← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 64

Sashe 6

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tausayin Mufeeda ne ya kamata dan iya sanin ta da ita idan mutum yace yana son ta shikenan ta samu abokin gaba, Amma yau da kanta take furta ta faÉ—a soyayya in dai hakane to tabbas dagaske take.

Cikin kulawa fati tace "Mufeeda bazan iya barinki cikin damuwa ba, Amma ta yaya zaki cigaba da son mutumin da kuka haÉ—u a titi, ke kike sonshi ba shi ke sonki ba"

"waya gaya miki baya sona? Ke nifa harna faÉ—a a gidan mu shi nake so"

ÆŠan zaro ido fati tayi tace "to shi yace yana sonki ne?"

"oho masa inma baya sona ni dai ina sonshi, tashi mu tafi gida kar Mama taimin faÉ—an nata akan na daÉ—e"

Suka tafi ba tare da Mufeeda fa kuma cewa komai ba.

Yanzu ma a kwance Mufeeda take tana jujjuya wayar ta, tana kallon Lambar Ammar da ta rubuta Yaya Ammar ɗina, ta rasa ta inda zata fara, ita dai bata taɓa soyayya ba, bata san ya take ba amma tana ganin wasu sunayi a lissafin ta yau sati uku rabon ta da Ammar, Amma kullum ta rufe ido shi take gani.

Zuciyar ta ta dinga bata shawarar ta kira lambarsa taji ko yana lafiya?

Danna lambar tasa tayi taita ringing be É—auka ba, ta sake gwada kiran wannan karon ya É—aga cikin muryar sa me kama da ta me Izza yace "Asslam Alaikum, a kira anjima zanyi salla ne"
Lumshe ido tayi jin muryar sa tasa ta sakin murmushi, ba tare da tace komai ba ya yanke wayar.

Miƙewa itama tayi ta gabatar da sallar isha'i ta nemi Abincin dare taci seda ta gama abunda take ta hau kan gadon ta ta kuma kiran Ammar, seda ta kusa yanke wa sannan ya ɗauka tare da yin sallama.
Se Ajiyar Zuciya take amma ta kasa cewa komai
"ina ji wake magana"

"Yaya Ammar nice" tana magana gaban sa ya faɗi, yaji ƙirjinsa na bugawa da ƙarfi, shi yama manta da yarinyar nan amma ya ƙara tsuke fuska yace
"Ke wa?"
"Ƙanwar ka ce Mufeeda"
"Ya a kayi?"
"Na kira in gaishe ka ne, ka manta dani"
"to Nagode ki gaida mutan gidan" ya katse kiran, Zuciya ce ta ɗibi Mufeeda saura ƙiris ta yi jifa da wayar ta amma ta fasa, ta ji haushin abunda Ammar yayi mata sosai tunanin mene mafita ta shiga yi ta nawa kanta tambayar

"dama haka soyayyar take? Wahala da ɓacin rai, ji yadda raina ya ɓaci a banza, da ina zamana lafiya nikaɗai Amma tunda na haɗu da kai na rasa nutsuwa ta, kai kuma kana can kana hutawar ka, kalli yadda ya amsa min waya, na kira shi dan inji sassauci amma ya watsan ƙasa a ido, aikam baka isa ba dani kake zancen bazan sha wannan wahalar nika ɗai baZan nuna maka WATA KISSAR... (SAI MATA) "
haka ta ci gaba da surutu kamar taɓaɓɓiya har Mama ta shigo ɗakin tace
"ke Mufeeda surutun uban me kike ne haka?"
"bakomai Mama"
Ƙarasowa Mama tayi gefen gadon Mufeeda ta zauna tace
"Mufeeda ki gayamin meke damunki ne? Tun bayan bikin Amina na lura kin zama wata iri, gayamin mene ne?"
Ai kaman Mama ta sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi ba fargaba kanta tsaye tace
"Mama Yaya Ammar ne"
"Waye kuma hakan?" Mama ta tambaya
"Mama me A daidaita sahun da ya kawomin kaya na"
Ɗan ƙara nutsuwa Mama tayi tace "Me yayi miki?"
"Mama tun ran bikin Yaya ban kuma ganin sa ba fa"

A fusace Mama ta kalleta tace "idan kika bari na tashi sena samo Madoki nazo na casaki a gurin nan, jimin Shashar yarinya, yarinya ƙarama dake kike wani zancen kina son wani ƙwaya nawa kike? Ki maida hankali akan karatun ki ki bar zancen wannan yaron in ba haka ba ni da kene"

Cikin shagwaɓa tace

"Mhmm Wallahi Mama ina son Yaya Ammar É—ina ni ba wani karatu da zan iya idan wata ta rigani Auren sa fa? dan Allah Mama ina candy ni Aure zanyi na ci gaba idan nayi Auren"
Riƙe haɓa Mama tayi tace

"Mufeeda rashin kunyar taki har ya kai ki kalli tsabar idona kice min ke ba zakiyi karatu ba Aure zaki yi, to yanzu in gaya miki mace mai Ilimi tafi daraja a gidan Aure"

"Haba Mama kefa kika ce bamu da sama dake duk abunda ke damunmu mu gayamiki ko mu tattauna a tsakanin mu, baki yadda wani yaji sirrin mu ba, ke kikace babu kunya tsakanin mu dake, Amma na gaya miki abunda nake so se hantara ta kike yi, kuma da su Yaya ne ba haka zakiyi musu ba"

Mama tace "Hakane Amma, ke kin san meye Aure kuwa? Mufeeda har yanzu ba ki gama hankali ba, kinyi ƙanƙanta da Aure, tsaya ma idan an miki Auren me zaki je kiyi? Me yasa kike son yin Auren?"

Seda Mufeeda ta kusa ƙyalƙyalewa da dariya, a ranta tace
"Mama me kika ɗaukeni ne" Amma ta maze  tace
"to Mama Auren wani abune me wahala, ba Kawai in dinga dafa masa abinci bane, yi nayi bari na bari da akai ta gayawa Yaya Amina, nifa wallahi kawai son Ammar nake, kar wata ta rigani auren sa"

Miƙewa Mama tayi tace
"baki da hankali, shi kansa Auren baki san menene ba, babu uban da ze miki Aure yanzu, tun wuri ki É—akko litattafan ki ki ci gaba da karatu keda Aure se naga hankali ya gama ratsaki, a yadda kike É—in nan baza ki iya kula da miji ba"

Bayan Mama tabi da kallo harta fice daga É—akin, murmushi Mufeeda tayi tace
"Mama kenan aikuwa zan baki mamaki, idan baki yadda ba zanje in yiwa Baba bayani nasan shi ze fahimce ni"
Wayar ta ta ɗauka ta shiga lambar Ammar ta tura masa saƙo

"Wulaƙanci be kamaci mutum me karamci da Amana kaman ka ba Yaya na, ka kula da wanda ya damu da kai, Allah yasa in ganka ko a cikin mafarki ne zanji daɗi Sosai.
Allah ya tashemu lafiya ya tsare ka daga dukkanin sharrin abun ƙi, a gaida Mamana.
Your sister Mufeeda"

Ammar na ɗakin Abokin sa Jabir da Aminu suna hira, shi Aminu yana da Aure shikuma Jabir ya kusa su Ammar kuwa ba labari, ƙararrawar saƙo ta buga alamar Saƙo ya shigo wayar Ammar, gaba ɗaya suka bishi da ido, wayar na gefen Aminu ya kalli screen ɗin wayar yace
"Ammar an turo maka saƙo kuma lamba ce"
Ammar ya karɓi wayar ya buɗe saƙon, juya saƙon ya dinga yi badan tasa sunan ta a ƙarshen saƙon ba cewa zeyi ƙaryane ba ita ta rubuta ba, wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar ce ta zauna ta rubuta wannan saƙon?

shiru ya É—anyi yana nazari kafin daga bisani ya aje wayar tare da jan gajeren tsaki.

Jabir yace "ya dai naji kana tsaki meye ya faru?"

Wani tsakin ya kuma yi sannan yace "wani shirme aka turomin"
"shirme kamar yaya? Waye ya turo maka?"

"Hmm wata fitinanniyar yarinya Allah ya haÉ—a ni da ita daga na É—auke ta a babur É—ina duk ta addabeni"

Dariya Aminu yayi yace "Malam kaimana bayani kai tsaye, Ashe kawai mu fara tara kuÉ—in goro"

"Aminu meye haka? Yarinya ce fa ƙarama, kuma kasani bani da ra'ayin Auren ƙaramar yarinya"

Jabir yace
"kaifa abun haushin ka yafiye yawa, ƙaramar yarinyar wataran ba ita zata zama babbar ba?"

Aminu yace "ganemin hanya dai"

"Bazaku gane ba, bafa tafi shekaru goma sha biyar ba, in tayi wuta shekara sha shida, uwar me zanyi da Jaririya dan wannan bata isa zaman Aure ba se dai ayi rainon ta"

Wata irin dariyar ƙeta su Aminu suka yi Jabir yace
"Wallahi Ammar kai ba ƙaramin ɗan rainin hankali bane, to meye a ciki ka raine ta harta zama yadda kake so se kuyi zaman Auren"

"Allah ya kiyaye, wannan yarinyar me shegiyar tsiwa, tana magana kaman wata tsuntsuwa ga iyayi"

Aminu yace "Ahhh kaman tsuntsuwa yabonta fa kayi gaskiya É—ankwali ya ja hula"

Banza Ammar yayi masa ya haÉ—e rai a ransa yake tambayar kansa "dagaske yabonta nayi kenan?"

Jabir yace

"Abun mamakin ma Aminu shine ya akayi ta samu lambar sa?"

Aminu yace "ƙwarai kuwa, gayamana ta yaya tsuntsuwa ta samu lambar maza gumbar dutse"

Tsaki Ammar yayi ya miƙe ya ɗau wayar sa dan sun fara bashi haushi, dama gashi ba wuya yayi fushi.

Aminu yace "Ammar ina Zainab ne?" banza yai masa ya fice ya bar musu É—akin.
****************

Mufeeda tayi sallama É—akin baban ta yai mata izini ta shiga, ta shiga ta tarar da shi yana 'yan rubuce2,
"me girma professor barka da zuwa Auta na, ya akayi ne zoki zauna"
Ƙarasawa tayi kusa da Baban ta ta zauna, ta kalli Mahaifinta tace

"Baba na sirri nazo muyi da kai nasan zaka fahimce ni, ita Mama komai nayi laifine a gurin ta"

Murmushi yayi yace "Ai ta nayi ne saboda son da take miki"

"A'a ai kai baka yimin yadda take min, a hankali kake gyara min laifina banda Mama ta fiye faɗa, dama tunda bikin yaya Amina take jin haushi na, na gaya mata abunda ke damuna amma taƙi saurara ta"

Dattijon ya gyara zaman sa yace "Ina jinki Autana"

"Baba nifa na fasa zama wannan professor É—in a yanzu"

"Meyasa?"
"Baba" sekuma tayi shiru
Baba yace "karki damu Baba ne fa, me zaki ɓoye masa, mun saba yin sirri mu tattauna karki ji komai gayamin"

"Yawwa baba na, dama.. Amm dama.. Gaskiya Baba ni idan nayi Candy.. Yaya Ammar nake so"

Shiru yayi yana nazarin ta sannan yai murmushi yace "Wannan me Napep É—in?"
Da sauri tace "Yawwa shi Baba"
"Me yasa kike son shi, kuma kika zaɓi ki aure shi?"

"Baba yana da kirki ne sosai, kuma ni ban san yadda akayi na fara sonshi ba, kawai kullum in ta tunanin sa na tambayi uncle yace min wai sonshi nake"

Baba yakuma murmushi irin na manya sannan yace
"Autar Baba daɗi na dake faɗar gaskiya komai ɗacin ta, gayamin me yayi miki, ko me yake gaya miki haka daya sa kike sonshi haka, har kika janye ƙudurinki na zama professor?"
Chapter 6 · 0% Book details