← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 64

Sashe 42

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka yiwa Mufeeda kaca kaca da gida, ga zagi da cin mutunci da suka zazzage mata sannan suka tafi. Zama Mufeeda tayi tai shiru tana Hawaye, ta rasa me tayi wa bayin Allah nan suka tsane ta haka.

Wayar ta ce ta fara ringing, tasa hannu É—aga ta kai kunnen ta.

"Amarya ba kya laifi shine kika yi blocking ɗina a what's App ko? To ai ba zaki taɓa gujemin ba, baze yuwu inta Azabtuwa da ƙaunar ki ni kaɗai ba, kuma idan ba kiyi wani abu a kai ba to ina tabattar miki dani zanyi, ki huta lafiya abar sona"

Ya katse wayar sa, Mufeeda ta kasa ko motsawa daga inda take ta rasa me ya kamata tayi, tayi tunanin ko ta gayawa Mama halin da take ciki, se kuma taga yayi wuri ace ta fara gayawa Mama ga matsalolin da take ciki, dama Abunda Maman taita jiye mata kenan, ina ma na bi abunda Mama ta faɗamin wataƙila da hakan bata faru ba, wata zuciyar tace ai duk daren daɗewa ai zanyi Auren kuma ƙaddara ta ba zata canza ba.

Tayi nisa sosai a cikin tunanin dan haka ba zato ba tsammani taji Ammar yana ƙoƙarin buɗe ƙofar falo, dan sam ba taji tsayuwar babur ɗinsa ba, zumbur ta miƙe da nufin tattare kayan da su Fa'iza sukayi kaca kaca da su, Amma Ammar ya riga ya shigo, turus yayi yana bin falon da kallo, Anyi kaca kaca da Madara a tsakiyar falon ga kwalin cornflakes da jarkokin lemo komai an zubar da shi a wulaƙance, da sauri ta ƙara so inda yake tana masa sannu da zuwa ta miƙa hannu da nufin karɓar kayan hannun sa ya kalle ta yace
"Meye haka a falon ki? Abincin Akayiwa haka?"
"A'a Yaya Ammar dama baƙi nayi shine....
" Shut up " ya mata tsawa.
" baƙi kikayi shine za'a wulaƙanta min Abinci haka, kalli falon nan fa ji almubazzaranci kuma kina kallo? Kin sani saboda ke nake ajiye wannan abubuwan ni ba damuna suka yi ba, Amma kika bari a ka wulaƙanta haka, kalli Abinci har a tsakar gida an ajiye shi fal a bakin tap, da yake baki san zafin nema ba ko shiyasa kike wulaƙanta wa, bazan ƙara siyo wa ba, zan ajiye Abinci ne kawai, in kinyi hankali na siyo a nan gaba amma ko Madara ba zan sake siya ba, sakarya kawai "  ya watsar da ledar da ya shigo da ita a falon ya wuce ɗaki Fuuuuu.

Jiki a sanyaye ta durƙusa ta shiga gyara inda ya ɓaci a gidan, gaba ɗaya ta rasa mafita akan lamuran nan, Allah ya temaki Mufeeda hankalin Fa'iza be kai kan Flask ɗin Abincin Ammar ba, dan haka seda ta gyara ko'ina sannan ta ɗau Abincin ta bishi ɗakin sa.

Ya kwanta yayi rigingine yana kallon ceiling da alama tunani yake yi, ta ajiye Kayan Abincin tace
"Yaya Ammar ga Abinci na kawo maka"
Banza yayi mata yaƙi kallon ta, cikin sanyin Jiki tace "dan Allah kayi haƙuri, zan kiyaye insha Allah dan Allah kayi haƙuri"
A fusace yace "É—auke Abincin ki ki fitar min daga É—aki"
"Dan Allah kay.....
"ki ɗauke Abincin ki nace na ƙoshi, idan baki fita ba ni zan bar miki ɗakin"
Cikin hanzari ta É—auke Kwanukan ta fito.
ÆŠakin ta ta koma ta kwanta, ta rasa me ke mata daÉ—i
"ya Allah idan abunda bayin nan naka sukemin da mugun ta sukemin Allah kayi musu abunda suka yi min" ta ƙarasa maganar hawaye na zubo mata,
"har zuwa yaushe zan cigaba da É—aukar laifin da ba nawa ba, babu Amfani in gaya masa abunda sukemin dan ba abunda hakan ze haifar se wata rigimar da tashin hankali, Allah ka bani mafita"
Haka ta ci gaba da Hawaye tana surutai.
Kiraye kirayen sallar magariba ne yasa ta tashi taje ta ɗaura alwala ta daɗe akan sallaya har kusan ƙarfe sha ɗaya tana ta Addu'a tana kaiwa Allah kukan ta, kamar yadda taga Mama ta nayi a lokuta da dama.

Da gari ya waye farkawa kawai tayi taji ƙarar Napep ɗin Ammar yayi ficewarsa, ji tayi gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi bata ƙaunar ganin ya share ta. Idan ya fice tun safe baya dawowa se sha ɗaya kuma yana dawowa ɗakin sa yake wucewa, ko kula ta baya yi balle ya ci Abincin ta, Ammar be iya fushi ba sam, gaba ɗaya idan yana fushi tsoro yake bata dan wani irin kwarjini yake mata, ko tunkarar sa bata son yi, dan idan ya mata tsawa ba ƙaramin firgita take ba.

Yau tana idar da sallar Asuba bata koma ba ta fito, ta shiga aikace aikace, aikuwa ƙarfe bakwai ya fito ze fice, tana kitchen ta fito da sauri tana kiran sunan sa, be saurare ta ba yayi gaba, cikin sauri ta bishi amma ta bige goshin ta da ƙofa da sauri ya tsaya ya juyo, ƙarar da ƙofar tayi zesa kasan ta bugu sosai ya kalle ta yace

"ke komai ba zakiyi a hankali ba, da kinjiwa kanki ciwo fa?"

Bata kula da me yake cewa ba tayi kneeldown akan gwiwowin ta, ta riƙe rigar sa tana kuka tace
"ba dan hali na ba dan girman Allah kayi haƙuri, Insha Allah bazan sake wulaƙanta maka Abinci ba ko in bari wani ya wulaƙanta maka ba, kayi haƙuri dan Allah mijina ka dena fushi dani komai ya denamin daɗi saboda kana fushi dani, kayi haƙuri dan Allah"

Jin kukan nata yayi har cikin zuciyar sa, ya kalleta yace
"shikenan get up"
"A'a dan Allah kace ka haƙura se in tashi"
"Ninace ya wuce ai"
"ka haƙura?" tai maganar wasu hawayen na bin fuskarta, ya jinjina mata kai alamar eh.
Ya juya ze fice tai sauri tace "dan Allah Yaya Ammar, ka tsaya in dafa Abinci kaci ba dan ni ba dan Allah"
"Shikenan muje"
Har Mufeeda ta kammala girkin kuka take, ta kawo ta ajiye masa tana ƙoƙarin haɗa masa ya kalleta yace "Kukan be isa haka ba? Se kanki yayi ciwo?"
Ai kaman ya tunzura ta, ta sake fashewa da kuka hadda sheshsheƙa.

"Idan kuka za kiyi zan fasa cin Abincin"

Kasa denawa tayi tasa hannun ta, ta toshe bakin ta tana ci gaba da kukan, zubawa sarautar Allah ido yayi, seda tayi me isar ta sannan ta koma gefe ta dinga sauke Ajiyar zuciya, bece mata komai ba ya shiga cin Abincin sa ya nayi yana kallon ta, har ya kammala ya fita, tunani ya dingayi a ransa anya ba wani abu ne yake damun Mufeeda ba, ace dan yana fushi da ita ne zesa taita wannan kukan? Ba yadda zeyi ya zama dole idan tayi ba daidai ba ya hukunta ta.

Kamar Yadda Ammar ya gaya mata be ƙara siyo duk wani abu da ya saba siyowa domin ita, ya dena ajiye mata kaman Madara, Milo tarkacen buscuit da lemo da yake ajiyewa duk ya dena sedai yayi cefanen abunda zaa'a ci kawai, Sam bata nuna masa ta damu da hukuncin ba, Sedai har yanzu sama sama yake da ita ko sakar mata fuska ba yayi, haka take gaba ɗaya a takure sedai idan ta bashi Abinci ze ci, idan ta gaishe shi ze amsa mata.

Tana son shiga maƙota tayi wa Maman Nur ya jiki taji ance ta dawo dan haka tun kafin ya fita ta tambayeshi yace seta dawo.

Seda rana tayi sanyi bayan la'asar sannan ta saka hijjabin ta ta rufe gida ta shiga gidan Maman Nur, duk maƙotan nan na layin su wanda ta sani da wanda bata sani ba sun cika gidan suna ta shewa, Mufeeda tai Sallama ta shiga ta samu guri ta zauna suka gaisa, tace musu
"ina me jegon ne?"
Banza suka yi mata, Wannan Yayar Maman Nur É—in ce Anty hauwa tace mata "ta shiga wanka amma yanzu zata fito"
Mufeeda ta zauna zaman jiran Maman Nur ta fito, Yayin da Maman Amir se wani binta take da kallon banza.
Su Maman Sadiq na gefen ta taji suna ƙusƙus da wata maƙociyar su, Maman Sadiq tace
"Kin san wani abu Hafsa jira nake inga Yadda maman Nur zatayi ranar suna, ta ishi mutane hadda fidda anko wai za'ayi shagali ta dinga tatsar mijin ta kuɗi tana hana yaranta Abincin kirki tana tara kuɗin cefane dasu fa dama zata yi taron sunan, to yanzu ta haihu kuɗin data ƙulle za ta birge 'yan unguwa su ta ɗakko akayi mata magani, Mijin ta yace bashi da kuɗi "

Wadda aka kira Hafsa tace
" Dama abun nata duk burga ce da ƙaryar banza, gani take kamar duk layin nan mijin ta yafi kowa kuɗi "

" Dalla duk ƙarya ce, shegen ƙaryace da ita ga roƙe roƙen tsiya ita kuma ga rowa "

Mufeeda dai na jinsu ba tace komai ba, Maman Nur ce ta shigo ta fito daga wanka, dama Mufeeda duk ta gaji da zaman, a tsakanin su da suke tare ma suna zagin juna ina ga ita da ba sayi da ita.

Mufeeda tace " Maman Nur ya jiki? " se lokacin Maman Nur ta lura da Mufeeda ya tsine fuska tayi tace
"Naji sauƙi da ba kije dubani bama na warware"
"Nima ba haka naso ba, lokacin da suka biyo min muzo duba ki baya nan ban tambaye shi ba, kuma ni ba wani sanin kan uguwanni nayi ba, baya barina in fita nika É—ai"

Wata uwar shewa suka saki, Maman Nur tace "Allahu Akbar masu miji kaga masuyi dan Allah"
Maman Sadiq tace "Taɓ kaga matar so, dama ina ze bari kifi ta ke kaɗai duniya ba yadda"
Mufeeda ta basar da su tace
"A bani Babyn in ganshi"
Har za'a miƙa mata Jaririn Maman Nur tace "gaskiya Anty hauwa karki bata ɗana"
Anty hauwa tace "saboda me?"

"Haka kurum, daga zuwa gidan ta, in kai mata ankon suna se cewa tayi inyi fatan in haihu lafiya ba rabon anko ba, ƙarshe na haihu lafiya amma seda na dangana da Asibiti"

Anty hauwa tace "to ai gaskiya ta gaya miki, yanzu kingama rabon anko amma kin ƙarke babu lafiya"

Mufeeda ta miƙe tsaye tace "Bakomai, Allah ya baki lafiya, ya raya abunda aka haifa"
Chapter 42 · 0% Book details