← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 64

Sashe 7

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan ta kuma zayyane masa yadda ya kawota gida da zuwa bikin Amina da yayi.
"niba abunda yamin ko ya gayamin, yana da kirki ne, kuma É—an gayu ne, ai ka ganshi ranar ko?"

Baba ya jinjina kai yace "hakane É—aan gayu ne kam, yanzu idan kinyi candy aure zakiyi?"

"Baba zanyi candy kafin in cika shekaru goma sha bakwai ne, sefa na jira na shekara sha takwas zan shiga University, kuma gashi wasu suyita zagin matan da suke zuwa jami'a, ko kuma su dinga musu kallon marasa tarbiyya, Amma idan nai Aure sannan nayi karatun ai se anfi ganina da mutunci, kuma fa badan Ammar ina sonshi ba bazan ce zanyi Aure yanzu ba, kullum se naita tunanin sa nafi son in dinga ganin sa kullum"

Jinjina kai Baba ya dingayi sannan yace
" 'yar ƙarama me tunanin manya, maganar ki gaskiya ne Auta na, indai ze barki kiyi karatun ai babu damuwa, dama ita soyayya ai gamon jini ce, wani halinsa ne kawai zesa kaji kana sonsa, in dai yayi miki kuma nai bincike akan halayen sa na yadda da halayen sa babu damuwa kije ki gaya masa ina son ganin sa"

"to Baba nagode da fahimta ta da kayi sannan... "

Shigowar Mama ce tasa ta yin shiru, Mama ta Harare ta.
Mufeeda tace "Baba zan dawo mu ƙarasa zancen mu"

"to shikenan Auta na"
Ta miƙe ta fice.

Ta koma É—akin ta tana ta farinciki, se kuma ta shiga zullumin me zata cewa Ammar wanda ze kai ga yazo yaga mahaifin ta har ya yadda da maganar auren su?.

"Taɓɗijan ga ƙoshi ga kwanan yunwa"

(Duk abun nan fa Oga Ammar bece yana son ta ba 🙄🙄🙄)

More Comments More typing. In ba comment zan aje littafin gaba É—aya

Domin sharhi, gyara ko kuma shawara
A tuntube ni akan wannan lambar
What's App
Ayshercool
07063065680
✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

                            Page 4

Juyi kawai Mufeeda take akan gado tana tunanin mafita, Amma ta kasa samawa kanta mafita, ji tayi kanta ya fara sarawa dan haka tai Adduoin ta na bacci ta rufe ido.

Maman Mufeeda ta kalli mahaifin Mufeeda tace

"Wai yanzu dagaske yarinyar nan zuwa tayi ta same ka akan maganar nan? Ban san lokacin da Mufeeda za tayi hankali ba, waya gaya mata zaman Aure aikin rago ne, guda nawa Mufeeda take da har zata tun kare ka da batun ita Aure take so"

Mahaifin Mufeeda yace
"Kwantar da hankalin ki maman yara, Abun ai duk bana zafi bane, ki sani tarbiyar da kika yiwa su Murja a zamanin su idan har kika ce irin ta zakiyi wa Mufeeda a wannan zamanin da muke ciki zata iya bijirewa"

"Hakane dan taurin kanta yayi yawa, halinta ya fita daban dana 'yan uwan ta kaman bani na haife ta ba, ace yarinya ba kunya sam"

Yai murmushi yace
"Karki manta a tarbiyar da muka yi wa yaran mu babu kunya tsakanin mu dasu, mun ɗora su akan kome ke damunsu game da rayuwar su mu zamana mune mutane na farko da zamu fara sani, karki manta kowace yarinya kafin in Aurar da ita babu wadda ban san date ɗin da take Al'ada ba, ni nake siya na basu abunda za suyi amfani da shi lokacin Al'ada, hatta ƙanan kaya inner wears ɗin su in sun lalace kai tsaye suke tunkura ta su gayamin haƙƙi nane inyi musu, kuma babu inda Addini yace hakan haramci ne, idan haka ne wace kunya kike tunani tsakanina da su? kin fi kowa sanin ban yadda da kunya tsakani na da 'ya' ya naba, basu da sama damu jansu a jiki da muka yi ne ya sa suke iya bayyana mana matsalolin su, me kike tunani idan har da kika gwale Mufeeda nima Gwale ta nayi? Tana kan ƙanan shekarun ta na Adolescent period komai ze iya faruwa musamman idan tana ta'ammali da gurɓatattun ƙawaye, inda na godewa Allah Mufeeda rawar kan ne kawai da surutu amma tana kula da kanta"
ÆŠan lumshe ido Mama tayi tace

"Hakane Amma menene mafita? Tayi ƙanƙanta da Aure"

"Ke kike ganin tayi ƙanƙanta, a hirar da mukayi da ita na fuskanci cewar Ita ba wai Auren ya dame ta ba, tana ƙaunar yaron ne sosai, na bugi cikin ta inji ko wani ke zigata ko wani abun yaron yake mata take sonshi, kin santa bata rufemin komai, yadda na fuskanta Soyayya ce kawai, tana sonshi sosai kuma mafita ɗaya ce shine zan cewa yaron ya fito "

Da sauri Mama ta kalleshi tace
" haba shekarun ta nawa da za'a aurar da ita? Dr. kana kallon yadda nake fama da ita a cikin gidan nan ta yaya zata iya riƙe miji? Kuma karatun ta fa?"

"Sarat shekarunki goma sha huɗu nikuma ashirin da biyu muka yi aure, muna tare ki kayi karatun sakandire har zuwa diploma, ko kin manta? yadda kika iya riƙeni itama zata iya"

"Dr. Yanzu fa ka gama faɗin zamanin mu na da, da yanzu ba ɗaya ba, mazan yanzu ga rashin tabbas da rashin haƙuri ta yaya mufeeda na zata iya zama da miji yarinya ce ƙarama fa"

"Calm down my wife, muyi mata Addu'a, Soyayya ba ruwan ta da shekaru kin san a baya, ko zancen Aure bata so dan baya gabanta, da kanta tace tunda ni ban kai ga zama professor ba ita zata zama, tana son karatu matuƙa, Amma tunda tace yanzu ta fasa. kuma ta bani gamsassun hujjojin ta na son yin aure kafin karatu.
Kuma da yaro ƙaramine tace tana so nasan wannan shashanci ne, Amma naga yaron kaman yana da shekaru ba yaro ne ƙarami ba, muyi mata Addu Allah ya sanya musu Alkhairi "

Haka Baba ya ci gaba da rarrashin ta, yana kuma nuna mata illar rashin amincewa da bukatar 'yar autar tasu.

*****************

Ammar ya sai Sabuwar waya, ya maida simcard É—in sa kai, yayi setting WhatsApp É—in sa da sauran Abubuwansa sannan ya ajiye wayar ya kwanta.

Cikin Bacci Mufeeda ta farka da zazzafan zazzaɓi da ciwon kai, yamutsa fuska tayi ta juya da nufin ta ci gaba da bacci amma abu ya gagara, ta ture abun rufarta ta tafi banɗaki tayi wanka ta dawo ta kuma kwanciya tana tunanin zazzaɓin ze sauka.

Sosai zazzaɓin ke kuma hawan ta se rawar sanyi take yi, bata son taje ta ɗagawa iyayen ta hankali a daren nan.
"ko wayar Baba zan kirane?" ta faÉ—a a fili taita tunani ta rasa menene mafita.
Kasa komawa bacci tayi ta ɗakko wayarta ta ga ƙarfe sha biyu saura na dare.

Ta rasa lambar wa zata kira, data ɗin ta ta buɗe saƙonni suka dinga shigowa, ta shiga what's App ɗin ta tana duba contact, ba zato ba tsammani taga lambar Yaya Ammar ɗina tayi appearing a contact ɗin ta.
Da sauri ta miƙe zaune dukda zafin da jikin ta ya ɗauka, ta shiga kan hoton dp ɗinsa, tabbas shine hoton sa ne a tsaye a gaban Napep ɗinsa hannun sa ɗauke da makulli da handkerchief kalar kayan jikin sa, ya ɗanyi murmushi ba ƙaramin kyau yayi wa mufeeda ba, zooming ɗin hoton tayi tana ajiyar zuciya
"You are handsome my man" ta furta a fili tana kuma ƙare masa kallo, message ta tura masa

"Asslam Alaikum warahmatullah, Yaya Ammar dama kana what's App amma baka kulani ba?"

Ta ci gaba da kallon hoton sa, sannan tayi murmushi ta ajiye wayar ta kwanta, Amma bacci yaƙi zuwa tamkar jira zazzaɓin yake ta kwanta, kanta ya dinga sarawa ga cikin ta ya ƙulle yana ciwo, Nan ta dinga shrara kuka ita kaɗai a ɗaki, se juyi take ga Amai yana taso mata.

Wayar ta ta kuma É—akkowa da nufin ta kira Mama a waya, amma tana cire key É—in kan wayar ta hoton Dp É—in Ammar ne bata fita ba.
Wani saƙon ta tura masa, Tana gama tura saƙon ta saki wayar ta faɗo ƙasa daga kan gadon daga nan bata ƙara sanin inda kanta yake ba.

*****************

Alarm ɗin Ammar ya buga ƙarfe uku na dare, ya miƙe ya shiga banɗaki yayi alwala ya zo ya tada salla, yai nafilolin sa ya ɗakko wayar sa ze karatun Al'qur'ani amma yaga data ɗin sa a buɗe messages suna ta shigowa.
Rufe data yayi ba tareda ya duba saƙonnin ba yai karatun sa be koma bacci se Da yayi sallar Asuba.

*************

Mufeeda kam se farkawa tayi ta ganta a gadon Asibiti an ɗaura mata ruwa, tana ganin haka ta fashe da kuka, Baba ya ƙaraso da sauri bakin gadon ta yana faɗin

"Sannu Auta na yi shiru kin gammu a kusa da ke, sannu ya jikin naki?"
Jinjina wa Baba kai tayi ba tare da tace komai ba, ta cigaba da kukan ta.

Mama tace
"Ke meye kuma na kukan kiyi mana shiru, idan mutum bashi da lafiya addu'a yake ba kuka ba, meye Amfanin kukan?"

Cikin kuka Mufeeda tace
"Na dauka na mutu ne fa"

Dariya Baba yayi yace  "A'a baki mutu ba, meyasa baki da lafiya baki gayawa kowa ba? seda Asuba Mamanki taje tashin ki ta ganki a ƙasa a sume a cikin amai, me yasa baki faɗa ba?"

Maimakon ta amsawa Baba tambayar sa sema fashewa da ta kuma yi da kuka tace "Baba ciki na da kaina ciwo suke min"

"Ya isa haka yi shiru, yanzu likita zezo ya duba ki"

Ammar ya bayan sallar asuba ya É—an koma bacci.
Chapter 7 · 0% Book details