← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 64

Sashe 38

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaya Ammar ka haƙura?"
Shiru ya kuma yi mata.
Cikin Muryar Shagwaba me cike da Yarin ta tace
"Dan Allah kace ka haƙura"
Still bece uffan ba, shiru tayi bata kuma cewa komai ba, ji tayi gaba ɗaya ta takura da yadda suke ɗin nan, Yanayin ya mata wani iri banbarakwai, dan haka ta Yunƙura zata miƙe taji ya riƙe ta gam, a hankali taji yace
"Turaren wa kika shafa?"
"Turare na ne"
"Hmm ba irin wannan kike sawa ba" Yai maganar a hankali tare da Ajiyar zuciya
Ɗan tura baki tayi tace 
"Yaya Amina ce ta bani ranar da ka kaini gida"
Jinjina mata kai Yayi.
Cikin shagwaba tace "Yaya Ammar bacci nake ji"
"to yi mana ai ba hanaki nayi ba"
"to ka cikani mana ka tafi É—akin ka"

ÆŠan Murmushi yayi yace
"Ni kike kora? To ai gida nane a inda nake so anan zan zauna"

Ammar yana jin yadda zuciyar ta ke harbawa da sauri sosai, gaba É—aya ya takura ta.

Gajiya tayi da ƙoƙarin barin jikin sa tai shiru, amma ta kasa bacci tana jin Yadda yake sauke Numfashi ta ɗauka bacci yayi.
A hankali ta kai hannun ta ta taɓa gemun sa dake matuƙar birge ta, ji tayi ya riƙe hannun ta, ɗan zaro ido tayi tace
"dama idonka biyu wai?" bece komai ba se É—an murmushi da yayi yace "Yau hankalin ki ya kwanta ko? Gobe zan aske shi"
"Idan ka aske ko hmm ni nasan me zan maka".

A hankali bacci me nauyi ya ɗauki Mufeeda, bugun zuciyar ta ya koma normal, Tunda Ammar ya shiga ɗakin ta zuciyar sa ke saƙawa tana warwarewa, ya rasa abunyi gaba ɗaya, wani gefen na zuciyar sa yace "Yarinya ce tayi ƙanƙanta"
Amma Cikin bacci Mufeeda taji abunda bata saba ba dan haka da ɗan ƙarfi tace
"Yaya Ammar meye haka ne? Nifa bacci nake ji, dan Allah ka koma É—akin ka"
Ƙarshe Ammar be gama yanke shawara ba, se bayan da komai ya lafa ya dawo hankalinsa, dafe kai Yayi tare da faɗin
"Subhanallah, what the Fucking shit i did"
Yama rasa me ya kamata Yayi, ya dafe kansa yai shiru, Yayin da kukan Mufeeda ke fita ƙasa2, ta shi Yayi a hankali ya kunna fitilar wayar sa ta dunƙule a cikin bedsheet tana kuka, gaba ɗaya tausayin ta da haushin kansa suka kama shi, wai yau shi ne ya kasance da wannan 'yar mitsilar Yarinyar da yake wa kallon me ƙuruciya.

Ya miƙe ya fita, yaje ya kunna gas ya ɗora ruwa, Allah ya temake shi aka dawo da wuta, ɗakin ya dawo ya same ta yadda ya barta, yama rasa me zece mata.

A hankali yace "Can I help you? Ga ruwa can na kai miki toilet"

Sanin Halinsa yasa ta É—an juyo ta tashi zaune tace masa
"bakomai zan iya kula da kaina"

Ta sakko daga kan gadon ta nufi toilet tana taka wa a sannu a hankali ya riƙe ta har ƙofar toilet,

Ammar yace
"but do you know how to take the ritual bath?"

Juyowa tayi ta Harare shi a ranta tace "Sekace da shi yake min?" Amma a fili tace
"An ko yamana a Islamiyya"

Seda ta shiga toilet Sannan Ammar ya canza mata zanin Gado ya fita da wancan.

Bayan yayi wanka yayi shirin kwanciya yaji kamar ya koma ya kuma duba ta, kuma se yayi tunanin karta raina shi, wani kallo zata yi masa idan ya koma?
( Yo Yaya Ammar raini na nawa kuma? 🤔🤔 bayan..... 😜)

Ya nemi guri ya kwanta.

Wani irin farinciki ne ke ratsa Ammar wanda ya rasa na mene ne? A zahiri yana matukar raina Mufeeda yana ganin ƙanƙantar ta amma ta bashi mamaki fiye da yadda yake zato matuƙa, lokaci lokaci se ya ɗanyi murmushi wani lokacin kuma yayi tsaki a hankali zazzaɓi ya dinga rufe shi, tare da wani bacci me daɗi yayi gaba da shi.

Da ƙyar Mufeeda ta iya bacci, dan har bacci ya ɗauke ta kuka take tana kiran wayyo Mama a hankali.

***************
Da safe wata uwar makara yayi, dan bayan Yayi sallar Asuba har goma da rabi bacci yake, a hankali ya buɗe idon sa da suka yi masa nauyi ga kansa na sarawa, Ya miƙe ya shiga toilet ya wanke bakin sa ya fito.
tunani yake idan ya fito ta ina ze fara haɗa ido da ƙanƙanuwar Yarinyar da ya kasa controlling ɗin kansa a kanta.
Ita kuwa Mufeeda gajiya tayi da kwanciyar, dukda Jikin ta babu ƙwari tashi tayi ta sake wanka ta sha kwalliya ta shiga kitchen.

Ga mamakin Ammar yana fitowa yaji ƙamshin Abinci, tana kitchen tana aikin ta, lallai Yarinyar nan wani lokacin akwai ƙarfin hali sannan ya jinjinawa juriyar ta, a hankali ya taka zuwa ƙofar kitchen ɗin, ta bawa kitchen ɗin baya dan haka bata san yazo ba.
Ƙura mata ido Yayi yana kallon ta.
Waya take yi da Yaya Amina, tasa wayar a hansfree ta ajiye tana waya.

Mufeeda tace "Yaya Amina wai dan Allah wani irin turare kika bani ne?"

"Turare ne kawai Amma meya faru?"

"A'a bakomai tambayar ki kawai nake"

Dariya Yaya Amina tayi tace
"Kai Auta ki labarta min mana"

"Uban me zan labarta miki? Keda Allah kawai Yaya Amina"

Dariya sosai Yaya Amina take, suka yi sallama ta ci gaba da aikin ta.

Seda Ammar yayi dariya mara Sauti da yaji tace wa Yaya Amina ita da Allah.

babu tsammani ta juyo taga Ammar ta É—an razana ta ce
"Haba Yaya Ammar ni gaskiya ka bani tsoro, ban san kazo ba fa"
Ya wani maze yace
"Kingama girkin ne? Na makara zan fita"
"yi haƙuri saura kaɗan" ya jinjina mata kai ya koma falo, dama ita tasan za'ayi haka, mazewa ze tayi kamar be komai ba.

Har Yanzu da ta taho kawo masa kayan breakfast a hankali take tafiya tana yamutsa Fuska, wani irin tausayin ta ne ya kama shi, amma shi sam gani yake idan ya buÉ—e baki yai mata magana akan abunda ya faru koya mata sannu zata raina shi.

Yana lura da ita Abincin ma bata ci ba Sosai, kaɗan taci ta barshi, seda ya gama ta miƙe zata kwashe kwanukan Kaman an masa dole cikin basarwa yace
"Yi zaman ki kawai"
Da yake yasan yayi aika aika, duk wani aiki na gidan shi yayi, amma ya buÉ—e baki Yace mata Sannu ya gode ne baze iya ba.

Har Mamaki Halayen Ammar suke bata wani lokacin Yana dai ta kula da dukkanin Moves É—in ta.
Mufeeda ma kuwa ta nuna masa kaman babu abunda ya faru tunda haka yake so, har wani respect na musamman ta shiga bashi ko da wasa bata nuna masa sauyi saboda abunda ya faru jiyan ba.

Wuni yayi a gida beje ko ina ba, Duk shi ya dinga ayyukan gidan, duk da shima baya jin daɗi, Mufeeda kam bakin ta yau mutuwa yayi, wuni sukayi kaman kurame, kusan akan kujera ta wuni gaba ɗaya jikin ta babu daɗi ciwo yake mata, Amma sedai Ammar ya kalleta ya ƙi ce mata komai.

Daddare tea ya dafa mata ya sha Madara da Milo ya kawo mata, É—an yamutsa Fuska tayi za tayi magana ya haÉ—e rai yace
"ki karɓa ki ci Abinci kawai"
Tana tura baki taci Abincin seda ya tabattar ta ƙoshi sannan ya sata a gaba ta tafi ɗakin ta ta kwanta, shima ya tafi nasa.

Wayar ta ta ɗauka ta tura masa saƙo
"Yaya Ammar bani da lafiya fa"
"Meke damunki?" yai mata reply

Emoji É—in kuka ta tura masa tace
"Ai kafini sanin meke damuna"

"Ai ba jikin mu É—aya ba da zan san meke damunki, ki gayamin mene ne, idan ya kama muje Asibiti semu tafi"

"Shikenan tunda haka kace, Seda Safe have a nice dream Hubby, I love you"

Juya message É—in nata yaita yi, wani irin tausayin ta ne ya kama shi, tabbas yasan yayi mata ba daidai ba, dan shi kansa ya yabawa dauriyar ta, dan ta bashi mamaki, Amma baze iya zuwa yace mata wani abu ba, to idan yaje meze ce mata?

Mufeeda harta rufe data zata kwanta aka kira ta a waya, ganin dare beyi sosai ba ta É—aga, muryar Namiji taji suka gaisa tace
"ban gane me magana ba"

"Muffy beb, nasan bazaki gane waye ba, Amma me ƙaunarki ne, mezan samu ne daze sani nishaɗi"

"Dalla Malam Saurara, ina da Aure meyasa zaka dinga kirana, ko so kake ka kashemin Aure?"

"ƙwarai kuwa nasan ke Matar Aure ce, Amma kyakywar mace kamar ki baki dace da zama da Ammar ba, meze hana ki Auri wanda zaki huta kaman sauran 'yan uwanki?, zan baki zaɓi guda biyu ne, ko dai ki kashe Auren ki ki Aureni, ko kuma ki Amince mu dinga Soyayya muna hutawa ko kuma nida kaina ina kashe Auren, zaɓi ya rage naki"

Mufeeda ta tashi zaune tace "Allah ya shiga tskanina da kai, yayi min maganin ka, Kuma koma waye kai Na barka da Allah ya nuna maka ikon sa, Kuma nida Ammar Mutu ka raba"

Ta kashe Wayar ta, tayi blocking É—in lambar, what's App ta koma taga Yaya Amina a online, nan ta gaya mata abunda ya faru da wanda ya kira ta yanzu da wanda ya biyo ta É—azu.

Amina tace "Anya Mufeeda ba duk mutum ɗaya bane, inaga wanda ya biyo ki ɗin nan ne, kuma da ƙyar in be sanki koya san Ammar ba, Abunda ya kamata shine ki gaya masa"

Mufeeda tace "Kai Yaya Amina nasan halin abina, ƙyaleshi kawai idan, nayi blocking ɗin lambar sa"

"Amma kina ganin babu matsala idan baki gaya masa ba?"

"Zan gaya masa amma ba yanzu ba".

Ɓangaren Ammar har ya kwanta yaji saƙo ya shigo wayarsa, da sauri ya ɗakko ya duba yayi zaton Mufeeda ce

"KASA IDO SOSAI AKAN MATAR KA, DAN TANA AIKATA WANI ABU A BAYAN IDON KA, DAGA ME ƘAUNAR KA!!!

In an karanta amin share zuwa wasu groups É—in dan Allah

Ayimin afuwa ba Editing

Domin sharhi gyara ko Shawara
Ayshercool 07063065680
[11/07, 8:43 PM] Ayshercool: ..✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )
Chapter 38 · 0% Book details