransa a haɗe haka, ta ƙarasa ta shiga gidan.
"Umma wai me kikayiwa Uncle ne? Na ganshi da zan shigo kamar ransa a ɓace"