Sashe 60
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru tayi masa tana ƙoƙarin raɓawa ta gefe ta wuce, amma ya sha gaban ta yace
"Naji labarin ashema mijin naki ɗan ta' adda ne, yana hannun 'yan sanda, matsalar Auren mutane irin mijin nan naki kenan, ki kwantar da hankalin ki, kici Arziki ki barshi a inda yake, ni me ƙaunar kine, tunda an riga an kama shi ki manta da shi kawai"
Cike da ɓacin rai Mufeeda tace
 "Kaji labari ko kuma kasa aka kama min Miji saboda son zuciyar ka? , kuma kasan baya gida kazo gidana cikin dare kana ƙwanƙwasamin ƙofa, kasa an cajemu kuɗi masu yawa, to insha Allah Ammar baze ƙara kwana a hannun hukuma ba, ze fito, kuma kasani shi Allah baya bacci idan har dasa hannun ka akan abunda ya samu mijina, ko bance komai ba Allah yana kallon ka"
Ta Æ™arasa maganar cikin hawaye, ta raÉ“a gefen motarsa ta wuce, ya girgiza kai yaceÂ
"wannan Yarinyar akwai shegen taurin kak, baki da rabo amma muje zuwa da kanki zaki kawo kanki, dan talauci masifa ne, sannan bazan iya haƙura da yarinyar nan ba"
Mufeeda tana zuwa gida ta turawa Aminu kuɗin nan, tana kuka gami da tausayin Ammar ta tura kuɗin nan. Ammar yana matuƙar ƙoƙari da gwagwarmayar neman halak, ya tara kuɗinsa da ƙyar beci ba be sha ba, A banza an raba shi da haƙƙin sa, sosai ta dinga kuka tana tunanin wannan wane irin zalunci ne haka?
Bayan ta tura kuɗin ne ta shiga kitchen ta duba me zata girkawa Ammar kafin ya dawo, kayan Abincin su duk sun ƙare, ranar daza'a kama shi yace mata tayi masa list ɗin abunda ya ƙare ya siyo, Amma wannan ƙaddarar ta haushi.
Aminu ne ya cika kusan dubu Arba'in sannan kuɗin suka cika ya biya, da zasu taho daga station ɗin Ammar yace a bashi mukullin Babur ɗinsa, amma suka ce ba zasu bashi ba, zasu riƙe Babur ɗin se sun kammala bincike.
Mufeeda ta shiga tana duba kitchen, Taliyace da ita guda biyu ta É—auki É—aya ta dafa, tana da sauran miya ta gyara ta, ta zuzzuba a Flask ta ajiye masa tana dakon dawowarsa, se la'asar sannan taji ana knocking É—in gate, da sauri ta tashi taje ta buÉ—e, Ammar ne shida Aminu, suna shigowa Mufeeda ta rungume Ammar tana kuka tace
"Allah ya saka mana Yaya Ammar, Allah ya ƙwatar maka haƙƙin ka, duk wanda yayi maka sharrin nan Allah ya saka maka"
Sosai suka bawa Aminu tausayi, Mutum me ƙaramin ƙarfi kamar Ammar ya tara 'yan kuɗaɗen sa da ƙyar Amma lokaci ɗaya a raba shi dasu abun da tausayi.
Aminu ya Jajanta musu, Sannan yace Insha Allah ze cigaba da bibiyar case ɗin a samu Ammar ya karɓi babur ɗinsa, Ammar yayi masa godiya da irin gudunmuwar da ya basu.
Ammar yayi wanka ya fito amma Mufeeda kuka take bata dena ba, ya zauna ya dinga rarrashinta, shi yanzu babban abunda ya dame shi shine babur ɗinsa da'aka riƙe, da Allah ya dogara da babur ɗin nan ya dogara, gashi kusan komai nasu na Abinci ya ƙare, ya daɗe yana tara kuɗaɗen sa gashi dare ɗaya babu su.
*******************
Saima ta fara samun Sauƙi, tunda akayi wannan sa'insar tsakanin kawunta da gwaggonta, gidan mariƙanta babu wanda ya sake zuwa duba ta, gwaggonta ce kawai a gurin ta take ta kula da ita se sauran wanda ba'a rasa ba, Jabir ma ya ɗauke ƙafarsa ya dena zuwa, ya samu Nutsuwar ci gaba da neman Auren Fatiyya.
Da'aka Sallameta tabi gwaggonta gidan ta, dukda itama me ƙaramin ƙarfice ga nata marayun Amma haka ta tafi da Saima tace Allah baze hanata yadda zata yi ta riƙe su gaba ɗaya ba.
******************
Rayuwa ta fara yiwa su Ammar wahala, da ƙyar yake iya samo abunda zasu ci inya fita, wataran sedai ya samo abunda Mufeeda zata ci shikuma ya haƙura.
Duk wata Sana'a da Ammar zeyi ta ƙarfi dan ya samu ya riƙe gidan sa yanayi komai ƙasƙancinta, Cikin Mufeeda ya shiga wata na biyar, ga wani irin yawan cin Abinci da take yi.
Duk Abunda ya kawo ya bata, bata raina wa hannu biyu take karɓa da murna tana Godiya koda kuwa abun be mata ba.
Itace ma take ƙoƙarin kwantar masa da hankali.
Gari ya waye da Safe, Ammar yana kallon ta ta ɗakko tuwon masara ta yayyankashi ƙanana tasa masa gishiri ta zauna tana cin Abunta da uwar safaiyar nan, saboda babu abunda zasu ci da Safen, tana yi tana kallon bollywood da suke wani shiri, yadda aketa sarrafa Naman kaji, tai shiru tana kallo gwanin ban tausayi da alama tana son ci ne. Ammar ji yayi kamar yayi kuka, gaba ɗaya tausayinta ya kama shi.
Ammar a rayuwar sa idan akwai abunda ya tsana be wuce ya keta bullensa yayi roƙo ba, tun yana ƙarami yake da wannan ɗabi'ar, idan har kaga ya nemi taimakon wani sedai idan ya rasa yadda zeyi ne abubuwa sunyi matuƙar ƙure masa
A hankali ya kalli ta yace "Mufeeda"
Ta juyo ta kalle shi, tare da yi masa murmushi tace
"Na'am my sugar"
"Dan Allah kiyi haƙuri, ni kaina bana jin daɗin halin da muke ciki, a halin da kike ciki be kamata ace kina cin wannan Abincin da sassafen nan ba, Dan Allah ki ƙara haƙuri Mufeeda, sannan naji daɗi da kika rufamin Asiri baki gayawa kowa halin da muke ciki ba, Insha Allah komai ze wuce"
Ya ƙarasa maganar kamar zuciyar sa ta fashe dan ɓacin rai.
Mufeeda tayi masa shiru ta cigaba da cin Abincin ta, tuwon data ci ma ba ƙoshi tayi ba, taci ta ƙarasa da ruwa, ta kalle shi tace
"Mijina, idan har na gujeka kona ɗaga maka hankali saboda yanayin da muke ciki Allah ma baze barni ba, duk abunda ya same ka ni ya sama, lokacin da kake samu dukda ba ƙarfi ne da kai ba, daidai gwargwado babu abunda baka bani na jin daɗin rayuwa iya ƙarfin ka, to wani dalili ne zesa in ɗaga maka hankali a yanzu, Jarrabawa ce Allah ne ya jarabce mu ina fatan Allah ya kawo mana mafita "
Shiru Ammar yayi yana kallon ta, ya kasa cewa komai.
"Yaya Ammar rufin Asirin ka nawa ne, Ina sonka Yaya Ammar fiye da yadda kake tunani, zan iya zama da kai a duk halin da kake ciki,saboda haka duk abunda ka kawo ka bani zan karɓa inyi Amfani da shi komai ƙanƙantar sa, sannan ina Amarya lokacin da su Baba suka zo sun ban dubu Goma, ban gaya maka ba saboda nasan zakamin faɗa kace meyasa na karɓa, shiyasa na haɗa da kuɗin da wanda kake bani kusan dubu goma sha biyar na bawa Yaya Amina nace ta yi Business dashi, idan ina buƙata zan mata magana, yanzu nayi mata magana na bata Account Number ɗinka zata sakomin kuɗin, seka ɗau dubu goma ka bani biyar tunda fridge ɗina biyu ne kuma ana samun wuta se in fara saida kayan sanyi, Amma me kace? "
Ajiyar zuciya yayi yace "zaki iya sana'a a haka? Karki wahalar da kanki fa"
"zan iya Yaya Ammar, zaman haka baze yuwu ba, kaga da ina Sana'a da abun yazo mana da sauƙi"
"Shikenan, Amma be kamata in karɓar miki kuɗi ba, sedai ko rance in Allah ya hore in mayar miki"
HaÉ—e rai tayi tace "Niba rance zan baka ba, kyauta zan baka kayi abunda ya dace dasu, kaga da Abba ze yadda a cikin dabbobi na ya baka ka siyar da wasu ka haÉ—a"
"A'a kin san halin Abba, baze yadda ba, Naji daÉ—i Sosai Mufeeda Nagode, Nag.....
"Shhhhh babu wannan tsakani na da abun sona, dan Allah Yaya Ammar ka kwantar da hankalin ka kaji, ni ba zan É—aga maka hankali ba, mubi komai A sannu, Allah yasa haka shine mafi Alkhairi"
Ya amsa mata da Ameen, sannan yace "ranar Litinin ya kamata ki koma awo, amma baki je ba, Amma in Allah ya kaimu sati me zuwa zaki koma Awo ina sane, Insha Allah"
Jinjina masa kai tayi tana masa murmushi.
*******************
Mijin Jidda ya dage kai da fata seya ƙara Aure, duk wani abu data san zata yi ta tayar masa ds hankali tayi amma kamar tana ƙara ziga shi, haka ta haƙura ta shiga gyare2, ya gina sabon gidan sa inda zasu koma gaba ɗaya ya haɗe su.
Tana so ta koma da sababbun furnitures, tace ya canza mata yace bashi da kuÉ—i, ita kuma kuÉ—inta ba zasu kai ba, tace bari taje tasa Ammar a gaba ya cika mata.
Sedai da taje ta tarar Ammar baya nan, Rashin mutuncin nata dai data sabawa yiwa Mufeeda bata dena ba, taita zuba ido Mufeeda ta zubo mata Abinci amma shiru nan ma ta samu nayi, ita dai Mufeeda ko uffan ba tace mata ba, ana haka Ammar ya dawo ya tarar da Jidda.
Se wani harare hararw take tana hura hanci ita ga me É—an uwa, Bayan sun gaisa ta gaya masa abunda takeso yayi mata.
Ammar yace "A gaskiya Jidda sedai kiyi haƙuri, bani da hali a yanzu bani da kuɗi, naga kayan kujerun naki aiba wani abun suka yi ba, ki tare dasu mana"
"dalla Yimin shiru, kace dai bazaka bani ba, ka taɓe a gindin mace se abunda take so, tunda kayi Auren nan ko ɗan Alherin da kakewa Mutane ka dena, Saboda wannan lotsatsiyar Yarinyar mara hankali"
"Ya isheki Yaya Jidda, a baya da ne miki babu nauyin kowa a kaina, kuma kinsan ina miki, yanzu kuma Akwai Nauyin Mufeeda a kaina, A yanzu idan na tauye haƙƙin ta nayi miki se Allah ya tambayeni, balle kuma bani da shi"
Abun ya nemi ya koma musu faÉ—a suka yi baran baran ta koma ta zage Mufeeda tsaf, Ammar yana tare mata, da haka ta bar gidan.
Ammar yaita rarrashin Mufeeda yana bata haƙuri akan irin abubuwan da Jidda take mata, Mufeeda tace
"Bakomai Yaya Ammar, ai wataran se labari nasan ze wuce"
"Yawwa 'yar Aljanna, É—azu bayan fita ta Amina ta turo kuÉ—in nan, amma dubu Ashirin da biyar ta turo'"