← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 64

Sashe 15

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mijin Anty murja yace "ƙyale Antyn nan taki ki cigaba da son abunki, Allah ya baku zaman lafiya, aishi namiji indai yana son mace duk wata izza baze mata ba"

Haka ya ci gaba da zigata, se wajen sallar isha'i sannan Mijin Anty Murja ya maida Mufeeda gida a motar sa da rakiyar É—ansa.

Ammar tun sallar magariba yake unguwar su Mufeeda akace bata nan taje gidan Yayar ta, daya ke ba da napep É—insa yazo ba ya samu guri yana jiran ta, amma ga mamakin sa ya hango Mufeeda ta fito daga motar wani, seda ta É—an tsaya suka yi sallama da me motar ta É—aga masa hannu sannan ta shige gida.

Ammar ji yayi duniyar tayi masa zafi yaji zuciyar sa tamkar ta fasa ƙirjin sa wani abu ya tokare masa rai.

Har ya yanke shwarar yayi tafiyar sa amma ya fasa ya kira ta a waya, seda yayi mata missed calls uku wayar tana cikin jakar ta a É—akin ta bata sani ba, kaman wadda aka mintsila ta É—akko jakar ta taga wayar ta na ringing ta É—aga da sauri tace
"Am Sorry My Ammar wayar tana cikin jakata ne"

"Ina kofar gidan ku" shine abunda ya furta da ƙyar.

Da murna ta ajiye wayar ta kalli kanta a mudubi, tsaf da ita kwalliyar fuskarta tana nan, janbaki ta ƙara ta sake gyara ɗaurin kanta ta fesa turare ta leƙa ɗakin Mama tace

"Mama Yaya Ammar ne yazo bari inje"

Mama tace "au be tafi ba dama, tun magariba yazo ai na É—auka ya tafi"

Mufeeda tace "Allah sarki Yaya Ammar É—ina, Allah yasa saurk be cije shi ba"

Ƙwas ƙwas da takalmin ta me tsini tai waje da sauri.

Tana zuwa ta leƙa bata ganshi ba, ta kira shi a waya, se gashi ya ɓullo ta lungun dake kallon gidan su Mufeeda ta juya ta koma sitting room inda idan yazo take saukar sa.

Yana shigowa ta fara magana cikin shagwaɓa Yaya Ammar ashe tun ɗazu kazo baka kirani a waya ba, yau Allah yayi zan ganka ba tare da nayi magiya ba, kallon sa tayi taga fuskarsa a ɗaure babu annuri hakan yasa tasha jinin jikin ta.

Ammar yayi niyyar ya nuna mata ainihin waye Ammar amma maimakon haka seya kasa yi mata faɗa yadda ya ƙudurta a ransa, gani yayi ma yau tayi wani irin kyau sosai ko dan yau ba kukan take ba, amma daya tuna a motar wani yaga an sauke ta se ya ɗaure fuska sosai cikin kakkausar murya yace
"Daga ina kike?"
"É—inki na kai" ta bashi amsa cike da fargaba

"É—inkin ne se yanzu zaki dawo? Daga motar wa kika fito?"

Ya faɗa yana ɗan ɗaga murya, gaba ɗaya mamaki ya lulluɓe Mufeeda tace
"Wace motar kuma?"

"Tambaya ta ma kike yi? Waye ya sauke ki a mota? Sannan ina kika je? Bari kiji in gaya miki bazan É—auki rainin hankali ba, tun wuri idan kin san abun da zaki dinga yi kenan ki koma ki janye batun auren mu, bana son rawar kai, saboda kin rainamin hankali jiya har sha biyun dare kina chatting na tambaye ki kince wai dame sonki kike chatting, yau kuma dan ki tabbatar min shine aka sauke ki a mota ko? Tun farko inkin san me motar kike so meye na cewa kina sona har in kawo kuÉ—in aure, me yasa baki tsaya a me motar ba kika ce kina son talaka kamata, idan har kinsan kina da hange karki soma yadda da aure na" ya tako har gaban ta ya kusa haÉ—e ta da bango yace
ki gayamin waye ya sauke ki a mota"

Gaba ɗaya jikin ta ya mutu, wani irin ƙamshin turare yake me daɗin gaske, yayin da shima dakewa yayi dan ƙasan zuciyar sa na yaba kyawun da tayi.
Idonsa ta tsaya tana kallo taji zafin maganganun sa, amma tana iya ganin tsagwaron kishin ta a cikin idon sa, a ranta tace Ammar kenan a fili kuwa tuni hawaye ya wanke mata fuska.

"ina tambayarki kina min kuka, kin san abunda bana so kenan, ki gayamin abunda na tambaye ki"

"tabbas da ina da hange kuma so zemin adalci dabe yi gigin kaini ga afkawa son wanda bana gaban sa ba, idan har ina hangen me kuɗi ne to bazan kalle ka ba, amma zuciya ta ta makance kai kaɗai nake gani, ni kaina ina ganin kaman na fiye zaƙewa, jiya da nake chatting daka tsaya munyi waya zanji daɗi a raina ɓacin ran abunda kamin da tunanin wane irin mutum Allah ya haɗa ni dashi zamuyi zaman aure ya hanani bacci na ɓige da chatting muna shirye2 biki da ƙawaye na, yanzu kuma ɗinki na kai unguwar su Anty murja ina tsoron hanya shiyasa mijin ta ya dawo dani gida, mahaifina mutum ne me matuƙar tsauri akan tarbiyya baze taɓa bari na inje unguwa inyi dare a kawoni a mota ba, kuma mijin yaya Aminar ma akwai ɗanta da yayi mana rakiya, Amma Allah ya baka haƙuri Allah ya huci zuciyar ka insha Allah zan kiyaye faruwar hakan a gaba"

Ta juya zata tafi ya kira sunan ta
"Mufeeda" banza tayi masa ta ƙara sauri hawaye na bin idon ta tana jinsa taƙi ko waiwayowa tayi gaba abunta.

Gaba É—aya se jikin Ammar yayi sanyi tare da tunanin meyasa yayi mata faÉ—a haka gashi ya sata kuka
(🙄🙄🙄)

Kuma inba comment zan ajiye typing É—in littafin nan
Domin sharhi, gyara ko shawara
Ayshercool
07063065680

[23/06, 10:48 PM] Ayshercool: ✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

                      Page 8

Ammar bashi da zaɓin daya wuce ya tafi, a zuciyar sa yana jin kaman be kyauta ba abunda yayiwa Mufeeda.

Ita kam data koma gida seda ta sha kuka tayi ya ishe ta sannan ta hau Addu'a "ya Allah kai ka jarabceni da son wannan bawan naka Allah ka kawomin mafita"

Seda ta idar da addu'ar ta ɗakko wayar ta, ta buɗe hoton Ammar ta ƙura masa ido sannan tace

"Yaya Ammar kenan faɗan kawai ka iya amma sam bazaka yi wahalar sarrafawa ba, kace baka iya soyayya ba amma ina ganin kishina ƙarara a idonka, ba a kishi idan babu soyayya, se ƙwaila ta baka mamaki"

Ammar yaji ya fara damuwa da abunda ya aikata tsaki yayi yace "toni ina ruwana ma meye zan damu kaina akan wannan ƙaramar yarinyar"

Shirye2 se nisa suke lokaci na ƙaratowa, ba tare da Ammar da Mufeeda sun samu wata kyakywar fahimtar juna ba.

Mufeeda ta shareshi ta dena kulashi, tana kallon sa online amma ba zata kula shi ba saƙonnin ma ta dena tura masa.

Dukda can ƙasar zuciyar sa seya dinga jin zafin shareshin nan da tayi amma shima ya ƙyaleta.

Mufeeda ta maida hankali akan Neco exams ɗin ta, duk ta ƙara ramewa ga pressure ɗin exams ga na shirye2 biki dukda tana ta shan gyara ta ƙara kyau hakan be hana ramar da tayi fitowa ba.

Tana kwance tana chatting tana kallon Ammar online taƙi kulashi ya turo mata saƙo

  "ki gayawa su Baba ranar Asabar insha Allah za'a kawo kayan lefe"

Zumbur ta miƙe zaune tana ƙara juya saƙon, maimakon taje ta gayawa Mama seda ta kira Yaya Amina ta fara gaya mata suka yi ta murna tare sannan taje ta sanar da Mama, Mama tace "to Allah ya kaimu"

Sam bata nuna ma taga saƙon ba balle tayi wa Ammar replying.

Mama tayi shirye2 tarbar masu kawo lefen aka yi sa'a mazane suka kawo, Akwatuna uku da kida ƙaramin buhun shinkafa da bagcco na takalma, aka basu tukuici suka ce ba zasu karɓa ba.

Mama tayi mamakin kayan da'aka zubowa Auta, dukda ko kaɗan basu kama ƙafar wanda aka kawowa 'yan uwan ta ba, amma ba laifi yayi ƙoƙari a matsayin sa name ƙaramin ƙarfi yayi ƙoƙari dan kayan ta ba masu arha bane.

Ammar shikaɗaine namiji gidan su, yayyen sa uku mata se biyu ƙannensa, suna ta tsokanar sa "Bana Allah yayi, Allah ze yaye masa gwauran taka, Allah yayi an samu wadda tayi nasarar shiga ran 'yan mazan umma" jinsu kawi yake yi, dan shi be ɗau wannan auren nasa wanu auren kirki ba kawai dai sunan zeyi aure ne.

Labari ya ishe  budurwar sa a da wato zainab wai Ammar zeyi Aure, ta shiga tashin hankali da damuwa dan ba ƙaramin so take masa ba dukda tana masifar tsoron sa saboda zafin kansa da izzarsa, amma tana matuƙar son Ammar, kasa jurewa tayi ta ɗau waya ta kira shi.

Akayi sa'a yana gida dan ya gama cin Abincin rana kenan ta kira shi bayan sun gama gaisawa tace
"Ammar dagaske aure zakayi?"

Ammar sam be san wani abu rarrashin mace ba se kace ba cikin mata ya taso ba dan haka yace mata "Eh aure zanyi, nima auren ne yazomin ba shiri Allah ya kawo auren"

"Amma Ammar duk son da nake maka, na sakankance sekamin haka"

"ke nima fa auren nan ba wai da son raina zanyi shi ba, kawai dai Allah ya nufi zanyi ne, ba yadda zanyi"

"Ammar bakamin adalci ba, ina nan na sakankance kawai se inji labarin zakayi aure, kuma ma wai ƙara mar yarinya, bayan ka gama cemin kai ba zaka auri yadinya ƙarama ba ashe dama duk yaudara ta kake yi?"

Ajiye wayar Ammar yayi dan bashi da lokacin cigaba da sauraren ta tana ɓata masa rai, ya gaya mata gaskiya amma tana ƙoƙarin kaishi bango.
Chapter 15 · 0% Book details