Sashe 40
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mamaki ne ya kama Ammar shiru yayi yana tunani, yana sake juya saƙon, wani irin rashin gaskiya ne Mufeeda zata aikata a bayan idonsa? Tunani yake akan Yadda take masa biyayya iya yinta, taya za'ace tana aikata wani abu a bayan idon sa? Amma zeso yasan wanda yake ya turo masa wannan saƙonnin.
A hankali ya ajiye wayar ya miƙe jiki a sanyaye ya fito falon.
Yana fitowa ya tarar da Mufeeda ta saka mini Skirt da wata 'yar ƙaramar riga shara shara bata ƙarasa rufe mata cikin ta ba, tayi parking ɗin dogon gashin ta, ta saka hular hat tana rawa a falo tana juya jikin ta a hankali tana bin sautin waƙar dake tashi a talabijin ɗin dake falon, ba tsammani ta juyo taga Ammar a tsaye yana kallon ta, da Sauri ta ƙaraso inda yake tsaye tana faɗin
"Happy birthday to you Hubby"
Kallon ta kawai yake yi, ta riƙo hannun sa zuwa falon ya samu kujera ya zauna ta cire hular kanta ta dube shi tace
"barka da zagayowar ranar haihuwar ka Mijina Allah yayi wa rayuwar ka Albarka"
"Ya akayi kika san yaune ranar zagayowar haihuwa ta?"
"Barwa zuciya abunda take so Hubby, ina son yin wani abu daze faranta maka kawai na samu labarin wannan kwanan watanne na haihuwar ka, shiyasa na maka barka da zagayowar ranar haihuwar ka"
A hankali ya janyo ta jikin sa yana shafa gashin kanta da yasha gyara ya kwanta yana ta tashin ƙamshin mayuka, tunani yake akan saƙon da aka turo masa, yana cikin tunanin yaji muryar ta tace
"Abun sona naso mu kasance cikin farin ciki yau, Amma naga kamar baka walwala, Allah ya sa ba laifi nayi maka ba"?
Tai maganar jiki a sanyaye, Ajiyar zuciya yayi yace "muyi breakfast ko?"
Jinjina masa kai tayi, har suka kammala Mufeeda na kallon sa tana tunanin meke damun sa? Sosai kayan da ta saka suka karɓi jikin ta tayi kyau sosai, Amma tunanin da yake yaƙi barin sa ya kalleta sosai.
Ya shirya tsaf ze fita Mufeeda ta bishi
Cikin sanyi jiki tace
"Allah ya kiyaye hanya, Amma gaba ɗaya inajin babu daɗi da yanayin da kake yau, ban sani ba ko be kamata inji damuwar taka ba, Amma idan ni nayi maka laifin kayi haƙuri dan Allah"
Bece mata komai ba ya fice.
Gaba É—aya Mufeeda haka ta wuni babu daÉ—i, ta shirya masa abubuwa da dama yau amma taga kaman baya cikin farin ciki, haka ta dake ta ci gaba da abunda ta shirya masa.
Æangaren Ammar ma yana tunanin wani irin Abu Mufeeda zata yi haka a bayan idon sa, wani sashe na zuciyar sa na Æ™ara yadda da matar sa akan babu wani abu da zata iya aikatawa na rashin gaskiya a bayan idon sa, a zaman da suka yi ya yadda da amanar ta.
Da daddare ya dawo gida a matuƙar gajiye, tunda ga falo yaga ta sauya tsarin falon, ta canza gurin zaman kujerun, ko ina se ƙamshi yake a gidan.
Fitowa tayi daga É—akin ta tayi simple make up, yanzu ma English wears ne a jikin ta, murmushi tayi masa tace
"Birthday man sannu da zuwa, shine ka fita ka daɗe ko? Ko ka leƙo gida ai shikenan, zomu je ɗakina am having a surprise for you, na shiryawa wannan ranar sosai fa"
A ɗan hasale yace "Ke ni ki ƙyaleni, bana son duk wannan abubuwan shirmen naki, ki rabu dani"
Gaba ɗaya jikin ta yayi sanyi ƙwalla ta cika idon ta tace
"Yi haƙuri, Allah ya baka haƙuri, ban san baka so ba, dana san baka so da ba zanyi ba Insha Allah bazan sake ba, Allah ya huci zuciyar ka, Allah yabaka haƙuri" tai maganar muryar ta na rawa hawaye na bin Fuskar ta.
Da sauri ta juya ta koma ɗakin ta ta rufe ƙofa.
Jikin Ammar ne kuma yayi sanyi da abunda yayi matan, a hankali ya nufi É—akin sa shima, yana buÉ—e É—akin yaga shima tayi masa ado, ga zane zane na heart da tayi me É—auke da sunan su a jiki da kalaman Soyayya dana fatan Alkhairi.
Ga balloons data hura ta ƙawata ɗakin se ƙamshi yake, gefe ga cake me fari da pink ta saka HAPPY BIRTHDAY HUBBY, ga lemuka da alawoyi data shirya, tausayin ta ne ya kama shi, besan adadin lokacin da tayi tana wannan shirin ba, be san adadin kuɗin da ta kashe akai ba dan kawai ta sashi farinciki, amma lokaci ɗaya ya Gwale ta.
Rage kayan jikin sa yayi ya shiga yai wanka yana ƙara kallon ɗakin yadda yai matukar kyau, fitowa yayi ya nufi ɗakin ta.
Yana zuwa yaga ta cire kayan adon da tayi, ta zauna a tsakiyar gado idon ta sharkaf da Hawaye ta hargitse gashin kanta tana kuka.
Ƙarasowa yayi ya kalle ta yace
"Taso muje a bani cake É—in"
ÆŠagowa tayi tana kallon sa hawaye na cigaba da bin idon ta,
"Taho mana"
yai maganar yana ƙara kallon ta, a hankali ta matsa inda yake zata sakko daga kan gadon, tausayin tane ya ƙara kama shi, bata iya fushi da shi, banda lokacin da tayi fushi harta fasa masa waya, bata iya fushi dashi ko tayi ma ita ke fara sakkowa ta bashi haƙuri.
Kafin ta sakko daga kan gadon yasa hannu ya É—auke ta, kamar wata 'yar yarinya kuwa ta kwanta tai lamo a jikin sa.
ÆŠakin sa ya nufa da ita, ya ajiye ta a bakin gado ya kalleta yace
"waye ya koya miki zane ne?"
"bakowa kawai iyawa nayi" jinjina kai yayi, kayan snacks ta gabatar masa, ai kuwa Ammar yaci sosai, shi irin wannan abubuwan basu dameshi ba shi dai kawai yaci Abinci ya dena jin Yunwa, wani abunma zama da Mufeeda yasa shi iya cin sa.
Ta yanka cake ɗin nan takai bakin sa, buɗewa yayi tasa masa, tunda Ammar yake be taɓa cin cake ɗin birthday ba, jin cream ɗin nan yayi har kansa dan daɗi.
"A ina kika siyo cake É—in nan?"
"Ni nayi fa"
"A'a gayamin gaskiya dai"
Taso ta tsokane shi tace santi yake, amma ta tuna ze iya dena ci in tace haka dan haka ta ƙyaleshi, gaba ɗaya Ammar ya manta da abunda yake damun sa kuma yaji daɗin abunda ta shirya masa sosai, Amma kunsan halin mutumin bazece ya yaba ba.
Seda suka gama ciye ciyen su, Sannan Ammar ya nemi gurin kwanciya, har zata tafi É—akin ta, ta fasa ta dawo ta hau kan gadon tace
"Yaya Ammar har yanzu baka gayamin laifin da nayi maka ba yau, gaba É—aya yau haka na wuni raina babu daÉ—i ka gayamin dan Allah"
Juyowa yayi ya zuba mata ido ba tare da yace komai ba.
"Kayi Magana mana, kabarni a cikin damuwa fa"
Maimakon yace wani abu sema janyo ta da yayi jikin sa yace
"meyasa kika ɓata gyaran gashin da kika yi?"
"Ai cewa kayi baka so"
"Ni nace bana so? Bance bana so ba"
A hankali Ammar ya canza akalar hirar zuwa wani abu daban, tun tana jurewa harta fara kuka, A hankali ya ɗagota amma taƙi kallon sa, miƙewa yayi yaje yai wanka ya dawo yai kwanciyar sa a gefen ta, bata da zaɓi itama ta shiga banɗakin sa tai wankan, maimakon ta tafi ɗakin ta, seta haye gadon sa tai kwanciyar ta, seda ya tabbatar tayi bacci sannan ya juyo ya ƙara rungume ta a jikin sa yana fatan Allah yasa message ɗin da ake turo masa ƙarya ne.
Da Asuba da ya dawo daga salla seya kwanta a falo, Mufeeda kuwa da tayi sallar Asuba kwanciyar ta ta kuma yi a gadon sa tana bacci.
Seda gari yayi haske sosai sannan ta farka, tashi tayi ta fito ta tarar da shi yana bacci akan carfet, zuwa tayi kusa dashi ta kwanta tana ƙarewa fuskarsa kallo, A hankali ya buɗe idon sa ya kalle ta ya mayar ya lumshe.
A hankali ta ɗora hannun ta a ƙirjinsa dai dai inda zuciyar sa ke bugawa tace "Yallaɓai ina da saƙo ka bawa zuciyar ka"
BuÉ—e ido yai yana kallon ta
Mufeeda cikin salon muryar tausayi ko wanda ya karaya da wani abu ttace "ka gaya mata akwai zuciyar da take matuƙar begen ta ba dare ba rana, Akwai zuciyar da ke son kasancewa da ita har ƙarshen rayuwar ta, ta zama me yiwa wannan zuciya da take son ta afuwa, idan tayi ba dai dai ba tayi mata uzuri kasancewar wannan zuciya me rauni ce, kuma 'yar jaririyar zuciya ce dake girma yanzu, zuciya ce dake girma da soyayya ba zata iya ɗaukar tsatstsauran hukunci daga gurin ta ba, ina fatan saƙon zuciya ta ze isa ga zuciyar Abun so na, zuciya ta bata ganin kowa se kai, ban taɓa son wani ba in bakai ba akanka na fara, kuma daga kai na gama, ina roƙon ka kamar yadda kake min kallon yarinya Koma ince Jaririya ina fatan idan na maka laifi ka duba ƙanƙanta ta kamin hukuncin da Jaririyar zuciya ta zata iya ɗauka, ina fatan saƙona ze isa ga zuciyar ka kai tsaye nagode Hubby na" ta sumbaci fuskarsa ta miƙe.
Bayan ta yabi da kallo harta shige kitchen yana sake tunani daban daban a ransa.
**************
Wajen ƙarfe goma na dare dan har sun fara shirin kwanciya, dan Mufeeda har ta masa Sallama ta tafi ɗakin ta, aka fara buga musu gate, Ammar ne yaje buɗe ga mamakin sa yaga Faruk ne da yarinyar sa, se kuma Fa'iza abun ya bashi mamaki matuƙa ganin Faruk da Fa'iza a tare a wannan lokacin haka, amma ya ɓoye mamakin sa yace "kune kuke tafe yanzu?"
Yai musu iso har cikin gidan, zuwa falo
Faruk yace "Ai gani nai rashin kirkin nawa yayi yawa, dan haka naje har gida nace Fa'iza ta rakoni gidan ka dai inga Amarya har gida kafin in kawo Madam"