Sashe 49
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ya zaki ce ina cutarta ni bance ta cutar dani ba da Aure na take kula maza a waje"
"Karka ƙara cewa tana kula wasu mazan a waje tunda baka gani ba, baka da tabbas ashe duk Nasihar da Baba suka dinga yi maka lokacin da aka baka Auren Yarinyar nan da wadda nayi maka duk baka ɗauka ba, iyayen ta sun baka ita a mutunce da girmamawa amma kayi haka, kai a marrar nan ka samu Yarinyar da harta san tayi laifi ta baka haƙuri, amma kake wulaƙan ta ta, niba abunda zan iyayi maka akai, kaje ka samu Su Baba kayi musu bayani aje gidan su a duba, in tana can in taga zata dawo shikenan, ko dayake ma ai babu Aure a tsakanin ku tunda har zargi ya shiga ciki "
Zaro ido Ammar yayi yace " Ubanwa yace miki zargin ta nake, ko duk duniya zasu taru akan Zata aikata zina zan ƙarya ta kowaye, Yanzun ma na yadda ne saboda da kunne na na ɗaga wayar naji, kuma ita mace ce me son kulawa da soyayya sosai "
Yaya Maryam tace "Eh Mace ce me son kulawa da Soyayya, kai kuma bazaka iya nuna mata soyayya da kulawa ba kana ganin yin hakan kaman ka faɗo ne ko? Shiyasa ka yadda za tayi Soyayya da wani a waje, ai in gaya maka kaɗan da aikin mace idan har zatayi abu ba zaka yaba ba tayi ta burge wasu a waje, ai ita mace tana so a yaba mata kai kam nasan bazaka iya ba"
Ammar ya É—an kalleta ya É—auke kai,
"Nasan halinka ai Ammar, Yarinyar nan tana sonka bekamata kayi mata haka ba, da kaji wani ya kira ta bincike ya kamata kayi, Idan tana chatting ne a social media akwai sakarkarun maza marasa tarbiyya da suke bin lambar mutane su dinga kira, zata iya yuwuwa a cikin su ne, kuma me ya kaika É—aga mata waya? Da har kaji wannan maganar"
Cikin damuwa Ammar yace "Amma fa har message ake turomin akan in saka ido akan ta tana aikata rashin gaskiya a bayan idona da ban yadda ba amma abun ya fara É—auremin kai"
"Taɓɗijan to waye yake turomaka?"
"Nima ban sani ba, anyi hiding É—in lamabar"
"to tabbas me turomaka saƙon yana da Alaƙa da wanda ya kira ta a waya in ba haka ba ya akayi yasan tana aikata rashin gaskiyar? Kuma me yasa ya ɓoye lamba, ai kamata yayi ku zauna ku tattauna, ko ka yi bincike a ɓoye ka gane gaskiya kafin ka yanke mata hukunci "
Shiru Ammar yayi ya dafe kai yana tuna lokacin da Mufeeda ta biyo shi tana riƙe rigar sa tana kuka, yadda bata son ɓacin ransa sam, gaba ɗaya tausayin ta da nadama ya kama shi, Jiki a sanyaye yace
"Yanzu meye abunyi? "
"Abunyi kaje ka samu Abba kuyi maganar"
"Haba Yaya Maryam, idan har zan gayawa Abba meye amfanin zuwa gurin ki, Abba bazemin da daɗi ba, inason sanin takamaimai tana ina, na kirata yafi a ƙirga bata ɗauka ba, ƙarshe ma ta kashe layin ta gaba ɗaya"
"Koma menene dai kai ka janyo shi, dan ka kaita bango ne shiyasa ta tafi ta bar maka gidan ka, da alama ka daÉ—e kana muzguna mata, yanzu abunyi shine kaje gida zuwa gobe in Allah ya kaimu se asan yadda za'ayi"
Zare ido yayi yace "har zuwa gobe? Ban san inda ta tafi ba kuma bansan a wani hali take ba?"
"to seka fita kaje ka neme ta ai, kasan da haka amma kai mata wulaƙanci"
Jiki a sanyaye Ammar ya tashi ya koma gida, gaba ɗaya ya shiga damuwa tare da tunanin ina ta tafi haka? Abunda zesa Mufeeda taƙi ɗaga wayarsa ba ƙaramin abu bane, lallai indai tana cikin ƙoshin lafiya ba ƙaramin fushi take da shi ba, ɗakin ta ya kuma komawa yana dubawa kota dawo amma still bata nan, Ammar ya kasa zaune ya kasa tsaye.
Ya shiga tunanin idan Mufeeda wani gurin tayi da wani ido ze kalli iyayen ta, Abun duniya ya ishe shi gidan yayi masa faɗi, daren ranar sam bacci ya ƙauracewa idon sa, yayi zurfi a tunanin ina ze gano 'yar mutane.
Æangaren Mufeeda ma tunanin sa take yi, tasan hankalin sa yana tashe besan inda ta tafi ba, A ranata tace "Allah yasa kar yaje gida nemana bana son su Mama su san abunda ke faruwa"
Ji take kaman ta kunna wayar ta ta kira shi saboda tasan ze shiga tashin hankali rashin ganin ta, amma da ta tuno kalmar mayaudariya munafuka da ya kira ta da su se wasu zafafan Hawaye su zubo mata, ƙoƙari ta dinga yi ta manta da shi amma abu ya faskara, dan wani tausayin sa ne ya mamaye zuciyar ta dan tasan tabbas Ammar baze iya bacci ba yau.
Wasa2 kwana uku babu Mufeeda babu labarin ta, hankalin Ammar ya gama tashi, ko Abinci baya iya ci, yaje gidan su Mufeeda ya fake da gaishe su yaje yi Amma ya tarar bata nan, kuma bega wata alama a fuskar Mama da yake nuna wani abu ba, Ammar ba bacci babu cin Abincin kirki saboda tunani da fargaba, Yayi niyyar ya nemi Aminu koda shawarar daze bashi se kuma ya fasa, sam Ammar ya rasa kwanciyar hankali.
Yaya Maryam ma nata ƙoƙarin trying lambar Mufeeda amma taƙi shiga.
Har yanzu Mufeeda tana fama da damuwa ga shi bata da lafiya har yanzu, Mijin Yaya Amina yace idan ya dawo zasu tafi Asibiti.
Yanzu ma Yaya Amina ta saka Mufeeda a gaba akan tayi breakfast, gaba ɗaya mufeeda bata jin daɗin Abincin ta riƙe cokali tayi shiru tana zancen zuci, Yaya Amina tace
"Kinga Auta karki wa kanki illa da wannan tunanin ki maida kai kici Abinci kafin Ya dawo mu tafi Asibiti"
Mufeeda ta ajiye cokalin ta kalli Yaya Amina tace "Yaya Amina wallahi tunanin Mijina nake, besan inda nake ba hankalinsa ze tashi sosai, kuma ma ko yaci Abinci yanzu? Nasan ba lallai yana cikin nutsuwar da zeci Abinci ba"
"Sannu Tattabara uwar ƙauna, ko ince sarkin Aure, ke ba kiga halin da kike ciki ba saboda shi, amma tausayin sa kike ji baki da zuciya"
"Ba rashin zuciya bane Yaya Amina, abun da Yaya Ammar yayi shi duk wani Namiji da yake son matarsa zeyi, tun É—azu na kunna wayata kiran sa yake shigowa, Zuciya ta na rayamin in É—aga nasan zuwa yanzu yana cikin nadama"
A fusace Amina tace "Wallahi kika ɗaga wayarsa sena gayawa Mama abunda ke faruwa"
Wayar Mufeeda ta fara ringing, tana dubawa taga Anty Maryam ce, ta kalli yaya Amina tace
"Yaya, Anty Maryam ce Yayar Ammar"
Yaya Amina tace "bani wayar nan" ta karɓi wayar tare da yin sallama, suka gaisa da Anty Maryam.
Anty Maryam tace "dan Allah Mufeeda nake nema"
"Ba ita bace Yayar tace"
"Masha Allah, gurin ki ta taho kenan?"
"Eh muna tare, nan ta taho"
"Dan Allah ki temaka ki gayamin inda gidan ki yake zanzo muyi magana"
Yaya Amina tayi mata kwatancen gidan ta, befi awa ɗaya da rabi ba sega Anty Maryam, Yaya Amina tayi mata kyakywar tarba, Kallo ɗaya Anty Maryam tayi wa Mufeeda taga ta rame sosai kuma kana ganin ta kasan bata da lafiya, Anty Maryam tacce "Mufeeda ran da naje gidanki ba yadda banba ki gayamin in akwai matsala amma kika ƙi"
Yaya Amina tace "Ai ba zata gaya miki ba, yanzu ma dan taga ta kusa mutuwa ne yasa ta zo gidana, dan lokacin da tazo ko numfashi bata iyayi"
Nan Yaya Amina ta zauna ta gayawa Anty Maryam komai kamar Yadda Mufeeda ta gaya mata, kallon jinjina take wa Mufeeda tace
"Sannu Mufeeda Allah ya baki ladan biyayya da haƙuri, amma maganar gaskiya koni bazan iya wannan haƙurin da kikayi ba, Amma ku ƙyaleni dashi ze gane kuskuren sa, yanzu Alfarma ɗaya nake so kiyi min, ki bani ita in tafi da ita, zan kaita Asibitin ta zauna a gurina na wani ɗan lokaci, bana son wani daga iyayen mu yasan hamin da ake ciki, amma tabbas zan koya masa hankali "
Da farko Yaya Amina bata yadda ba, se daga baya ganin Yadda Anty Maryam wadda ta girmesu gaba É—aya keta magiya yasa ta Amince, ita dai Mufeeda bata da ta cewa, Yaya Amina ta bawa Mufeeda wasu daga kayan sawarta da yake ba tazo da kaya ba sena jikin ta tabi Anty Maryam gidan ta.
Ammar kam seya raba dare a falo a zaune, idan yayi salla kuwa bashi da Addu'a se Allah ya bayyana masa Matarsa yasa tana lafiya, idan ya zauna a falon nan ya dinga tuna yadda take tattalin sa tana kula dashi, be taɓa tunanin ya shaƙu da Mufeeda haka ba se yanzu, ji yake duniyar tayi masa zafi rashin ganin giftawar ta a gidan.
Kwanan Mufeeda biyu a gidan Anty Maryam kulawa take bata kamar ƙanwarta da suke ciki ɗaya, tana kula da ita, ita da mijin ta suka kai Mufeeda Asibiti, aka bata magunguna aka tabbatar musu da jinin ta ya hau, ta rage damuwa ga ulcer da tayi mata mugun kamu saboda rashin cin Abinci, Mijin Anty Maryam se mita yake yace
"Ummu Iman wannan ƙanin naki Halinsa se shi, Ya samu yarinya me haƙuri amma ze wasa da damar sa yana nema ya kashe musu 'ya"
Anty Maryam tace "ƙyaleshi zega tsiya sena koya masa hankali"
Da sassafe Ammar ya shirya ya tafi gidan Anty Maryam, gaba É—aya yana cikin kiÉ—ima yace
"Maryam na rasa inda zan saka zuciya ta rashin ganin Mufeeda, wallahi ina cikin tashin hankali"
"Illar Fushi kenan da rashin bincike, seka kiyaye gaba"
"Maryam yanzu ba lokacin wannan bane, na yanke shawarar inje in gayawa Abba, tun kafin lokaci ya ƙure in karɓi duk hukuncin daze min"
Har ya juya ze tafi Anty Maryam tace "badan halinka ba na gano inda take"
Da sauri ya juyo a gigice yaceÂ
"dan Allah tana ina?"
"Babu ruwan ka da inda take, Amma na ganta har munyi magana"
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhamdilillah dan Allah ki bar batun wasa tana ina?"
"Sanin inda take bashi da Amfani a gurin ka, dan tace min ita da gidan ka har Abada ba zata koma ba"