Sashe 27
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Se la'asar sannan ta farka, ta shiga tayi wanka ta samu ta saka kaya a jikin ta, ta gyara gadon ta ta nemi guri ta zauna.
Ammar ya dawo É—akin yaga har tayi wanka ta canza kaya, ya kalle ta yace "ya jikin?"
"Da sauƙi Alhamdilillah"
"Saka hijjabinki kizo mu tafi"
Kaman tace masa A'a amma ta fasa saboda yanzu seya ɓata rai, haka ta saka hijjabi ta fito.
A hankali take tafiyar, Ammar ya riƙo ta suka fito zuwa cikin a daidai ta sahunsa, Matan layin da yake sana'ar su ce leƙen ƙofar gida suna gulma, suna ganin Ammar ya riƙo Mufeeda sun fito gaba ɗaya hankalin su ya koma kansu, yasa Mufeeda a babur ɗin ya zagaya ya zauna a mazaunin direba ya kunna suka tafi.
Suna tafiya matan layin suka dasa gulmar su, wasu suna itace matar gidan, wasu suna ba ita bace ba sedai ko baƙuwa suka yi ko 'yar uwassa ce, da yake basu san itace matar gidan ba.
Wani Clinic na kuÉ—i ya kaita, suna zuwa ta samu guri ta zauna Ammar yaje aka buÉ—e mata file, sannan suka shiga gurin ganin likita.
Suka gaisa da Likitan, ya kalle su yace "to kai ta kawo ko kai ka kawo ta"
Ammar yace "itace ba lafiya"
Likitan ya kalleta yace "meya ke damun ki ne?"
Kallon Ammar tayi tai shiru, Ammar yace "kiyi magana mana"
"Ciki nane yake min ciwo"
Ammar yace "ba ciki ba dai mara ko?"
Kunya ce ta kamata tai shiru tare da sunkuyar da kai.
Likitan yai murmushi yace "Nagane, menstrual cramp ne, yaushe kika fara?"
"haka yake min idan zanyi"
"Yaushe kika fara menstruation?"
"four years back"
Ba Likitan ba har Ammar seda ya kalleta Ammar yace "are you sure?"
"Very sure" ta bashi amsa
Likitan yace
"Ok hakan ba wani abun damuwa bane, mata suna shiga wannan yanayin idan suna Al'ada, sedai a kula da ita da abubuwan da zata ci, Sannan idan ta samu ma nemi a mata Aure, idan akayi musu Aure in akayi sa'a wasu yana raguwa koma su rabu dashi baki É—aya"
Ita dai Mufeeda ba tace komai ba.
Likitan yace
"tsakanin magani da Allura wanne kike so?"
Kafin tayi magana Ammar yace "Allura zaka rubuta mata"
Zare ido tayi tace "Haba Yaya Ammar wallahi bana son Allura, dan Allah kar ayimin"
"Likita rubuta mata Allura, Allura tafi quick Action, in ba haka ba muka koma gida zuwa zata yi ta cigaba da lanƙwashewa"
Mufeeda tuni ta fara kuka, liktan yace "We have to respect her autonomy, tunda magani take so a rubuta mata"
Ammar yace "No Allura zaka rubuta mata"
Haka likitan ya rubuta mata Allura da sauran magungunan, ya kalle Mufeeda yace
"Sorry Baby Allura ba zafi fa, Wannan Yayan naki yace se an miki Allura"
Basu kuma kulashi ba, Ammar ya sunkuya yace mata "gobe ma ki ƙara min rashin kunya, ina sane nace a miki Allura" zumɓura baki tayi suka fito daga OPD ɗin, Ammar yace ta zauna ya siyo maganin, ta zauna tana jiran sa.
Bayan ya siyo maganin ne yaci karo da Faruk, suka gaisa Faruk yace "Ahh mutumina me kake anan?"
"Mufeeda ce bata jin daÉ—i na kawo ta A duba ta"
"Allah sarki, nima nazo in duba wasu patients ɗina ne da na yiwa CS jiya, muje semu gaisa tunda kuka tare ko leƙoku ban kuma yi ba"
Suka tafi tare suna hira, Faruk yaga Mufeeda ta ƙara ƙiba, dukda kuka take amma tayi wani fresh da ita, Faruk yace "Madam har yanzu ba'a dena rikici ba? Hala laulayi ne?"
Ammar yace "Haihuwa zata yi ba laulayi ba"
Ganin irin kallon da Faruk ke mata yasa Mufeeda tace "Na gaji Mu tafi"
Ammar yace "to Faruk se anjima se munyi waya" ya kama hannun Mufeeda suka tafi Injection room.
Fafur Mufeeda taƙi shiga Nurses suyi mata allurar, Ammar ya fara ƙulewa ya janyo ta zuwa cikin gurin, kuka take sosai kamar wadda za'a yanka.
Ammar yace "haba Autar Baba sonake ki warke da wuri shiyasa nace ayi miki allurar ai, hug me you won't feel the pain"
Ya buɗe mata hannayen sa, a hankali ta ƙarasa ta kwanta a jikin sa, ya riƙe ta, Nurse ɗin tace
"Ikon Allah, dan Allah ƙanwarka ce ko matar ka?" da yake babbar mace ce dan haka Ammar ya bata amsa
"Mata ta ce"
"gaskiya ran haihuwa da kallo, Allura kawai tana wannan abun, Allah ya ƙara maka haƙuri ɗan nan, kana fama da shagwaba" murmushi kawai Ammar yayi.
A hakan ma da ƙyar ta tsaya aka yi, Hawaye sharkaf fuskarta, maimakon da'aka gama ta tashi sema ƙara narke masa da tayi a jiki tana kuka.
Ammar yace
"ya isa haka harfa an gama, Insha Allah yanzu zaki dena jin ciwon"
"Wallahi Allurar da zafi sosai"
"to ai zafin kaÉ—an ne akan ciwon da kike ciki"
Nan ta shiga zabga shagwaɓarta, ƙarshe nurse ɗin se fita tayi tabar musu room ɗin.
Ammar yace "ki tashi mu tafi kinji an fara kiran sallar magariba"
Noƙe masa kafaɗa tayi,
"idan munje gida zan baki biscuit ai zaki ci ko Jariri ya ta?"
Murmushi tayi masa tana lumshe ido, a hankali ta miƙe ta biyo shi suka fito, suka hau babur ɗin su zuwa gida.
Da sukaje gida Mufeeda tace ita ba zata iya tafiya ba, ƙafar ta ta sage jikin ta babu ƙwari, ƙarshe seda Ammar ya ɗauke ta ya kaita har kan gadon ta a ranta tace
"tunda kasa akamin Allura se kayi jinya kaima"
Ammar yaje yayi salla, ya dafo mata tea ya kawo mata, ta karɓa ta sha sannan ya miƙo mata ledar pharmacy yace
"gashi nan pampers É—in da kika ce in sai miki ne" ta kalle shi tace
"Pampers kuma?"
"Eh mana ko kin manta ne?"
Karɓar ledar tayi ta duba, pad ce guda uku da sababbin pants guda biyar, wata kunyace ta kama ta, banda abun Ammar panties ɗinta kona lefe bata taɓa ba amma ya sai wasu. Sunkuyar da kai tayi taƙi ɗagowa su haɗa ido.
Yace "zanje masallaci idan nayi sallar isha'i zan É—an za gaya, kinga yau ban samu nayi aiki ba yadda yakamata"
"Shikenan amma karka yi dare sosai dan Allah"
Jinjina mata kai yayi, ya miƙe ya fita.
Bayan ya idar da Sallar isha'ine Aminu ya kira shi yace "yana so su haÉ—u za suje gidan Jabir"
Haka kuwa akayi a gidan Jabir suka haÉ—u, Jabir yayi farincikin zuwan su, Yace
"Kai Ammar Mufeeda ta ɓoye ka, ko a hanya sam bama haɗuwa, ga yadda kayi kumatu"
Yaita zolayar Ammar sannan yai musu iso zuwa cikin gidan, falon sa ya kaisu suka zauna suka dinga hira, Can Ammar yace
"Jabir abar hirar nan muyi abunda ya kawo mu? Ina matar gidan ne?"
Jabir yace
"tana gidan É—akin ta"
"a gaskiya naji wani labari dabe min daÉ—i ba game da auren ka, Jabir ya'akayi haka ta faru?"
Jabir yace "bari Ammar ai nayi zaɓen tumun dare dana san haka Auren yake da banyi ba, wallahi mata basu da mutunci nayi dana sanin Auren Saima"
Ammar yace "Dana sanin mene?"
"Yarinyar nan sam bata da Mutunci bata ganin girma na, bata da tarbiyya Sam, ban isa in gaya mata taji ba, wallahi badan ina tsoron abunda iyayena zasu ce ba da tuni na sake ta"
Aminu zeyi Magana sega Saima ta fito, tana ganin su ta faÉ—aÉ—a murmushin ta tace
"Manyan Baƙi aini har nayi fushi, sau ɗaya kuka zo mana tun bayan bikin mu, Ammar ina Amaryar?"
"tana gida, idan ma baku zoba zan kawo ta Insha Allah"
Saima tace
"Insha Allah ai zanzo har gida mu gaisa, Jabir baka gayamin sunzo ba ai be kamata abar baƙi babu ko ruwan sha ba, bari in baku ruwa"
Ta wuce ta nufi kitchen, Jabir yaja wani uban tsaki yace
"Munafukar Banza"
Aminu yace "Subhanallah, haba Jabir a gaban mu kake kiran ta Munafuka"
"mece idan ba Munafukar ba, danta ganku take nuna ita ta Allah ce, Amma tafi sheÉ—an iya rashin mutunci"
Saima ta dawo da lemuka da ruwa faranti da kofuna, ta ajiye Musu a gaban su.
Saima ta kalli Su Ammar idon ta fal Hawaye tace
"Aminu wallahi Abokin ku Azzalumi ne, dan Allah ku gaya masa idan mutum ya auri mace baya na nufin ya auro baiwa bane, Jabir Jahili ne besan darajar É—an Adam ba"
Miƙewa Jabir yayi yana zare ido, ya fara narko mata Ashar, Saima tace
"Wallahi ba iyaye na ba sedai naka"
Da sauri Aminu ya miƙe ya riƙe jabir yace "Jabir meye haka? Matarka ta Aure kake wa wannan mummuna ashar agaban abokan ka?"
Saima tace "baka ga komai ba a gurin sa, dana san haka yake wallahi bazan Aure shi ba, mutanen kirki suka fito suna sona na liƙe nabi soyayya nace seshi, amma bayan Auren mu, shine kullum cikin chatting da 'yan mata, ba dare ba rana lokacin da nake buƙatar lokacin sa lokacin ne yake chatting, idan nayi magana seya ce wai na taɓa ganin anyi campaign bayan zaɓe? Da ina haƙuri ina ƙyale shi, Amma Ba damar inyi masa laifi se ya fara zagarmin iyaye, wallahi baka isa ba iyaye basu fi iyaye ba kakuma zagarmin iyaye sena zagi naka iyayen "
Ammar yace
"Saima yi haƙuri ki koma ɗaki, zamuyi magana da Jabir "
Haka ta wuce É—aki tana kuka, Aminu yace
"gaskiya Jabir kaine mafarin samar da matsala a cikin gidan ka, ta yaya zaka dinga ce mata ba'a campaign bayan zaɓe, hakan fa na nuna bata da wani mahimmanci a gurin ka, haba dan Allah Jabir kaman ba wayayye ba kaima fa kana da ƙanne mata baza kaso ayi musu haka ba, kuma wallahi in gaya maka kaida ta ƙara ganin mutuncin ka har gaban abada sedai tayi pretending, amma a matsayin ka na namiji daga lokacin da ka buɗe baki ka zage ta ka zagi iyayen ta mutuncin ka ya zube a idon ta musamman idan ta buɗe baki ta rama, Jabir meye Amfanin hulɗa da 'yan matan daba Auren su zakai ba bayan ga matarka ta halal a gefen ka? Kawai ka zauna fadi banza faɗi wofi a haka har sheɗan ya kawo muku wani tunani na daban"