← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 64

Sashe 14

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasancewar Unguwar su Mufeeda ma cike take da masu ƙaramin ƙarfi nan da nan unguwar ta ɗauka akaita surutai wai wannan 'yar yarinyar mara kunya za' ayiwa Aure, kuma abun kunya duk bokon baban su ace ɗan a daidaita sahu zata aura, hada wanda suka tari mahaifinta wai mezesa ya aurar da ƙanƙanuwar yarinya kaman Mufeeda, shi kuma ya kan basu amsa da 

"wannan abune da ya shafi iyalina, kuma nan duniya duk wanda ze ƙauna cesu a bayana yake, dan haka banga laifin hakan ba"
Hatta malaman su Mufeeda sunyi mamakin jin aurar da Mufeeda za'ayi kasancewar mahaifinta ɗan boko wanda yasan mahimmancin Ilimi, shima seda suka gayyace shi makarantar amma ya ƙara tabbatar musu da baze canza ra'ayin sa ba, ba wanda ya gayawa Mufeeda da kanta ta nuna aure take so.

Haka mufeeda ta cigaba da fama da Ammar, mutum ne da baya son raini shi gani yake idan har ya sakewa Mufeeda raini ne ze shiga tsakanin su dan sam ba sa'ar auren sa bace, kaman yadda ya barwa zuciyar sa wannan ba aure zeyi ba kawai dai an hada shi da aiki ne.

Ita kuma Mufeeda ta sawa ranta cewar idan harta shiga gidan Ammar zata tabbatar masa da wata kissar se mata, seta sauke masa wannan zafin kan nasa, zata nuna masa itafa mace mace ce, komai ƙanƙantar ta kuwa.

Idan ta kwana biyu bata ji muryar sa ba, duk seta damu seta kira shi kota tura masa saƙo, dan harta gaji da magiyar yazo inda take, shima ɓangaren sa idan aka kwana biyu beji ɗuriyar ta ba se yaji babu daɗi amma baze iya kiran ta ba gani yake idan yayi hakan tamkar ya faɗo ne.

Mufeeda ta fara zana jarrabawar ta ta WAEC, ta dawo gida ta gaji ta tarar da 'yan uwan baban su na ƙauye sunzo.

Mahaifin Mufeeda ɗan garin garko ne dake jihar kano, yayi karatun sa na boko dana arabiya, Matar sa cousin sister ɗinsa ce duk' yan uwane bayan ya kammala degree ɗin sa na farko ya samu aiki ya dawo cikin gari zama, yana da yara bakwai huɗu mata uku maza Mufeeda itace ƙarama.

Mufeeda na zuwa ta tarar dasu, suka dinga mata guÉ—a suna ga amaryar su.
Mufeeda ta shiga suka gaisa ta wuce É—akin ta tai wanka ta zubo Abinci Mama tace "ya jarrabawar?"

"Alhamdilillah Mama Jarrabawa tazo da sauƙi na amsa mafi yawa daga tambayoyin"

"Allah ya bada sa'a"

"Ameen Mama"

Mama ta fita 'yan uwan Baba suna ta tsokanar Mufeeda, wata ƙanwar baban ta tace

"ya kamata kizo in fara koya miki yadda rayuwar aure take tunda ke an saka naki auren a ƙurarren lokaci, kuma ke kaman har yanzu baki gama wayo ba balle kisan dabarun zama da miji"

Mufeeda ta ɗago ta kalleta tace "ki koyamin mene gwaggo? Taɓɗijan ai na haddace irin wannan faɗan naku da akaita nanatawa Yaya Amina yi nayi bari na bari, wannan karatun naku na mutan da ai munce wannan ƙarnin"

"Au haka ma zakice?"

"Eh mana ko akwai wani bayan wannan?"

Gwaggo safiya tace "hmm ai wannan yarinyar in baki rage wannan kaifin bakin naki ba da tsiwa wahala zaki sha a gidan aure lokacin mu, ai ƙasa ƙasa akewa miji magana, har tsuma kake karka yi wani kuskure daze ɓata masa rai"

Mufeeda ta ƙyalƙyale da dariya tace "Hajiya gwaggo ashe kuma kun iya iyayi, aini gani nake zamanin ku tsoron mazanku kuke ji, ni mijina baze zama abun tsoro a gurina ba, zan masa biyayya amma ba dai inji tsoron sa ba, saboda shine Abokin wasa na, Abokin shawara ta kuma Abokin kuka na"

Gwaggo sahura tace "ai kinji irin ta shiyasa auren yanzu baya zuwa ko ina"

Mufeeda tace "haba gwaggo sahura akan me zan auri miji bazan dinga wasa da shi ba se dai in dinga jin tsoron sa? Ba dani ba"

Gwaggo safiya tace "ba cewa akai kiji tsoron sa ba, ki girmama shi, zamanin mu kinga kwanon abincin miji kawai da butar sa  girmama su muke bama son wani abu ma ya taɓa su balle mijin"

Gwaggo sahura tace "ai Safiya mu miji na bisa mu muna ƙasa a zaune, idan magana yake duk nutsuwar mu muke tattarawa muna sauraren sa, miji na kujera mu muna ƙasa a zaune"

Mufeeda ta kwashe da dariya tace "Wallahi baze zauna akan kujera in zauna a ƙasa ba se kace zaman fada, ai yana kan kujera ni kuma ina kan cinyarsa" tai maganar tana watsa shinkafar ta a baki, ai gaba ɗaya suka ɗau salati, ta ɗago tana kallon su tace
"wai Salatin me kuke haka?"

Gwaggo safiya tace  "A'a bakomai ke wannan sha'anin naki babba ne"

Mufeeda tai murmushi a ranta tace  "ai maganin ku zan dinga yi ba zaku takuramin da wannan faɗan ba, ni se an koyamin wani zama da miji na haddace wanda aka koyawa su Yaya, yaushe zakumin huɗubar mutan da, shikenan bazan yi walwala da miji ba"

****************

Mufeeda tana ta Jarrabawa, Ammar har yayi ɗan wuya dan shirin aure ba na rago bane, dukda 'yan uwa da abokan arziki na tallafa masa amma shirin aure a gurin me ƙaramin ƙarfi abun akwai tausayi.

Ɓangaren su Mufeeda suna ta shiri suma, Yayyen ta har sun gaji da tsangwamar ta akan batun aure duk shawarar da zata yi akan shirin bikin ta da Baba take yi ko Yaya Amina.
Mama kam ta kasa sakin jiki tayi wa Mufeeda bayani sosai akan Aure da ƙalubalen dake cikin sa, kaman yadda take wa 'yan uwan ta a baya tana ganin ƙanƙantar Mufeeda sosai sedai lokaci2 tana gaya mata abunda ba'a rasa ba.

Se Mufeeda tayi sa' ar gaske ta haÉ—a da mita sannan Ammar zezo, idan yazo baya fin mintuna biyar ze tafi.

Babban abunda yake bashi mamaki yake kuma burge Ammar da Mufeeda bata taɓa ce masa ya sai mata abun naira biyar ba, ba ruwan ta da wannan bata roƙar sa komai, yana jin yadda Jabir ke complain akan yawan roƙon sa da wadda ze aura take yi amma sam Mufeeda bata wannan, yakanga Haliman gidan su da abubuwa tace saurayine ya bata amma shi ba wani abu da yake bawa Mufeeda amma sam bata taɓa masa magana akan hakan ba, sannan ko gurin ta yaje ta dinga murna kenan tana godiya, sannan wataran da yaje haka za ta haɗoshi da kayan ciye2.

Mufeeda Ta kammala Waec tana jiran lokacin fara Neco ta tura masa saƙon ta kammala jarrabawar Waec, yaga saƙon amma bece mata komai ba dan haka ta kira shi a waya

"Yaya Ammar shine nace maka na gama Jarrabawa ko kayi min Addu'a ko?"

"Na miki addu'a ai É—azu da nayi salla"

"dagaske nagode sosai, ya kake yasu Mama?"

"lafiya ƙalau, zan ci gaba da tuƙi yanzu se anjima" ya kashe wayar sa, ɗan ƙaramin tsaki tayi ta ajiye wayar.

Daddare ta kasa bacci ta É—au wayar ta seta ga Ammar ya turo mata da katin naira dubu biyu seda ta zare ido, har zata tura masa message É—in godiya amma ta basar dole ta nunawa Ammar itama mace ce me cikakken aji.

ta buɗe data hira take da ƙawayen ta suna ta tsara yadda bikin Mufeeda ze kasance hirar tayi mata daɗi Sosai dan haka har bayan sha ɗaya tana chatting.

Ammar yayi mamakin ganin ta online kuma bata tura masa saƙo ba, dan haka ya tura mata

  "what are you doing online by       this time?"

"chatting nake" ta bashi amsa
"keda wa?"
"Me sona wanda ya damu dani yake bani kulawa"

Dummm zuciyar Ammar tayi be ƙara tura mata komai ba, ya kashe wayar gaba ɗaya, Abun mamaki bacci ya gagari Ammar yaji zuciyar sa tayi masa babu daɗi sam beji daɗin baccin yau ba.

Washegari da ya fita ma daya tuna abunda Mufeeda tace masa se yaji ransa ya ɓaci
"da kuÉ—in auren nawa akan ta take gayamin haka?" Ammar ya yanke shawarar zeje gidan su yau.

Mufeeda bata san da zuwan Ammar ba da yamma ta shirya taje ta kai ɗinkita gurin ƙanin mijin yayar ta Naziru da yake a anguwar su Yaya murja gidan nasa yake

Naziru yace  "Mufeeda se naji wai aure zaki yi wallahi ba amana, duk yadda na dinga nuna ina riƙo ina jira ki kammala secondary in bayyana manufa ta amma kawai inji wannan mummunan labarin"

Mufeeda tace "a gurin ka yake mummunan labari amma a gurina me daɗi ne, kuma ranar da nazo na karɓi ɗinkina da bikin yaya Amina a ɗan gaban shagon ka muka haɗu da shi"

Naziru yace "wallahi Mufeeda banji daÉ—i ba, nima ina so fa"

Mufeeda tace "sekuma kayi kana son nawa ne idan aka kawo ɗinkin gidan mu ka ɗinka na kowa kaƙi ɗinkamin nawa"

Kwastomomin dake shagon da abokan aikin sa suka saka dariya sun san dayake sun san Mufeeda sosai

Naziru yace "Ai duk cikin son naki ne, ina son inga kina wannan tsiwar ne shiyasa se in ajiye ɗinkin naki in ƙiyi miki"

"wallahi zaka sa in raina ka, ka kiyayeni"

"Raini na nawa kuma? Ai kin daɗe da rainani, tijarar da kikayi min da bikin Amina ma ai ta isa in san kin rainani, amma ai inada  kyau ko? Har Anty Murja fa na gayawa ina kamu"

"Kai Naziru dan na dena ce maka Yayan, wallahi mijina yafi ka komai kyakkyawan gaske ne in gaya maka, kuma ka nemi wata ko ka jira idan na haihu in baka 'yata"

Dariya Naziru ya dinga yi  "lallai kin gama raina ni Autar amma nikam ba gudu ba ja da baya"

Ganin abun Naziru bane ƙarewa bane ya sata fice tayi tafiyar ta, gidan yaya murja ta tsaya seda aka yi sallar magariba Mijin Yayar ta ya dawo shima tsokanar ta yake
"Allah sarki autar mu ta kusa zama amarya, amma mijinki zeyi fama da wannan bakin naki"

Anty murja tace "Kuma wallahi idan ka ganshi ko fara'ar kirki ba yayi, yazo É—aurin auren Amina dan dai ba lallai ka gane shi bane, Amma wannan banga alamar yana son hayaniya ba, naga yadda za'ayi wannan zaman, gashi da wani jin kai"

"Ni ban san me Ammar É—ina ya tsare miki ba wallahi duk kinsa mana ido, haka nake son abuna"
Chapter 14 · 0% Book details