← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 64

Sashe 59

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammar ma bayan ta ya biyo ya kunna babur ɗinsa suka tafi, shi kansa ransa a ɓace yake, yana jinjina wulaƙanci da rashin mutunci irin na Jabir, sesa Mufeeda tayi kuka saboda tausayin Saima.

Haka suka tafi kamar kurame, a daidai danja 'yan sanda suka zo suka kewaye babur É—in su Mufeeda, suka sa hannu suka kashe babur É—in suka zare key, É—aya ya kalle shi yace
"Ammar ko?"
Ammar yace  "Eh nine Yallaɓai amma me nayi?"

"dalla rufewa mutane baki, kalle ka kamar mutumin kirki ashe ma cuci ne, ana haÉ—a kai da kai anyiwa Fasinja fashi fito yai dubunka ta cika"

"Kai Yaya Ammar É—in? Wallahi bashi bane ba, ba yaya Ammar É—ina bane, wallahi bashi bane baze aikata haka ba"

Shikam gaba ɗaya kan Ammar ya kulle, yama rasa meze ce, shi dai ba da wani suke exchanging ɗin babur ɗinba, balle ace shine shi a iya sanin sa ko fitinar nan ta ƙuruciya beyi ba balle yanzu da girman sa.

"zaka fito ko sena ɓaroka munafuki"

Ammar jiki a sanyaye ya fito daga babur É—in, yasa hannu a aljihunsa ya É—akko kuÉ—aÉ—en dake ciki ya kalli Mufeeda yace
"Mufeeda kinga dare yayi, karɓi kuɗin nan maza ki tafi gida, Insha Allah da safe zan dawo, tunda nidai nasan ban aikata laifin komai ba"

Mufeeda ta fashe da kuka ta riƙe rigar Ammar tace  "Wallahi sedai a haɗa dani, ni Ammar ɗina mutumin kirki ne Officer dan Allah, wallahi bashi ake nufi ba"

"Yi haƙuri 'yan mata maza ki tafi gida, yana division ɗin gangare zamu tuhume shi"

"Maza ki tafi gida dare yanayi, sannan karki sanar da kowa se zuwa gobe in Allah ya kaimu inga yadda hali zeyi"

Aka saka Ammar a motar ' yan sanda, suka tuƙa Napep ɗinsa suka tafi da shi.

Kai masha Allah, ban san haka kuke son book ɗin nan kuke following ɗinsa ba, kwana biyu da ban posting ba nasha kira a waya, ina godiya ta musamman Allah ya bar ƙauna, kar' amanta in an karanta ayimin share dan Allah ba dan halina ba
🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏

Wanda sukamin magana akan voting na gasar dana shiga, se an kammala gasar ne za'a bada link É—in da fans zasu shiga suyi mana voting, nagode da kulawar ku

Domin gyara, sharhi, ko shawara, ƙofa ta a buɗe take
Ayshercool
07063065680..✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨

( *Sai Mata* )

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

ELEGANT ONLINE WRITER'S

NOT EDITED

                         Page 29

Gaba É—aya jikin Mufeeda rawa yake, ji take tamakar a mafarki, wace irin masifa ce wannan? Daga wannan se Wancan
"Ya Allah ka fitarmin da mijina"
Haka ta tari Abun hawa ta tafi gida, unguwarsu baƙi ƙirin saboda duhu, har ƙofar gidanta me Napep ya kai ta.

Safa da  Marwa Mufeeda ta dinga yi a ɗaki ta rasa me ya kamata tayi, se sharce hawaye take tana tunanin ya Ammar ze iya kwana a ceil, waye yai masa wannan sharri haka?
Tayi tunanin ko ta kira Baba a waya ta gaya masa, seta tuna Ammar yace karta gayawa kowa.
babu Alamar Bacci a tattare da Mufeeda, tai alwala dinga salla tana kai kukan ta ga Allah, har dare ya raba kuka Mufeeda take sosai ga tsoro da take ji.

Tana zaune a tsakar ɗaki ta dunƙule a guri ɗaya tana kuka, ji tayi ana buga gate ɗin gidan, da sauri ta miƙe ta koma kan Gado tana rarraba ido, cigaba da bugun aka yi, wata zuciyar tace idan kuma Ammar nefa ya dawo, da sauri ta sakko daga kan gadon ta buɗe falon ta fito tsakar gida cikin sanɗa.

Buga ƙofar aka cigaba dayi, cikin sanɗa take tahowa ta tsakanin gate da garu Mufeeda ta leƙa yanayin inuwar wanda yake tsayen ba tayi kama data Ammar ba.

Da gudu ta koma ta rufe falon ta, ta koma ɗaki ta kulle ƙofa, ta hau gadon ta ta dinga Karanto Addu'oin da suka zo bakin ta.

Yadda Mufeeda taga rana haka taga dare, cikin tashin hankali ta wayi gari.

A gurguje tai wanka ta shirya, ta girka Abinci ta rufe gida ta fice.

Station ɗin da'aka kai Ammar ta tafi, tun ƙarfe takwas na Safe ta tafi, taita Jira a station ɗin, se ƙarfe Goma aka fito da Ammar daga shi se dogon wando da vest, da alama an dake shi ma, sedai cikin Jarumta yai mata murmushi yace

"meyasa kikayi Sammako haka?"

Kuka ta fashe da shi Sosai, ta kalli ɗan sandan tace  "Yallaɓai wai baku gama binciken ba? Dan Allah ku sake shi wallahi Yaya Ammar mutumin kirki ne"

ÆŠan sandan yace "Ke kije gida kizo da wani Babba daga gidan ku, ko baban ku ko wani babba, 'yar mitsitsiya dake ba dake za muyi magana ba"

Mufeeda tace "haba Yallaɓai cewa kukayi zakuyi bincike ku sake shi, wallahi mijina mutumin kirki ne"

Zare ido ɗan sandan yayi yace  "Miji kuma? Ke yanzu wannan ne mijin ki, kai Ashe banda tuhumar da muke maka, akwai buƙatar Human right su bincike ka, wannan ai child Abuse ne Wannan Yarinyar ce matarka?"

Banza Ammar yayi masa ya kalli Mufeeda yace
"Ina fatan kinyi bacci jiya, dan nasan halinki"

"Wallahi yaya Ammar banyi bacci ba, aka dinga bugamin gida jiya a tsorace na kwana ga hankalina yana kanka" tai ƙarasa maganar tana kuka.

"ki kwantar da hankalin ki, ki kira Aminu a waya ki gaya masa ina nan"

"Yaya Ammar, Har yanzu basu gama binciken ba? nasan ba zaka aikata haka ba"

"Mufeeda ni kaina na kasa gane kan lamarin nan, har yanzu banga fasinjojin da ake zargin nayiwa fashin ba, sun tirsasani in amsa laifina naƙi, Amma ki kira Aminu"

"Yaya Ammar, ba zamu gayawa su Baba ba"

Girgiza mata kai yayi yace  "ba yanzu ba, kina gaya musu hankalin su ze tashi, ki bari mu ga yadda hali zeyi"

Haka Mufeeda ta koma harabar station É—in ta kira Aminu ta sanar da shi halin da'ake ciki, Aminu ya kaÉ—u sosai da jin Abunda Mufeeda ta gaya masa

Yace "ki kwantar da hankalin ki Mufeeda, gani nan zuwa Insha Allah, Amma abun da mamaki gaskiya"

Befi mintuna Arba'in ba sega Aminu yazo station É—in.

Ya shiga ya samu officer on duty, suka gaisa Aminu yace
"Yallaɓai nazo ne akan case ɗin ɗan uwana da aka kama"

Ɗan sandan yace  "Eh mun kama shine saboda muna zarginsa da haɗa kai da 'yan iska suka yi wa fasinjansa fashin waya da kuɗaɗen sa, munyi2 yaƙi ya amsa laifin sa"

Aminu yace "Amma Yallaɓai ai se mutum ya aikata laifi sannan ze amsa yayi, sannan wanda kuke zargin nan da iyalinsa da mutuncin sa beyi kama da wanda ze aikata wannan laifin ba kag.....

"Kai zaka koyamin yadda zanyi aikina ne? Su mutanen banza a fuska ake gane su?" É—an sandan ya katse shi

Aminu yace  "A'a Allah yabaka haƙuri, yanzu meye abunyi? Ina so abani belin sa"

"zamu bada belinsa amma zaku biya yaron da akayiwa Fashi kayan sa, yaron ɗan makaranta ne yana school yanzu amma in anjima zezo, in bahaka ba mu miƙa ku kotu"

"Amma yallaɓai abunda ba'a tabbatar ba, har a yanke masa wannan hukunci haka"

"kaga idan baku shirya karɓar belinsa ba, zamu tura ku kotu a satin nan kuma kasan hukuncin fashi da makami za'a yanke masa"

Aminu yace  "Shikenan ina jinka meye abunda za'a biya yaron?"

"Naira dubu É—ari da goma ne abunda za'a biya"

Da sauri Mufeeda ta ɗago kai ta kalli ɗan sandan, idon ɗan sandan kawai ze nuna maka rashin imani, yanzu ace da ire iren wannan bara gurbin  'yan sandan a cikin Al' ummar mu ta ina za'a zauna lafiya.

Mufeeda tace "Yanzu kai ko tsoron Allah ba kaji ba, dubu ɗari fa saboda mugunta, wallahi se Allah ya saka mana, duk wanda yake da hannu a cikin yiwa mijina sharri se Allah ya wulaƙanta shi, idan da haɗin bakin ku Insha Allah sekun rasa aikin"

"Ke ni kike gayawa haka? A gaban hukuma fa kike"

"Hukumar banza da Wofi, Allah ya Tsinewa hukumar indai irin wannan ce, Azzalumai kawai"

"Ke idan baki wasa ba sena saki a ceil na koya miki hankali, mutuniyar Banza kawai"

Aminu na ƙoƙarin rarrashin ɗan sanda, amma Mufeeda ta hasala ƙarshe tace

"Kai ka isa kasani a ceil, wallahi ka sani a ceil seka rasa aikin ka har gaban Abada, indai Alfarma ce nima inada wanda zasu tsayamin a fitar da mijina, sannan a hukunta ku"

Da ƙyar Aminu yasa Mufeeda tayi shiru yasa ta tafi gida, dan indai tana nan ƙarshen ta Ammar baze fita a yau ba, seda aka kai ruwa rana Aminu yaita fama sannan aka bari Aminu yaga Ammar, Aminu ya gaya masa abunda suka ce, Ammar yace

"shikenan, Mufeeda ta É—au wayata tayi maka transfer É—in dubu tamanin da biyar, su kenan a Account É—ina, dama ina tara kuÉ—inne saboda in fara yiwa Mufeeda siyayyar haihuwa, ka ciro ka basu in bar gurin nan, na barwa Allah"

Mufeeda na Adaidaita sahu zata koma gida tana ta kuka a Napep É—in, Aminu ya kira ta ya sanar da ita abunda Ammar yace, tace
"to bari in ƙarasa gidan, se in turo maka"

A titi ta sauka ta biya me Napep kuɗin sa, ta fara tafiya sedai tana zuwa bakin layin taci karo da motar Alhaji Idris yana zaune akan motar, yana ganin ta ya sakko da Ƙaton cikin sa yana wangale mata baki yace
" 'yan matan daga ina haka? Naga kamar kina kuka, da safe naga fitar ki, shine na zauna ina jiran dawowarki"
Chapter 59 · 0% Book details