← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 64

Sashe 31

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maman Sadiq tace "ai insha Allah zata rabu da cikin nan lafiya, duk 'yan layin nan za suyi fa anko zamuyi, mene dan ya miki lefe kwanan nan, ke yarinya bari kiji mazan yanzu ba' a tausayin su, ki zage duk abunda kike so ki sashi gaba seya miki"

Murmushi sosai Mufeeda tayi tace
"to nikam se an jimanku zan shiga kitchen, nagode sosai da shigowar da kuka yi"

Ta tashi ta barsu a falon, suka fito suna mamaki gami da zage zage.

Maman Sadiq tace "yau naga kinibabbiyar yarinya, wani wai kinfi buƙatar addu'a akan anko ji munafuka"

Maman Nur tace "ke niba wannan ba ina mijin ta É—an a daidaita sahu ne, kawai base naga saman fridge É—in ta da kayan shayi ba hadda su butter ga biscuits da kayan daÉ—i, naga dai bata haihu ba amma data buÉ—e fridge zata É—akko mana ruwa hadda chocolates a cikin fridge É—in, wallahi raina ya biya, bari gobe in Allah ya kaimu aikawa zanyi ta sanmin milo"

Maman Amir tace "hmm kedai bari muda mazajen namu suke da sana'oi da suke samun kuÉ—i rabona da baban Amir ya saimin kayan shayi tun haihuwar Amir yanzu yara na uku, danma ba kiga É—akin nan na tsakar gida ba ke kinga kayan Abinci kamar a kanti?"

Maman Nur tace "wallahi shiga gidan zan dinga yi nida yara, a dinga shan madarar nan damu"

Maman Sadiq tace "in kinga fuska muma semu biyo ki"

Suka cigaba da gulmar su dai

**********************

Mussaman Jidda ta shirya ta tafi gida, domin ta ziga Umma akan Auren Mufeeda da Ammar.

"Umma wallahi Idan ba'a tsaya akan Ammar ba, wallahi ze zama mijin tace, su Fa'iza basu gaya miki abunda yarinyar nan tayi musu ba"

Umma tace "A'a nidai sunzo nan Halima ta rakasu gidan Sa amma ba su dawo ta nan ba"

"to sun biya gida na, sun gayamin yadda ta dinga musu wulaƙanci"

Halima tai farat tace "Wallahi ƙarya sukeyi, tare fa muka je ba wani wulaƙanci da tayi musu"

Jidda tace "dan ubanki dake nake magana? Ko kuma ƙanwar uwaki ce da zaki goyi bayan ta?"

Tura baki Halima tayi tace "ai ni gaskiya na faÉ—a"

Umma tace "to ni Jidda na kasa gane inda maganganun ki suka dosa sam, wani irin wulaƙanci ne haka?"

"wallahi Umma rashin mutunci ta dinga yi musu, kuma da naje gidan ta baki ga kayan Abinci ba kamar abun banza, kashe mata kuÉ—i yake kaman kaman me amma ku nan baya kawo muku, se anyi magana yace ba shi da kuÉ—i"

Umma tai Murmushi tace "To meye a ciki dan ya kashe mata kuɗi matar sa cefa, kuma Ammar ko be mana a yanzu ba a baya yayi mana balle har yanzu Ammar yana iya ƙoƙarin sa akan kyautata mana, Jidda lokacin da mahaifinku yake da shi na wata ya ya kashe min kuɗi kaman babu gobe, shi ba mace ce ta haife shi ba? Ko kuma lokacin da yake kashe mana kuɗin meyasa ba kiyi complain cewar be kyauta ba? Ina yanzu keda 'yan uwanki kuma' ya'yan wasu kuke aure kuma suke muku hidima, dan me za kuce ɗan uwan ku baze wahaltawa wata ba? Ai abun Alfaharinku ne ace ɗan uwan ku ya auro 'yar mutane kuma yana iya riƙe ta, nikam Alhamdilillah Ammar har yanzu yana ƙoƙarin kyautata mana, kuma ni ina ƙaunar ta, Dukda murɗaɗen hali irin na Ammar duk da yadda bashi da tarin dukiya tace tana sonsa a haka ni ta gama yi min komai ina ƙaunar ta"

(ƙalubale gareku iyaye, haka ya kamata ku zamo masu adalci ga matayen 'ya' yan ku, dukda wasu sirikan basu da kirki, amma da yawan lokuta ƙannen miji da yayye suke jawowa matar ɗan uwansu a gurin iyayen su, su faɗi abunda akayi da wanda ba'ayi ba suce anyi, ku kuma iyaye babu binki ce babu komai ku hau kai ku zauna, Allah ya kyauta)

Jidda tace "Shikenan Umma tunda baki yadda ba, zaki gani da kanki wataran ai"

********************

Ammar ya dawo ya shiga ɗakin sa, ƙaton flower Mufeeda ta zana da sunan sa da Nata, gefe tayi rubutun kalaman Soyayya ta ajiye masa akan gado ɗan girgiza kai Yayi a ransa yace

"sam Yarinyar nan bata rabo da shiriri ta"

Ya fito falo ya tarar da Abincin sa sedai be ganta ba, yayi tunanin ko tana wani abun ne, dan haka ya zauna ya fara cin Abincin sa, sam Abincin baya masa daɗi saboda babu Mufeeda a kusa dashi balle taita masa wannan shirirtar tata, yana gama ci har ya tafi ɗakin sa ya dawo ya duba yaga ko tana lafiya, yana buɗe ɗakin ta ya tarar tayi ɗaiɗai akan gado tana bacci, ta tafi ƙarshen gado wanda idan tayi ƙwaƙwƙwaran juyi zata iya faɗowa, kome ya sata bacci da wuri haka oho?

A hankali yaje gaban gadon nata da niyyar ya gyara mata kwanciyar, yana É—agota ta firgice ta saka ihu.

Rirriƙeshi tayi tana zare ido, yace
"Ke menene haka? Nine fa"

Ajiyar zuciya tayi ta lumshe ido tace "wallahi ka bani tsoro, wani ɗan jaririn ƙadangare ne ya shigo gidan nan shiyasa na taho ɗaki fa"
tai maganar tana kwanciya a jikin sa.

"Yanzu Jaririn ƙadangaren ne yasa kika dawo ɗaki kika kwanta hadda rufe ƙofa?"

"eh mana idan kuma ya shige min É—aki fa?"

"Shikenan cikani zanje in kwanta"

Ta É—an kalle shi tace
"kaci Abinci kuwa?"

"Naci kwanciya zanyi yanzu"

Ta langaɓar da kai tace "nifa yau ban ganka sosai ba"

"Nifa bana son rigima, cikani ki koma baccin ki"

Wani irin kallo take masa, lumshe ido take alamar akwai bacci akan ta sosai amma Ammar gani yake kaman da gayya take masa wannan kallon.

"I love you sweetheart" shine abunda ta furta masa a hankali.

"Naji, karki manta gobe in Allah ya kaimu ki shirya da wuri zamu fita"

Jinjina masa kai tayi tana lumshe ido, ya zame ta daga jikin sa, ya kwantar da ita sosai akan filo ya fita ya koma É—akin sa.

Daya koma ɗakin ma tuni ta dafa masa ruwan wankan sa kafin ta kwanta, da zafi sosai ya haɗa ruwan yayi wankan, sannan ya samu guri ya kwanta, tunani yake da ƙoƙarin sama wa kansa mafita akan zaman sa da Mufeeda, baze yuwu su ci gaba da zama a haka ba dan ba ƙaramin cutuwa yake ba, yana mata kallon Yarinya ƙarama amma a lokuta da dama kasancewar su tare yana ƙara jefa shi cikin wani hali, lallai salon da take amfani da shi yana matuƙar tasiri ga zuciyar 'yan mazan.

Haka yaita tunani har yayi bacci.

Da safe Mufeeda tana ta ɗoki zata fita, watan ta biyu a gidan nan amma sau ɗaya taje Asibiti sekuma maƙota data shiga, Suna gama breakfast ta saka Ammar a gaba suka ware kayan Abincin gara da su rarraba da wanda zasu tafiwa da su Umma, har na su Yaya Maryam seda da su Jidda seda ta ware masa, ta rarraba kayan zaƙin nan na alkaki ta warewa kowa nasa hadda wanda ze bawa abokan sa su Jabir su bawa matan su.

Ammar ya kalle ta yace "Ai wannan kayan da kika rarraba sunyi Yawa, saboda ke aka kawo be kamata ki kwashe ki rabar ba, wanda zaki bawa su Umman ma ya isa nagode"

"Abunda kaci kashi ne wanda ka bayar shine rabon ka, ka sani ko dalilin bayarwar da mukayi Allah ya ninka mana, ai abun duniya ko ka bayar ko baka bayar na seya ƙare"

"Amma babu wanda zaki bawa a family É—in ku? Be kamata ace kin rabar da kayan nan haka ba"

"Ai kowa seda aka bashi kafin a kawomin, kaga wannan ai ya ishemu kaima kwana biyu seka huta, Allah dai ya ƙara maka buɗi babban mutum, ciyarwa ba aikin rago bane, kana ƙoƙari sosai seka huta kafin su ƙare"

"maganar hutu ai babu shi tunda na riga na ajiye ki, dole in fita in nemi abunda zan riƙe ki, kaman yadda yake a shari'a"

Miƙewa tayi tsaye tace  "kana ƙoƙari mijina, Allah ne kawai ze biyaka ladan ɗawainiyar da kake, Allah ya ƙara Arziki, bari inje in shirya karmuyi rana"

Ya jinjina mata kai, ta koma ɗakin ta ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, tayi to match da mayafin ta da Jakarta, Mufeeda akwai Gayu, da ta fito falo Ammar be fito ba ta bi shi ɗakin sa, tana zuwa ta tarar ya shirya yana ƙoƙarin saka links ɗin hannun rigar sa.
  Da sauri ta ƙarasa inda yake, ta fara ƙoƙarin saka masa tace

"Babban mutum kayi kyau sosai kaman in sace ka in gudu"

Kallon ta kawai yake ba tare da yace mata uffan ba, amma itama tayi kyau sosai, amma sam ba tayi kama da matar Aure ba.
Ta É—akko turare ta feshe masa jikin sa, tace
"Allah ya barni da abun sona har ƙarshen Rayuwa ta" ita dai duk wani motsi da zata yi se tayi masa Addu'a kokuma tayi masa kirari, kota nuna masa irin soyayyar da take masa, lokuta da dama har mamaki take bashi.

Haka ya shiga gaba tana binsa a baya, suka kulle gidan suka fita, Ammar idan ya fita tare da Mufeeda baya É—aukar passenger.

Seda tasa Ammar ya tsaya suka saiwa su Abba Fruit sannan suka tafi, Basu tsaya ko ina ba se gidan su Ammar, Mahaifin Ammar yana tsakar gida yana jin radio suka shiga da Sallama.

Abban Ammar yana É—aga ido, Mufeeda ya fara kallo ganin su tare da Ammar yasa ya gane itace Sirikar sa, Murmushi yayi yace
"barka da zuwa Yarinyar kirki sannu da zuwa sirika ta"

Har ƙasa Mufeeda ta durƙusa tana murmushi ta gaida Mahaifin Ammar, shima cikin dattaku ya amsa mata, yace
"Zauna mana sirika ta" gefen tabarmar Abba ta zauna

Ammar ya É—anyi gyaran Murya yace "tunda ni baka maraba da zuwa na, bari in koma"

Abba yai Murmushi yace "ni ai ka daÉ—e muna tare, ni nayi 'ya dama ba a Auta da namiji babarka tayi Auta da kai, ni yanzu ga auta ta nan"

Ammar yace
"Aikuwa zaka ga halin Auta kam"

Murmushi Mufeeda tayi tace
"dama shima É—an auta ne?"

Abba yace
"ƙannensa uku ne suka rasu, kinga kuwa shi ne ɗan Auta"
Chapter 31 · 0% Book details