Sashe 55
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mufeeda kam Amai ne hana ta sakat, gashi cikin ta ba komai ga amai se taso mata yake, jin layin nasu yayi tsit ne yasa ta É—auka sun watse dan haka tasa hijjabin ta, tafi ta ko guava ta samu ta siya.
Aikuwa tana fitowa bakin layi inda Sa'idu me kayan miya ke siyar da kayan miya ta tarar da mata sunyi dandazo a gurin, ga wasu kayan miyan na iyo a kwata, wasu an tattake.
mata sun sashi a tsakiya suna zagin sa tare da tsine masa har zata wuce Maman Nur taceÂ
"Yawwa Mufeeda gara da Allah ya kawo ki, ga munafukin da yaje yana yamaÉ—iÉ—i a unguwa wai ya ganki kina zance da wani, har mijin ki aka tara aka gayawa, lokacin da kika tafi gida ba lafiya yace auren ki ne ya mutu"
Mufeeda tace "to ni ina ruwana? Me kike so ince ko zan manta yadda ni kika sani a gaba da sharri da cin mutunci a layin nan, a fakaice har maita kika ɗoramin yanzu da ta kwaɓe muku zaki dinga gayamin, kuje Allah ne ya kama ku"
Mufeeda tai wucewarta ta tafi gurin me guava, tana tsaye tana cinikin guava, sega Alhaji Idris yayi parking a motar sa, Sam Mufeeda bata ganshi ba seda me guava yace mata "Hajiya ana magana" tana juyawa Alhaji Idris yace "me guava zubawa babyn nan ko ta nawa take so in biya"
Banza tayi masa taceÂ
"me guava ban ta iya kuÉ—ina"
Me guava Ya zuba mata kamar yadda tace ya bata ta nufi hanyar gida, aikuwa Alhaji Idris ya biyo ta, ta ratse tabi ta lunguna dan ta guje masa, Amma yayi parking É—in motar sa ya bita.
Sosai Mufeeda tasa gudu yana binta yana ta tsaya taji, da ƙyar ta kai gida tana zuwa ta buɗe ta shige ta rufe ƙofar ta, a tsakar gida ta zube tana ta haki, ya daɗe a gurin yana buga gate ɗinta wai ta fito suyi magana ko nawa take so ze bata, hawaye ne ya fara bin idon ta, wannan wace irin masifa ce daga yin Auren ta zuwa yanzu ta haɗu da ƙalubale daban daban wanda bata san iyakar sa bama, wani irin zamanine wannan ace dattijo kamar Alhaji Idris yana bin yarinyar da yayi jika da ita kuma yasan matar Aure ce.
Tana cikin wannan tunanin taji ƙarar harbin bindiga, ai da gudu ta shige ɗaki ta ƙule a gado jikin ta na cigaba da tsuma.
Hajara ce tayi waya ta kira sojoji, Ashe baban ta babban General ne na Sojoji, mijin ta ma babban soja ne tunda aka haife ta a barrack take, aka turo mijin ta aiki kano tace ta gaji da zaman barrack tana so yakama mata gida ta zauna a wajen barrack, suna shirye2 dawowa kanon aka tura shi yaƙi Maiduguri, dan haka se yasa abokin sa ya kama mata gidan ta dawo ta zauna, dan haka tai waya aka zo hadda Sojoji mata aka tattare mata su Sa'idu da su Maman Nur da suka yi wa juna jina jina saboda duka, dan har jaririn da Maman Nur take goyo aka fasawa kai saboda dambe.
*********************
Maman Fa'iza taji hasuhin abunda Ammar yayi matuƙa da yace babu ruwan sa akan lamarin, ita kanta Fa'iza taji daɗi da yace ba ruwan sa dan tana tsoron Asirin su ya tonu.
Faruk yana gurin aikin sa 'yan sanda sukazo suka tafi da shi, Yayan Fa' iza Abubakar shi ya kai ƙarar sa gurin 'yan sanda akan marin da yayi wa Fa' iza.
Maman Fa'iza ta kira Maman Ammar a waya ta gaya mata abunda ya faru da yadda suka yi da Ammar, Umma ta bata haƙuri tace za tayi masa magana
Umma ta kama mita tana "Nikam na rasa wannan hali irin na Ammar, meye a ciki dan yaje ya taimakawa 'yar uwarsa, kawai yaje station aji
ba' asin meyasa ya mareta ayi musu tsakani tunda Abokin sane shine baze iya ba, kai Allah ya shirya Ammar.
Abba yace " Banga laifin sa ba, tunda bashi yayi marin ba kuma ba shi yace ayi ba, da alaƙar kirki ce tsakanin ta da Shi Farukun da baze mareta ba, babu yarinyar da zata kama kanta wani ya mare ta a banza"
Umma tace "dukda haka dai, tunda har Maifiyar Fa'iza ce ta nemi yaje ai se yaje, inda mutunci ai itama uwarsa ce"
Abba yace "hakane"
Umma ta kira Ammar a waya, yana tsaka da tuƙi sega kiran umma, Yayi parking ya ɗaga wayar, bayan ya gaishe ta umma tace
"Ammar kai duk maganar da za'a gaya maka sedai ta shiga ta dama ta fita ta hagu ko? Yanzu abunda kayiwa Maman Fa'iza ya dace? Meye laifi dan kaje police station anji ba'asin da yasa ze mareta? Aiba raguwa zakayi ba"
"Umma kenan, Allah ya baki haƙuri, amma ni dai nasan Faruk abokina ne, Amma bansan wace irin Alƙace a tsakanin su da har yasa ya mareta ba"
Umma tace "koma dai wace iri ce, kaje kaji kodan Mahaifiyar ta"
"shikenan zani Insha Allah"
"Ai ba zaka ba kaje yanzu suna police station É—in unguwar su Fa'iza na nan babban titi"
"to Umma"
Ya katse wayar, ita dai Umma indai akan lamarin 'yan uwane setaita cusashi, abunda ya shafe shi da wanda be shafe shi ba.
Ya ajiye wayar kenan ya nufi unguwar su Fa' iza aka kira shi da baƙuwar lamba, ya kuma tsayawa ya ɗaga, ko gaisawa basu yi ba balle yasan wake magana yaji ance
"Kai maza ka koma gidan ka, Sojoji sunzo unguwa suna ta kwashe matan mutane suna tafiya da su" aka katse wayar
Ai a gigice Ammar yabi lambar amma shiru, ya kira Umma yace
"Umma dan Allah kiyi haƙuri ba zan samu zuwa station ɗin nan ba, yanzu aka kirani wai sojoji sunje suna kwashe matan mutane a unguwa"
Umma tace "Subhanallah,ƙ Allah yasa lafiya shikenan Allah ya kiyaye kai maza ka koma, zanyiwa maman Fa'izan bayani"
Ammar ya kashe wayar ya tafi, aikuwa yana zuwa ya tarar unguwar tasu tun daga titi kamar anyi ɗan ƙaramin yaƙi kowa ya kulle a gida ss hayaƙi unguwar take.
Har yaje ƙofar gidansa bega kowa ba, yasa key ya buɗe gidan ya shiga da sauri ya shiga yana ƙwalawa Mufeeda kira, ya nufi ɗakin ta da sauri yana zuwa ya tarar da ita ta ƙule akan gado tana kuka, a gigice ya ƙarasa kan gadon nata ya ɗagota yace
"Mufeeda lafiya meyafaru? An kirani a waya wai Sojoji na kwashe matan mutane a unguwar nan meyafaru?"
Mufeeda ta gaya masa duk abunda ya faru gaba É—aya a unghwar na dambe da tons tonen Asiri da suka yi hadda zubarwa da juna jini, shiru Ammar yayi yace
"Alhamdilillah da Allah yasa baki zama daga irin su ba Mufeeda, da yau bansan wani baƙin ciki zanyi ba ace anyi dambe da mata ta a layi, dambe na tashanci hadda keta sutura kuma ace sojoji sun tafi dasu Allah kaɗai yasan meze faru, Allah yayi miki Albarka"
Mufeeda ta goge Hawayen ta tace "Yaya Ammar wai ashe me kayan miya ne yaita cewa ya ganni ina zance da wani, har akazo aka tare ka aka gaya maka?"
Ammar yace "bansan waye ya fara zancen ba, amma maƙocinmu ne ya tareni bayan sallar asuba ya gayamin"
"shikenan ai koba komai Allah ya sakamin yanzu"
"hakane kam, kiyi haƙuri ki dena kuka kinji, ni mema yasamin ke kuka haka?"
Nan ta kwashe abunda ya faru tsakanin ta da Alhaji Idris ta gaya masa data fita ɗazu, nan da nan Annurin fuskar Ammar ya ɗauke, wani irin gumi ya shiga tsatstsafo masa, gaba ɗaya gashin jikin sa ya miƙe.
" meyasa baki gayamin tun tuni ba? "
"saboda ina gudun ɓacin ranka"
"Wannan ba hujja bace" ya faÉ—a a É—an hasale.
"Allah ya baka haƙuri, Yaya Ammar nasan halinka fiye da yadda kai kasani, na ɗauka ze dena bina amma yau kam da gudu ma ya biyo ni har ƙofar gidan nan"
A hankali ya raba Mufeeda da jikin sa ya miÆ™e, cikin zafin nama ta riÆ™e shi taceÂ
"Yaya Ammar kabi komai a sannu, mutumin nan yana da kuÉ—i sosai kar yasa ayi maka wani abun"
Ammar ya ƙwace hannun sa ya fita da sauri, yana fita ya tarar Mazajen wanda aka kwashe sun daddawo suna salallami, babu wanda yasan inda aka tafi da matan nasu, gashi Hajara bayan an tafi dasu ta rufe gidan ta ta ƙara gaba.
**********************
Faruk yana police station a bayan kanta yana rarraba ido, tun safe Su Fa'iza basu je ba se bayan la'asar da suna jiran Ammar kuma beje ba.
Lokacin da suka je suka yi sa'a D. P. O yana nan, aka buɗe file ɗin da aka rubuta ƙorafin da su Fa'iza suka shigar, aka kalli Faruk akace "Kai me wannan baiwar Allah tayi maka ka mareta?"
Faruk yace "Yallaɓai saɓani ne muka samu, amma dan Allah ayi haƙuri hakan ba zata sake faruwa ba"
Abubakar yace "Yallaɓai ba wani ayi haƙuri ya faɗi wani irin saɓani ne yasa har ze mari ƙanwa ta?"
D. P. O yace "waima tsaya meye a tsakanin ka da ita?"
Faruk yace "ƙanwar Abokina ce"
"ina Abokin naka?"
Nan Maman Fa'iza ta faÉ—i dalilin rashin zuwan Ammar, D. P. O yace
"yanzu dai sulhu ya kamata ayi, tunda shi sulhu duk inda yake Alkhairi ne"
Zumɓura baki Fa'iza tayi tace "bawani sulhu kawai a fitar min da haƙƙina dan baze mari banza ba"
"
D. P. OÂ yace " ke nutsu, idan kika yi min rashin kunya zan saka a saki bayan kanta kema, waima meye dalilin Yin marin ne, dan ba yadda za'ayi da mutuncin ki, abokin Yayanki ya mareki"
Faruk yace "Yallaɓai zagina tayi"
"to zagi yana fitowa a jiki ne? Banda shashanci da nusaranci meya kaika dukan mace banda ragwanci"
Nan maman Fa'iza suka zage akan lallai se an fitarwa da Fa'iza haƙƙin ta basu yadda da sulhu ba, ganin da Faruk yayi ze kwana a ciki dan sunyi masa taron dangi, ya kwashe abunda ya faru tsaf tsakanin sa da Fa'iza ya gaya musu.