← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 64

Sashe 36

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"to yanzu dai in koma ince mata kace ba zaka ci Abinci a gidan ta ba?"

"zuba inci"

Ta zuba masa Abincin, Amma da ƙyar yaci se kace mace.

Mufeeda tayi shirin tafiya ta haɗa bagco guda na shirgi zata tafi da shi, kome ta gani a gida seta ɗauka tana so sukai ta faɗa da Yaya Fadeela akan seta ajiye kayan data ɗiba amma taƙi.

Mama tace "dan Allah ki ƙyaleta karku yi faɗa, ke se kace kece sakuwar ta ba Amina ba"

"Mama kenan da wani ne a cikin mu bazaki bamu ba, amma da yake Auta ce ai kin bata"

Mufeeda tace
"baki ji ba auta fa kika ce"

Ammar yai Sallama a ƙofar falon yace "Mama zamu tafi"

Mama tace "shigo mana muyi sallama"

Ya shiga ya zauna a gefe Mama tace "Ammar naji daɗin yadda naga Mufeeda Allah ya ƙara muku zaman lafiya, Amma dan Allah idan muka bada abu daga gidan nan, ba mun bayar bane saboda ka gaza, da kai da Mufeeda duk 'ya' yan mune, A cigaba da haƙuri"

Ammar yace "To Mama Insha Allah, nagode sosai"

Fadeela ji take kaman tayi dariya idan ta kalli Mufeeda wai Ammar ne mijin ta, koya take da shi oho?.

Ta ɗakko kayan ta, ta fito guri ta samu ta zauna zata saka takalmi da yake takalmin me igiya ne ga tsini, ganin da Ammar yayi zata ɓata masa lokaci yasa ya durƙusa yana taya ta saka takalmin, ya gama samata sannan ya ɗagota tsaye suka fita.

Anty Murja ce ta fara hango su ta window ta nunawa Amina, sun sha dariya sosai, Amina tace "ai nasani indai da Mufeeda ze zauna duk wannan izzar ze dena ta ne"

*********************

Kwanci tashi asarar rai, Mufeeda ta cika watanni huɗu cif a gidan Aure, a zaman ta da Ammar ta gama karantar sa fiye da yadda yake tunani, ta san fushinsa tasan farincikin sa, Ammar be tsaya iya sana'ar tuƙa a daidaita sahu ba duk wata sana'a da yasan zeyi ya samu kuɗi yana yi, iya yinsa yake ƙoƙarin ganin ya sauke duk wasu buƙatun gidan sa dana gidan iyayen sa.
Dukda a fari baya son Auren yana ganin Matar tasa tayi ƙanƙanta da Aure, Amma a ransa yana jinjina tarbiyya da haƙurin ta, bata da damuwa sam ita dai kullum burin ta ta jadadda masa tana sonshi, laifi ko ita tayi koba ita bace, idan taga ya ɗau zafi se tayi shiru, kuma ta bashi haƙuri dan a zauna lafiya kuma dan kar ransa ya ɓaci, dukda a wasu lokutan shike da laifin ba ita ba amma seta karɓi laifin.

'yan kwanakin nan Ammar ya lura kamar akwai abunda Mufeeda take shiryawa, amma ya kasa gano menene, be takura mata baya son yawan damunta, da tana so ya sani da tuni ta gaya masa.

Aka sanar dashi Jidda babu lafiya, ta kwan biyu a kwance, dan haka yasa Mufeeda ta shirya suje su duba ta, dan tunda yasan Jidda bata ƙaunar Mufeeda beyi gangancin kaita gidan ta ba.

Koda suka je gidan Ammar ya tsaya gyara parking din Napep É—insa ita kuma ta riga shi yin gaba ta shiga gidan.

'Ya'yan Anty Jidda ta tarar a falo, se wata mata a zaune a falon, Jidda tana bedroom din ta .

Mufeeda ta gaida matar dukda matar ma ba wata babba bace, Matar se kallon ta take.

Babu tsammani Jidda ta fito daga É—aki taga Mufeeda, aikuwa take ta wani haÉ—e rai kamar taga kashi.

Mufeeda tace "Anty Jidda ina wuni"

"Lafiya"
"Ya jikin naki?"
"lafiya kalau"

Jidda ta kalli ta falon tace
"Zainab gafa Amaryar ku, matar Ammar"

Ai da sauri Zainab ta kalli Mufeeda tace
"Wannan É—in? To ai wannan da Auren wuri Ammar yayi da ya haifeta"
"to gata nan dai"
Zainab tace "to aini Anty Jidda banga abun so anan ba, wannan ai bata kai macen da Ammar ze kalla ba balle ya aura, amma dai a ƙauye take ko?"

Jidda tace "A'a 'yar cikin birni ce, wataƙila ta gallabi iyayen ne shiyasa suka aurar da ita"

"Amma dai Ammar ya bada maza wallahi, meze samu a jikin wannan' yar kaman mutum mutumi? Kalleta fa"

Da farko Mufeeda tai shiru taƙi kula su, amma ta fara ƙuluwa dan haka ta zumɓura baki tace

"Abunda ake samu a jikin ko wace mace"

Zainab tace "ke karki sake kimin rashin kunya wallahi, yanzun nan se in tattaka ki, aini wallahi Anty Jidda wannan abun kunya ne inyi kishi da ita wallahi"

Sallamar Ammar ce ta katse Zainab dan sam basu san tare suke ba.

Yadda Zainab take Zaune jikin ta babu mayafi da wata pitted shirt haka Ammar ya shigo ya same ta bata rufe jikin ta ba, Mufeeda ta koma gefe ta haÉ—e rai.

Ya samu guri ya zauna a gefen Mufeeda, Ya kalli Jidda yace
"Sannu ya jikin naki?"
"Da sauƙi Alhamdilillah nama warware"
"To Allah ya ƙara lafiya"

Zainab ta kalle shi tace "Ammar ina wuni"
ÆŠaga kai yayi ya kalleta yace
"lafiya kalau, ya me jikin?"

"gata nan taji sauƙi Alhamdilillah, Amma ta sha jiki"

Ammar yace "banga alama ba dan ƙiba ma tayi"

Jidda tace "a hakan ne ban rame ba, ai kuwa na rame sosai"

Zainab tace "Haba Ammar ka kalleta fa da kyau, Allah Anty na ta rame sosai, kalli fa na fita ƙiba yanzu" tai maganar tana wani girgiza jikin ta

Ammar yace "mhmm hakane"

Ya kalli inda Mufeeda take ta haÉ—e rai tai kicin kicin, tsagwaron kishi ne kwance a fuskar ta, ya É—an matso kusa da ita yace
"Ya dai? Meke damunki ne?"
"Bakomai" ta bashi amsa

Ƙara ƙasa yayi da muryar shi yana leƙa fuskarta yace
"gayamin a kunne na meyafaru ne? "
Girgiza kai tayi tana tura baki.
"ko chocolate É—ince?" yai maganar yana murmushi.

Sam Ammar yama manta ba a gida suke ba, ba Zainab ba hatta Jidda kallon Ammar take da mamaki, Ammar ya zauna yana wannan murmushin sedai in a cikin abokan sa yake.

Mufeeda cikin shagwaba tace "ni mutafi gida"

"Anƙi a tafin, se da magariba zamu tafi, ga Zainab nan seta ta yaki hira"

Wata uwar harara tayi masa, ta yunƙura zata tashi ya riƙe ta yana dariya. Ɗaga kai yayi yaga yadda Jidda da Zainab ke hararar su.

Miƙewa yayi yace "bari mu tafi, Allah ya ƙara afuwa, ga wannan ki sai wani abun" ya ajiyewa Jidda kuɗi.

Jidda kasa cewa komai tayi se binsu da kallo, Mufeeda tace
"Anty Jidda, Allah ya ƙara sauƙi"
Tai waje abun ta.

Zainab ce ta biyo su da sauri tace "Ammar dan Allah ina son muyi magana"

Yace "yi sauri ina jinki, Prof ta fara gajiya"
Harar Mufeeda tayi ta tabe baki, kallon su Mufeeda tayi tai tsaki tai gaba abun ta.

Ba tasan me Zainab ta cewa Ammar ba, ya fito daga soron ya kunna Napep din suka tafi.

Suna zuwa gida ta fice daga a daidaita sahun tai tafiyar ta É—aki, bata ko tsaya ta saurare shi ba.

Abincin daren sa a falo ta ajiye masa bata ko bi ta kan sa ba.

Da safe ma be sata a idon sa ba, dan haka ya bita É—akin ta, tana kwance tayi rigingine tana kallon roofing É—akin.

Ya kalleta yace "Azo a taimakeni da ruwan wanka in ba damuwa"

Juyowa tayi ta kalle shi, ba tace komai ba ta fito ta wuce shi, taje kitchen ta dafa masa ruwan ta kai masa banɗakinsa, ta fice seda ta tabbatar ya shiga banɗakin sannan ta koma ɗakin nasa tana gyara masa dan yayi ƙura.

Wayarsa ce take ta ringing, bata damu ba balle ta duba me kiran, Ammar ya fito daga banÉ—akin yana goge ruwan jikin sa yace
"bakyajin wayata tana ringing ne, miƙomin tunda ke bazaki ɗaga ba"

Ganin sunan Zainab akan screen ɗin wayar yasa ta ɗakko wayar hannun ta na rawa ta jefa masa a ƙirjinsa ta fice.

Binta yayi da kallo yana jinjina wannan kishi na Mufeeda, ɗaki ta tafi taje taita kuka saboda ɓacin rai, gani tayi kuka baze fishesheta ba dan haka ta fito falo tayi aikace aikacen ta.

Amma ta tarar Ammar yana waya a falon, ta daure ta tafi kitchen, ta kuma fitowa taga still waya yake, kuma alamu sun nuna da mace yake wayar, har tayi gaba kawai ta juyo a zuciye ta fizge wayar daga hannun sa ta buga ta da ƙasa.

Ɗagowa yayi a matuƙar zuciye cike da Masifa, ya kalle ta se huci take Hawaye na bin fuskarta.

Share please

Domin sharhi, gyara ko shawara
Ayshercool
07063065680.[08/07, 10:48 PM] Ayshercool: ✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP

 

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

                  

                        Page 19

Binta da ido Ammar yayi, a fusace yace

"baki da hankali ne? Meye hakan kikayi? Ɗazu kin jefomin waya na ƙyale ki yanzu kuma kin fasamin waya kin kyauta kenan? Wace irin Yarinya ce ke haka? Wane irin hali ne wannan? "

Ta É—ago manyan idanun ta ta kae shi tace
"Nice bani da hankali ko? Nagode bani da hankali na Yadda"
ta juya da sauri tabar masa falon, binta yayi da kallo yana mamaki, ta masa laifi kuma tayi fushi

(Nikam nace ashe babu daÉ—i, mutum yayi lefi ya maze ya É—orawa abokin zamansa laifin da gangan"
Chapter 36 · 0% Book details