← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 64

Sashe 48

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mufeeda ta daÉ—e tana wannan baccin sannan ta tashi, koda ta tashi seta ji sassauci a zuciyar ta, Yaya Amina ta kai mata ruwan wanka tayi wanka ta kawo mata Abinci Amma tace ba zata ciba
Mijin Yaya Amina yace " Haba Autar Baba ya zaki ce ba zaki ci Abinci ba? Kinzo a mawuyacin Yanayi gaba É—aya mun tsorata da halin da muka ganki a ciki, dan Allah kici Abinci kinji"
Girgiza kai tayi tana goge Hawaye tace "Na ƙoshi Yaya Auwal"
Auwal yace "Amina ko zaki tambaye ta idan wani abun take so a siyo mata"
Saurin girgiza kai Mufeeda tayi tace "Nifa na ƙoshi"
Yaya Amina tace  "wai ke meye hakane, ya za'ayi ta fama dake kici Abinci kamar wata Jaririya"
Auwal yace "A'a My love mu bita a hankali tana cikin damuwa ne, be kamata kiyi mata faÉ—a a wannan yanayin ba"
Da ƙyar suka takura Mufeeda ta sha tea da slides na dankali ta ture tace bata ci.
Seda Mijin Yaya Amina ya tabattar babu wata matsala Mufeeda ta samu nutsuwa Sannan ya koma É—akin sa dan ya basu guri, dan inda Amana Mufeeda ta hannun daman sa ce baze manta Yadda ta tayashi campaign a gurin neman Auren Amina ba.

Bayan tafiyar sa Amina ta kalli Mufeeda tace "Auta bana son wannan halin naki na zurfin ciki da ɓoye ɓoye, kiyi min bayani me yake faruwa?"
Shiru Mufeeda tayi ta sunkuyar da kai wasu hawayen na bin idon ta amma taƙi magana.
Ba yadda Amina ba tayi ba akan Mufeeda tai mata bayani amma taƙi, Yaya Amina tace
" shikenan tunda ba zaki gayamin ba bari in kira Mama in mata bayani, wataƙila ita zaki iya gaya mata"
Da sauri Mufeeda ta riƙe hannun Yaya Amina tace
"Yi haƙuri dan Allah zan gaya miki, Amma kiyi min Alƙawarin ba zaki gayawa Su Mama ba ko Anty Fadeela, kinga ke kaɗai ce abokiyar Sirri na wadda zata tausaya min, idan kuma Mama taji zata ji babu daɗi"

"Shikenan naji babu wanda zan gayawa, gayamin meyafaru ? Kuma bance ki ragemin komai ba indai kin yadda ni yayar kice kuma abokiyar shawarar ki"

Nan Mufeeda ta zauna ta warwarewa Yaya Amina yadda suka yi da Ammar da yadda take fama da Wasu daga cikin 'yan uwan sa, É—an shiru Yaya Amina tayi sannan tace
"Amma gaskiya Mijin ki bashi da kirki, se kace bashi da' yan uwa mata, ko dan keba ƙanwarsa bace ba uwa ɗaya uba ɗaya kuke ba shine ze dinga miki rashin mutunci? ko kuma yana ganin ya Aure ki a ɓagas seya dinga wulaƙanta ki, a da na goyi bayan ki Aure shi saboda naga yadda kike sonsa, Amma ya bani kunya wallahi zega tsiya tunda bashi da mutunci "

ÆŠan tura baki Mufeeda tayi tace
" Ni gaskiya ki dena zagarmin mijina "
BuÉ—e baki Yaya Amina tayi dan mamaki sannan tace
" Dan kin samu baki hallaka ba, kin manta yadda kika zomin rai a hannun Allah shine kike wani in dena zagin sa, an zage shi ɗin bashi da mutunci, kema kuma sokuwa duk surutun naki da rashin kunya akan 'yan gari ya ƙare ki zauna yana neman ya kashe ki da ƙuruciyar ki"
Yaya Amina ta harzuƙa sosai, tana da haƙuri dan tafi duk su Mufeeda haƙuri, Ba ƙaramin abu ne yake ɓata mata rai ba.

"Yaya Amina nice fa a ƙarƙashin sa, Idan har nace zanyi masa rashin kirki ban kyauta ba, duk abunda mutum yayi maka na laifi akwai buƙatar kayi masa Adalci, Yaya Ammar yana kula dani fiye da tunanin ki, in bani da lafiya ze kaini Asibiti na kuɗi in shine yaje na gwamnati, ya yadda ya hana kansa ko yaci Abinci mara daɗi ni inci abunda nake so, Saboda shi na dena ɗora kayan ƙyale ƙyalen mata akan status ɗina, ko in ajiye su a waya ta, da ya gani, komai tsadar su indai ze iya seya nema ya siyamin indai ze iya, ko a hira na faɗi wani abu idan yana da kuɗi se ya saimin abun nan, ba abunda na nema na rasa a gidan sa se Soyayyar sa da kuma yawan fushi da rashin bincike idan akace masa nayi laifi"
Ta ƙarasa maganar tana kuka hadda sheshsheƙa, Yaya Amina ba ƙaramin tausayawa Mufeeda tayi ba, gaskiya Ammar halin sa seshi, tayi mamaki da suke zaune da Mufeeda ma, Saboda babban abunda yake haɗa Mama da Mufeeda ko a gida yawan Faɗan ta da rashin ɗaukar raini, Amma yanzu Allah ya haɗa ta da murɗaɗɗen Namiji wanda tilas yasa ta ajiye nata rawar kan.

Yaya Amina ta numfasa sannan tace "Shikenan ya isa haka, Amma Gaskiya Mufeeda kinyi wauta, seda na gayamiki, ki gaya masa abunda yake faruwa amma kika ƙi"
"Yaya Amina ba ƙi nayi ba a lokacin ma sama sama yake dani, maƙota na sun kawo masa ƙara ta"
Yaya Amina tace "Maƙota kuma? Me kuma ya haɗaki da maƙota zasu kai masa ƙarar ki?"
Nan ma ta zauna ta warwarewa Yaya Amina komai, Yaya Amina ta jinjina kai lallai ƙanwar ta tana ganin ƙalubale a cikin rayuwar Auren ta, Yaya Amina ta riƙe hannun Mufeeda tace
"ki kwantar da hankalin ki kiyi haƙuri Insha Allah komai ze wuce ze daidaita, amma sena koyawa wannan mijin naki hankali, waima uban waye ya gaya masa ya ganki kina zance da wani?"
"Wallahi ban saniba Yaya Amina, Amma akwai wani mutumi da yake bina a unguwar wai yana sona, hana da kuÉ—i sosai, Amma wallahi Yaya Amina rashin mutunci nayi masa nace ni matar Aure ce, ban san waye ya gaya masa hakan ba"
"to ke uban me ya hana ki gaya masa ga abunda mutumin yake miki?"
"Hmm Yaya Amina kenan, me É—aki ai shi yasan inda yake masa yoyo, Nasan halin mijina tsaf kallo É—aya yakewa abu yai masa hukunci ba tare da dogon bincike ba, koda na gaya masa se yaga laifina nima"
"Shikenan ya isa, ki dena kukan haka nan" A hankali Yaya Amina ta dinga janta da hira domin ta rage damuwar da take ciki.

*********************
Gaba É—aya idan Ammar ya tuna abunda yayiwa Jaririyar matarsa da yadda take kuka se yaga be kyauta ba, ya tuna yadda ya baro ta a yanayi mara daÉ—i dan haka ya yanke shawarar komawa gida don yaga halin da take ciki.
Koda ya koma gida be san ta ina ya kamata ya fara ba, zuwa ɗakin ta zeyi ya duba ta kokuma yaya? Tuno irin maganganun da yaji ana yi mata a waya yayi nan da nan yaji ransa ya ƙara ɓaci ya nemi guri ya zauna a falo, shiru shiru be ji motsin ta ba, ya fara mamakin anya kuwa taji dawowar sa, ko yana fushi da ita idan ya dawo seta fito ko baze kulat ba za tayi masa sannu da zuwa, a hankali idon sa ya kai kan inda hular ta ta faɗi lokacin da ta biyo shi tana bashi haƙuri, se yanzu ya lura da yadda ya fita ya bar gidan haka ya dawo ya tarar da shi.
Da sauri ya miƙe ya fara leƙe leƙe amma komai yana nan yadda yake, ya nufi ɗakin ta da sauri ya buɗe ƙofar amma bata ciki ga ƙofar wardrobe ɗinta a buɗe, ya buɗe banɗaki nan ma bata ciki, a gaggauce ya dinga duba lungu da saƙo na gidan nan amma babu Mufeeda babu alamar ta.

Hannu yasa a Aljihun sa ya É—akko wayarsa ya fara kiran layin ta, Mufeeda na kwance a É—akin da Yaya Amina ta sauke ta wayar ta ta fara ringing, kallon inda wayar take tayi taga sunan My lovely Bae akan screen É—in wayar.
Ƙurawa wayar ido tayi tana ci gaba da ringing, idan ta katse ya sake kira ya kira ya kai sau takwas, Amma Mufeeda taƙi ɗagawa kuma ta kasa kashewa, Yaya Amina ce ta jiyo ringing ɗin wayar ta shigo ɗakin tace
"Auta ba wayar kice ke ringing ba?"
"Waya tace Yaya Amina, Yaya Ammar ne yake kira na"
Yaya Amina tace "maza yi rejecting É—in kiran nan ki kashe wayar"
Girgizawa Yaya Amina kai tayi tace "bazan iya rejecting É—in kiran sa ba" Wata uwar Harara Yaya Amina tayi mata, ta fizage wayar tayi rejecting ta kashe wayar gaba É—aya sannan ta cillawa Mufeeda wayar.

Hankalin Ammar ya tashi da yaji ya kira taƙi ɗagawa ƙarshema ta kashe wayar, nan da nan gumi ya fara tsatstsafo masa, yanzu ina Yarinyar nan ta shiga? Me zance wa Iyayen ta? Gaba ɗaya kansa ya kulle ya rasa abunyi, idan Yace zeje gida ya gayawa iyayen sa halin da ake ciki to tabbas ze fuskanci ɓacin rai musamman a gurin mahaifinsa, dama Yaya Jidda ba'a maganar ta dan babbar banza ce, ita kuwa Yayarsa Amina da suke cewa Ummi 'yar ba ruwana ce, har gara Maryam wadda yake bi tafi su fahimta, dan haka ya yanke shawarar yaje gidan Yaya Maryam yaji ya zasuyi dan gaba ɗaya ya rasa abunyi.
A sukwane ya rufe gidan ya É—au babur É—in sa ya tafi gidan Yaya Maryam, tayi mamakin ganin sa a wannan lokacin amma yanayin sa ya nuna mata Akwai matsala akwai abunda yake damun sa, Yaya Maryam ta kalleshi tace
"lafiya kuwa Ammar?, naganka kamar ba a nutse ba, meke faruwa ne?"
"Akwai matsala ne fa"
"Matsala kamar yaya? Allah yasa ba wani abun kayi wa Mufeeda ba"
Ammar ya É—an sosa kai, cikin jin nauyi yace "A kanta ne"
"ina jinka"
Nan Ammar ya kwashe komai ya sanar mata, shiru tayi tana kallon Ammar seda ya gama tsaf ta jinjina kai tana ci gaba da kallon sa, can tace
"Amma Ammar ban taɓa tunanin rashin hankalin ka ya kai haka ba wallahi"
HaÉ—e rai yayi yace "ya za'ayi dan nazo na gaya miki matsala ta ki kirani da mara hankali"
Babban abunda yasa Ammar yake shiri da Maryam shine yadda take girmama shi, daman akwaishi da son girma, Be taɓa zaton zata kira shi da mara hankali ba.

A fusace tace "Na faÉ—a mara hankali, dama da naje gidan ka wancan satin yarinyar nan tana cikin damuwa nayi nayi ta gayamin idan akwai matsala amma tace babu ashe cutar ta kake"
Chapter 48 · 0% Book details