← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 64

Sashe 18

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka ci gaba da lallɓa Ammar har suka tafi gurin ɗaurin Auren.

Aka É—aura Auren Mufeeda da Ammar akan sadaki har Naira dubu hamsin, Mutane sun yi mamaki musamman magulmata, Yaya Fadila ta shigo É—aki ta samu Mufeeda tace

"Auta buri ya cika an auri Ammar, an zama matan Aure su Mufeeda yanzu nidake mun zama É—aya fa ko?"

Banza Mufeeda tai mata taƙi ko kallon ta.

Fadeela tace "Yarinya zaki ga abunda muke jiye miki, seki tashi an É—aura, ki tashi kije za'ayi hotunan É—aurin Aure"

Kuka Mufeeda ta saka tare da noƙe kafaɗa, Fadila kuwa ta dinga mata dariya tana cewa

"Yarinya da an gayamiki Auren abune me sauƙi? Ai ki adana kukan ki"

Seda Mama tazo tai fama da ita Sannan aka gyara kwalliyar ta fito, Angwaye sun shigo anata gaisawa Mufeeda ta fito.

Tunda ta fito yake kallon ta da alama tana cikin damuwa amma tayi kyau, irin shaddrsa ce ya kawo mata itace a jikin ta, me hoto yazo anata É—aukar hotuna, dukda haka wasu anayi tana kuka, kallon ta Ammar yake sam kuka ba yamata wahala ko meye na kukan kuma yanzu oho?

Daga cikin abokan Ammar ne wani Faruk yace "haba boss ka rarrashi babyn taka mana, kana kallo tana kuka"

Wata uwar harara Ammar ya watsa masa, ya maze.

Abokan Ammar suka sasu gaba wai za'a musu hoto tare, Mufeeda taƙi tsayawa, Jabir yace

"dan Allah ka rarrashi Amaryar nan taka ayi hoton nan"

Ammar ya ɗanyi ƙasa da muryarsa yace
"wai ba zakiyi shiru ba? Kukan me kike haka waye yace kice kina son Auren? Kidena wannan kukan ko a fasa hoton, maza goge hawayen nan"

Abokan Ammar se ihu suke suna "kunga wani salon Soyayya"

Mufeeda tana kuka amma ta zumɓura baki daidai kunnen Ammar tace "ka bani handkerchief in goge"
"bazan bayar ba in bazaki dena ba kiyi tayi"
"wallahi in baka banba da babbar rigarka zan goge"
Da sauri ya ɗago ya kalleta, babbar rigar sa fara ƙal tasha aiki, Amma tace da ita zata goge hawaye, yanayin kallon da yayi mata ne kaman na soyayya, aka dinga ɗaukar su hoto.

"Ka bani mana Allah zan goge da rigar ka" girgiza kai yayi baya son yayi wani abu daze nuna rashin kyautawa a gaban mutane, amma tabbas yasan zata aikata abunda tace ya ɗakko handkerchief ya miƙa mata ta karɓa ta goge hawayen fuskarta, handkerchief ɗin se tashin ƙamshin turaren Ammar yake.

shi dai Faruk ji yake inama shi ya samu damar da Ammar ya samu, yarinya ƙarama gata me kyau ga shagwaɓa abunda yake matuƙar burgeshi da mace kenan ya samu mace shagwaɓaɓiya.

Nan ma aka dinga surutu 'yan matan layin su Mufeeda da suke ji da kansu su kaita gulma wata tace
"Taɓɗijan wannan yarinyar ya zata yi da wannan mutumin ai yayi mata girma, kalleta' yar mitsitsiya da ita jishi a murɗe kaman ɗan dambe"

ÆŠayar tace "ke Amma wallahi ya haÉ—u koni na samu wannan Auren sa zanyi wallahi yana da kyau, wannan beyi kalar auren 'yar mitsitsiyar yarinya ba, Amma se wani cin magani yake ko fara' ar kirki ba yayi kaman wanda akayiwa auren dole"

"Ke wallahi da na ganshi lokacin da yake zuwa zance ni zanyi ƙoƙari in cusa kaina, amma wannan ai da irin mu ya dace ba wannan fitsararriyar ba"

Ɗayar tace  "Allah ya kiyaye in auri me Napep nafi ƙarfin nan"

"A'a wallahi ni banfi ƙarfi ba, ba gamu a zaune a layi ba, ita kuma tayi wuf dame napep wallahi indai zanci in sha na samu kaman wannan tafiya zanyi gamu a zaune ai yarinyar da aka haifa a gaban mu ta shige muna zaune" haka suka ci gaba da surutunsu da gulmace gulmace

Haka aka gama shagalin biki a wunin ranar, Amma uwar gayya kanta har ciwo yake saboda kuka, bayan magariba motocin ɗaukar Amarya suka zo, maƙota suka dinga cika motocin nan suna tafiya zasu je suga ƙwal uwar daka suje ganin gidan mufeeda.

Kusan duk an watse Mufeeda ake jira a tafi da ita amma ta maƙale a jikin mama tana ta kuka, Mama ta aurar da yara mata amma bata taɓa zubda Hawaye danta aurar da 'ya ba se wannan karon tana cikin yiwa Auta nasiha mufeeda ta ƙanƙame ta tana kuka, kawai se Mama itama ta hau kukan, duk faɗan da suke yi da Mufeeda tana matuƙar ƙaunar' yar tata, suka rungume juna suna kuka, Yayan mufeeda ya shigo yace

"Mama dan Allah kidena kukan nan ki ƙyale yarinyar nan akaita ɗakin ta, tun ɗazu su gwaggo sahura na mota ita suke jira amma kin ƙanƙameta kuna kuka, haba Mama baki taɓa kuka dan zaki aurar da 'ya ba se Mufeeda"

Su Anty Murja sukai tayiwa mama mita, Sosai Mama taƙi saurara su ta ƙara rungume auta.

Seda Baba yazo da kansa, ya zauna ya ƙara yiwa Mufeeda nasiha me ratsa zuciya sannan yace ta tashi ta tafi a raka ta, amma Mufeeda tai mursisi ta sake hayewa kan gado bayan Mama tana kuka, Mama ji take kaman tace a ƙyale mata 'yar ta, Mufeeda tayi ƙanƙanta da fara fuskantar ƙalubalen dake cikin rayuwar aure, Amma tana mata addu'a Allah yasa Ammar ya riƙe ta Amana.

Baba ne yace "yaki Auta na zo da kaina zan raka ki É—akin ki, duk yayyan ki ba wadda na raka, amma dole in raka auta taho muje"

Baba yasa hannu ya kamo na auta, ta sakko daga kan gadon amma ta riƙe hannun Mama, shi kansa Baba daurewa yake yadda suke kuka gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi.

Baba yace
"Sarah dan Allah kiyi hakuri kiyi mata fatan Alkhairi"

Mama ta goge hawayen ta tace

"yi shiru Auta na kinji, kiyi hakuri haka dama rayuwar 'ya mace take, kedai ki riƙe nasihohi da muka yi miki zaki zauna lafiya da kowa a rayuwa Insha Allah, jeki Auta na Allah ya bada sa' a Allah ya sanya alkhairi yasa gidan zamanki ne, Allah ya Sanya alkhairi da haske a rayuwar auren ki Allah ya bada sa'a"

Daƙyar Mufeeda ta saki Mama, Baba ya riƙe hannun ta yasa ta a mota ya tafi kai Autarsa da kansa ɗakin miji.

***************

Ammar ya kammala shiryawa se zuba ƙamshi yake, abokan sa na waje suna jiran sa, gidan su Ammar wasu duk sun tafi gidan Amarya, yayin da wasu ke ƙarasa Wanke-Wanke da gyaran gida, Ammar ya shiga ɗakin Abban sa ya tarar da shi zaune da shi da Ummansa yaje ya durƙusa gaban su yace
"Abba zan tafi"

Abba yai murmushi yace "Ango ka sha ƙamshi, ubangiji Allah ya Sanya alkhairi ya baku zaman lafiya, dan Allah dan Annabi Ammar yadda suka baka 'yar su cikin mutunci ka girmama musu yarinya ka kula da ita, ka sauke dukkanin haƙƙoƙin ta dake wuyan ka, ka rage wannan zafin zuciyar naka da izza da wannan yawan faɗan naka, kaga yarinya ce ƙarama ka kula da ita Ammar "

Ammar ya jinjina kai yace
" Insha Allah Abba "

Umma tace
"to Ammar duk abunda zan gaya maka na riga na faɗa maka a baya, kuma mahaifin kama ya gaya maka, yarinyar nan da iyayen ta sun mana halacci, kaji tsoron Allah ka riƙe musu yarinyar su Amana, sannan ka tuna kaima akwai 'yan uwanka mata dake aure a gidan wasu, idan ka muzgunawa' yar wasu to tabbas kaima za'a cuzguna ma naka, ka riƙe ta da amana sannan kuma kayi haƙuri, kayi haƙuri rayuwar aure gaba ɗayan ta haƙuri ce, Allah ya baku zaman lafiya "

Ammar kasa cewa komai yayi, a hankali yace " Abba a zaman mu daku nasan baza'a rasa abubuwa marasa daɗi da nayi muku ba ina roƙon afuwar ku"

Abba yace "Aini dama matsala ta da kai É—aya, rashin Aure ga miskilanci, amma duk wannan ba komai bane akan tarin alkhairan ka a gare mu, mun yafe maka Allah yayi maka albarka"

Ya amsa da Ameen, sannan ya miƙe jiki a sanyaye ya fito tsakar gida, sauran 'yan biki suka dinga masa guɗa suna masa fatan Alkhairi, wasu har sunje sunga gida sun dawo.

Yayar sa Maryam wadda ita yake bi ta ja shi gefe tace

"To ɗan uwana ina maka fatan Alkhairi, Allah ya Sanya albarka yasa anyi kenan, sannan abunda nake so in gaya maka shine, ka kula sosai karka fifita matarka akan iyayen ka, sannan karka fifita buƙatun mu 'yan uwanka akan Na matarka, mu a gidan mazajen mu muke, duk wadda tazo maka da buƙatar ta indai bata da wani mahimmanci ka ƙyale namu buƙatar ka sauke haƙƙin matar ka, dan Allah ze tambaye ka akan amanar da ka ɗakko, Sannan Ammar tsakanin ka da iyayenka da mu 'yan uwanka daban, tsakanin ka da matar ka daban, dan haka ka yi wa matar ka abu ba lallai se mun sani ba, haka dan ka yi wa iyayenka abu base lallai ta sani ba, hakan ze toshe kafar samun matsala, Sannan kasan Auren nan naka yana da maƙiya mussman a gurin bikin nan na ƙara gani, kasan Yaya jidda bata son Auren nan, Sannan karka manta ko kuma in baka sani ba yanzu in gaya maka, Fa'izar Kawu Bala tana ɗaya daga cikin masu ƙaunar ka, ƙiri Ƙiri take nuna adawarta tareda kushe Auren nan, dan haka seka kula sosai, Allah ya baku zaman lafiya ƙanina"

Mamakine ya kama Ammar sosai, wai Fa'iza Yarinyar da ko gaisawar kirki ba sayi ace itake sonsa, da yake duk cikin 'yan uwan sa yana jituwa da maryam sosai dan haka yace

"Shikenan Sayyada Maryama, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, Allah ya huta gajiya"

Yai gaba tana É—aga masa hannu.

Yana fita nan ma abokan sa suka dinga tsokanar sa, daga nan suka hau abun hawa zuwa gidan Ammar.

Mutane kusan duk an watse, suka je suka tarar da Mufeeda da mahaifin ta yana jiran isowar Ammar.

Suna ganin mahaifin Mufeeda suka nutsu suka dena wannan rawar kan da suke, suka nemi guri suka zauna, Ammar da Mufeeda na gaban Baba, Baba yai musu addu'a da nasihohi irin na dattawa, ya kama hannun Ammar yasa na Mufeeda a ciki yace
Chapter 18 · 0% Book details