← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 64

Sashe 64

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Jabir ya fashe da kuka yace
"dan Allah Saima kiyi haƙuri ki yafemin, Alhaji kine yake ɗawainiya dani, dan Allah kizo mu koma mucigaba da rayuwar mu, wallahi na canza hali"

"Allah sarki, kuma gashi ka makara, dan ko baka makara ba babu ni babu komawa gidan ka, sedai ina maka Albishir ranar Asabar za'a É—auramin Aure, zan Auri sirikin ka wato mahaifin Saima, sedai ni ba Auren Jari zanyi ba"

Ta juya ta shige ta bar Jabir a tsaye, abun takaici yana komawa gida ya tarar da Saima yai mata rashin mutunci yace tabar masa gidan sa tace sedai ya bar gidan, dan gidan uban ta ne bana uban sa ba. Jabir yai mata saki uku sannan ya bar gidan.

Baban Fatiyya ya shigar da ƙarar Alhaji Idris akan ya sace masa 'ya yai mata Fyaɗe, aka hana shi kare kansa yanaji yana gani aka kulle shi.

Bayan ya Auri Saima haka Fatiyya ta koma gida, duk yadda babarta take juya mahaifin ta ƙarshe' yan kallo suka zama dan se abunda Saima take so akeyi.

Alhaji Haruna yaje gidan Ammar yaga Jariri yayi masa Addu'a sannan yace
"Ammar babban dalilin zuwa na gidanka shine, A baya na jarrabaka gurare daban daban, Na lura kana da Amana sannan ka birgeni saboda rashin girman kanka da Amanarka, wadda tayi ƙaranci a yanzu, shi ne nace Akwai branch da zan buɗe na saida kayan masarufi da nake yi, zan zuba kayan million Ashirin, ka riƙe gurin ka ɗau ma'aikata ku riƙe gurin, idan shekara tayi zaka dinga raba riba biyu kana biya na, a hankali har shagon ya zama mallakinka"

Zare ido Ammar yayi yace  "Aini ban taɓa kasuwanci ba, ta yaya zan iya juya dukiya me yawa haka?"

"zaka iya Ammar, ina so in taimake kane, dan a rayuwa ta ina son inga na temaki na ƙasa dani shima ya tsaya da ƙafar sa, na jinjina maka dan har unguwar nan nazo nayi bincike akan ka naji daɗin yabon da naji ana maka"

Ammar yayi shiru yace  "to zamuyi shawara da Madam, abun da muka yanke shikenan"

Alhaji Haruna yayi murmushi yace  "Kai wannan Madam ana ji da ita, ko dai in baka 'yane, naga ka iya riƙe gida"

Ammar yace "daga ita ba ƙari ai"

"shikenan Ammar, da wasa nake maka, sena jika"

Mufeeda tayi farinciki da jin labarin, tace
"Yaya Ammar mahaƙurci mawadaci, wataƙila da sana' ar A daidaita sahu kake ba lallai ka samu wannan Ni'imar ba, Ammar da yake Allah me hikima ne, seya raba ka da Napep ya maida kai kasuwa, yanzu dai muyi ta istikhara tukuna inda Alkhairi Allah ya tabattar, sannan kayi shawara dasu Abba "

Haka kuwa akayi, bayan yin Addu'oi da Neman shawara, Ammar ya Amince ya karɓi shagon, Allah yasanya masa Albarka ya dinga ciniki, nan da nan Ammar ya zama hamshaƙi.

Da Khalil ya isa yaye, ya kaiwa Umma shi ya nemo wa Mufeeda Admission, ta shiga makaranta, seda Ammar ya cika Alƙawarin da yayi wa Baba akan karatun Mufeeda.

A hankali Ammar ya gama biyan Alhaji Haruna kuɗin sa, shagon ya zama mallakin sa, ya canza gida ya sai mota, kullum cikin neman taimako ake a gidan Ammar, duk me wata buƙata in dai ya biyo ta gurin Uwargidan Ammar anyi ta an gama, dan Mufeeda bata taɓa cewa abu yaƙi, 'yan uwa da abokan Arziki babu wanda baya morar Arziƙin Ammar.

Faruk ya haɗu da ciwon sugar, gaɓoɓin jikin sa suka dinga gutsurewa suna zubar da ruwa.
Fa'iza kuwa har shekara talatin babu wanda ya Aure ta.

Ammar ya zama hamshaƙin ɗan kasuwa, ya buɗewa Mufeeda Ƙaton gidan gona, aka ci gaba da yi mata kiwo, ta zama wata uwar mata.

A duk lokacin da aka tashi yin interview da Ammar, idan aka tambaye shi meye matakin Nasarar ka a rayuwa? Waye wanda kake kwaikwayo, waye ya baka ƙarfin gwiwa akan harkar kasuwanci? Amsar ɗaya ce yake bayarwa
"Mata tace"

Duk lokacin da ya zauna zeyi misali se ya bada misali da Mufeeda, ya kance "A baya ina raina Mata, ina ganin babu macen da zata iya sauyamin ra'ayi, seda na Auri Mufeeda na gane 'WATA KISSAR SE MATA' Allah yayi musu baiwa da hikima, na sarrafa zukatan maza, idan Allah ya baka mace tagari kamar Mufeeda ka gode Allah, dan Mufeeda 'yar Aljanna ce Insha Allah "

Mufeeda ta haifawa Ammar yara huÉ—u, seda ta zama professor akan harkar sadarwa, mata da yawa sukanzo mata da matsololinsu ta basu shawara, mussman take gabatar da shirye2 a kafafen watsa labarai, sannan ta mallaki personal blog É—inta da take wayar da kan mata akan sha'anin zamantakewa.

Kullum a kamata tambaya ko zata bada misali da Ammar take bayarwa
"Mijina ɗan Aljanna ne Insha Allah, da dukkanin maza zasu sauke haƙƙoƙin dake kansu, su kuma mata suyi biyayya da tabbas mutuwar Aure zata ragu, kuyi koyi da hali irin na Alhaji Ammar"

Ire iren wannan hirarrakin nasu yana matuƙar burge mutane.

Tammat bihamdillah, Masha Allah, Alhamdilillah, Rabbigfir zanbi kullahu, diƙƙahu, wa jillahu, sirrahu, wa alaniyatuhu.

ANAN NA KAWO ƘARSHEN WANNAN GAJEREN LABARIN ME SUNA WATA KISSAR... SAI MATA, INA FATAN AN AMFANA DA DARUSAN DAKE CIKI.
ABUNDA NA RUBUTA NA DAIDAI DAGA ALLAH NE, AKASIN HAKA KUMA DAGA NINE INA FATAN ALLAH YA YAFEMIN.

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Haɗaɗen littafin nan dana fara kawo muku na dakata da kuka daɗe kuna jira me suna AƘIDA TA insha Allah yana nan tafe a watan September, ku kasance tare da Alƙalamina domin jin me littafin ke ɗauke dashi, idan kina daga cikin wanda basu karanta littafin ABDUL JALAL ba kuwa, to ki garzaya ki nemi naki, domin jin cakwakiyar dake cikin sa, Insha Allah bayan AƘIDA TA, Akwai sauran daɗaɗan litattafan da suke daf da isowa gareku domin faɗakarwa, da nishaɗantar da ma'abota fahimtar wannan harshe namu na Hausa.

Karku manta link ɗin voting na zaɓen gasar dana shiga yana nan tafe, ina fatan zakumin kara in lokaci yayi ku zaɓi labari BAƘIN TABO gajeren labarin gasa

Ina buƙatar jin ra'ayoyinku akan wannan littafi dana kammala, domin gyara, sharhi, ko kuma shawara, kai tsaye a tuntuɓeni ta wannan lambar

Ayshercool
07063065680

Ku asancni a cikin sabon littafina da zd e zo muku a 1st september insha Allah mai suna AƘIDA TA
Chapter 64 · 0% Book details