Sashe 61
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mufeeda tace "Eh munyi waya da ita, wai a ribar data samu ne nima ta sanmin, seka bani dubu goma ka siyomin ruwan leda, se in rubuta maka kayan lemon da nake buƙata, in sanar da mutane na fara saida kayan sanyi"
Ammar yayi murmushi yace "Shikenan, Allah yasa Albarka, Gobe in Allah ya kaimu da sassafe zan shiga kasuwa ana sauke kaya daga trailer, inje abunda na samu in ƙara da kuɗin hannu na se in siyo ko Omo ne da Sabulu a hannun 'yan sari in fito bakin kasuwa in siyar"
Idon Mufeeda fal ƙwalla tace "Yaya Ammar zaka iya wannan aikin me wahala kuwa?"
Murmushi yayi yace
"Nifa namiji ne, da aikin soja zan tafi dan dai Baba baya so ne, karki damu zan iya kije ɗakin tsakar gida na siyo miki nama kici, ki ƙara haƙuri Mufeeda Insha Allah komai ze wuce"
"Yaya Ammar seda ka siyo Naman nan"
"Eh mana nasan kina so, kin daÉ—e baki ciba"
Allah sarki Ammar, harda fruit ya haɗa ya siyo mata, duk yadda tayi dashi yaci ƙi yayi, Amma yaji daɗin ganin murmushi a fuskar ta, sanadin wannan Nama data ci.
Tun Ammar yana sintiri akan Napep ɗinsa har ya haƙura,
Kullum da sassafe yake tafiya kasuwar singa, haka ze zage yaita sauke manyan buhunhunan kayan Abinci, abun da ya samu haka ze haɗa da kuɗin hannun sa ya sai ƙanan abubuwa kamar Omo da su Sabulu a hannun 'yan sari ya fito bakin kasuwa ya siyar.
Ammar duk sana' ar daya san zeyi ya samu kuÉ—i babu ruwan sa yin abarsa yake, wataran ya samu riba wataran ya faÉ—i amma hakan baya hana gobe ma ya fita.
Kamar wasa Mufeeda ta fara Saida kayan sanyin nan, dama kafin su fara seda taita gayawa Allah, abu kamar wasa wuni ake zuwa siyan ruwan sanyi da lemo, randa babu wuta ta bayar a siyo mata mai ta kunna inji, Sosai take ciniki.
Ranar da taga ta samu riba da yawa bayan Ammar ya dawo ya huta tace
"Yaya Ammar ya kamata ka siyo mana banki, kullum mudinga ajiye É—ari biyu, duk sati dubu É—aya, zasu temaka mana wataran"
Ammar yace "hakane kin kawo shawara Jaririya ta, Insha Allah zan siyo mana mudinga ajiyewa"
Duk wannan hali da suka shiga Babu wanda suka gayawa, tare suke ta faÉ—i tashin su, randa suka samu suci me kyau randa babu suci abunda ya samu.
Allah yasa musu Nasibi akan sana'ar, Mufeeda tana daga gida amma tana cinikin ta sosai.
Kwana biyu Ammar beje gida ba saboda bashi da kuÉ—in daze musu alheri idan yaje, ranar wata Asabar yasa Mufeeda ta shirya suje, su fara zuwa gidan su Ammar idan yaso da Azahar, se suje gidan su Mufeeda.
Haka kuwa aka yi, suna Zuwa gidan su Ammar suka tarar da Abba a tsakar gida, suka gaisa.
Abba yaceÂ
"Aikuwa Halima tana Islamiyyar safe, ita kuma taje wata barka nan ƙasa amma yanzu zata dawo, Ina A daidaita sahun naka ne?"
Ammar yace
"tana gurin gyara, Amma zan karɓo Insha Allah "
Abba yace "To Allah ya dafa, 'yata fatan kuna lafiya?"
"Lafiya ƙalau Abba"
"Masha Allah, tunda Allah yasa yau kinzo kafin ku tafi kya je kiga dabbobin ki"
Mufeeda tace "To Abba nagode sosai Allah ya ƙara girma"
Abba yace "Bakomai Mufeeda, Allah yayi muku Albarka, ni zan fita nasan ba daɗewa zata yi ba, zata dawo"
Ammar yace "Shikenan Abba adawo lafiya"
"Allah yasa Ammar"Â Abba ya fice
Mufeeda da Ammar suka zauna suna Hirar su, É—akinsa na gwauranta dake cikin gidan ya buÉ—e musu suka shiga, Mufeeda tace
"Yaya Ammar wannan ƙatuwar katifar fa kamar ta Amarya?, bari in kwanta akai"
Ammar yace "Yi a hankali karki lotsamin katifa da wannan ƙaton cikin naki"
"Sena lotsa É—in, ai da bani da nauyi, kaika mayar dani me nauyin"
Dariya yake mata yazo ya kwanta a kusa da ita yace
"Allah sarki Jaririya ta, ta kusa zama Mum koya zata yi raino"
"Ai baka tuna ni Jaririyar bace, ka haÉ—ani da aiki"
Hirar su suka dinga yi cike da ƙaunar juna, wani lokacin Ammar yana kallon yadda cikin yake motsawa mussman idan tana bacci, ya ɗora hannun sa akan cikin nata, yana jin yadda yake ɗan motsawa, Da haka bacci ya ɗauke su.
Koda Umma ta dawo tayi mamakin ganin gidan a buɗe ba kowa, tana shigowa ta tarar da ɗakin Ammar a buɗe ga takalma a ƙofar ɗakin, tai magana kusan sau uku taji shiru, ta ɗaga labule, bacci suke sosai Umma ta sauke labulen tana ɗan murmushi.
Aikace2 ta shiga yi, Ta ɗora girki Amma duk su Ammar basu san tana yi ba, Mufeeda bata samun bacci sosai, tana raba dare gurin Ibada da kaiwa Allah kukan su, sannan idan tayi sallar Asuba bata komawa bacci saboda Ammar da wuri yake fita, wani lokacin shida da rabi ya bar gida, da rana ta ɗan ɗaga kuma an dinga sintirin siyen ruwa da lemo kenan, dan haka basa samun ishashen bacci, mussman Ammar da yake Aikin ƙarfi.
Jiddace tayi sallama idon ta Jawur kamar wadda aka koro, Umma ta kalleta tace "Jidda lafiya kuwa?"
Fashewa da kuka tayi, tace
"Umma na shiga uku, Baban su Haidar wai Zainab ze Aura ashe? ÆŠazu na samu labari, na shiga uku Umma, ta gama sanin Sirri na ta shisshige min, na yadda da ita Amma taci Amana ta, Nusaiba na taje har gida ta mata rashin Mutunci baki ga dukan da da baban ta yayi mata ba, na shiga Uku Umma.
Wata ta biyo ni private tace "Gaskiya baiwar Allah kin fiye tsananta masifa"
🤣 🤣 🤣 🤣 🤣 Sorry labarin ne yazo a haka. Ina godiya da Comments da shawara.
Ina Masoya na, lokaci yayi da zaku min kara ku nunamin ƙauna, kamar yadda kuka sani na shiga Gasar Matasan marubuta 2021, A gobe in Allah ya kaimu Asabar, 31 ga watan July rukuni na 7,wanda shine rukunin da nake ciki zamu saki litattafan Gasarmu, masu ɗauke da kalmomi 2500.
Na shiga gasa da littafi na me suna BAƘIN TABO, ku kasance dani domin ji ya taka ya a cikin wannan gajeren labari, ina fatan idan lokacin zaɓen labarin Gasar Yayi, zaku zaɓi labarina na BAƘIN TABO,
https://chat.whatsapp.com/J3lB9LvDu174M3yeR56BoK Mata kawai banda maza
Ina Alfahari daku Masoya a duk inda kuke.
Domin Sharhi Gyara, ko Shawara
Ayshercool
07063065680
✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨
( *Sai Mata* )
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞
( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.Aâœï¸
*_A SHORT LOVE STORY_*
*Story and written by*
'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''
Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba
Watpad @ Ayshercool7724
What's app 07063065680
Gmail [email protected]
Please follow me on Wattpad, vote and Comment
ELEGANT ONLINE WRITER'S
NOT EDITED
             Page 30
Hargowar Jidda ce tasa Ammar ya farka, yai shiru yana sauraron abunda Jidda take faÉ—a, rungume Mufeeda ya sake yi a jikin sa yana tunani, a ransa yace
"Allah nagode maka da ba Zainab na Aura ba, da ita na aura nasan tabbas ba zata iya haƙuri da halin da nake ciki ba"
ya cigaba da shafa kan Mufeeda yana kallon ƙanƙantar ta, Amma akwai haƙuri da hangen nesa, tana yiwa Ammar so na gaskiya da zuciya ɗaya.
A hankali Mufeeda ta fara motsawa itama sakamakon kukan Anty Jidda, ta kalli Ammar tace
"Yaya Ammar su Umma sun dawo"
Ammar yace "tun É—azu suka dawo ai"
"amma me yasa baka tasheni ba? Yanzu an gan mu tare muna bacci, yanzu ya zamuyi mu fita?"
Murmushi yayi yaceÂ
"Ya zakiyi ki fita dai, ni ficewa ta zan yi"
Ta kalli agogon dake É—akin ta É—an zare ido tace
"Yaya Ammar lokaci ya ja fa, kalli Azahar tayi"
Ammar yace "Eh tashi muje muyi salla"
"Yaya Ammar kunyar fita nake ji, Amma kamar muryar Anty Jidda nake ji fa"
"Eh ita ce" ya bata Amsa
Mufeeda tace "Kamar kuka fa naji ta nayi"
Ammar bece komai ba ya miƙe, ya basar ya fito tsakar gida, ya gaida Mama yai alwala ya fice masallaci.
Da ƙyar Mufeeda ta fito cike da jin nauyi, Jidda na ganin ta, wani baƙin ciki ya tokare mata zuciya.
Mufeeda ta durƙusa tace "Umma ina wuni"
"Lafiya ƙalau Mufeeda, kin tashi ashe?"
Cike da jin Kunya Mufeeda tace"Eh Umma"
Umma ta fuskanci Mufeeda nauyin ta take ji sosai dan haka tace "to yi salla kizo kici Abinci"
Mufeeda tace "to Umma, Anty Jidda ina wuni"
Banza Jidda tayi da ita, Mufeeda ta tashi ta tafi yin Alwala.
Umma ta kalli Jidda tace "Ke kina jin matar ɗan uwan ki tana gaishe ki amma baki amsa ba"
"Umma ba dole in mata banza ba, yarinyar nan ta cuceni ba dan Ammar ya Santa ba da tuni Zainab ya aura, Amma yanzu kalli ya Aure ta, ni kuma zata Auremin miji na shiga uku Umma"
"Haba Jidda, da bakin ki kike cewa kin shiga uku? Ki fawallawa Allah lamarin ki mana, sannan kija girman ki, karki shiga sabgar ta balle inya aurota ta raina ki"
"Haba Umma ya kike wannan maganar, yarinyar Zainab nan ba sirrina da bata sani ba, wataran a gida na take wuni, kawai seta ci Amana ta"
Duk haƙurin Umma seda ta ƙule tace
"to Ubanwa yasa kike gaya mata sirrin ki? ashe har yanzu baki da hankali, kina girma kina shiga dawa, waya gaya miki ana haka? Ai koni da nake mahaifiyar ki ba komai yakamata in sani ba game da zaman Auren ki, Amma kinje kina gayawa wata sirrin Auren ki, watanma bazawara, yanzu kinzo kinamin kuka, ai kinyi kuskuren da baze taɓa gyaruwa ba, kuma karki ƙara zargin Mufeeda ba ita tayi miki ba, dama can Allah ya rubuta Ammar ita ze Aura"
Mufeeda ta fito daga banɗaki tazo ta tada Salla, ana haka Sega Yaya Maryam tazo, tana zuwa ta tarar da Mufeeda ta idar da salla suka shiga Hirar su, tamkar bata san halin da Jidda take ciki ba, suka cigaba da hira hadda Umma suka ƙyaleta.