Sashe 20
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mufeeda ta shiga kitchen ta dafa tea tun dare Ammar ya shigo da bread, tayi amfani da ƙwan nan da albasa da kuma naman jiya da suka kasa ci ta sarrafa bredin nan ta gasa, har ta gama Ammar be tashi daga bacci ba.
ÆŠakin ta tafi domin tayi wanka kafin ya tashi, amma harta fito ta kintsa jikin ta bacci yake, É—akin sa ta tafi, tana zuwa ta tarar yana ta baccin sa.
Kan gadon ta hau ta É—an tsura masa ido a fili tai murmushi tace
"Masha Allah mijina yafi na kowa kyau"
Ta É—an daki fulon da yake kai, tana faÉ—in "Mijin So, ka tashi haka baccin ya isa fa"
A hankali yake buɗe idon sa har ya buɗe su duka ya sauke akan Ƙwailarsa, bakin ta raɗau da jan Jambaki, tayi ɗare ɗare akan gadon sa, ƙura mata ido yayi ba tare da yace komai ba ga ƙamshin turaren ta me daɗi yana ratsashi, se sake lumshe ido yake.
Murmushi tayi tace "good morning Baby, na dafa ruwan wanka, in kayi seka fito mu karya"
Yadda ta fita daga ɗakin sa a zuciye daren jiya beyi zaton zata kulashi ba, wani ƙarin mamakin wai har tasan ta dafa masa ruwan wanka.
Yanayin kallon da yake mata ne yasa ta tsarguwa, dan haka Ta juya ta sauka ta bar ɗakin, ta koma falo tana jiran sa, koda ya fito falon ƙamshi ne daban daban yake dukan hancin sa, ya samu guri ya zauna harta jere komai na breakfast ɗin.
Ta kalle shi a shagwaɓe tace "Nagaishe ka amma kaƙi amsawa ko"
"to sannu, lafiya ƙalau" ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin janyo flask ɗin shayi.
"No tsaya in zuba maka"
Ta haÉ—a masa tea, gurin zuba Madara tana zuba spoon É—aya yace "Ya isa haka"
"taɓ spoon ɗaya, gaskiya ni spoon ɗaya yayi min kaɗan" shiru yayi ya fara shan tea ɗin sa ya kalle ta yace "Ina bredin ne?"
Plate ta miƙo masa ɗauke da bredin da ta sarrafa, ya kalli bredin yace "meye Wannan?"
"kaci kaji mana"
"bredin kika wulaƙanta ya koma haka?"
"ni ban wulaƙanta ba, kaci kaji da daɗi"
Girgiza mata kai yayi yace "bazan ci ba"
Hannu tasa ta É—akko bredin ta matsa kusa da Ammar ta kwantar da muryar ta sosai tace
"dan Allah Yaya Ammar kaci, na yadda idan babu daɗi na wulaƙanta maka Abinci kamin duk hukuncin daya dace dani, dan Allah"
Yadda tai maganar ne cikin sanyin murya yasa ta bashi tausayi, hannu yasa ze karɓa, ta ɗan girgiza masa kai ta miƙa masa bakin sa, ya buɗe baki ta saka masa.
Ai ba ƙarya bredin nan ba ƙaramin kaiwa Ammar yayi ba, dan yayi test sosai a bakin sa, Mufeeda tasan idan tayi magana ze iya mazewa ya fasa ci dan haka ba tace komai ba ta ƙara miƙa masa wani, ba kunya ya amshe abun sa ya taune ba tare da yace komai ba.
Zata kuma gutsurowa yace "banni inci da kaina, zuba naki kici"
Murmushi kawai Mufeeda tayi tace "Shikenan zanci, gama cin naka"
Ammar yaci bredin nan sosai dan ba ƙaramin daɗi yayi ba, se yaji da'aka sarrafa bredin zuwa wani abun daban yafi bredin daɗi ma, amma be iya buɗe baki yace yayi daɗi ba.
Ya kammala ci ta miƙa masa tissue ya goge hannun sa da bakin sa, har ze tashi ta kalle shi cikin salon kashe murya tace
"Mijin baby ba kace komai ba, yayi daÉ—i kuwa?"
ÆŠan kallon ta yayi ya maze tare da É—an tsuke fuska yace "ba wani daÉ—i na dai cine kawai maganin Yunwa"
Murmushi tayi tace "Tunda dai har ya wuce cikin ka ba kayi amai ba ai shikenan" tai maganar tana murmushi, ta tattare Kwanukan taje kitchen ta wanke.
Ta dawo ta tarar da shi a zaune a falon be tashi ba "Yaya Ammar ya haka ba zaka fita bane?"
"Se an jima zan fita" ya bata amsa
"shikenan Allah ya kaimu anjiman, ai gara ka zauna in ta kallon abuna ko?" tai maganar tana kashe masa ido É—aya.
Hararar ta yayi ya kauda kansa daga kallon ta, tai murmushi ta zauna tana facing É—insa, lokaci lokaci suna haÉ—a ido se yayi sauri ya kau da kansa.
Ta tattara attention ɗin ta tana ƙoƙarin gano meya hana shi fita yau da wuri, kullum yana gama karyawa yake fi cewa, Amma yau yaƙi fita kuma yana zaune a falo, abun mamakin kuma se satar kallon ta yake, sake ɗaga ido yayi suka haɗa ido, ya ɗan maze yace
"lafiya kike min wannan kallon ƙurillan?"
A ranta tace "sekace shiba ni yake kallo ba" amma seta ta taso daga inda take tazo kusa da shi ta zauna ta kalle shi tace
"Kasan menene? So nake in taɓa gemun ka, shike tsolemin ido"
ÆŠan buÉ—e baki yayi yana kallon ta, lallai yarinyar nan ta mugun raina shi, kawai ya É—auke kansa yace
"tashi daga kusa dani mara kunya"
ƙara narkewa tayi a jikin sa tace
"dan Allah Yaya Ammar sau ɗaya fa zan taɓa dan Allah"
Juyowa yayi yana kallon bakin ta, wanda yayi raÉ—au da jan baki, se É—aukar ido yake, dukda kitson kanta ya fara tsufa amma har yanzu yana É—aukar hankalin Ammar, Yadda take maganar very serious kamar 'yar yarinya.
Ta kuma cewa "in taɓa dan Allah ?"
"Tashi kije kiyi breakfast seki zo ki taɓa"
Murmushi tayi tace "to"
Ta miƙe tana fara' a ta haɗa breakfast ta zauna tana karyawa, ta nayi tana kallon sa tana murmushi, ta kammala ta tattare Kwanukan, tana dawowa ta tarar ya ɗakko mukullin sa ze fita.
Ta ɗan ɓata fuska tace "haba Mijin bebi, haka muka yi da kai? Banfa taɓa ba"
"Ke bana son shiririta, ni fita zanyi Ungo wannan" ya miƙo mata kuɗi ɗari biyar
"Me zanyi da wannan? Naga ka siyo komai na amfani ai"
"Eh baki nayi ko zaki sai wani abun"
"ni babu abunda zan siya"
"Ke ki karɓa meye haka?" ya ɗanyi maganar a hasale.
Durƙusawa tayi tasa hannu biyu ta karɓa tace
"Nagode Allah ya ƙara Arziki, yaja da ran su Umma"
"Ameen"
Suka yi Sallama ya fice.
**********************
Fa'iza ce keta kaiwa tana komowa a ɗakin ta tarasa meke mata daɗi, tana ƙoƙarin tuna menene mafita akan halin da take ciki tabbas tana son Ammar kuma tunda har ya iya Aure ƙaramar yarinya kaman wannan to tabbas itama zata iya jarraba sa'arta akansa amma ta yaya? "
Fitowa tayi falo ta tarar da Maman ta tayi baƙuwa, ba tare da ta kalli inda baƙuwar take ba tace "Mami dan Allah zan fita anguwa, zanje gidan su Nasreen"
"To kiyi sauri karki daÉ—e, bana son babanku ya dawo yaita min mitar ba kwa nan"
(Nasreen ɗin 'yar ƙanin mahaifiyar Fa' iza ce)
"Ok"
Baƙuwar tace "Ahh Fa'iza ba magana?"
Fa'iza ta ɗan juyo ta kalli matar tace "Ohh sannu" a ƙalla matar tayi sa'ar mahaifiyar Fa'iza, bata kuma bi takan Matar ba ta wuce ɗakin ta.
A gurguje ta watsa ruwa ta shirya ta fice daga gidan, ba ta tsaya ko ina ba seda taje gidan su Nasreen, ta shiga da sallama tayi sa'a Nasreen É—in tana tsakar gida tana mopping, Nasreen na ganin ta tace "hajiya fa'iza wannan zuwa haka babu waya, anjima nake tunanin in zo gidan ku fa"
"Kinga gurin ki nazo dan Allah ina Umma?"
"ba ta nan tana Islamiyya"
"Muje É—aki dan Allah ina cikin damuwa"
Ɗaki suka shiga kaman yadda Fa' iza ta buƙata.
"Nasreen wallahi nayi sakacin kasa ga yawa Ammar abunda yake cikin raina, saboda ina ganin baze soni ba, se gashi ance yarinya ƙarama ya aura"
Nasreen tace "Wallahi yarinya ce sosai, ai ke baki je gurin dinner ba, mu munje munga komai wallahi yarinyar nan bata fi shekara sha shida ba, 'yar ƙarama da ita se iyayi in gaya miki tsaf zaki iya goya wannan' yar abar"
"dan Allah ba wannan ba meye abunyi yanzu? Wallahi Nasreen baki ji yadda nake ji a raina ba, ina son Ammar sosai fa ba da wasa ba"
"Aikuwa seki ɗau haƙuri tunda ya riga yai Aure"
Hararar ta Fa' iza tayi tace "haba Nasreen Ammar mijin mace huɗu ne fa, dan me zan haƙura?"
"to da sana'ar Adaidaita sahun ze riƙe ku ku biyu, kiyi tunani mana Fa'iza"
"Taɓɗijan ubanwa ya gaya miki mu biyu zamu zauna, ta isa in zauna da ita inyi kishi da 'yar mitsitsiyar Yarinya, wallahi sena fara da korar ta daga gidan tukuna, in saka Daddy na ya bashi aikin yi, dan bazan aure shi a dinga miji na ɗan a daidaita sahu bane"
"ta yaya?" Nasreen ta tambaye ta
"koma ta ina ne, sena fara da kora ta tukuna ni kuma zan shige"
"Naji amma kin san meze faru?"
"A' a sekin faÉ—a"
"Yanzu ki bari se an jima, ki shirya muje gidan su Yaya Ammar, semu sa Halima ta raka mu gidan sa dan nima banje gidan sa ba, muje kiga yarinyar muga yanayin kamun ludayin ta daga nan semu san ta ina zamu fara"
"Yawwa Nasreen naji daÉ—i Sosai, ina nan bazan koma gida ba, gama abunda kike, bari in É—ora girki idan yasa anjima se mu tafin"
"shikenan bari in samo Almajiri yai mana cefane kafin Umma ta dawo".
Haka kuwa akayi, bayan sun gama girki Maman su Nasreen ta dawo suka yi mata sallama cewar za suje gidan Yaya Ammar.
Maman Nasreen tace "Aikuwa kwa gano min gidan dan dama ban samu naje ba nima, dan Allah kuce ina gaishe su kafin inzo"
Nasreen tace "to Umma zamu gaya musu Insha Allah"
Daga nan suka fice basu tsaya ko ina ba se gidan su Ammar.
Mahaifihar Ammar taji daÉ—i da taji sunce gidan Ammar zasu je, da iyayen su da mahaifin Ammar uwa É—aya uba É—aya, Dan haka Umma tasa Halima ta shirya ta raka su gidan nasa, ta bada kayan kuka da su zogale tace akaiwa Mufeeda.
Sam Su Fa'iza basu nuna akwai wani abu a ƙasan ransu ba game da zjwan su gidan Ammar dan haka Halima ba taji komai ba ta shirya domin ta raka su.
**************************